Showing 42001 words to 45000 words out of 325849 words

Chapter 15 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

521

Middle Ads

shiga uku ni Zeituna, yau ya zanyi da kawu *Mamu*?"

Haba ai saita wuce da sauri har da gudu gudu take hannu d'aya a kai tana fad'in "Nasan ma kashe ni zaiyi wallahi, oh ni Zeituna, soyayyar wanda baisan ina yi ba na neman haukata ni."

Haba wannan mutumin da shima yake ganin ya samu abinda yake nema ai sai ya juya kan moton ya fara bin bayanta, dan in yace ya tsayar da ita ya tabbatar ba zata saurare shi ba dan alamu sun nuna sauri take, dan haka ya dinga binta har saida ta shiga wani layi dake da babban kwalbati gaban kwalbatin kuma katangu ne kawai wanda kake iya hango bukkokin ciki, d'aya daga cikin gidajen ta shiga wanda ke d'auke da bukka uku a ciki, yana ganin haka ya juya da moton shi da tunanin dawowa gobe da safe.

Shiru gidan da alama sunyi bacci sai wani dattijo dake kan tabarmar kaba kusa da wata bukka da redio yana saurare, kamar wacce k'wai ya fashe ma a ciki haka ta k'arasa gabanshi ta durk'usa cikin harshen fulatanci tace "Kawu walijam? noi chomrii (ya gajiya)?"

D'agowa yayi daga kwanciyar da yake ya sauke idonshi a kanta, kafin yayi magana ya d'auki k'aton takalmanshi na fata mai shegen nauyi ya mazga mata a fuska, Allah yasa bai sameta a kunci ba sai a goshi, taji zafi sosai dan haka ta dafe wuri ta fashe da kuka, cikin harshen fulatancin da yafi k'warewa akai ya fara zazzaga mata bala'i na daren da tayi, wannan surutun na shi yasa matarshi *Jumma* fitowa, maimakon bashi hak'uri sai ita ma ta dinga fad'in a harshensu "Ai dama na fad'a maka yarinyar nan karuwanci take zuwa, wani irin aiki ne zai tsayar da ita har wannan lokaci, ni fa tuni nayi nisa a bacci ace sai yanzu zata shigo gida, da k'ofa gare mu kenan saita bubbuga ta nunawa mak'wabtan mu ta dawo a zo a bud'e mata k'ofa, saida suka gama zageta ta uwa ta uba babu tunanin marainiya ce suke rik'o sannan 'yar d'an uwanshi sannan yace ta b'ace mishi da gani, ta tashi zata shiga bukkarsu wacce suke su uku a ciki ita da yaransu Jumma tace "Abincinki fa? Ko da yake ma ai nasan kin gama k'oshi a wajen yawon."

Cikin kuka tace "Mihari (na k'oshi)."

Kawu Mamu ne ya fara magana da hausa saidai a yanayin daya iya yace "Wane abinshi jaki bata? Ke ki shaurare ni ma da kyau kiji, wannan ishkanshin nata ya kusha karewa domin kuwa aure jan mata, janje kauyen *gwadojji* na shamo mata miji kafin ta ja min abun kunya, shannan na tsawon kwana uku ban lamunshe ki bata abincin gidan nan ba, ja ta shi ashan wajen yawon ishkanshin na ta."

Dad'i Jumma taji hakan yasa ta juya zata koma bukkarta tace mishi " Jamwala (saida safe)."

Tana shiga bukkar ba tare da damuwa ba ta cire hijabinta ta shinfid'a k'asa ko tabarma babu ta kwanta tana kallon yaran dake kan katifa duk da dai ba wata ta kirki bace, amma a wajenta da take kwana k'asa wannan d'in kamar gado ce na alfarma, tunanin iyayenta ta shiga yi wanda suka nuna mata gata da soyayya lokacin da suke raye, amma mutuwa ta d'auke su a lokaci d'aya sakamakon had'arin daya ritsa da su na mota, wani sabon kuka ta dasa ta ci ta k'oshi hata gode Allah kafin bacci yayi gaba da ita.

*Gaga's falimy*๐Ÿ˜‚

*10:30* na dare Amar dake zaune a falo suna kallo shi da duka 'yan uwan wayarshi tayi k'ara, yana dubawa ya d'auka yana fad'in "Ummy baki kwanta ba har yanzu?"

