Showing 240001 words to 243000 words out of 325849 words

Chapter 81 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

587

Middle Ads

damuwar duk daya shigo dasu, saida ya gyara murya ya saitata ya lumshe ido yace "Ok, ci gaba."

Jiki a sanyaye ya juyo ya fito, yanda ya barta ya sameta tana ba wa *Khairat* nono, kusa da ita ya matsa ya tsaya gabanta yana ma yarinyar magana, tana jin muryar babanta tayi tsal ta diro daga kan cinyarta ta mak'ale mishi, d'aukarta yayi duk da bata cikin yanayi mai kyau yarinyar, dan kayan jikinta ma basu da kyan gani sai k'arnin nono take, zaune yayi kujera mai fuskantarta ya d'ora Khairat kan cinya ya kalleta da kyau yace "Umaimah, domin Allah in zaki fad'i gaskiya kina ganin haka ya dace kuwa ki tura yarinya har d'akin bacci na wai ta gyara min? Ke kuma gaki zaune ba kya komai."

Cikin fad'a fad'a tace "Bana komai fa kace? Yanzu baka same ni ina bawa yarka nono ba, ko shi ba aiki bane? Yanzu haka girki na kan wuta ban sauke ba, kuma kafi kowa sanin ina da aikin yi tunda ba zaune nake gida ba, dan lokacin da zan dawo gidan haka kawai saina kashe kaina wajen bautar gyaran gida."

Wani kallo ya mata yace "Kashe kaine ke a ganinki?"

Kawar da kai tayi tana jan tsaki hakan yasa ya girgiza kai yace "To kiji da kyau, indai har ke baki da lokacin gyara min d'aki na karki k'ara baiwa kowace yarinya damar shiga d'aki na dan ta min gyara, inhar kinsan ba zaki iya ba ki ban makullin d'akina dana baki saina dinga gyarawa da kaina, kinji na fad'a miki."

Yana fad'a ya mik'e da Khairat suka fita daga d'akin, mik'ewa tayi ita ma zuwa madafa tana fad'in "Masifaffe kawai, sai kace wani tsohon daya gaji da duniya, ka k'i tamnuwa ka k'i had'uwa kullum da b'acin ranka nake kwana, duk abinda nayi banyi daidai ba."


Yana shigowa da sallama yaran biyu suka tafi a guje suka rumgume shi, kan Huda ya dafa yace "Beby ya kike?"

D'aukar *Abdul maleek* yayi ya kamo hannunta suka zauna, Jamila data zubo ma Huda abinci ce cikin jin haushin yarinyar ta aje mata kwanon k'asa tace "Ke."

Juyowa Huda tayi ta kalleta, shi ma idon ya sakar mata inda ta nuna mata abincin tace "Wuce ki zauna ki ci abinci ki je ki kwanta, na gaji da hayaniyar nan ba zan d'auka ba."

Cikin sanyin jiki ta nufi inda ta nuna mata ta zauna, girgiza kai kawai yayi ya mik'e ya aje Abdul ya shiga d'akin shi, bin bayanshi tayi ta fara taimaka masa wajen cire kaya ya dakatar da ita ta hanyar fad'in "Jamila me yasa ba kya sakin fuska ga yarinyar nan? Ita ma kamar 'yarki ce."

Kallon idonshi tayi tace "Ba dai 'yata ba yarka ce, da ta hanyar aure aka sameta zan iya mata wannan gatan."

Girgiza kai yayi ya nufi ban d'aki hakan ya b'ata mata rai tace "Wai meye haka? Shikenan kullum mun dinga samun matsala da kai akan waccen yarinyar, akan me zata shiga rayuwarmu tana neman hana ni jin dad'in rayuwa, duk abinda nake mata baka gani?"

A hassale ya juyo yace "Me kike matan? Kina mata sutura ne ko kuma ke kike mata wanka, ke kike nemo abincin da take ci? Dafawa ne kawai naki, kina biyan kud'in makarantar ta ne ko kuma ke kike kaita? Ko kaya wannan kina saka mata? Yarinyar nan a gidan nan take rayuwa, amma ba'a b'angaren nan ba, saina nemi alfarma wajen Mama kad'ai take bani ita ta zo nan ta kwana, baki tab'a wahala da ita ba na d'ai rana, amma har ki bud'a baki ki ce min wai duk abinda kike mata, to wace tsiyar kike mata bayan nuna mata k'iyayya kuma a gabana."

