Showing 171001 words to 174000 words out of 325849 words
bane ya mata yace "Uwa ko dai Hajia ce ta b'ata miki rai?" Kallonshi tayi da alamar tambaya a fuskarta, lura da hakan yasa yace "Eh mana, ita ce dai mai d'ab'iar b'atawa kowa."
Murmushi tayi tace "Ba komai." Tab'e baki yayi ya mik'o mata ledar yace "Ki bawa Amna wannan."
Har ya juya zai fita Zeituna tace "Ba zaka shiga kaga Ummy ba? Kamar tana cikin damuwa fa."
Yana juyowa ya kalleta da alamar damuwa da tashin hankali yace "Meya sameta? Wani abun ya faru ne?"
Girgiza mishi kai tayi hakan yasa ya mayar da akalarshi kan d'akin Ummy, yana ya tsaya bakin k'ofa, har ya d'aga hannu zai k'wank'wasa sai kuma ya tsaya, turawa kawai yayi ya shiga babu sallama sai dai babu kuzari a tare dashi, Ummy na fitowa daga ban d'aki ta wanko idonta ta ganshi tsaye, tunawa da cewa duk abubuwan nan da suka faru sanadinshi ne yasa Ummy jin haushi, aje k'aramin towel d'in hannunta tayi ta giftashi zata wuce ta bar d'akin, cikin taushin murya yace "Ummy me yake faruwa ne?"
A zafafe tace "Ban sani ba, koma meke faruwa ai kai ne sila, dan haka ka fita idona in rufe wallahi kafin na sab'a maka kaima."
A sukwane ta fice daga d'akin ta barshi tsaye, a kasalance ya juyo ya fita shima bai bi takan kowa ba, mai gadi na bud'e mishi k'ofa ya taka motar da k'arfi zai wuce, kamar an tsayar dashi kuma saiya taka birki da sauri wanda ya haddasa tashin k'ura a bayanshi, gidan dake manne da na su gidan ya k'urawa ido yana kallo, tabbas ada akwai mutane cikin gidan ya kuma samu labarin barinsu gidan, sai dai baisan waye ya siye gidan ba da yaga yanzu an mishi sabon gini, irin ginin da akama gidan ne ma ke bashi mamaki, alamu sun nuna babban gidane daga ciki, daga wajen kawai zai iya d'aukar hankalin mai kallo daga waje saboda wata kalar panti da aka shafa mishi mai kama da carreau (tiles), ga shukoki gajeru da suka k'awata k'ofar gidan sunyi luf-luf dasu gwanin kyau, hak'ik'a an kwana biyu da yaga ana ginin wurin, amma yanda aikin yayi sauri yana bashi mamaki, taka motar yayi ya wuce inda zashi.
Tun bayan sallah la'asar dangi na kusa dana nesa suka hallaro, ranar ta yau kam babba ce dan haka ma takanas takano aka d'auko mawak'i daga Agadez, nan fa aka fara kid'in guitar (jita) ba kama hannun yaro, duka mutanen kowa na zaune kan manyan carpet d'in da aka shinfid'a tare da mangal da butocin shayi anata zugawa, wasu kuma a gefe suna gasa gurasa ana ci ana sha ana raha da nishad'i. Ana haka kuma bak'i suka fara zuwa daga garuruwa daban daban, zuwa sallah magriba gidan nan baya zaunuwa ga duk mai son shiru, dan kowa da nashi dangin da suka zo.
Amare na d'aki cikin shiga ta buzaye inda aka lullub'e su ruf da turkud'i, sai bayan sallah isha'i aka fito dasu dan kowace nata angon ya hallara a wurin ana so su musu kari, haka aka shigo dasu tsakiyar filin inda aka ta kid'in guitar kamar zai tashi gidan, buzaye da suka san darajar abin sai b'arin kud'i sukewa mawak'in, amaren na zuwa aka jerasu gaban angayensu, har fuskarsu rufe take hakan yasa kowane ango ya fara nazarin ina tashi amaryar, dan kayan manya ne wanda suka sa basu wani banbantasu ba sosai, Ammar tuni ya hangi tashi dan dama duk ciki tafisu kumari da albarkatun jiji musamman mazaunai, Jibril dake tsaye kusanta ne ya ji Ammar ya janyoshi ya ajeshi gaban Jamila yana fad'in "Dan ubanka ina kai ina wannan kayan? Ai sai ni babban yayanku."