Ammar dake zaune nesa da shi kamar zaiyi kwance yana latsa wayarshi ne ya kalleshi ta gefen ido, daga wajen Ummy ta amsa mishi da "Banyi bacci ba Amar, ka ci abinci ne?"

Amsawa yayi da "Ban ci ba Ummy, bana jin yunwa ne."

"A'a ban yarda ba, maza ka shigo ka samu wani abu ko marar nauyi ne ka ci, kai baka tausayin kanka ne da halin da kake ciki? To ka zo yanzu ina jiranka."

Kashe wayar tayi shi kuma ya mik'e a gajiye yana fad'in "Ummy sai kace wani yaron goye, ni ba yunwa nake ji ba."

Junaid ne yace "To ina laifin Ummy, kulawa fa akace yabawa, ta damu da kai ne shiyasa."

Wani dogon tsaki Ammar yaja ya mik'e a hassale ya shige d'akin shi ya mayar da k'ofar ya rufe, da kallo suka bishi sai dai babu wanda ya damu bare yayi tunanin abinda yasa yayi hakan, fita Amar yayi a farfajiya ya had'u da Jibril ya dawo a matuk'ar gajiye, gaisawa sukayi kafin shi ya wuce babban falo shi kuma nasu falon.

Ammar na shiga cilli yayi da wayarshi kan gado ya fad'a ban d'aki, ba jimawa ya fito ya watsa ruwa ya kashe wutar d'akin ya kwanta daga shi sai gajeran wando, kifa kanshi yayi tsakiyar pilow yana k'ok'arin ya cire damuwar nan a ranshi, baya so abun ya dinga damunshi amma ya zaiyi mutum ne shi mai zuciya da jini, jin baccin na neman gagararshi yasa ya mik'e ya b'allo maganin bacci, a k'a'ida damuwarshi bata kai yasha guda d'aya ba, rabi ya kamata yasha, amma saboda haushi yasa yasha guda d'aya sannan ya kwanta, ai kuwa baifi minti sha biyar ba kwana ya d'auke shi marar dad'i sai dai mai k'arfi.

*Washe gari*

Kamar ibada yau ma hakane a wurin Zeituna, tana yin sallah asuba ta shiga d'ebo ruwa a panpo, layin data tarar yasa har gari yayi haske kafin ta samu ta turo kurar ruwan mai d'aukar jarka (bidon) takwas, da kanta ta dinga saukewa tana shigar da su tana juyewa a randa da tuluna da manyan bokitai, saida ta gama cas sannan tayi wanke wanke, data wanke ne ta samu ta d'ora d'umamen tuwon masara wanda miyar kukar taji daddawa, kafin yayi zafi ta gama sharar tsakar gidan, tana idawa ta zubawa duk wanda tasan tana zuba ma ta kai musu, tana dawowa babbar buta ta d'auka ta fara d'iban ruwa dan tayi wanka, amma Jumma na gani ta fito tace "Me ja kiyi da wannan ruwan?"

Cikin marairaicewa tace "Inna wanka nake so nayi , kinga fa yau kwana hud'u kenan baki barni nayi wanka ba, har Hajia ta fara min magana akan k'azantar jiki na."

Fizge butar tayi ta juye mata ruwan a jikinta tace "Ba ja kiyi ba, na ce ba zakiyi wankan ba marar mutunci kawai, ki wuce ki tafi hakanan in kuna son zuwa kafin nasa kawunki ya dakatar dake."

Cikin muryar kuka tace "Dan Allah Inna to ki bari na ci abinci saina tafi."

Da k'arfi tace "Abinci? Har abincinki ma kika fitar? To kiji da kyau jiya kawunki yace kar na sake baki abinci har na kwana uku, dan haka ki wuce ma karki wahalar da kanki."

Takawa ta fara yi cikin fitar da hawaye tana matse hijabinta wanda dattinshi yasa take sanyashi a birkice, yanzu gashi ruwan data zuba mata yasa duk wani tsohon datti da wari ya taso, ita kanta sai take jin k'yank'yamin kanta, tana zuwa ta ja kurar ruwan dake k'ofar gidan ta nufi wajen aikinta da ita, saboda tafiyar dake akwai dama yasa ta fad'awa mai kurar zata dinga kawo mishi in zata je wurin aiki, tana tafiya tana share k'walla harta isa ta aje kurar ta wuce.

