Showing 123001 words to 126000 words out of 325849 words
b'oye ba tare da saninka ba kafin suka yarda ma da maganar aurenku, saboda basu so ka lak'awa yarinyarsu cutar da mahaifinka ya d'auko ya kuma gogawa mahaifiyarku, idan kuma baka yarda ba Abdul kaje ka tambayesu, inhar ba k'arya zasu fad'a maka ba to tabbas zasu fad'a maka gaskiyar zancen."
Cikin mamaki ya dafe goshinshi yace "Ke! Wai me kike nufi ne?"
Cikin b'acin rai tace "Ban sani ba, kaje ka tambaya kaji, kai ka mayar da mutanen kamar ababen bautarka, alhalin kuma baka uya fahimtar mai sonka na gaskiya, ni ce ke maka so na hak'ik'a amma Raihan ko a tunaninka bata saka ka, ko da yake ai hausawa sunce *sanin masoyi sai Allah*."
Tana fad'a ta kashe wayar ta cillar ta fashe da kuka, shi kuma zaune yayi bakin gado ya dafe kai ya shiga tunani, shaid'an nata d'awainiya da zuciyarshi sai kuma ga kiran Saleem (masu tambayar waye Saleem da Abbakar, Abbakar shine mijin daya auri Zeenat yar Tahir kawun Abbas), yana d'auka shima ya gama rikita mishi lissafi da nuna mishi Raihan budurwarshi ce ai, suna rayuwar soyayya kuma suna son juna, jiya kuma an kira mahaifinta ne an fad'a mishi an gansu tare a hotel a basraba, dan haka ya umarceta ta dawo, bayan ya nad'a mata na jaki kuma yayi gaggawar d'aukar matakin aurar da ita gare shi shi dake sakarai, nan yace idan bai yarda ba ya duba WhatsApp d'in shi zai gani, ganin wannan hotunan suka saka Abdul fashewa da kuka yana dana sanin yarda da yayi da iyayen Raihan, gashi tun jiya dama da kawunshi ya fad'a mishi halin da ake ciki ya dawo gida nan ya kwana, shiryawa yayi cikin shiga ta ango ya tafi da niyyar nuna musu shima ba kanwar lasa bane.
Misalin *07:30* a masallacin k'ofar gidan aka taru dan d'aurin auren, bai wani samu mutane ba dan ba'a shirya ma hakan ba, dan wani abokin kasuwancin Abbas dake mutumin Niger ne ma masifa ya dinga yi wai ya zai aurar da yarinya haka kamar wata bazawara, shi dai saurarenshi ba har suka shiga masallaci dan gabatar da abinda ya tarasu, Abdul na kallo aka nemi waliyanshi da kuma waliyin Raihan wanda Abbas ya nuna Bashir, saida aka gama d'aura aure akan sadaki dubu d'ari aka shafa fatiha Abdul ya mik'e tsaye yace "Kuyi hak'uri iyayena, auren nan da kuka d'aura yanzun nan zan warware shi, dan ba zan uya zama da fasik'a ba, kamar yanda ba zan iya kiran wad'anda bansan meye nufinsu ba na had'a ni aure da 'yarsu ba a matsayin srukaina ba, dan haka *na saki Raihan saki uku*, idan ta samu miji ko yanzu ma tayi aurenta."
Kallonshi duk mutane cikin masallacin sukayi yayin da kawunshi ya mik'e ya ci kwalar rigarshi yace "Kai Abdul meye haka? Baka da hankali ne? Ya zamu d'aura maka aure yanzu yanzun nan kawai ka saki yarinya? Akan wane dalili?"
Abdul kallon Abbas yayi wanda shi ko d'ago kai baiyi ba saboda yanda yaji abun har tsakar kanshi, yarshi Raihan, ita ce ya d'aurawa aure yanzu kuma aka saketa a gabanshi? Lallai rayuwar nan abar tsoro ce, kallon kawunshi yayi yace "Kawu ina da dalili na, ba haka kawai nayi abin nan ba."
Yayan Safeena mahaifiya Abdul d'in ne yace "Dalilin k'aniyarka, koma menene dalilinka saika saketa daga d'aura muku auren, dama soyayyar k'arya kake mata?"
