Showing 54001 words to 57000 words out of 325849 words
"Muje ciki muyi magana da Ammar yana nan, Amar idan ya shigo zamu fad'a mishi kuma kasan ba matsala zai bamu ba."
Wucewa sukayi ciki Junaid na fad'in "Wai duk wannan saurin na miye haka? Kamar wanda zaije ganin tashi budurwar."
Wani murmushi Jibril yayi, dan haka kawai ya ji kamar ana fizgarshi da yaje garin, yana so ya Allah ya sake had'a shi da yarinyar nan, suna zuwa suka saka Ammar tsakiyarsu Junaid ne yace "Babban yayanmu, dama wata alfarma muka zo nema, dama yarinyar nan da nake so ce ta fad'a min garinsu, to akwai yar matsala tsakaninta da iyayenta, shine nayi shirin tafiya neman aurenta wajensu tare da shirya tsakaninsu, to bana so ne naje ni kad'ai gaskiya, nafi so muje tare da ku dan su san ni d'an dangi ne."
Ammar da hankalinshi ke kan waya saida yaji ya kai aya kamar mai ciwon haure yace "Ina da abinyi."
Yana fad'a kuma ya mik'e ya shiga d'akin shi, Junaid ma ya mik'e yana tab'e baki sai ga Amar ya shigo, nan suka fad'a mishi kuma kamar yanda suka sani dama ba zai basu matsala ba, shirya yanda tafiyar zata kasance sukayi kafin kowa ya nufi d'akin shi.
*Zanyi magana, amma ba yanzu ba.*
03/06/2020 ร 23:33 - Ummulkhairi: ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
๐ _*MASOYA NA*_๐
_Bismillahir rahamanir rahim_
๐ณ๐ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```
_6_
Ma'arufa ce da Ma'aruf a d'aki kowa da wayarshi yana dannawa, kwance take akan katifa mai tufun gaske shi kuma tashi katifar bata da maraba da bargo, kallonta yayi yace "Ke wai kin fara shirin tafiyar ne gobe ko kuma kina nan kina jan jikin?"
Ba tare data kalleshi ba tace "Ba gobe zan tafi ba."
Ba tare daya daina kallonta ba yace "Saboda me?"
Kai tsaye tace "Saboda akwai wasu kud'i da Labo zai bani gobe idan ya zo, kuma ina so na shiga kasuwa na siyo sabbin yadin da za'a min sabbin riguna dogaye, tunda waccen gurguwar tace mutumin ba wai harkar matan banza yake ba."
Tsaki yayi yace "Ke dan Allah kiyi duk iskancin da zakiyi zuwa jibi ki bar garin nan, na k'osa kud'in nan si shigo wallahi harka ta bud'e, dubi shegiyar katifar da nake kwana akai."
Sai lokacin ta kalleshi tace "Wai kai yanzu ko kunya baka ji? Kana kwance gida ni ce zanje na nemo maka kud'in da zaka ji dad'in rayuwarka da su."
Ba tare da damuwa ba yace "To meye a ciki? Ke ma sau nawa ina miki anfani? Yanzu lokacinki ne yayi."
Tsaki taja ta mayar da kallonta kan wayarta tace "K'aton banza kawai."
Kallonta yayi amma bai biye mata ba saboda yana wata hira data d'auke mishi hankali, wata budurwarshi ce mai sunan *Meena* ke ikrarin daina harka dashi tunda baya sonta baya kashe mata kud'i, maida mata sak'on yayi da "Rabuwa dani a daidai wannan gab'ar na nufin ke asararriya ce."
Maido masa tayi da "Sai dai in kaine asararren, shege d'an iska wace tsiyar kake tsinana min?"
Shima mayar mata yayi da "Ke haba matsalata dake banza ce, kanki baya kawo wuta ko kad'an, ina nufin idan kika barni a wannan lokacin to zakiyi asarar wata opportunity da muka samu."
"Ban gane ba d'an rainin hankali, fahimtar dani?"
Nan ya fad'a mata wai sun samu wani Alhaji gara zasu wanke shi, kuma k'ashin bayan tafiyar abokiyarshi ce Ma'arufa, dan haka karta bari damar nan ta wuce ta, nan dai suka sulhunta komai ya wuce.