Kallonshi Jibril yayi yana dariya ya mishi rad'a a kunne yace "Ni ma da zaran ta shigo hannu na zan mayar da ita manyan kayan ai."
Mayar da kallonshi yayi kan Amna yace "Allah yasa kana da ingantacciyar madarar da zata zamar mata vitamin a jiki."
Jibril fashewa yayi da dariya ya kai mishi duka a kafad'a yace "Gaban k'annan ka kake fa."
K'ala baice ba sai fito da kud'i da yayi a aljihu, sabbi ne a mik'e suke kar wanda bla (2000) nasu ma mai kyau ne, mayar da d'aya hannunshi yayi ya goya a bayanshi d'ayan hannun kuma ya fara zuba mata kud'in, suma dai kowa ya fito da tashi suka fara zuba musu kud'in, saida kowa ya gama sannan aka mayar da amare d'aki su Ammar na fita wasu matasa suka shigo gidan suka ce an aikosu da sak'o yana waje, biyu daga cikin dangi ne suka fita wajen, suna zuwa suka samu wasu manya manyan shanu guda biyu, d'aya ta Ammar d'aya ta Amar, gud'a aka saka tare da shelantawa na cikin gida abinda suka bayar, shanu guda biyu daga angaye ayi sabgar gobe dasu, ana cikin wannan farin cikin jiniyar motoci ta karad'e unguwar, GVR Gambo ne ya zo tare da matarshi, ikon Allah aka ce wai sai kallo, kowa na wajen yasan Hajia da yauk'i da kamkamba da miskilanci da shan k'amshi, amma sai gashi yau sunga surukurta wacce ta taketa a komai, ba kowa take kallo ba kamar yanda ba kowa take amsa gaisuwarshi ba, bugu da k'ari tare take da wasu matasan mata biyu, wanda kowa na gidan ya samu labarin cewa d'aya wacce zata dinga mata girki ce, d'aya kuma matashiyar mai yi mata kwalliya ce ta musamman, hatta masauki na musamman da aka ware musu saida tasa suka gyara mata shi sannan ta kwanta, sai dai bata ji dad'in yanda Hajia da kuma babbar matar gidan wato Ummy suka k'i kwantar da kansu a wajenta ba, domin kuwa Ummy a sama sama suka gaisa dan halin da take ciki ma ya isheta, Hajia ma k'amshi tasha sosai ta hakimce saida taje ta gaisheta. Yau ma haka gama sabgar saidai har gari ya waye wasu basu kwanta ba, saboda anata gyaran kayan abincin da za'a girka da safe wanda za aci bayan d'aurin aure.
*Weeding day*
(๐๐๐๐๐๐๐)
Da misalin k'arfe *08:30* na safe dubbanin mutane ne suka shaida d'aurin auren amare uku da angayensu a k'ofar gidan *Alhaji Suleymane Gaga*, sai auren Maryama da aka d'aura shi a gidan malam Rabi'u dake nan cikin garin, su Husseina duka sun halarci d'aurin auren, bayan an d'aura anata gaisawa har Alhaji ya nemi gabatarwa da malam Rabi'u k'annan shi Hassana da Husseina dan su gaisa, Husseina na daf da shiga mota Labaran zai jasu Alhaji ya dakatar dasu ta hanyar fad'in "Yan biyu ku gaisa da kakan yarinyar mana."
Juyowa Husseina tayi da murmushi a fuskarta, ido cikin ido, ido hud'u sukayi da malam Rabi'u, kakkafewa idonta sukayi a kanshi ta kasa katab'us, da k'yar ta d'aga yatsarta ta nuna shi murya na rawa tace "Kkk...kai, Rabi'u."
Duk da shekaru sunja kuma ta tsufa, amma babu abinda ya hanashi ganeta, sunkuyar da kai yayi da alamar rashin gaskiya tare da cire hular kanshi ya fara firfita da hannun babbar rigarshi, Alhaji ne ya kalleta yace "Husseina, kin sanshi ne dama?"