"A'a kawu, soyayyata gareta ba k'arya bace, sai dai su ne bansan wace irin soyayya suke min ba da har zasu lullub'e min kura da fatar akuya su ban a matsayin mata wacce zata zama uwar 'ya'yana."
Abba ne ya taso daga inda yake zaune yana tattare balaluwarsa, yana zuwa ya kife Abdul da mari yace "Kai butulun ina ne? Wato ka gado a wajen mahaifinka ko? Ni dama da yaron nan yabi ta tawa da bai had'a jininshi da jinin wannan macucin ba, shine yanzu daga d'aura aure a tsakiyar masallaci zaka saki yarinya, kenan nufinka dama ka mayar da ita k'aramar bazawara?"
D'agowa Abbas yayi danya takawa Abba birki kafin allura ta tono garma, suna kallon juna ya mishi alama da dan Allah Abba kayi shiru, Abba daya fahimta fita yayi daga masallacin.
Sunkuyawa yayi kusan Abbas da har yanzu kanshi ke k'asa yace "Na d'auke ka kamar mahaifina, ina girmamaka, duk da nasan mahaifina ya cutar da kai, amma meyasa zaka rama a kaina? Meyasa zaka aura min Raihan bayan kasan wacece ita? Meyasa kayi gaggawar tsayar da ranar auren mu? Bayan kaga wannan ne?" Ya tambayeshi yana nuna mishi hotunan Raihan, a hankali Abbas ya kalli hotunan take ya d'auke kanshi, Bashir dake kusa da shi ne ya fizgo wayar yana fad'in "Meye wannan d'in? Wane sakarci n..."
Bai k'arasa ba shima saboda ganin hoton Raihan tsirara, da sauri ya d'auke kanshi ya jefa mishi wayar, Abdul kuma na karb'ar wayar kawunshi dake tsaye bayanshi ya nuna ma yace "Kawu ganin wannan hotunan ne yasa uncle Abbas saurin aura min yarinyar, bayan haka kuma wai ni har gwajin jini suka min bada sani na ba saboda basu so na aureta ace ina da wata cutar wanda mahaifina ya d'auko ya sakawa mahaifiyata."
Shiru sukayi sai yan maganganu k'asa k'asa yayin da Abbas ya kalleshi yana mamakin inda yaji batun gwajin jinin kuma, suna zaune haka da d'aya d'aya mutanen cikin masallacin suka fece suka bar daga Abbas sai Naseer da Bashir da kuma liman da abokin Abbas d'in nan, abokin kasuwancin Abbas d'in ne mai sunan *Alhaji Khamis Abbas* ya dafa kafad'ar shi da niyyar rarrashinshi, amma zuciya tasa Abbas tashi da k'arfi ya bar masallacin, kai tsaye gida ya nufo kuma ta falonshi ya wuce d'akin Sameera, Sameera na gama shiryawa tana rufe wadrob d'in ta ta juyo ta kalli Raihan dake kwance tana baccin wahala, zata fita kenan Abbas ya shigo d'akin da k'arfi wanda yasa gaban Sameera fad'uwa dan yanayin shi zai nuna maka ba lafiya ba, wajen Raihan ya nufa dake bacci yana zuwa iya k'arfin shi yasa ya mata wani bugun tsiya a baya, da k'arfi ta farka tare da ihu da kuma wani tarin wahala, kafin ta tashi zaune ya finciko dogon gashinta ya jawota k'asa yana shirin fita da ita daga d'akin, da gudu Sameera ta k'arasa ta durk'ushe ta rik'e ta tana rufe mata jikinta, dan dukan da taci ranar yasa bras kad'ai take iya zama da ita sai wani dogon wando wanda bai kamata jikinta ba, kallonshi tayi ido jawur cikin b'acin rai dan abun ya fara isarta tace "Abban Ameer meye haka wai? Ya zaka mayar min da yarinya kamar wata jaka? Me tayi maka?"
Sakin gashinta yayi ya nunasu da hannu yace "Ni yarinyar nan zata kunyata ta tozarta a idon al'umma? Kinsan meya faru yanzu? To auren da aka d'aura mata yanzun nan Abdul ya saketa saki uku saboda ganin hoton shaid'ancin da take aikatawa a waje, me zan mata idan ban illata ta ba?"
Kallon fuskarta Sameera tayi ta kuma kalleshi tace "Abdul d'in ne ya saketa? Wane hoto kuma?"
