Showing 126001 words to 129000 words out of 325849 words

Chapter 43 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

532

Middle Ads

motar, maganganun Ummy ne kawai ke dawo masa a k'wak'walwa, awa d'aya da rabi ya d'auka a wurin nan kamar mai bacci kafin wayarshi ta fara ruri, saida kiran ya tsinke aka sake maidowa kad'ai ya taso daga kwanciyar da yayi ya d'auki wayar, a zuciyarshi yace "Abdullahi kuma? Meyasa zai kirani a wannan lokacin?"

Tsaki yayi saboda wata zuciyar data fad'a masa watak'ila zai maka k'orafine saboda baka je d'aukar amarya ba, d'auka yayi ya d'ora a kunne yayi shiru, daga can b'angaren Abdullahi yace "Ammar yane? Kana cikin gari ko kana gida?"

Can k'asan mak'oshi yace "Lafiya?"

Abdullahi ne yace "Lafiya ba lafiya, dama a cikin yan matan amarya ne aka bar wasu basu samu komawa tare da sauran mutane ba, kuma gashi duk wanda na kira wallahi wasu ma sun fad'a min kai tsaye ba zasu iya dawowa d'aukar su, ni ma kuma mota ta tun safe tana hannun k'ane na, yanzu haka nafi awa d'aya ina jiran adaidaita sahu ko taxi na samar musu amma wallahi shiru, gashi dare na k'arayi shiyasa nace bara na kiraka dan Allah ka zo ko Hamna ka d'auka, tunda kaga gidanku ba bari fitar dare ake yi ba inba da dalili mai..."

Ammar ne ya dakatar dashi cikin sanyayyar murya yace "Ya isa haka dan Allah, magana ba tsayawa ba numfasawa, yanzu kenan nufinka naje na zama drebata na d'auko ta? Bayan kuma a gida babu wanda ma yasan da fitarta, to ba zan iya ba."

Abdullahi ne yace "Dan Allah Ammar ka taimaka, bana so ne ta shiga matsala a dalilin halartar bikin nan nawa, dan Allah."

Tsaki yayi ya kashe wayar, hakan kuma yasa Abdullahi yarda d'ari bisa d'ari cewa zai zo, dan haka ya ci gaba da tsayuwa a bakin titin, ai kuwa baifi minti ashirin ba saiga motar Ammar, dan dama yasan gidan da jimawa dan anjima ana ma gidan tsare tsare tsare da tanadi, k'arasawa sukayi k'ofar gidan Abdullahiya shiga ya samu su Hamna cirko cirko su biyar a farfajiyar gidan, Hamna ya kalla yace "Hamna ki taso ga Ammar nan zai tafi dake."

"Wa!? Ta fad'a da k'arfi tana zaro ido ta d'ora da "Waya fad'a mishi ina nan? Meyasa sai yanzu ya zo bayan ban ganshi d'azu ba?"

Abdullahi ne yace "Yanzu dai ba lokacin magana bane ki taso ku tafi kafin ya mana tijara ni dake."

Mik'ewa tayi tace "Ina zuwa." Cikin d'akin ta shiga ta samu amaryar tare da babbar yayarta tana k'ara gyara mata d'aki, uwar d'aki suka shiga Hamna tace "Dan Allah k'awata taimako zaki min."

"Taimakon me kuma k'awata?" Cikin fargaba tace "Yah Ammar ne ya zo d'auka ta, kuma jiya ma a wurin kamun ku saida ya min fad'a kan fita babu hijabi, shine nake so dan Allah ki ara min ko da babban mayafi ne, insha Allahu gobe idan na taso daga école zan biyo na kawo miki."

Murmushi tayi ta nuna mata wurin kayan tace "Besty akan wannan ne har kike cewa wani taimako? Ki duba ga kayan nan sai ki zab'a."

"Yawwa." Ta fad'a tana bud'a wurin kayan, wani babban mayafi ta d'auka wanda ya dace da kayan nata, ita kanta data kalli madubi sai taga tafi kyau da kamala, sai ta ganta kamar wata amaryar ita ma, fitowa tayi zata fita sauran k'awayen suka ce ai ba zata barsu ba, tare suka fito inda ta zagaya zata shiga motar, da kallo ya bita har ta shigo, amma take jikinshi ya bashi wannan ba mayafinta bane, cikin lallami Abdullahi ya zuro kai yace "Abokina ka taimaka ka aje wad'annan ma mana, in kayi haka zaka samu lada fa."

