Showing 255001 words to 258000 words out of 325849 words

Chapter 86 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

524

Middle Ads

kanta tayi ta kuma kallonshi har yanzu dai hankalinshi na ga tuk'i, cikin sanyayyan murya tace "Kai likitan zuciya ne, amma me yasa baka tsoron saka mutane a damuwa?"

Saida ya fara d'aga idonshi sama sannan ya d'an kalleta, da alama nutsuwa ta zo mishi dan cikin sanyin murya shima yace "Ba damuwa nake saka mutane ba, ina musu magani ne."

A hankali tace "Comment?"

Kallonta yayi sosai sai kawai yayi murmushi mai sauti yace "Tu ne comprends rien, rien Hamna."

Kallonshi tayi tace "Me yasa kace haka?"

Ba tare faya kalleta ba yace "Peut être wata rana."

Cikin odonshi ta kalla tace "Ammar je te connais bien, (na sanka sosai), mai jusqu'à présent je ne comprends rien (amma har yanzu bana fahimtar komai a game da kai)."

Dariya yayi wacce ta fito da hak'oranshi yana girgiza kai yace "Idiote."

Kallonta yayi yace "Dana bari kin fahimce ni da kin k'ara tagayyara ni kankana."

Da mamaki ta kalleshi tace "Kamar ya?"

"Comme je le dit (kamar yanda na fad'a)." Ya fad'a yana kashe mata ido d'aya, girarta ta d'aga sama ta kalli titi tace "Moi aussi."

Kallonta yayi yace "Ke ma me?"

kallonshi tayi tace "Dana tagayyari daka gane."

Bushewa yayi da dariya yace "Ni na sani dama."

Da sauri ta kalleshi tace "Vraiment?"

Sake kanne maya ido yayi yace "T'inquiète pas ma puce, chaque chose a son temps, petit à petit les oiseaux..."

Sai kuma ya bushe da wata dariyar yana k'yalk'yalewa da ita, ita ma da bata fahimce shi ba sai kawai taji ta bushe da dariya, kallonshi take tana tayashi dariyar kamar zararru, sun jima suna dariyarsu kafin suka tsagaita kuma akayi shiru, kallonta yayi yace "Me kika ma dariya?"

"Abinda kake ma." Ta fad'a tana hararenshi, da wannan ne sai tafiyar tasu ta d'anyi dad'i, dan har tsayawa yayi a station d'in Alhaji suka sha mai suka wuce, haka ma saida ya siya mata kayan k'walama suka ci, tafiya tayi nisa sosai kawai ya tsayar da mota a gefe ya kalleta yace "Fita kiyi fitsari yarinya karki min shi a mota."

Da zata ce masa bata ji, sai kuma taga ya raina mata hankali ma sai kawai tayi banza dashi, cike da zolaya yace "Ko na siya miki 4 (kun dai gane kalmar da english ai) ne kiyi?"

Fuska a had'e ta kalleshi tace "Eh, ko kuma penpers ba."

Wani kallon shak'iyanci ya mata yace "Wannan ki bari sai zaki fara bulbuli."

Yamutsa fuska tayi tace "Bulbuli kuma? Yara fa ke bulbuli."

Kallon baki da hankali ya mata yace "Waccen bulbulin nake nufi wanda ku kukeyi duk wata."

Murmushin baka da hankali ita ma ta masa tace "Da har na fara tunanin ko an canza ka ne da naji baka saka kaina yayi nauyi ba, amma yanzu na ji na gamsu da kai nake tare."

Wayarshi ya d'auka yana dannawa inda Hamna ta gyara zamanta ta jingina sosai, Amna ya kira suka gaisa tare da shiga hirarsu ta soyayya, tana kallonshi har bacci ya d'auketa a haka, yana idawa ya kalleta, murmushi kawai ya saki ya ci gaba da tuk'i cikin aminci.

Ganinsu tare ya ba kowa mamaki, har d'akin Hajia ya kaita ya gindaya sharud'anshi wai ko fita karta sake yi ba tare da dalili ba, saida ya gama tsaf Hajia ita dai ta kalleshi tace "To za'a kiyaye."