Cikin b'acin rai ya fito da wayarshi ya nuno hoton ya nuna mata, tana gani ta lumshe ido tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, Raihan? 'Yar dana haifa?"
Kallonta data mata yasa Raihan ganin ta sake shiga uku, da sauri ta mik'e tayi baya nesa da su cikin matsanancin kika tana fad'in "Iyayena dan Allah ku fahimce ni, wallahi ban aikata abinda kuke tunani, idan baku yarda ba zaku iya kaini duk likitar da kuke so a duba ni."
A fusace Abbas yayi kanta ganin haka Sameera da sauri ta mik'e ta shiga tsakaninsu tace "Kayi hak'uri dan Allah ka nutsu, idan muka bi ta zuciya zamu iya kasheta, a k'arshe zamu iya yin nadama."
Yatsa ya nuno mata ya bud'a baki zaiyi magana wayar shi tayi k'ara, juyawa yayi ya koma inda Sameera ta saki wayar ta taso ya duba, lambar Alhaji Khamis ne wanda suke mutumta juna, juyawa kawai yayi ya fita daga d'akin inda Sameera ta juyo kan Raihan ta wanketa da mari tace "Mamana abinda zaki saka min dashi kenan? Me na miki a rayuwa da kika zab'i hukuntani ta wannan hanyar?"
Dafe kunci tayi tana kuka zata durk'usa k'asa ta fizgota ta nufi toilet da ita, suna shiga ta mayar da k'ofar ta rufe ta kama Raihan da k'arfi ta zage mata dogon wandon had'e da pant d'in ta, kunya ce tasa Raihan ja baya tana rufe gabanta, wata harara Sameera ta wurga mata hakan yasa ta d'an kawar da kanta, ba zato ba tammani taji wani zafi ya ratsata da k'arfi sakamakon shigar da yatsa da Sameera tayi na kusa da manuniya, k'ara tayi lokaci d'aya kuma tayi shiru har wasu hawayen wahala sun zubo mata, fito da yatsan tayi ta kalleta sai kuma ta zauna dab'as a tsakiyar toilet d'in, ita gaba d'aya ma kanta ya kulle ta rasa taya zata iya fahimtar yarinyarta budurwa ce, ba zata iya kaita likita ba gaskiya saboda sanannun mutane ne su, hakan zai tab'a kima da kuma mutuncinsu, Raihan kuma d'aukar wandon tayi ta mayar ta sunkuya tace "Ammie, dan Allah ki daina kuka a kaina, Ammie zan sake samu wani mijin na aura, nayi miki alk'awari da idonki sai kin tabbatar da yarki bata watsar da tarbiyyarta da kika bata ba."
A waje kuma yana fita Alhaji Khamis ya samu k'ofar masallacin ya tsaya, cikin nutsuwa Alhaji Khamis yace "Alhaji Abbas na fahimci duk abubuwan dake faruwa, idan zaka bani dama zan so na karb'awa babban d'ana *Baban gida* aurenta? Dan bai kamata a fasa d'aura auren nan ba."
Kallonshi Abbas yayi sosai, hak'ik'a yasan Alhaji Khamis mutumin kirki ne mai sanin ya kamata da dattako, sai dai kuma baisan komai a game da d'an sa ba, duk lalacewar Raihan kuwa zai yarda yayi wannan gangancin? Ganin baice komai ba yasa Alhaji Khamis cewa "Nasan abune mai wahala, amma karka damu ka fad'a min abinda ke ranka, maganar aure tafi k'arfin wasa, Baban gidan bai tab'a aure ba, karatu ya saka a gaba, yanzu haka ma yana *Maroc* wurin karatu, amma shekara mai zuwa zai kammala ya dawo gida, sunan mahaifina ne da shi, wato takwaranka ne."
Kallonshi Abbas yayi sai kawai yace "Ba damuwa Alhaji Khamis, ai hallaci ka mana, kasan yarana ka haifesu amma baka haifi halinsu ba."
Take suka shiga masallacin yan mutanen da suka rage suka shaida d'aurin auren *Abbas Khamis Abbas* da kuma *Khadija (Raihan) Abbas Abdul rahaman* akan sadaki dubu d'ari biyu.