โกโกโกโกโกโกโกโกโกโก
Yanda Abbas yayi tunanin aikin zai kaishi kwana uku sai ya zo da sauk'i, dan haka ya shirya ya taho ba tare daya fad'awa madame ba, su a lokacinsu dare ne dan har sun shiga bacci, saida ya fara shiga wajensu Ammie da suma har sun kwanta ya gaishe su, daga nan kuma part d'in shi ya wuce ya aje jakarshi yayi wanka, kayan bacci ya saka ya feshe jikinshi da turare mai sanyin gaske kafin ya d'auki makullin k'ofar da zata sada shi da falon Sameera ba sai ya fito ta farfajiyar gidan ba, yana shiga ya tabbatar sun jima da kwantawa, d'akin Raihan ya fara bud'a k'ofar a hankali ya lek'a, saida ya sauke ajiyar zuciya sabida ganin tana bacci hankali kwance, duk da har yanzu bai siya mata waya ba amma dai yana tsoron sharrin zamani da dubarar 'ya'yan yanzu, rufewa yayi ya lek'a d'akin Rauda, Khalifa da sauran yaran, amma yana ganin Abdul raheem shi kad'ai kwance a gadonshi babu Ameer ya tabbatar yana wurin mamanshi, a hankali ya shiga can cak ya tsaya, rarraba ido yakeyi tare da shafar kai, a hankali ya fara takowa har ya zo kusa da ita ya tsaya, jefar da makullayen yayi kan gado ya bud'e mata hannayenshi yace "Come on my angel, i miss u."
Sameera da tunda mota ta shigo gidan ta farka a hankali cikin turo baki ta bud'e hannayenta ta kwanta luf a k'irjin shi, lumshe ido yayi ya sauke wata ajiyar zuciya mai d'an k'arfi wacce iska da gumin bakinshi har suka sauka kan fuskarta, k'ara shiga jikinshi tayi tana sake matseshi sosai saboda k'aunar mijin nata, ido rufe take sauke ajiyar zuciya tana shak'ar turarenshi dake son mayar da ita bacci, cikin muryar shagwab'a tace "Me yasa baka fad'a min zaka zo ba?"
Saida ya fara yawo da hannayenshi a gadon bayanta yana latsawa saboda taushi da laushi ba tare daya bud'a ido ba yace "I'm sorry, nima bansan aikin zai sakeni yau ba, ina k'arasawa kuma naji ba zan iya kwana nesa da ke ba, shiyasa na garzayo na zo gareki."
K'ara daidaita zamanta tayi cikin k'irjinshi shi kuma yana sake matseta yana shafata, cikin wata murya mai kama data bacci yace "Meerata."
"Uhmmm." Ta fad'a ba tare data kalleshi ba, d'orawa yayi da "Zan samu kulawarki a wannan daren kuwa? Naga baba na yayi kane-kane a kan gadon."
D'agowa tayi ta kalleshi ta juya ta kalli Ameer dake ta baccinshi, sake kallonshi tayi tace "Ka d'auke shi mana saika kaishi d'akin su."
Kallon Ameer yayi shi ma ya zagaya zai d'auke shi yace "Allah kasa kar yaron nan ya hanani sakewa."
Murmushi tayi wanda harya fitar da sauti, kallonta yayi yace "Wallahi yaron nan rigimarki ce ya koya, ko da yana jariri bai hanani yin rayuwa da ke ba kamar yanda yanzun yake hana ni."
Zaune tayi bakin gadon tace "Watak'ila yana tsanani buk'atar a kasance auta ne shiyasa, yasan idan ya baka fili saika masa k'ane."
Harara ya cillo mata yace "Idan na tashi yi a hanani na gani, kinsan dai ko gabanshi na so zanyi yanda nake so ko?"
Dariya tayi tace "To ka barshi yanzu saimu jaraba mu gani."
A lokacin daya d'auki Ameer ne yace "Bana so na jefo shi k'asa ai."
K'arar bud'a k'ofa yasa Ameer bud'a ido tare da zabura ya kalli wanda ya d'auke shi dan ya hango mamanshi zaune, rintse ido Abbas yayi wanda yasa Ameer cikin muryar bacci cewa "Yeee! Dady na ganka bud'e idon."