Juyawa yayi zai shiga tace "Yanzu a kanta ne kake d'aga min murya haka?"

Sake juyowa yayi yace "An d'aga miki kiyi abinda zakiyi?"

Saida ta matso kusanshi tace "Kasan ina da abunyi da dama, amma ina so ya zama na k'arshe ne wannan, dan haka in ka gaji da zama dani ka ban takardata na tafi gidanmu, ni kaina na gaji da wannan auren."

Saida ya mata murmushi yace "Kije, da safe zan aiko miki da ita, yanzu banda lokacin rubutu."

Hararanta yayi sama da k'asa ya shige ciki, jingina yayi a jikin bango yana sauke numfashi, yana son zama da Jamila sosai fiye da yanda take tunani, amma bai tab'a tsammanin raini irin haka zai shiga tsakaninshi da ita ba, sam yanzu bata ganin girmanshi, kuma yana b'oyewa ne dan baya so iyayensu su sani, amma ta fara kaishi bango.

Jin ta buga k'ofar d'akin da k'arfi yasa shi fitowa shi ma da sauri ya bi bayanta, ko kallon Abdul ba tayi ba da Huda ke bashi abinci ta fita da mayafinta, da gudu gudu ya bita yana kiran "Jamila saurare ni, Jamila, dake fa nake magana."

Tana bud'a k'ofar b'angaren nasu daidai Ammar ya fito daga nasu b'angaren, tsayawa tayi da niyyar ya wuce saita shige ita ma, amma saiya tsaya yana musu kallon tuhuma, Jibril ya kalla yace "Lafiya kake gudu kai kuma? Ina zaki je?"

Ya jefa mata tambayar yana kallonta, sunkuyar da kai tayi gabanta na d'an fad'uwa, Jibril kam yana ganin Ammar yaji sanyi dan yasan babu inda zata je, ai bai tsaya b'ata lokaci ba yace "Yah Ammar wai ita nan fa yaji ne zata yi."

K'ank'ance ido yayi ta kalleshi ya kalleta yafi sau ashirin kallon daya musu, saida ya jawo hannun Jibril ya zo kusa dashi sannan ya nuna ta yace "Yanzu kai domin Allah wannan yarinyar ce zatayi yaji kuma shine kake binta da gudu? To tayi yajin mana, barkono ma ya ci ubanshi."

Tureshi yayi baya yana fad'in "Dallah matsani daga nan." Kallonta yayi cikin tsawa yace "Kalleni nan."

Cikin turo baki ta d'aga kai ta kalleshi, saida ya kalli Junaid yace "Idan ta tafi ka je ka fad'a min, ni kuma har d'akin tanti Zeinabu zan same ki wallahi in cire miki hak'ori."

Cikin d'aga murya sosai yace "Malama wuce min ciki ko."

Da sauri ta juya ta shiga ciki tana fashewa da kuka, Jibril ya juya zai bita ya rik'oshi yace "Kai sakaran wane gari ne? Yarinyar data tashi gabanka zaka zauna tana maka iskanci, kai ala wadaran naka ya lalace."

Sakinshi yayi ya juya da sauri ya sameta shi kuma ya wuce b'angaren Hajia, dama dai har yanzu ba sallama yake yi sai randa yaga dama, Shureim dake ta wutsilniyarshi tsakiyar falon yana ganinshi ya taho da gudu kamar zai fad'i, da sauri ya d'aukeshi yana juyi dashi, kallon fuskarshi yayi yace "Ina Ummy?"

Juyawa yayi ya nuna masa k'ofar d'akinta alamar tana ciki, nufa yayi dashi suka shiga d'akin da sallama yanda ba kowa yaji ba, Ummy na zaune da wasu takardu tana dubawa ta bishi da kallo har ya tsaya gabanta, cikin tausar da murya yace "Ummy barka da dare."

Saida ta mayar da dubanta kan takardun tace "Wani abu kake so ne?"

Murmushi ya mata yace "Eh Ummy." D'agowa tayi ta kalleshi inda ya fara fad'in "Dama gobe zamu je wajen tanti Hadiza ne, shine nake neman alfarma ki bamu Shureim mu tafi dashi."

Sake d'aga kanta tayi sosai ta kalleshi, ba zata hana shi ba, amma kuma bata san me yasa kullum yake k'ara kusanci da yaron ba, saida ta sake duk'ar da kanta sannan tace "Ba damuwa, amma ka kula min da yaro na, ba zan lamunci komai ya same shi."