Suna fitowa daga masallaci ana taya juna murna suna tattauna yanda tariyar zata kasance, amma Abbas cewa yayi ai kawai tunda shi Khamis gobe ne zai tafi to kawai zai tafi tare da surukarshi, sannan a yau zai gama mata shirye shirye taje can ta samu mijinta, kuma duk yayi hakane dan ya kawar da ita daga gabanshi, dan ranshi b'acewa yake idan ya ganta kuma tana tuna mishi da abinda shi ma ya aikata, nan Alhaji Khamis ya kira gida ya sanar da iyalai, mahaifiyar Baban gida ta rasu sai kishiyoyi, hakan yasa babu wacce tayi murna da jin haka, dan su abinda suka hango ba wai dalilin auren da gaggawa ba, a'a, tarin dukiyar da mahaifin yarinyar ke da shi, mutumin daya mallaki jirage na kanshi, compagnie da masana'antu ba adadi, sannan uwarta ma jinin sarauta ce, wannan bak'in cikin yasa suka kasa farin ciki, saidai sunyi abincin sadaka kamar yanda mai gidan yace, dan in basuyi ba rai zai b'ace kasancewarshi mutum jajirtattace a gidanshi.
Baban gida ma da yaji musu yayi wa mahaifin nashi, amma dayake yana da zafi saiya balbaleshi da bala'i yace idan ya turo mishi yarinyar ya yankata idan ya cika d'an halak ne shi, haka yaja baki yayi shiru shima yana jiran isowar yarinyar.
*Ma'aruf* da kanshi ne ya shigo musu da abun kari, babu abinda Ma'arufa tayi tunani dan dama kusan kullum shi ke siyowa, ko da baya da kud'i ita zata bayar ya siyo, yana kallonta har ta gama cin indomie ta d'auki lemun daya siyo mai sanyi ta fita dashi tana sha, fatan alkairi ya mata har da cewa tayi sauri ta dawo fa, tana kan hanyar zuwa ta kira Abbas a lokacin an d'aura auren yana wa su Ammie bayani, ganin lambarta yasa shi barin waje ya d'anyi nesa da su, Harira data fito d'auke da jus jus d'in da zata kaiwa bak'in dake gidan ta ganshi yana amsa waya, tsayawa tayi ta lab'e ta kasa kunne tana sauraren shi.
Abinda taji kawai shine "Naji, mu had'u a inda muka had'u jiya, amma ki sani wannan uta ce had'uwarmu ta k'arshe dake."
Tana ganin ya nufi wajen ajiyar motoci ta d'an fito daga lab'ewarda tayi ta aje jus jus d'in ta rigashi fita, yana fitowa ya d'auki hanya ita ma cikin sa'a adaidaita ta fito daga kwana, shiga tayi tace su bi bayan motar...
๐๐๐
22/06/2020 ร 17:26 - Ummulkhairi: ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*BADAK'ALA*
๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ _*AHALI NA*_๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
๐ณ๐ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```
_Bismillahir rahamanir rahim_
_21_
"Dan ubanka meye haka? Wallahi idan ka sake dukanta saina rama mata tunda d'an iska ne kai, Ammar meye haka? Zalincin ne ya motsa maka? Wannan wane irin haukane da iskanci? Me yarinyar nan ta maka da zaka kamata da duka haka?"
Cikin d'aga murya kamar zai fasa gidan yace "Ummy inba raini da iskanci ba ni Amna zata rainawa hankali? Na d'auke na kaita shagon Ilu amma dan iskanci a gabana zata tsaya kula wani bayan kuma tasan nine mijinta, akan me zata min haka? Laifin me nayi? Tana so ta nuna ni ba cikakken namiji bane ko me? Waccen d'in da me ya fini? Kyau? Ilimi ko kud'i? Ko kuma lafiya da girman jiki taga ya fini?"
Cikin hassala Ummy tace "Mijinta? An d'aura maka auren da ita ne? Kai bari ma na tambayeka? Ka k'addara an d'aura muku auren, kenan haka zaka mata wannan dukan tana matsayin matar taka?"
Zaro ido yayi yace "To me zan mata? D'aki zan sakata na dinga rera mata wak'a ina mata rawa dan na kwantar mata da hankali?"