Labaran dake cikin mota zaune fitowa yayi ya zo ya tsaya gabansu ya k'ura musu ido, ita ma duk'ar da kai tayi ta fashe da kuka, Labaran ne ya sake matsawa cikin tashin hankali yace "Hajia lafiya kike kuka? Meya faru?"
Fad'awa tayi jikin Labaran hakan ya sashi shafata yana daddab'ata alamar rarrashi, Hassana ce ta sake cewa "Husseina wai meke faruwa?"
Da k'yar malam Rabi'u ya d'ago cikin i'ina yace "Ee.h to..ina ga dai.. ko bata da lafiya ne?"
D'agowa tayi ta kalleshi tace "Banda lafiya? Me zai hana ka fad'a musu abinda ya faru."
Alhaji ne yace "Wai me yake faruwa ne? Ku fad'a mana."
Cikin tsananta kuka ta kalli Alhaji tace Ba komai, kawai mu tafi."
Labaran daya kafe malam da ido shi dama har yanzu al'amarin mutumin na gindayar dashi yace "Hajia daga ganin mutumin nan yanayinki ya canza, dan Allah ki fad'a mana ko da wani abu mana ko hankalinmu zai kwanta."
Juyawa malam Rabi'u yayi da nufin barin wurin sai Labaran yace "Hajia ko dai wannan shine..." Shiru yayi bai k'arasa ba dan da k'arfi malam Rabi'u ya juyo yana kallonshi, ita ma Husseina kallonshi tayi, sai Hassana ce tace "Shine me?"
Cike da ladabi yace "Hajia kwanan baya sanadiyar ganinshi yasa na miki tambaya akan mahaifina, jikina yana bani kamar akwai wani abu tsakanina da shi, kuma alak'ar zata iya zama mai k'arfin gaske, amma gudun b'acin ranki yasa bana iya aiwatar da komai."
Duk shiru sukayi sai Husseina data share hawaye ta kalli Labaran tace "Tabbas shine, ba zan tab'a manta kamanninshi ba."
Hassana da Alhaji ne suka ce "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Alhaji ne ya d'ora da "Ya ilahi, malam Rabi'u?"
Husseina shigewa tayi mota ba tare data kalli kowa ba, Hassana ma shiga tayi tana waigen malam, Labaran dake kallonshi rasa abinyi yayi, sai kawai ya juya shima ya shiga mota ya tayar, Alhaji ne yayi k'arfin halin matsawa kusa dashi yana kallon idonshi yace "...
*Alhamdulillah*
09/09/2020 ร 17:58 - Ummulkhairi: ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*BADAK'ALA*
๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ _*AHALI NA*_๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
๐ณ๐ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```
_Bismillahir rahamanir rahim_
_34_
"Gaskiya banyi tsammanin haka ba, sam abun baiyi min dad'i ba, cikar kamalarka tasa ban tab'a maka wannan zaton ba, tashin hankalin daka jefamu cikinshi Allah kad'ai yasan iyakarsa, amma yanzu a matsayinmu na manya ba zamu ce da kai bamu yafe maka ba, domin kuwa bayyana da kuma tonuwar lamarin nan a yanzu bayan tarin shekarun da aka kwashe ya isa yasa mu fahimci akwai wani al'amari mai girma, kuma gashi a bayyane auren *Maryama* da Junaid yayi, sai mu musu fatan alkairi."
Yana gama fad'a ya wuce shima inda colonel da kanshi ya bud'e mishi mota ya shiga suka wuce. Husseina na zuwa gida d'akinta ta wuce ta dinga kuka, sam bata so had'uwar ta da shi ba, amma gashi yau ta gani, haka farin cikinta ya koma bak'in ciki, haka shima Labaran, kana ganinshi zaka gane yana cikin damuwa, sai dai shi har zuciya yana so ya gana da mahaifinshi, *uba*, wanda ya rasa tsawon shekaru, bai tab'a d'ora idonshi akan ko da dangin ubanshi ba bare uban. Kamar yanda baya b'oyewa Soueiba komai yanzun ma bai b'oye mata ba, ita kanta abun ya d'an dameta sai dai bai hanata karb'an duk wani daya zo gidan dominta ba.