Kafin ya bud'e idon ido ya sake cewa "Dady yaushe ka dawo? Ka kawo min computer ta?"
D'ago shi yayi suka kalli juna yace "Muje na kaika d'akinka ka kwanta da safe zan nuna maka wacce na siyo maka, ko Khalifa baya da irinta."
Ai sai Ameer ya dirko daga kafad'ar Abbas yace "Um um Dady, ni tare da Ammie na zan kwana, abinda ma tunda ka tafi tare muke kwana, kai kaje d'akin ka."
Da gudu ya yo kan Sameera ya kwanta kan cinyoyinta yana kallon Abbas, ganin yana nufoshi yana fad'in "In dai kana son na baka computer sai ka zo mun tafi, idan ba haka ba kuma sai dai na bawa *Amjad* (d'an Naseer) ita."
Zagaya hannayenshi yayi ta kunkumin Sameera ya mak'aleta sosai yace "Um um, bana so ni dai."
Dariya Sameera tayi rumgume shi tace "Babana kenan, yaro kwana a gado d'aya tare da mahaifiyarshi yafi mishi komai na duniya ko?"
"Eh Ammie." Kwance Abbas yayi kan gadon dan ko yace ya zare mishi ido kuka ne zai saka musu a daren nan, kallonshi yayi yace "Zo nan baba na nayi kewarka sosai."
Rarrafawa yayi ya kwanta kan k'irjin shi ya rumgume shi, Sameera ma kwance tayi ta d'ora kanta a kafad'ar shi tace "Ka ci abinci kuwa?"
Ido lumshe yace "Um." Tsautsayi yasa Sameera cewa "Auta na kayi abinci kaji, kasan..."
Wata k'ara ta saki saboda mintsinin da Abbas ya mata a mazaunai, zaune ta tashi idonta har sun fara ja saboda zafi, kallonshi tayi shi kuma ba tare daya kalleta ba yace "Gobe ma na sake jin kin kira shi auta kiga yanda zanyi da ke."
Kamar zata fashe da kuka tace "To meye a ciki dan na kira shi da auta dan Allah?"
Ido rufe kamar wanda zaiyi bacci yana ci gaba da shafa bayan Ameer yace "Saboda yawon kiran na shi da auta zaisa wata rana ki fad'a lokacin amsar addu'a, ni kuma so nake sai kin dire min sha biyu insha Allahu." Shiru ta mishi ta kwanta, gashinta yake shafawa da d'aya hannun a haka har bacci ya d'auke su.
*BASRABA*
Tunda garin Allah ya waye Takawa yake jin kamar ba shi ba, a haka har akayi sallah la'asar ya dawo b'angaren shi kan kilisarshi ya kishigid'a, haka kawai yaji yana buk'atar ganin liman, dan haka yasa d'aya daga cikin masu tsaron k'ofar shi ya nemo mishi liman, kusan dama unguwar duk duk fadawan fada ne a ciki, dan haka ba jimawa sai gashi ya dawo tare da liman, jakadiyar uwar d'aki na ganin haka ta garzaya ta fad'awa uwar d'aki, cikin tashin hankali tace "Kin tabbatar liman ne ya shiga wajenshi?"
Cikin girmamawa tace "Ko zanyi k'arya uwar d'aki harshena yayi kad'an daya furta miki k'arya, yanda na ga liman tare da bafaden nan ina fatan ganin annabi haka."
Wata ajiyar zuciya ta sauke marar dad'in sauti tace "Tashi kije, amma kar kiyi nisa dan zan buk'ace ki."
Tashi tayi ta fita ita kuma ta d'auki waya ta kira waziri, yana danna ok ya sake danna wurin nad'ar duk maganar da zasuyi kafin yayi magana, cikin tashin hankali tace "Waziri ka ce na bar komai a hannunka, amma gashi kana neman ka mana kwance da aiki, ko kasan cewa takawa ya nemi ganin liman? Yanzu haka suka turakarshi."
"What!" Cewar waziri, sausauta murya yayi yace "Ki gafarce ni uwar d'aki, yau ba sai gobe ba zan miki maganin matsalar nan."
"Ka tabbatar?"
"Na baki tabbacin haka." D'if ta kashe wayar, sai lokacin kuma ta tambayi kanta "Amma me yasa baki tambayeshi meye zaiyi ba?"