Kallonshi Ummy tayi tace "In kuwa hakane lallai ba namiji bane kai, ba zaka tab'a zama jarumin namiji a gurin mace mai hankalin da tasan ciwon kanta, tun ranar da aka ce Amna ce k'addarar aurenka ta fad'a mata na fara mata kukan tausayi, dan indai har akayi kuskuren had'a ta da kai to babu makawa yarinyar nan tana daf da ajalinta."
Take yaji wasu hawaye na son taho mishi, mahaifiyarshi ce data haifeshi take fad'a masa haka? K'ok'ari yayi ya mayar da hawayen ya kalli Amna yace "Kina ji ko? A dalilinki ne take fad'a min haka, ni kuma nayi alk'awari saina tabbatar muku da namiji ne ni."
Girgiza kai Ummy tayi ta kama Amna suka mik'e tana gyara doguwar rigarta, Husseina ce da mamaki ya isheta tace "Amna kuma? Ai ba Amna bace Hamna ce, Ammar meyasa baka tsaya kayi tunani ba kawai ka hau dukanta haka?"
Dafe k'ugu yayi da hannu d'aya hannu d'aya kuma ya nuna kanshi yace "Kenan yanzu na zama mahaukaci ne da ban iya gane yaran da har goyasu nayi a bayana? Yaran da suka tashi a gaban idona ne zan kasa fahimtar wacece wannan ko wacce waccen?"
Kallonta Ummy tayi dan ta gane wacece ma a ciki, sai dai duhun dake akwai wajen bai bari ta iya ganewa ba, hakan yasa tace "Da gaske ne? Amna ce?"
Gyad'a kai tayi alamar eh, sallalami Husseina ta fara ta rik'e baki tace "Oh ni Husseina, yanzu dama Amna ce nake wa kallon Hamna? Amma meyasa dana kira Hamna kika amsa? Ita tana ina?"
Amna da har yanzu take jin marin nan daya mata da takalmi kuka kawai ta sake fashewa dashi, shi kuma k'wafa yayi ya kalleta ya nunata yace "Daga yanzu duk inda zaki je saina baki izini indai har nine wanda zai aure ki." wucewa yayi inda Ummy ta bishi da kallo ganin jikinshi biji-biji ga kayanshi sai k'yallin mai suke, kama Amna tayi suka shiga ciki bata yarda sun tsaya falon ba, sama suka haura d'akin su suka zaunar da ita, fad'a Ummy keyi sosai na haushi da takaici, har da cewa "To ubanki ne shi da har zaki tsaya ya miki wannan dukan? Ba dan kin zama sakarya ba ma akan me zakiyi tsaye yana d'irkarki haka? Amna aure fa ake shirin yi miki dashi, da hakane zaku zauna kinsa tsoronsa a ranki? Na tabbata da yer uwarki ce Hamna wallahi ko gudu ne tayi daga gurinshi, dan baya da maraba da mahaukaci idan ranshi ya b'ace."
Amna dai shiru tayi sai sharar hawaye take, hakan yasa Ummy cewa "Kiji harda wani cewa wai in zaki fita saida izininshi, to mu duk aikin banza ne kenan a gidan? To zaki fita bada izinin nashi ba sai naga in kasheki zaiyi."
D'agowa Amna tayi cikin kuka tace "A'a Ummy, tunda dai yace haka ni zan bi umarninshi, zan nemi izininshi kafin na fita, shikenan sai a zauna lafiya, ko Mama ma tana fad'a mana mu dinga jin maganarshi dan shi kad'ai ne ke tsawatar mana."
Da mamaki Ummy tace "Ke yanzu sai ki biye masa kuma?"
Jinjina kai tayi alamar eh tare da cewa "Ummy hakan shine zaman lafiya na, nasan ni ba yer uwata Hamna bace, nice mafad'aciyar kuma mai zuciyar, amma akan yah Ammar bana da ko d'aya, bansan meyasa ba."
Tab'e baki Ummy tayi tace "Lallai kina da aiki Amna."
Ko da yayi wanka shiryawa yayi cikin riga da wando bak'ak'e, makullin mota ya d'auka ya sake fita, k'aramin gurin cin abinci ne *Kebab* ya zauna ya ci abinci, daga nan kuma hanya ya d'auka saida ya samu inda babu hayaniya ya paka nan, jingina kawai yayi yana sauraron wa'azindake tashi a