Tako kamar na gwiwa, d'aya bayan d'aya sai kace wata sarauniya, yayin da mai aikinta ke biye da ita a baya rik'e da jakarta, babbar riga ce jikinta mai kama da babbar rigar maza, d'aurin d'an kwalin ya hau kanta sosai, sai yalolon gyalen data d'ora a kafad'a d'aya da manyan waya har biyu a hannuwanta, zobuna da sark'a da yan kunnai duk gwal ne, dogayen takalma a k'afarta da suka dace da kalar kayan, da gani babu tambaya kasan mai yana aiki a wurin, jan nata har ya k'azamce ta yanda take d'aukar ido, ga kuma hodar data d'auka ta k'ara fito da ita, cike da k'asaita da jin kai da isa ta k'arasa tsakiyar filin da ake kad'in guitar. Yau a k'ofar gida ne ake kad'a guitar d'in sai tarin yan zaman biki da suka zagaye mawak'an suna kallon rawar da wasu maza keyi irin ta buzaye, bayan k'arar guitar haka wurin ya hargitse da shewa irin ta buzaye (ma Sajida nasan zaki fahimci irin shewar, ๐) wasu na karkad'a harshe abun birgewa ana rawa wacce tafi kama da tsalle tsalle, dan wani tsallen sai anyi k'asa sosai ake yin sama ana harba k'afafu ๐(abun birgewa). Zuwan *Aissata* yayi daidai da zuwansu Ammar shi da abokanshi wanda suka zo d'aukar abincin da yasa Zeituna ta girka mishi, zai shiga gidan Sayyada yar Fatime da kuma wasu daga cikin yan mata suka taho wurinshi, nan suka tilasta mishi sai sun d'auki hoto dashi, sun d'auki hoton zai shiga sai kuma ya kalli wurin taron, nan ya hangi Aissata ta bud'e bakin jaka tana watsa kud'i kamar hauka, murmushin zaki gane kurenki yayi mata ya nufeta, nan ya kutsa filin taron ya sameta yana murmushi yace "Uwarmu sannu da k'ok'ari."
Kallonshi tayi a sama tace "Cava."
Kallon mai bisa ruwa ya mata yace "Uwa irin wannan lik'i haka, kice dai aljihun uban namu yayi kuka yau?"
A wani yamutse ta kalleshi tace "Qu'est ce que tu remarque (Me ka lura dashi)?"
Murmushi ya mata yace "Eh to, da yake ai a lokacin aurenku da tonton munje Niamey, kuma har gidanku muje kafin ma d'aurin auren, in baki manta ba ai har d'akin Ummynki na shiga na ci abinci."
Kallonshi tayi da alamar rashin fahimtar zancenshi ko d'aya, hakan yasa tace "De quoi tu parles? (Akan me kake magana), je ne comprends rien (Ban gane komai ba)."
๐ _Hyahyahya, bata gane komai ba, yana nufin ya ga gidanku ke d'in ba yar kowa bace bare ace zaki iya fantamawa da kud'in gidanku._
Murmushi ya mata ya k'urawa fuskarta ido yace "Amma uwarmu powder nan fa ta karb'i fuskarki, wallahi yanda kika san wata kyakyawar sarauniya."
Dariya ya mata ya wuce cikin gidan, ganin babu isassar hanyar da zai wuce yasa shi tambayar *Farisa* k'anwar Jibril inda uwa Zeituna take, ita ta fad'a mishi suna gidan da za akai amare suna girki, da mamaki ya kalleta yace "Gidan da za akai amare? Wane gidan to? Bayan kowa da nashi gidan, Ina ne gidan?"
Nuna mishi gidan nan tayi tace "Yah Ammar gaya nan, yanzu ma ana kai kayansu ne ana gyaran d'aki."
Jim yayi alamar tunani, murmushi ya saki yace "Duk yanda akayi wannan aikin Alhaji ne, dan shine kad'ai yake matuk'ar son ya ga iyalinshi a wuri d'aya, baya son ganin sunyi nesa da juna, shiyasa duk da kowa na da hali amma suke manne gida d'aya." Kallon Farisa yayi yace "Je ki kira min ita."