*Babban gida*

Tunda asuba da sukayi sallah basu kwanta ba, yaran dama duk matasa ne suna iya shirya kansu, dan haka kowa yayi shirin zuwa islamiyya, iyayen ma shirywa sukayi sai Hamna, Amna da Jamila da kuma Umaima, zuwa k'arfe bakwai suka gama kintsawa tare da cika cikinsu, nan fa aka fito dan tafiya gayya guda, masha Allah mota shida sukayi idan aka had'a data tsaron colonel suka cika takwas, a hakan ma wai dan Amar da Ammar da su Junaid sunce sai bayan azahar zasu tafi, motar Jibril aka ce yan matan su shiga, Umaima ce ta shiga gaba tana ta wani basarwa kamar dai Hajia kakarta, Amna ce ta kama murfin mazaunin baya zata bud'e yace "Tsaya."

Tsayawa tayi tana kallonshi shi kuma ya lek'o yace wa Umaima "Malama fita ki koma baya akwai mai wannan wurin."

Cike da gadara tace "Wa fa?"

Had'e fuska yayi yace "Ban sani ba, ki fito na ce ko."

Tsaki tayi ta fito saida ta bangaji Amna kafin ta shiga ta rufe tana kallo ta ga wa zai shiga gaba, kallon Amna yayi yace "Shiga nan."

Yana fad'a ya shiga ya tayar hakan yasa Amna shiga ita ma ta rufe, sahu ya shiga da motar inda aka bud'e musu k'ofa suka fara fita, Umaima ce tace "Yanzu dan rainin hankali dama Amna ce zata shiga gaba kasa na fito daga nan? Lallai ma yah Jibril ba ka da mutumci wallahi."

Juyowa yayi kai tsaye kuma ya kalli gabanshi yace "Qur'ani in ban sauke ki ba kice d'an iska ne ni, ke ni zaki kira marar mutumci, kaji min shegiya kai."

๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚ *Fad'an na yau kuma tsakanin mace da namiji ne*

Nuna shi tayi da yatsa tace "Allah kar ka sake sheganta ni, inba haka zan maka tijara a wurin nan, kuma da kake cewa ka sauke ni, ka jima baka sauke nin ba, ko kai baka ga duk motocin dake gabanmu da bayanmu na gidansu ubana bane."

Cikin tashin hankali yace "Na gode Allah da yasa akwai motar ubana a ciki, na kuma yi farin ciki daya zama ubana ba matalauci bane bare ace yana zaman kawai ne a gidan na ku, kuma Allah kika sake min magana sai na ci uwarki a cikin motar nan naga abinda zai faru."

Hamna dake latsa wayarta cike da damuwa tace "Kai, wallahi wata rayuwar ma batayi ba, ku yanzu da girmanku zaku tsaya kuna wannan musayar yawun haka, a cikin maganganunku fa harda gori kuke son ku shigo da shi, yanzu idan ace iyayenmu suka ji kuna tunanin zasu ji dad'i ne?"

Umaima ce tace "Ke bana son iskanci, kar yau dan kun ganni na had'a kafad'a daku yasa kuyi tunanin raina ni, tom."

Cikin jin hushi ta ture Jamila dake tsakiyarsu wanda hakan yasa har Hamna saida ta kaiwa glas d'in motar karo, ita ma cike da tsiwa ta bangazo Jamila har ita da ake cutawa tace " A'a kai, ni kuma mena muku? Kunga kuyi fad'an ku amma kar ku saka dani."

Suna cikin wannan ture turen Jibril ya juyo yace "Billahil-azim duk wacce naga ta turi yar uwarta saita yabawa aya zak'inta, kunji na fad'a muku."

Jin haka yasa suka harari juna sukayi shiru, da wannan kuma suka isa cikin yardar ubangiji, nan dai suma sukayi tasu ta'aziyar, sun samu Hajia kuma ta dire tace da ita zasu koma dan ta gaji da hayaniya da zahi, suna haka colonel ya samu kira na gaggawa a babban birni Niamey, dama tare da mutanenshi yake dan haka ya musu sallama suka d'auki hanya.