Ummy kuma kallon al'ajabi take da ikonshi, inda Hassana da wasu daga cikin dangin Hajia suka bishi da kallo suma, har zai fita Hamna ta fara gunguni k'asa k'asa tana fad'in "Wallahi babu wanda ya isa ya hana ni fita tunda ba yar zaman banza bace ni, kaji mutum kamar wani uba na ehee."

Juyowa yayi ya kalleta yace "Ki jaraba ki gani to."

Fita yayi duk suka raka shi da ido, a ranar dai kamar wasa Hamna ta rantse cewa ba zai hanata abinda tayi niyya ba kamar wanda ya haifeta, kai ita ko dan ta nuna mishi bai isa ba ma saita fita a yanda ta ga dama d'in. *Washe gari* tsaf ta shirya dan zuwa salon d'inta, doguwar riga ce ta saka ta kanti kuma ta mata kyau sosai, kallabin rigar ta yane kanta dashi ta fito, a falon suka had'e yana sallama da su Hajia zai wuce, gaisu tayi tasa kai zata fita tsohuwa mai tambaya😂 tace "Amina (yanda take kiransu kenan) banji kin gaishe da shugaba ba?"

Juyowa tayi ta kalleshi sama da k'asa tace "Tsohuwa wane shugaba kuma?"

"Ammaru mana, ba yayanki bane da zaki fice baki gaishe shi ba?" Cewar tsohuwar, tab'e baki tayi tace "Sauri nake Hajjo."

Cikin rarumar gani tace "Ina Sa'ada take?"

Ummy dake rik'e da kular abinci ce ta tsaya tace "Hajjo gani, wani abu kike so?"

Cikin dattako tsohuwar tace "Yanzu Sa'ada kina ji Amina bata gaishe da yayanta ba kuma baki mata magana ba?"

Kallon Hamna tayi da ita ma take kallonta, rasa abin fad'a tayi sai Ammar daya kalleta yace "Ki rik'e gaisuwarki ma, kije ki saka hijab kawai saman jayan nan naki."

Cike da raini tace "Doguwar riga ba'a saka mata hijab, ko baka san haka bane?"

D'auke kanshi yayi daga kanta yace "Ki canza wasu kayan da zaki iya saka hijab."

Cike da gatsali tace "Malam wai me ya maka zafi ne da shigata? Ina ce haka kuke son gani?"

Hajia ya kalla yace "Hajia dan Allah ban son tashin hankali, ki fad'a mata ta dinga rufe jikinta kafin ta fita, nan fa babban gida ne da ake ganin mutumcinmu, ita kad'ai bai kamata ta zubar mana da daraja ba, ni ina ga ko dan rasuwar da akayi zata iya kama kanta ai."

Dariya tayi tace "Kama kai? To wane irin kama kai kuma bayan ko ka kama shi akwai masu warware maka, kaga malam ka fita a hanyata idan kana da zuciya dan Allah, kuma fita haka zan fita na ga wanda zai hana ni, zaka zauna kawai kana sa min doka kamar kai ka haifeni, bayan kuma duk wani mugun abun kaine ka fara shi, saika nuna kai na Allah ne amma kuma ba haka bane, to idan tayar maka da hankali nake ka fad'a min inda zamu had'u, a shirye nake yanzu tunda na ga abinda kake so na zama kenan."

Saida ta dasa aya, ta kai k'arshen abinda take son fad'a, d'ago kai yayi ya kalleta ido cikin ido, idonshi sun canza kala sunyi ja, maganarta ta sokeshi fiye da tunanin mai tunani, ta kassara zuciyarshi da kalamanta, ta sa shi jin kunyar soyayyar da yake mata, zai kuma nuna mata a aikace ba yanda take tunani yake ba.