Kallonshi yayi fuskar nan a d'aure yace "Me zai hana ka basu makwanci a gidan naka? Ai sabgaka suka zo? Ni munyi da kai zan zo d'aukar maka mata ne?"

Murmushi Abdullahi yayi yace "Ba haka bane, amma dai ka taimaka."

Mayar da kallonshi yayi kan titi yace "Kasan zasu rage maka jin dad'i kenan? Shine ni ma zaka takura min."

Kallon yan matan yayi da suka saki baki suna kallonshi yace "Ku muje."

Da sauri wuka bud'a suka shiga suka zauna, ko kallon Abdullahi baiyi ba ya ja suka wuce, saida sukayi tafiya mai nisa babu mai magana kafin ya daidaita madubin gabanshi yana k'arewa yan matan kallo, a ranshi yake k'yamar irin shigarsu kamar ba yaran musulmi ba, babu wacce babu k'arin gashi a kanta da muguwar kwalliya ta d'aukar hankali, girgiza kai yayi ya juya ya kalli Hamna, sai kace wata malama k'wafa yayi ya ci gaba da tuk'i, sunyi nisa muryar d'aya daga cikin yan matan tace "K'awa Hamna da kina da yaya kyakyawa haka shine bamu sani ba?"

Wani buhun haushi ne ya tasowa Hamna, tasan halin k'awarta dan haka ta d'aure fuska ta kalli Ammar da yake tunanin kalar iskancin da zai tatawa yarinyar, tab'e baki tayi a zuciyarta tace "Wai kyakyakwa, humm."

Ammar kuma juyawa yayi zai kalli k'awarta ta sai kuma ya ga ita sai wani had'e fuska take, kallon gabanshi yayi hakan yasa k'awar cewa " Yayanmu mun gode fa daka d'auko mu, dan har mun fara tunanin k'aryar da zamu fad'a a gida zuwa gobe."

Cike da shak'iyanci yace "Karki damu, ai mace irinki tafi k'arfin ta rasa mai sa'ar da zai d'auko ta, ni ne da godiya."

Fasa mata kai yayi da wannan maganar tashi, sai kawai tace "Nagode, amma nima sa'ata ce ace na shiga motarka har muna musayar yawu da kai."

Tsaki sukaji wanda yasa shi kallon Hamna da tayi tsakin, to na meye? Haka kawai taji ranta na b'acewa sai kumbura take, kamar Ammar yasan me take ji a zuciyarta sai kuwa ya biyewa k'awar suna ta hira, saida aka kawo inda zasu sauka tace "Mai kyau zaka iya aje ni anan ma."

Da murmushi yace "To mai kyau." Pakawa yayi su biyu suka sauka ya zuro kanshi yace "Bansan nawa ne farashin lambar wayarki ba, amma zan so ki fad'a min komai tsadarta zan biya dan a bani."

Cike da duniyanci tace "Farashinta mai tsadar gaske ne, amma kai na musamman ne, dan haka kawo wayarka na saka maka kyauta."

Cikin fara'a ya mik'o mata wayar yace "Ina godiya da wannan karamcin."

Tana cikin saka masa tace "Ai karrama mai karamci yafi k'arfin iyawata ni kad'ai, kai babban mutum ne."

Saida ya saci kallon Hamna yayi murmushi yace "Kinsan ba kowa yake gane girma da darajarka ba, wasu idan sukaga suna rayuwa tare da kai sai su mayar da kai kamar abun banza."

Bashi wayar tayi ya amsa tana fad'in "Ka rabu da su kawai, zasu fahimta ne a sannu duk ranar daka mallaki wacce zata dinga nuna musu darajar taka."

Wani murmushi yayi na iskanci yana goge lambar yayin da ita kuma take tunanin yana saka lambar ne a wayarshi yace "Ke wasu fa mahaukata ne basa fahimta duk yanda zakiyi da su, ki barsu da shan kayan ruwa kawai suna cika musu mafitsara."

Dariya tayi sosai yayin da sauran kuma sukaji kunya, kamar tasan da Hamna yake sai cewa tayi "Barta kawai, zan dinga fahimtar da ita matsayinka ko ta fara ganin girmanka."

Ammar ne yace "Amma zan iya sanin adadin matakan tsaron dake gidanku? Domin idan na tashi zuwa nasan irin shirin da zanyi."