Murmushin gefen labb'a yayi yace "Dan na baki tabbaci akan kulawar da zan masa Ummy ba ma zan tab'a cewa shi d'in k'ane na ne ba, sai dai nace *d'ana* na fari ne."

K'uri ta masa da ido, me yake nufi? Ita ma al'amarin Ammar d'in nan wani lokacin kamar mai shafar aljanu, k'ala ba tace mishi ba sai juyawa da yayi ya fita yana d'auke dashi, suna fitowa farfajiyar Hamna ta shigo tana gyara siririn mayafinta dake kan kafad'a da jakarta a hannu, tana ganin Shureim ta saki murmushi inda shima yaron ya fara d'aga mata hannu yana son yaje wurinta yana fad'in "Ta..ta."

Da sauri ta k'araso tasa hannu d'aya ta tallabo bayan yaron da nufin ta karb'eshi, amma sai Ammar ya rik'eshi ya k'i sakar mata shi yana kallonta, a zuciyarshi yake fad'in "Oh Allah, yaushe al'amarin nan zai k'are ne?"

Kallonshi tayi tace "Malam bani yaro na mana."

Kallon daya mata yasa ta kawar da kai tana lalabar cikin jakarta, chocolate ta fiddo ta bawa Shureim tare da juya mishi kumatunta tace "Bizou."

Sumbatarta yayi hakan yasa ta mishi dariya, Ammar ta kalla ta had'e fuska, zata wuce ta barsu yace "Ke daga ina kike?"

Cikin matsanancin jin haushin yace mata ke ta kalleshi cikin d'aga murya tace "Ban sani ba, ban sani ba Ammar."

Murmushi ya mata na jin dad'in ya cikata, ta juya ya sake cewa "Ke meye sunan turaren nan naki? Naji shi kamar na yan bori."

Juyowa tayi cikin mayar da martani tace "Aljana barhaza ce iyakar borin."

Ta juya zata shige ya rik'o hannunta, cak ta tsaya amma bata juyo ba, idonta ne suka cicciko da k'walla ga fad'uwa da gabanta yayi, tsikar jikinta duk ta tashi ga jijiyoyinta da taji duk sun saki, cikin tausasa murya yace "Gobe zamu tafi wajen tanti, ko zaki je ke ma?"

Bata uya juyowa ba sai kai data girgiza masa alamar a'a, sakinta yayi zata shige yace "Tare da Shureim zamu tafi, Ummy ma ta amince."

Juyowa tayi da sauri ta kalleshi sai hawayen suka taho mata, da sauri ta matso kusanshi kamar zata fad'a jikinshi sai kuma ta tsaya, marairaicewa tayi duk tayi kalar tausayi tana matsar ido cikin raunin muryar kuka tace "Ammar ka hutar dani dan Allah da zuciyata, na gaji wallahi Allah ba zan iya jura ba, ka daure ka dinga yin nesa dani kaji."

Shi kanshi saida ya lumshe ido yanda ta k'arashe maganar, kallonta yayi da idon fahimta da kuma basira, idan ya fahimta daidai abinda ke d'awainiya dashi shi yake galabaitar da ita, to amma ya zasuyi? K'addararsu ce haka, yanda suke kallon juna ne yasa Hamna saurin kawar da kanta ta juya da gudu ta shiga ciki, saida Hajia ta bita da kallo ita dake zaune wurin, tana shiga d'aki ta fad'a kan gado ta fashe da kuka, sosai take ruzgar kuka kamar wacce aka wa mutuwa, ko wanka bata iya tashi ba saida taji wayarta na kuka, fito da iya tayi a jaka ta duba, wani Alhaji ne da yake matuk'ar sonta yake bibiyarta amma Allah yasa ta kasa bashi ajiyar zuciyarta, ba wai shi kad'ai ba akwai irinshi bila adadin da suke bibiyarta amma ta kasa bawa ko d'aya dama, aje wayar tayi ta ci gaba da rera kukanta da tunanin mafita a rayuwarta.

*Da safe* tsaf suka shirya dan tafiya, kaya kala d'aya Ammar yasa tare da yaran har Shureim, Amna ma cikin wani had'add'en leshe ta shirya kalar kwalliyar aikin kayansu, suna gaishe da iyayen suka musu sallama suka fito, har zai bud'a motarshi yaji Amna na fad'in "Yer uwa dama baki fita ba? Ai na d'auka kin tafi shiyasa ban shiga d'akinki ba."