A sukwane ya mik'e yayi kanta, saida ya tsaya gabanta ya d'aga hannunshi mai d'auke da zarta zartan yatsu ya sauke mata kyakyawan mari a fuskarta, kafin ta d'ago daga sunkuyawar da tayi tare da k'ara ya sake sauke mata wasu yatsun, ta dafe kunci zata d'ago a karo na uku ya sake gabza mata wani marin, rud'ewa tayi ta ja baki tayi shiru daga ihun da take tana murza kumatu da taji suna mata wani zuuuu zuuuu zuuuu kamar zasu tsinke, daga wayarta jaka da makullin mota duk ta jefar dasu, sam babu abinda take ji sai ko take gani, tana cikin wannan halin ya sunkuya ya nunatada hannu yace "...


*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

👨‍👩‍👧‍👦 _*AHALI NA*_👨‍👩‍👧‍👦

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_59_

Cikin matsanancin b'acin rai yace "Hamna ni? Ni zaki kalla ki fad'a ma wannan maganar? Yaushe aka haifeki? Yaushe har na miki caccakar da kike ganin ta isa ta zama katangar da zaki b'uya a bayanta ki raina ni? Ko yar uwarki da nake kwana tare da ita na tashi tare da ita babu kaya a jikina bata isa ta min rainin da kike son min ba, har ki kalle ni wai kice na fad'a miki ina zamu had'u, ke yanzu nan har kin shirya zaki iya dani? To saurara kiji Hamna ba tsananin so ko kishinki bane yasa nake takuraki kan dinga suturta jikinki, mutumci ne nake so na kankaro miki a idon jama'a, duk idon mutane yana kanki saboda daga babban gida kika fito kuma yar babban mutum ce, amma daga son taimaka miki sai abu ya zama tashin hankali."

Kujerar daya tashi daga kai yasa k'afa ya tokara cikin b'acin rai kujerar tayi baya da k'arfi ta daki kwabar gilas d'in turare, hakan yasa wasu daga cikin kwalaben girgizawa suka fad'o k'asa hakan ya haddasa sauti marar dad'i mai kayar da gaba, bai kula ba yasa hannu yana dukan k'irjinshi yana fad'in "Allah ma shida ne, sannan kuma ku zama shaida."

Ya fad'a yana nuna duk mutanen dake d'akin yace "Inhar na k'ara magana kan Hamna ta suturta jikinta ku ce ta hanyar zina aka haife, na kuma yarda ba zanyi gadon mahaifina ba, ba wai iya dukiyarshi ko d'aukakar shi kawai ba, har da sunan shi, na yarda ba zan sake saka sunanshi a gaban suna na ba."

Kallonta yayi yace "Kiyi duk abinda kike so da rayuwarki, banda matsala a kai Hamna."

Da saurin bala'i ya fita daga falon zuwa barin gidan gaba d'aya, yana tuk'i yana dukan sitiyari da k'arfi. Falo yayi shiru ko numfashin mutane baka ji, wasu tunda suka rintse ido sakamakon fad'owar kwalaban turare basu bud'e ba har yanzu, Ummy da hankalinta ya gama tashi tasan yau asirinsu zai tonu, dan dukansu sunyi magana ne a yaran da duk mai hankali zai fahimta, kallon Hajia take da taga kanta k'asa tayi shiru, a hankali ta juya kanta ta kalli Hajjo, sai taji tsohuwar ta bata haushi dan duk ita ta b'abb'ako musu aikin nan, data barta ta tafiyarta da yanzu an rabu lafiya.

Kakkauran numfashi Hajjo ta sauke cikin muryar alhini tace "Hajia, dama haka yaron nan yake?"

Hajia ma da tasan komai kuma bata so abun ya fito kallonta tayi cikin jin haushi tace "Duk ke kika ja mana wanan sababin fa, da bakiyi maganar gaisuwar nan ba duk da haka bata faru ba."

Kallon Hamna tayi da sai yanzu kad'ai take jin magana a hankali a hankali tace "Ki tashi daga nan ki bani wuri, kije kiyi ta fita duk yanda kike so babu mai hana ki, idan kina so ma ki tafi tsirara, amma karki kuskura ki zubar mana da mutumcin gida kinji na fad'a miki."