Shiru tayi tana tunani kafin daga bisani ta d'aga kafad'a irin bai dameta ba tare da cewa "Koma me zaiyi indai zaisa a fasa auren kuma naga yarinyar can Ameera cikin garari to hakan ya isheni."
A wajen takawa da liman kuma sun jima suna tattaunawa kafin ya mishi maganar neman auren Safiyya, nan liman ya nuna mishi ba komai ya kuma gamsu da bayanan takawa, amma duk da haka saida yace idan har akwai matsala to gwara abar maganar, takawa ya nuna mishi babu komai kawai suyi musu fatan alkairi, da haka takawa ya nemi alfarmar a d'aura auren nan kusa, amma liman yace a bashi lokaci dan sanar da mahaifiyar yarinyar da ita yarinyar kanta, cikin mutumta juna suka gama tattaunawarsu liman ya bar takawa lafiya.
Bayan tafiyar liman haka kawai takawa ya nemi ganin duka iyalin na shi a turakarshi, nan suka hallara uwaye da 'ya'ya maza da mata, nasiha ya dinga musu da gargad'i da jan kunne akan rayuwa, daga bisani ya musu addu'a tare da jadadda musu rik'o da zumunci, kar su yarda su bari mulki ko abin duniya ya shiga tsakaninsu, da haka kowa ya tashi ya koma inda ya fito suka bar takawa lafiya k'alau.
Wannan ganin shine na k'arshe da suka mishi da numfashi a tare da shi, domin kuwa waziri ne ya biya wasu yan daba guda biyu sukayi shiga irinta fadawan gidan aka shigo dasu gidan a motar dreba ta kai yara makaranta, wajen takawa suka shiga suka taushe mishi kai da pillow har saida ya daina numfashi, tunda asuba kuma aka farga da rasuwar takawar, liman daya zo masallaci da k'arfin gwiwar sanar dashi kowa ya amince, kuma bayan nan yayi istikhara kan lamarin, duk da ubangiji ya nuna mishi wani duhu a cikin abun amma kuma hasken dake ciki shi yafi yawa, dan haka ya zo da niyyar idan sun gama sallah ya fad'a mishi ya amince ko juma'ar da zata zo ma za'a iya d'aura auren ba damuwa.
*Abuja*
Tunda asuba da sukayi sallah sukayi karatu suke zaune falo cikin raha da k'aunar juna, Abbas ne ya kalli Raihan yace "Mama na wai har yanzu sakamakon na ku bai fito bane?"
Cikin sakin fuska tace "Dady yau zai fito, anjima kad'an zamu je mu dubo."
Kallon Abdul yayi yace "Abdul, anjima ka shirya zamu fita tare da kai a motarka."
Da girmamawa ya amsa da "Ok Dady, zuwa k'arfe nawa?"
Kallonshi Abbas yayi yasan ya tambaya ne dan ya shirya kafin lokacin, dan haka yace mishi " 08:00 pm."
Jinjina kai yayi yace "Ok Dady."
Cike da kunya Raihan ta kalle shi tace "Dady, alk'awarin mu?"
Da mamaki yace " Wane alk'awari kuma nayi mama na?"
Sanda kanta tayi k'asa cikin kunya tace "Dady u promise me zaka fitar damu abroad idan result d'in mu yayi kyau."
Murmushi yayi yace "To banda rigimar mama na ai result d'in bai fito ba, ki jira ya fito sai mu gani."
Cikin sangarta tace "Dady gaskiya mun fasa zuwa abroad d'in, mu *Niger* muke so mu tafi."
Murmushi yayi kafin yace wani abu Ammie dake zaune tace "Shawara mai kyau, kinga kenan lokaci yayi da zaku kaiwa auntynku ziyara."
Rauda ce da sauri tace "Wace auntynmu kuma?"
Hararanta Ammie tayi tace "Husna da zatayi aure niger ba dalilin auntynku dake aure a can bane ita ma harta samu miji a can."
Cikin yanayin na tuno Rauda tace "Ohhh hakane fa, ki ce aunty *Khairiya* ('yar Bakura yaya ga Husna), gaskiya indai hakane aunty Raihan zanje tare da ke nima na ga niger."