Bayan sallah azahar kuma saiga Ammar da su Junaid da Amar a mota d'aya, basu wani shiga cikin gida ba nan suka zauna ana ta hira da jimami, bayan sallah la'asar kuma Hajia ta fito cikin shirin tafiya tace gobe ta dawo sai ayi sadakar uku, loiacin Amar suna d'an nesa da gidan dan haka bata ganshi ba, nan aka had'a ta da yan matan da samarin da kuma iyayen maza aka ce su tafi gida tunda babu kowa, saida kowa ya gama shiga aka fahimci Hamna bata shigo ba, saida aka kirata ta fito ashe tana can tana gyara jikinta tana fesa turare, kasancewar Hajia na tsaye ta fito nan ta duba motar da zata shiga sai taga babu wuri, dan haka ta nuna mata motar Ammar data hangeshi shi da Junaid kad'ai, can ta nufa zata shiga baya Junaid ya fito yace "Gimbiya Hamna shigo gaba, ni na ma samu motar da zan shiga."

Ita kuma murmushi tayi ta shiga kamar yanda yace, a ranshi kuma cewa yayi "Ba gaira ba dalili na had'a mota da ku kafin mu kai ta kama da wuta, ai wannan tafiyar babbar tafiya ce.".

Saida Ammar ya ji motoci na oda alamar sun fara tafiya ya d'ago kanshi, juyawa yayi inda Hamna ke zaune suna had'a ido gabanshi yace wani "Dassss." Ya fad'i ba tare da sanin dalili ba.

Inda ita kuma na ta gaban yace "Dammm." Kallon tsoron da take mishi ne yasa ya had'e fuska yace "Dallah ni bari kallo na sai kace mayya."

Da sauri ta kalli gabanta a ranta tana fad'in "Toh, aifa kuma na shiga uku, gashi yanzu babu ni babu guduwa idan ma na k'ular da shi."

Tashin motar yayi ya fizga da gudu inda ta bi hannunshi da kallo yanda ya murza sitiyarin, k'aramar jakarta ta fito da ita ta d'auki abun sauraro (รฉcouteur) ta danna a kunne saboda tasan zaman shiru ne za ayi, suna shiru haka tana sauraren wak'ok'inta kira ya shigo wayar, d'auka tayi suka fara hira ita da saurayin na ta duk da ba wai son shi take ba, yanda take kashe murya dan kar Ammar yaji yace tayi laifi ashe dai bata tsira ba, dan yanzun ma haushi ne ya kama shi wai akan me zata wani kashe murya haka tana hira da saurayi, cikin hassala ya fizgo wayar hakan yasa abun sauraron ya fita muryar saurayin ta bayyana, yanda shima ya kashe murya ne ya k'ara tunzura Ammar, dan haka saurayin da baisan meke faruwa ba yace "To ai dole ne ko? Yanda kika kashe min jiki haka da muryaki ai sai bacci ya d'auke ni alhalin ina cikin tuk'i."

Tsabar neman fita Ammar sai ce mishi yayi "Insha Allahu kana baccin nan ba zaka bud'e ido a ko ina ba sai cikin k'abari, ku ko kunya baku ji ku tsaya hira da 'ya'yan cikinku haka, yanzu haka matarka na can ranta a b'ace amma baka san ya zakayi ka kwantar mata da hankali ba, k'aryar banza kawai."

Kashe wayar yayi ya cillata k'asan k'afafun shi inda birki yake yana jan wani tsakin, Hamna dake kallonshi ta kasa gane me yake nufi tace "Yaya Ammmm..."

Bai bari ta k'arasa ba ya nuno mata yatsa yace "Kar ki sake ki min magana."

Yanda ta ga fuskarshi yasa taja baki tayi shiru, suna tafiya taji shirun yayi yawa, hannu ta zura ta kunna redion motar dan shi tsabar baya son hayaniya ko redio na mota baya kunnawa, tana kunnawa yayi daidai da tashar ana wak'a, cikin jin haushi ya buge hannunta yace "Kar ki sake tab'a komai dake motar nan."