Tana fad'a ta mik'e tayi d'akinta, Ummy na ganin haka wata ajiyar zuciya ta sauke tana godiya ga Allah, ita ma sulalewa tayi ta bar wurin ko Hamna bata kula ba dan maganar gaskiya tasan Hamna ce ta jawo magana, shi kuma dama ba hak'uri gare shi ko na k'wayar zarra. Hamna ma mik'ewa tayi cikin hassala ta d'auki jaka wayarta da makulli ta fita, ko da ta shiga mota saida ta gyara fuskarta da duk sawun hannayensa suka fito, wannan haushin na cin zarafin daya mata da kuma abinda Hajia ta fad'a mata yasa ta niyyar ba zata canza d'in ba, haka ita ma ta fita daga gidan rai a b'ace, ko da taje salon saida tasa aka nemo mata maganin ciwon kai tasha dan gaskiya fa tasan ta maru, mari ne data tabbata daya sake mata na hud'u to kunnenta ko idonta zasu iya barin k'wallon kanta.

Mutanen wurin babu wanda bai fahimci me ake nufi ba, anyi shiru ne kawai saboda babu wanda ya isa yayi magana, sai dai kowa ya yarda Hajia ma tayi shiru ne yanzu saboda abin daga iyalinta ya fito, amma da wasu ne da tuni ta cire musu wando ta kai ta bisu da dariya, sannu sannu maganar ta fita daga falon ta kai farfajiyar gida, daga farfajiyar gida ta fita k'ofar gida, to fa iska na surarta yayi gaba da ita har wasu garin ma saida aka ji wannan tsirku, inda aka ma maganar ado da kwalliya cewa Hamna yar iska ce kawai, shiyasa ba tayi aure ba kuma ana gani an saka mata ido, iskancin ne ma ke tsakaninta da mijin yer uwarta, nan fa kowa ke fad'in albarkacin bakinshi, inda wasu ke fad'in ai muna ganinta cikin garin, tun tana hawan moto dama take more rayuwarta, yanzu kuma da take hawa mota ko magana ba ayi ba, wasu kuma fad'i suke ai sun ganta biki kaza da kaza ko kuma wacce da wacce ce k'awayenta, mutum kenan mugun icce.

Haka akayi rabon gadon Alhaji inda kowa yaja nashi babban rabo😂, kowa ya k'ara yawan jari ya kud'ence abinshi, shagali kawai ake iyaye da yaransu, kowa ya k'ara d'ora yaranshi kan manyan harkoki, hakan ya tilastawa Ammar dawowa wata ukun bai cika ba aka duk'ufa harkokin duniya, wani lokacin kamar kanshi zaiyi bindiga tsabar abunuwa, yaje asibiti yaje station shaguna da sauransu, a hakan ma wai dan Amar ma da inda yake kulawa haka ma Kamal suna saka shi kowane b'angare tunda ya fara mallakar hankalinshi shi ma.

Tunda abun nan ya faru ko sannu shi da ita bata sake had'asu ba, ya watsar da al'amuranta ya sake rumgumar matarsa hannu bibbiyu, sau da dama sukan had'u ko wajen shiga mota ko farfajiya ko k'ofar gida ko kuma falon Hajia, amma kallonta ma baya yi bare yaga shigar jikinta abun ya dame shi, hasalima ko ganinta yayi canza fuska yake yi yayi abinda ya kawoshi yayi gaba.

*Wannan* shi ake kira da kisan mummuk'e, gashi dai ya fita harkarta kamar yanda take fad'a a kullum, ya daina ko kallon fuskarta, ko d'akin matarshi zai shiga ya ji tana ciki saida ya koma har sai ta fita, tun tana jin kamar dad'i take ji har ta fahimci ba dad'i take ji ba a zuciyarta, kawai tana nuna tana jin dad'in ne a zahiri, ita ma bata kula shi kamar yanda yake yi, sai dai bata jin dad'i ko kad'an. Amma kuma hakan baisa ta canza abinda duk shine ya jawo matsalar ba, sabon babin rashin mutumci da fitsara ta bud'e, Amie dama ita ma ba aure tayi ba dan haka ta taya b'era b'ari suke sharholiyarsu, yawan biki da bi-gari kullum cikinshi suke, sun shiga sahun manyan matan da ake kiran sunansu, wannan matsatsun kayan dai kullum sune jikinta, wani lokacin ko gyale bata d'orawa haka zata shiga mota.