Murmushi ta masa tace "Ka zo duk sanda kake so, zaka samu k'ofa a bud'e."

Da wani yanayin shegantaka yace "Allah ko?" Ita ma a salon wayewa ta marmad'a masa ido, hannu ya zuro ya bata da niyyar su gaisa yana fad'in "Saina kiraki mai kyau."

Bashi hannu tayi wanda yasha akaihu zargama zargama ita ma suka gaisa tace "Sai na jika mai kyau."

Kashe mata ido yayi ba tare daya saki hannunta ba yace "Za dai ki jini a waya mai kyau, amma jina ai sai bayan aure."

Murmushi tayi harda sunkuyar da kai tana d'an matsa hannunshi mai laushin gaske tace "Har kasa na fara tunanin kaina a matsayin matarka."

Kallon wannan mahaukaciya ce ya mata yace "Ni fa tunda na ganki nake jin ina k'amshin lalle."

Cikin b'acin rai da jin kamar ta rufe shi da duka tace "Dan Allah ni muje ka kaini gida na gaji da jin wannan zancen na ku."

Juyowa yayi ya mata wani kallon zan ma ci ubanki ne yarinya, kawar da kai tayi shi kuma ya saki hannun k'awar ta ta yana fad'in "Saida safe."

Jan motar yayi suka wuce har saida ya aje sauran ma kafin suka d'auki hanyar gida, babu mai magana ko kallon wani har suka kusa isa gida, a daidai su sha kwana motar police ke nan da alama wucewa zasuyi motar ta samu matsala, haka kawai wani police ya tsayar dasu, tsayawa yayi ya sauke madubin motar yana kallonshi daga shi har shi kowa fuska babu annuri, police d'in ne yace a harshen fransanci " Malam daga ina haka a daren nan?"

A hankali Ammar ya kalli agogon hannunshi k'irar gucci ta fata, ganin duka yanzu ne k'arfe *11:18* na dare yasa ya kalleshi yace "Daga inda ka aike mu mana."

Da alamar tambaya police d'in yace "Me? Malam wace irin amsa ce haka? Tambayarka muke daga ina kake?"

"Amsar kenan na baka, akan me zaka tare ni yanzu kana tambayata daga ina nake?"

Hassala yayi yace "Wai waye kai da zaka ce ba za'a tambayeka ba? Kafi k'arfin doka ne ko me? To fito daga motar sannan ka bamu takardun motar."

Murmushi yi wanda har yasa Hamna tsorata dan tasan k'aramin aiki ne yayi bala'i da shi yasa su kwana a gark'ame, murfin motar ya kama zai fito yana fad'in "Bara na fito kaga tsawo na to."

Cak ya tsaya saboda hannunshi da Hamna ta rik'e, yana kallonta ya ga hawaye har sun cika idonta, cikin rawar murya tace "Dan Allah ka basu takardun mu wuce."

Fizge hannunshi yayi yace "Sake ni dallah, ni zai nunawa wannan k'azamin kakin nashi, waye shi da har zai tambaye ni waye ni? Bari na nuna masa daidai nake da shi, uban wa ma ya bashi damar tsayawa nan d'in."

Zai fito ta sake rik'e rigarshi hawaye suka zubo mata tace "Dan Allah fa nace yah Ammar, ina jin tsoro."

Da k'arfi ya kawar da kanshi daga kallonta saboda jin zafin ganin hawayenta da yayi, police d'in dake tsaye ne yace "Kai nake jira ai ka fito, madame ki barshi mana naga me zaiyi, naji kana fad'in wai k'azamin kaki na, to fito na nuna maka k'arfin ikon kakin nawa."

Cikin hassala da k'ufula ya daki sitiyarin motar da k'arfi, yana son ya fita ya nuna mishi bai tsoronshi sai dai ya kulleshi, amma kuma baya son ganin Hamna cikin damuwar nan, ganin hawayen ta ma yasa shi jin babu dad'i haka yasa shi dole ya juyo ya kalle shi ya saisaita nutsuwarsa ya k'ak'aro murmushin na ganeka kuma zamu had'u ya masa yace "Yallab'ai, ka barmu mu tafi mana, madame d'in nan rigima ce da ita, kasan mace mai ciki saurin hawa."