Cikin ruwan sanyi Raihan tace "Babu inda zaki bini yarinya, ki jira idan auren Husna ya tashi saiku tafi tare da Ammie."
Abbas ne yace "To ai ko ke baza ki ba sai auren ya tashi, in ya so daga basraba saiku wuce niger d'in."
Turo baki tayi tace "Amma dai Dady za'a baro ni can wurin aunty Khairiya ko?"
Mik'ewa yayi yana fad'in "U have a choice." Ganin ya nufi kitchen yasa Khalifa cewa "Dady kayi b'atan kai, nan fa madafa ce."
Juyowa yayi yace "Wajen matata zanje, dukanku nan kun manta da ita tana can tana faman girka mana abinda zamu ci."
Dariya Khalifa yayi ya d'ago mishi yatsa irin ๐yace "Fatan alkairi Dady, amma fa banda fad'a kuma, kar ku zo ku rikice mana sai munje rabo."
Dariya Abbas yayi ya mishi dak'uwa yana fad'in "Hancin ubanka Imran."
Yana bud'a k'ofar kitchen d'in Harira ce ya fara hangowa suna ta kai da kawowa, wani bak'in ciki ne yaji ya taso mishi tare da tuna abubuwan da suka faru a baya, k'aramin tsaki yayi ya juya zai fita sai kuma Sameera ta juyo, murmushi ta sakar masa ta mik'awa Razeena had'in kabejin da tayi tace "Ki saka a fridge kafin a kammala sauran."
Karb'a tayi ita kuma ta juya wajenshi tana ci gaba da murmushi harta isa tana fad'in "Barka yallab'ai, har kun kammala karatun?"
Hannunta kawai ya kama ya nufi wajen cin abinci da ita, Harira na ganin haka cikin dubara ta aje aikinta ta bi bayansu, dan dama ana aikin banda hararan Sameera babu abinda take tana ayyanawa a ranta wai ita ce mai bayar da oda a duk fad'in gidan nan, lab'ewa tayi tana jin me suke fad'a, Abbas ne cikin rashin son magana yace "Sam, dan Allah me zai hana ki sallami yarinyar can? Idan taimakonta kike so kiyi why not ki bata kud'i tayi sa'a, amma dai ta bar gidan."
Da mamaki tace "Why? Me tayi kuma yanzu?"
K'ura mata ido yayi yace "Tambayata ma kike? Kinga, ina so ne nasan zaki iya sallamarta ko kuwa?"
D'an had'e fuska tayi ta turo d'an bakinta gaba tace "Please sir forget about Harira, mun riga da mun gama maganar nan fa, kuma fa ni bance kai zaka biyata kud'in albashinta ba, so dan Allah ka manta kawai."
Wani kallo ne ya mata baki bud'e sai yayi kamar zai girgiza kai sai kuma ya fasa, wai Sameera ce ke fad'a mishi ai ba shi zai biya mai aiki ba, sai lokacin ya girgiza kanshi tare da sakin mamakin dake kan fuskarshi yasa hannu ya shafi yalwataccen gemunshi yace "Ok, duk abinda kikayi d'aya ne, amma ki sani duk abinda zaije ya dawo babu ruwa na ni."
Da k'arfi ya fara takawa da nufin tafiya b'angaren shi, da sauri ta rik'e hannunshi a lokacin kuma Harira dake lab'e harta koma kitchen, kafeta yayi da ido fuska ba annuri, ita kam cikin kwarkwasa tace "Do something now, ka samu kayi wanka kafin ka fito na had'a maka break a part d'in ka, dan bana son yara ma su dameka."
Fizge hannunshi yayi yana fad'in "Sai me? Ina ruwanki idan sun dame nin?"
Juyawa yayi zai fice ta bishi da murmushi tana fad'in "Kayi wankan fa, yanzun nan zan kawo maka break d'in."
Juyowa yayi harda dafe k'ugu yace "Mayunwaci ne ni? Kinga yunwa a jikina ne?"
Gimtse dariyarta tayi ta girgiza mishi kai alamar a'a, saida ya sake juyawa tace "Allah dai ya huce zuciyar mijina."
Cak ya tsaya ba tare daya juyo ba, wato ta mayar dashi wani shagirigirbau, sake rik'e k'ugun shi yayi ya juyo yana kallon cikin idonta ya nunata