Kud'i kullum cikin kashesu take wajen siyan anko na k'awaye da d'inki, anko ba wai guda d'aya ba a'a sama da haka, abune daya zama na yayi kowa na so a fad'i bikinshi, hakan yasa kamu bridel party kan amarya damu, duk wannan abubuwan anko ake fiddowa kuma tana siya da kud'i, wasu lokutan d'inkin da akayi iri d'aya akeyi duka yan mata, wani d'inkin ko wata shigar idan kaga sunyita ka rantse ba yayan musulmi bane.

Amar ne ma ya d'an fara k'orafi kan abinda take, shima daga baya ya ja bakinshi yayi shiru, Hajia na gani amma an rasa dalilinta na saka mata ido tana abinda ta ga dama, Ummy ce ke tsaye kanta take mata fad'a da magana, amma magana d'aya ce "Ummy ki yarda dani wallahi ba zan tab'a zubar muku da mutumci ba, ko ban fita biki ba ai zan je wajen sana'ata, dan haka ki kauda idonki daga abinda mutane zasu ce ko suke fad'a."

Hadiza taga canji sosai a game da yar ta ta, hakan yasa ta tambayi yar uwarta Amna, a lokacin Amna ta ji a cikin gidan cewa Hamna ta ma Ammar rashin kunya shi kuma yace ba zai k'ara mata magana ba, yanda taji ta fad'a ma uwar wanda hakan yasa ranta b'aci fiye da kima, a waya ta kirata ta fad'a mata tana son ganinta, wannan karan ko da ta zo ko wurin zama ba'a bata ba bare ruwa aka balbaleta da masifa, ta inda Hadiza ta fita bata nan take fita ba, ta mata fad'a sosai kamar yawun bakinta zasu k'afe, tana gamawa kuma tace ta tashi ta koma bayan ta bata umarnin ta fito da miji wata d'aya kawai idan ba haka ba kuma zata dawo da ita gabanta ko da hakan zaisa sai tayi shari'a da dangin uban nata, haka ta juyo ta dawo tun a hanya take tunanin abinda mahaifiyarta ta fad'a, cikin jin haushi take tambayar kanta waya fad'a mata abinda ya faru? Wa zata fitar a matsayin miji? Ita fa bata shirya aure yanzu ba ma, idan fa tayi auren ma asiri ya tonu fa?Tsaki tayi ta d'an daki sitiyari saboda tuna abinda mama ta fad'a, a hankali ta shiga jero kalmomin data fad'a mata a k'walwarta.

*"Ashe shiyasa kika zama tsagera, saboda mai fad'a aji a gidan ya tsame hannayensa daga kanki, to ke inba hauka irin naki ba duk gidan nan waye zai tsawatar miki inba Ammar ba? Sa'ada dama ba mazauniya gida bace, sannan tun farko ita da lieutenant sun riga da sun lalata ku da sangarta, colonel a shekara d'aya zaman da yake a gidan lissafaffe ne, Labaran kuma dama tun farko baya shiga sabgar iyalin Hajia saboda baya son ta ci zarafin mahaifiyarshi, dan shi zai iya yin laifi amma har Hajiarshi saita wanke ta tas, to Amar Junaid Jibril dukansu aikin banza ne, babu wanda ya damu dake ko tsirara zaki fita, mahaifinku kuma kinfi kowa sanin baya da lokacinku, to ki fad'a min inba Ammar ba waye zai sa ido akan ki? Ke ba ma ke kad'ai ba kaf yaran gidan shi kad'ai ne mai taka musu birki, dan haka ki same shi ki bashi hak'uri in ba so kike kiga b'acin rai na ba."*


Shawarar Amie tayi aiki da ita wajen fito da *Habib* a matsayin wanda zata aura, ba wai dan tana son shi bane sai dan shine yafi tsarin da take son mijin aurenta ya kasance, ba'a wani tsaya bata lokaci ba aka shigar da manya maganar kuma suma suka nuna manyantaka, dan danan aka saka rana inda aka kawo kaya, k'ok'arinshi ya birgeta dan

End Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login