Tab'e baki tayi suka ci gaba da tafiya, ana haka ta ji masuburbud'ar sanyi (ac) na bata sanyin dayawa ita kuma bata so, sai kawai ta zura hannu zata d'an juyar da shi gefe, ai kuwa sai ji tayi kanta ya bugu da abun sanyin saboda wani wawan birki da Ammar ya taka, kafin ta ankara taji ya fizgo hijabinta dake jikinta wanda dama ta sanya ne saboda zasu zo wajen rasuwa, kamo hannayenta yayi duka biyun ya had'e wuri d'aya yasa hijabin ya d'aure su tamau, kallonta yayi da jajayen idonshi yace "Kinfi kowa sanin bana magana sau uku akan abu d'aya, nayi biyu ba zaki sani bayi uku ba, idan har na ji bakinki yanzu wallahi bolar dake kan hanyar nan zan tattaro na tusa miki su a baki har sai mun kai gida."

Hamna da ido suka cika da hawaye shiru tayi dan babu damar bashi ko da hak'uri ma, bai sake kallonta ba har saida suka isa cikin gari ya kalleta yace "Ke gaki marar kunya, a gabana wani d'an iska zai kira ki har kina kashe mishi murya, shi kuma dayake babban kwarto ne har yana fad'a miki wai zai yi bacci, haba."

Hamna dai ko kallonshi batayi ba har suka isa gida, motoci na tsayawa a farfajiyar gida aka firfito, Hamna babu hannayen bud'ewa saida Ammar ya bud'e mata k'ofar ta zuro k'afafu ta fito, take kallo ya koma kanta inda Junaid da dama yasan abinda zai faru kenan ya riga kowa bushewa da dariya, da sauri Amna ta k'araso ta kunce mata hannuwa tana fad'in "Yaya Ammar ne ya d'aure ki? Ke kuwa me kika masa haka kamar wata dabba?"

Kamar zatayi kuka tace "Me kuwa zan masa, bak'in halin ne ya motsa da mugunta."

Lieutenant ne yace "Yanzu Ammar d'aure yarinyar nan kayi kamar wata dabba, me tayi maka to?"

Yana cikin rufe mota ya nufi b'angaren su yana fad'in "Bata jin magana."

Cikin b'acin rai lieutenant yace "Kai maganar kake ji? D'an iska kawai yarinya bata maka komai ba ka kamata ka d'aure."

Juyowa Ammar yayi ya kalleshi, juyawa yayi ya ci gaba da tafiyarshi haka suma, ana shiga falo Hajia tace "Wai ina shalele na? Ance tare muke amma har yanzu ban ganshi ba."

Umaima ce ta tab'e baki a ranta tace "Mu da ba shalelenki ba ma dai gamu ko ba'a san ganinmu."

Sai lokacin sukayi ido hud'u da Amar, ai kuwa sakin jakarta tayi ta zaburo ta daddafe fuskarshi tana tambayar "Shalele lafiya? Meya sameka a fuska haka? Ba dai hatsari kayi ba kuma shine babu wanda ya fad'a min."

Cikin halin ko in kula yace mata "Eh, ba wani babban abu bane, karki d'aga hankalinki."

Hamna ce tace "Amma yaya Amar na d'auka cewa akayi fad'a kukayi kai da yaya Ammar."

Da sauri kusan kowa ya kalleta inda Amar har saida yaji kamar ya mareta, Hajia ma kafeta tayi da ido tace "Fad'a kuma? Waya fad'a miki?"

Yanda duk taga wasu na kallonta ne yasa tayi shiru, cikin zaro ido Hajia tace "Ba dake nake magana ba kina ji na kinyi shiru."

Cikin duburburcewa tace "A'a Hajia nima ban sani ba, jiya dai naji su aunty suna fad'in ko sunyi fad'a ne lokacin da zasu tafiya, amma bansan meya faru ba, mu bamu ma gidan a lokacin."

Lieutenant ne ya kalli Amar yace "Amma ai jiya ba haka kuka fad'a mana ba, ka ce hatsari kayi da moto."

Hajia ce ta mishi wata tsawa kamar k'aramin yaro tace "Rufe min baki malam, dama ko kun sani wace tsiyar zaku tsinana, duk ba ku kuke d'aure mishi gindin ba."

Amar ta kalla tace "Shalele da gaske ne abinda ta fad'a?"

Ba tare daya had'a ido da ita ba yace

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login