Galala ta kalleshi jin yace wai ta kira mishi ita, Zeituna fa yake nufi, wucewa tayi shi kuma ya fito dan ya jirata a waje, sai dai yana tunanin yanda zasuyi rayuwar aurensu a kusa da iyayensu, a gaskiya ya so ya bar gidan nan ko ya samu salama, amma kuma ba zai iya yi wa Alhaji musu ba, yana cikin tunanin nan Zeituna ta fito cikin shirinta sai dai duk ta had'a gumi saboda aikin da suke, girki ya tambayeta tace an ida dan haka yasa aka fito da manyan kuloli aka zuba musu, su Amar na zaune a k'ofar gida suma suna nasu casun, sai dai ko magana bata had'a shi da ko d'aya daga cikinsu ba, sai Junaid wanda tuni wasu daga cikin dangin Alhaji da kuma dangin Soueiba suka tafi d'aukar amaryarshi Goรปrรฉ tare da abokanshi.
Hajia ce tsaye a d'akin Alhaji ta tisashi gaba tana fad'in "Akan mene zaka musu gini ba tare dana sani ba? Sai yanzu kawai ana maganar gyaran d'akin sai ka wani ce wai ga gidansu nan, sun fad'a maka suna sha'awar zama anan d'in ne?"
Shiru Alhaji ya mata kamar bai jin me take cewa sai jan carbin hannunsa da yake, d'orawa tayi da "Babu wanda baya da lafiyayyen gida a cikinsu, an musu wannan tanadin ba tun yau ba saboda irin wannan ranar, kuma kai ma kasan da haka, amma ka had'e musu gida d'aya su hud'u, kuma wannan kurkukun gidan me zai musu? Sai kace wasu jarirai ne su da ba zasu iya kula da kansu ba saida taimakonmu, to ni gaskiya wannan gidan bai min ba, inhar kana son su zauna kusa da kai ne to sai dai in zaka raba musu gidan ko da hakan na nufin ka siye duk rabin unguwar nan ne."
A hankali cike da dattako ya d'ago kai ya kalleta, hak'ik'a shi d'an halak ne, kuma har yanzu yana tuna hallacin mahaifinta gareshi, wanda kusan shine silar arzik'in shi, ya mishi hallaci sosai a rayuwa, dan haka har yanzu yake iya shanye duk wani wulak'anci da k'ask'anci daga wajenta. Murmushi ya sakar mata tare da mayar da kanshi ya sunkuyar, hakan kuma k'ara b'ata mata rai yayi, cikin hassala tace "Wato ga mahaukaciya ko? Shikenan ba komai, yanzu fad'a min ita kuma waccen k'ofar da naga ana yi ta kusa da b'angaren samari ta mecece?"
Ba tare daya kalleta ba yace "K'ofar da zasu dinga shigowa kai tsaye ba sai sun shigo ta waje ba."
"Amma w..." Kallon daya mata yasa taji ta kasa k'arasawa, ita kanta tasan a cikin zamantakewarsu akwai ragowa da d'aga k'afa, ta kuma san yana k'yaleta ne kawai saboda mahaifinta, amma ba dan haka ba ko a zahiri tasan yafi k'arfin zama lusari a gidanshi, turo mishi d'an k'aramin bakinta tayi mai kama dana Ammar tare da jujjuyashi ta fice da sauri, murmusawa yayi tare da girgiza kai yace "Allah ya shiryaki Zeeya'atu, ina fatan ganin ranar nan."
Duk da a k'afa aka shigar da amare d'akunansu, amma hakan bai hana abokanan angayen yin kururuwa ba a k'ofar gidan kan ababen hawansu, saida suka tayar da k'ura sukayi juyi da motoci, Maryama ma sun iso lafiya ta shiga d'akin ta. B'angare hud'u ne a cikin gidan wanda daga waje ake mishi kallon k'arami, kowane b'angare matsakaicin doron zabuwa ๐ ce aka mishi, a kowane b'angare kuma yana d'auke da falo da d'aki uku a ciki sai k'ananun madafa (cuisine), a kowane d'aki kuma akwai ban d'aki a ciki bayan wasu ban d'akin dake akwai guda biyu a waje, idan ka cire Maryama da ita ma babu laifi an mata kayan d'aki, duka amaren saida aka cika dak'unan da kaya, Gambo da Labaran ne sukayi wannan k'ok'ari bayan doguwar musu da akayi, Labaran yace shi ya d'auka zaiyi musu kayan d'aki, colonel yace shi zaiyi, lieutenant ma haka, a k'arshe dai Gambo da Labaran suka barma,