Ko kallonta ba tayi ba tace "Amma ai da kin tambayeni da an fad'a miki ina nan ko bana nan.

Juyowa yayi ya kalleta, kamar dai yanda yanzun tafi zama yanzu ma hakane, doguwar rigar bak'in leshe ce jikinta d'inkin simple amma ya hau jikinta sosai musamman wajen mazaunanta, d'aurin d'an kwalin ma kawai tayi shi ne simple, fuskarta ma tayi fes da ita babu komai data shafa mata, amma k'amshin tattausan turarenta kad'ai zai iya kwantar maka da hankali, wayarta gyalenta da makullin mota duk a hannunta suke, Shureim ne ya tafi wajenta ta d'aukeshi tana mishi magana, matsawa tayi kusanta tace "Yer uwa idan baki da aiki sosai me zai hana ki zo muje tare, Mama zatayi farin cikin ganinmu gaba d'aya a tare."

Kallonsu tayi dukansu, Ammar k'arami ne ya zo kusanta shima yana d'aga hannu sai Amna dake mak'ale wajen Mamanta, murmushi tayi ta kalli Ammar tace "Sai dai muje a mota ta, bansan ko mijinki ya lak'a min bom d'in da zata tashi dani ba."

Kallon daya mata tare da cije leb'enshi yana wani shegen murmushi yasa ta kallon Amna dake dariya tace "Taya kike tunanin zai tasar min yer uwa, kuma ko ba komai ai ni da yaranshi duk muna cikin motar."

Motarta ta nufa tana mik'a masa makullin tace "Bismillah."

Hararanta yayi yace "Drebanki ne ni da zan tuk'a ki?"

Jefa mishi makullin tayi ta bud'a gidan baya ta d'auki yaran d'aya bayan d'aya duk ta zaunar dasu, har zata zauna ya jawo ribom d'inta daya fito waje ya shiga wajen yaran ya zauna yana fad'in "Ba inda zan tuk'aki kinji yarinya."

Cikin jin haushi ta kalleta ta cire d'an kwalin ta mayar da ribom d'inta ta d'aura kallabin, zatayi magana Amna ta zagaya wajen mai tuk'i tana fad'in "Ya isa dan Allah, zauna nan ni saina tuk'a."

Lek'owa yayi daga ciki yace "Ke duniyata fita a idona in rufe, ai da kinga kina tuk'i to ki tabbata tukunyar tuwo ce ko kuma kan gado kike kina wainani son ranki, amma ba dai mota ba."

Sunkuyar da kai Amna tayi ta dawo gaba inda Hamna ta kalleshi tayi tsaki tace "Anji sanyi ba'a rufa ba Ammar, wai kai yaushe zaka girma ne?"

Ko kallonta baiyi ba yace "Ranar dana samu isasshen nono nasha."

Wani kallo ta masa mai nuni da cewa ashe ni ce banda hankali, saida ta shiga ta zauna tana mak'ala mad'aurinta tace "Yace baya so ki tuk'a mota mana saboda yana takaicin ya siya miki."

Saida ya d'auki Ameera ya d'ora kan k'afarshi yace "To banda kud'i, yan gidan nan naku kuma kowa taurin zuciyar tsiya ne dashi, k'aramin abu baya sa zuciyarsu ta kusa tsayawa bare na samu kud'i ta hanyarsu, dubi kakar nan taku kwanan baya mun d'auka zata shek'a ne amma ta tashi da ranta kuma."

Dariya suka bushe da ita Hamna har da rik'e ciki, tayar da motar sukayi taja suka fita, tun kafin ta hau titi yace "Ke kin tabbata dai kin iya tuk'i ko? Karki zo ki jawo min mutuwa, burina nan gaba duniyata ta haifa min yara goma sha d'aya."

Kallon Amna tayi tace "Ki ce mijinki ya min shiru akwai abubuwa da nake so su zauna min a kai, dan in ya ci gaba da surutun nan na tabbata saina manta har sunana ma."

"Haka kawai malama saina rufe baki na, babu wanda ya isa ehe."

Tafiya suke sosai cikin farin ciki dan dariya kawai yake basu suna karb'a, duk yanda Hamna take son ta dake ta fita shirginshi abun ya gagara, idan yayi wata katob'arar dole take darawa, yanzun ma yara duk sunyi bacci, kallon Hamna yayi ta madubi yace "Kankana wai ina budurwata ne?"