Jin haka sai police d'in ya k'ara jin wata izza ai sai yace "Kawai ka fito daga motar ka bamu takardunka, yo har mu zaka d'auka wasu sakarkaru har kake fad'a mana magana, yau zaka gani."

Kallon Hamna yayi ita ma ta mishi kallon taimaka ka basu dan Allah, hakan yasa yace mata "Akwai takardun, amma wallahi ba zan bashi ba."

D'aya daga cikin wanda suke tare ne yana duba motar ya matso yace "Ya dai? Lafiya?"

Kafin police d'in yayi magana Ammar yace "Abokina wannan mutumin ne ke son b'ata min lokaci, to wai halan baya da aure ne? Inba haka ba ai da zai fahimci larurar da kan iya saka miji fitowa a dare kuma tare da iyalinshi, ka ganta nan."

Ya fad'a yana nuna mishi Hamna da gabanta fad'uwa yake ido taf da hawaye ya ci gaba da cewa "Tun sallah isha'i ta sani zagaye garin nan da neman wani wai karas, na fad'a mata yanzu ba lokacin karas bane amma ta k'i yarda, kai har karas d'in da Allah ya hore min na ce ta gatsa ☹️ amma tace bai mata ba, da k'yar na samu yanzu na lallab'a ta ita da d'an baba na siya mata alewa zamu koma gida, yanzu gashi kasa min ita kuka, domin Allah haka ya dace?"

Jami'in da yaga Ammar daban ne da mamaki yace "Dan Allah me sunanka?"

Murmushi ya masa yace "Ammar, Ammar Hassan Gaga."

Zaro ido yayi ya bashi hannu yace "Abokina kace yan biyun lieutenant ne? Ah masha Allah, zaku iya tafiya kawai, Allah ya tsare Allah ya raba lafiya."

Hannu ya bashi suka gaisa kafin ya kalli waccen yana hararenshi suka wuce, suna tafiya ya kalleta ya mata rank'washin tsiya a kai yana fad'in "Shegiya yanzu baga anfanin saka babban mayafi ba, da wannan shegen siririn ne a jikinki da yanzu tayaya zan iya kallonki na ce matat..." Sai kuma yayi shiru, turo baki tayi gaba ba tace komai ba har suka isa gida, saida suka tsaya sun fito a tare suka nufi hanyar b'angaren su, tana daf da shiga falon ta juyo ta kalleshi tace "Allah ya isa rank'washi na da kayi."

Juyowa yayi hakan yasa ta arta a guje tayi falon, girgiza kai yayi a ranshi yace "Ai zamu had'u ne, zan miki horon da har ki mutu ba zaki manta dani ba."

Tana shiga falon ta tsaya das saboda Hajia data samu zaune kan kujerarta fuskarta a had'e sai kuma Ummy da Zeinabu gefenta da alama fad'a ta musu ke take musu, ko kuma dai tuhumarsu take, cikin tsananin fad'uwar gaba da sanyin jikin ta tako zuwa tsakiyar falon, murya k'asa k'asa tace "Assalama alaikum."

Kallonta kawai sukayi amma babu wanda ya amsa, nufa hanyar da zata sada su da d'akin su tayi, a hankali Hajia tace "Zo nan."

Kamar wacce k'waiya fashe ma a ciki haka ta taho ta durk'usa gabanta kanta k'asa, tsaye Hajia ta mik'e hakan kuma baisa Hamna yunk'urin kare kanta ba dan bata san Hajia da saurin hannu ba inba abu ya kai mak'ura ba, bata ankara ba taji saukar yatsu biyar, tana dafe kunci ta d'ago ta kalleta yayin da Hajia kuma tace "Ke har ni zaki mayar wata mahaukaciya a gidan nan, ina cikin gidan nan amma kike nema kiyi rayuwar da kika ga dama, me kike so ki zama Hamna? Yar iska? So kike ki zama kamar uwarki kenan? To baki isa ba wallahi, yanzu fad'a min a cikinsu wacece tasan da fitarki a gidan nan?"

Ta fad'a tana nuna su Ummy, Hamna kuma babu abinda ya mata zafi kamar cewa wai tana so ta zama yar iska kamar uwarta, kenan mahaifiyar tasu ce yar iska? Lallai ni na jawa mahaifiyarmu wannan wulak'ancin, tsawa Hajia ta mata tace "Dake nake magana kina jina."

Kallonsu Ummy tayi ta girgiza kai tace "Basu san fita ta ba."

Cikin masifa tace "To gidan ubanwa kika je? Me kika je yi da baki dawo ba sai yanzu? Hamna kina 'ya mace ace ba kya cikin gidanku kina waje, to me kikeyi? Kuma ba a motonku kika fita ba, kenan wani ne ya zo ya d'auke ki kuma ya dawo dake."

Kallonta Hamna tayi tace "Wallahi Hajia adaidaita na shiga, kuma wurin kan amarya ne muka tafi, nasan idan na tambaya ba za'a barni ba shiyasa, kuma ki tambayi yah Ammar kiji tare ma muka dawo yanzun."


Kallonsu Ummy tayi tace "Ku b'ace min da gani ku Allah ya taimake ku." Tashi sukayi inda ita kuma ta koma ta zauna tana kallonta tace "Tare da Ammar?"

Kai ta gyad'a alamar eh, amma me Hajia za tace sai cewa tayi "To na sani ko tare dashi kuke yawon iskancin na ku, dan ni ban yarda dake ba, shi kuma dama idonshi tsakar kai suke ba kunya ne dashi ba, yanzu idan na kira shi zai iya fad'a min abinda ya faru tsakanin ke da shi."

Mamaki ne yasa Hamna kallon Hajia kawai ta kasa cewa komai, hakan yasa Hajia cewa "Je kirawo min shi, dan wallahi ko iskanci kuke yau saina kawo k'arshen shi a gidan nan, watak'ila dama wannan dalilin ne yasa kika k'i amince da auren nan."

Mik'ewa tayi ta fita jiki a sanyaye da tunanin halin kakarsu, tana zuwa k'ofar d'akin ta tsaya dan tana jin hayaniyarsu, sallama tayi Amar ya amsa, ba tare data shiga ba tace "Yah Amar Hajia ke son ganin yah Ammar yanzu."

Amar ne ya amsa da "Yana d'aki bari na fad'a masa." Juyawa tayi ta fita shi kuma ya shiga ya fad'awa Ammar, fitowa yayi babu ko riga zai fita Junaid yace "Haka kuma za'a tafi wurin Hajiar?"

Ko kallonshi baiyi ba yace "To ko nine Hassan meye a ciki? Ba haihuwarmu tayi ba? Tunda ita ko dare da Allah yasa mana mu samu nutsuwa a cikinshi bata bari mu nutsun ai sai mu fara zuwa mata tsirara inta neme mu."

Jibril dai da abun duniya ya isheshi da kallo kawai ya bishi, ai kuwa yana shiga Hajia ta kalleshi da wani mamaki, zaune yayi kujerar dake kallonta ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya wanda hakan yasa suke iya ganin kwantaccen gashin k'afar shi mai silb'i, ido cikin ido ya kalli Hajiar yace "Mutan makka gani, ance kina kira na yanzu a daren nan, shine nace bara na zo da gaggawa kar azo ko zuciyar ce ta fara bugawa ba daidai ba."

A murtuke ta kalleshi tace "Duk maitarka wallahi zuciyata tafi k'arfin ka nuna k'warewarka a kanta, shege kenan burinka kenan a kai na."

Murmushi ya mata na shegantaka yace "To in kuwa hakane baki shawara mana? Ki rage b'acin rai da sakawa mutane idanu, ki dinga samun isashen bacci hakan zaisa ki dinga samun nutsuwa, sannan ki rage yawon surutu da hayaniya, inba haka ba Allah in kika bari zuciyarki ta kamu da ciwo da hannu na zan parkaki na fito da zuciyar na 'yar da ita."

Murmushi Hamna tayi harda rufe baki inda Hajia ta gama cika, cikin fad'a tace "To yanzu wace rashin d'a'ar ceta saka shigo min falo babu riga?"

Murmushi ya mata yasa hannu ya shafi k'irjin shi har zuwa kan nonon shi yace "To dan kin kalli wannan meye? Ko jariri dai ba zai iya tsotsar wannan ba, kuma ma Hajajju me kike tsammani dama ga marar mata wanda yayi shirin kwanciya."

Tsaki tayi yayin da Hamna ta sunkuyar da kai kamar tace k'asa bud'e na shiga, tana mamakin wannan rashin kunya tashi ita kam, a nutse ta kalleshi tace "Wannan take fad'a min wai tare kuka shigo

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login