Saida ta nuna alamar b'acin rai tace "Wallahi Ammar karka sake kirana kankana, na fad'a maka bana so ko."

Amna kuma tana juyowa tace "Wacece kuma budurwarka?"

Kallonta Hamna tayi tace "Amie, ita yake so ita kuma bata da lokacin shi, ya addabeta nima kuma ya addabeni, na fad'a masa idan ya k'ara min maganar ta zan fad'a miki dan ba zai yiwu na ci amanarki ba."

Dariya yayi ya kalli Amna yace "Ya kike kallona? Ki fad'a mata mijinki mai lafiya ne ire irenku goma ma zan iya ji daku."

Juyowa Hamna tayi baki bud'e tace "Bala'i, ire irenmu ko ire iren matarka?"

Saida ya kalli tsakiyar idonta yace "Ku nace, dukanku dake da ita da takwas kamar ku."

Sun d'auki awa d'aya a k'alla kafin suka isa dan ba gudu take ba, kamar yanda suka yi tunani kam hakane ya faru, Hadiza da Chua'ibu sunyi farin ciki sosai na ganinsu tare, sunyi walwala sunyi hira da mahaifiyarsu sosai, inda daga k'arshe Hadiza ke tambayar Hamna ya labarin aure, kamar dai yanda ta saba yanzun ma cewa tayi kawai tayi ta mata addu'a, har yanzu bata samu wanda ya dace bane, amma data samu zasu ji labarin aurenta ita ma, Amna ce ta kalli mahaifiyarsu tace "Mama wallahi tana da samari masu nutsuwa da hankali, kawai bata shirya aure bane, amma kar kiga manyan mutanen dake zuwa wajenta gida."

Cikin jin haushi tace "K'arya nayi kenan? Ina ruwanki da maganarmu? Karki koma saka min baki."

Kallon mahaifiyarsu tayi zatayi magana Hadiza tace "Dakata Hamna, inhar kinsan gaskiya ne abinda ta fad'a to kiyi gaggawar tsayar da mijin aure, Hamna ba zan ji dad'i ba yau idan kika lalata mana sunan zuri'a, duk da ba a hannuna kuka tashi ba amma Hajia zata d'ora min laifin gurb'atarki, dan haka ina rok'onki dan Allah ki fitar da miji kiyi aurenki ki huta tun kafin girma ya k'ara kamaki, mace ce ke d'an lokacinki k'alilan ne, sannan idon mutane dayawa zai iya komawa kanki duba da aikinki da kuma abinda kike hawa yanzu, ki taimaka kinji ki rufa mana asiri da ma kanki."

Saida tayi k'ok'arin had'e kukanta tace "Naji Mama."

Hararan Amna tayi da take ganin ita ta had'ata da Maman, dariya ta mata ta mik'e ta fita daga d'akin, cikin nutsuwa Hadiza ta sake kallonta tace "Hamna, ki tabbatar min da wani abu d'aya mana."

Kallonta tayi hakan yasa ta cewa "Ki kula da kanki, ki kare mutumcinki kema bar ki kaishi inda ya dace."

Kasa tsayawa sukayi sai kawai suka zubo mata, cikin tausayin kanta ta fad'a k'afar maman tana kuka, hakan ne ya tayar mata da hankali ta fara tambayarta "Hamna lafiya? Daga magana, ko wani abun ne ya faru?"

Girgiza kai kawai tayi amma ba tace komai ba, da k'yar ta rarrasheta sai ajiyar zuciya da take saukewa.

*A da* malam Rabi'u kad'ai take shakka, amma yanzu har shi d'in ta daina tsoronshi musamman daya k'ara tsufa, fita ma bai cika yi ba inba masallaci ba ko wani abu daya zama dole, a baya mai zaman kanta ce, amma yanzu bayan rabuwar aurensu da Junaid ta zama karuwar gida, tana fita sanda take so ne kuma ta dawo sanda ta ga dama, kakarta ta rasu wata biyu da suka wuce daga ita sai mahaifiyarta yanzu a gidan, bud'ewar idonta yanzu babu inda bata zuwa neman kud'inta ta dawo, mahaifiyarta ta zubawa sarautar Allah ido, dan maganarta ba dama ba sosai take fitowa ba har yanzu bare kuma ta mata fad'a sosai har ta jita, sai dai fatan shiriya kawai ta gari.

Sai bayan magriba suka shigo gari, gaba d'aya falon Hajia suka yada zango suna sauke

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login