Showing 234001 words to 237000 words out of 325849 words
watsewa daga wurin a tsiyace, yana wucewa ya zuro kai ta k'ofa ya musu gwalo, kai dukansu suka girgiza, bai d'auki lokaci ba ya isa asibitin, ya samu Ummy da ma'aikaciyar dake aikin kwana a asibitin sun gama kimtsa Amna duk abinda take buk'ata sun mata tare da yaran, har an shiga da ita d'akin hutu ta kwanta tare da duka yaranta, su Hajia ne suka musu sallama suka tafi sai Husseina aka bari da Ummy su kwana anan, har Hamna zata shiga mota yace "Ki bari zamu tafi tare dake."
A lokacin babu wanda ya iya tanka masa dan ba k'aramin shan kunu yayi ba, hatta Ummy sai taji tsoron ko da hararansa bare tace a'a, ita kanta Hamna ta tsorata sosai sai kawai ya shige ya barsu, ko da suka koma ciki Ummy ya tambaya abinda suke buk'ata, magunguna ta rubuta wanda zasu taimaka mata ya siyo ya dawo, lokacin sukayi saida safe suka fito shi da ita.
Tunda suka d'auki hanya babu mai magana sai Hamna dake addua'r Allah ya kaisu lafiya, saida suka kusa kaiwa gida ya taka birki ya jingina bayanshi a kujera, kanshi na kallon sama kamar ba zaiyi magana, tunda taga haka ta fara sallalami da duk addua'r da ta zo bakinta, tana tsaka da addua'rta taji muryarshi irin babu wasa a ciki yace "D'azu kinyi maganar yara uku, me kike nufi da abinda kika fad'a?"
Saida ta zaro ido tsabar tsoro kafin ta k'ank'ancesu a ranta tace "Yayin da wasu ke zuwa duniya lokacin wasu ke barinta, Hamna kuma ta wannan hanyar k'arshenki zai zo."
Ba tare data kalleshi ba cikin b'ari da rawar murya tace "Ba..ba abinda na...ke nufi, ina tambayarka ne kawai."
D'agowa yayi ya daki sitiyarin motar da k'arfi ya kalleta yace "Hamna na miki kama da sakarai ne?"
Haba wane mutum, ai sai ta fashe da kukan da babu hawaye tana girgiza kai tace "A'a, a'a yah Ammar, dan Allah kayi hak'uri ka kaini gida."
Cikin tsawa yace "Idona zaki kalla ki min magana."
Da sauri ta kalli fuskarshi sai kuma tayi k'asa da kanta tace "Dan Allah kayi hak'uri karka cutar dani."
Bayan wuyanta ya shak'o ya matso da fuskarta gaf dashi yace "Ni zaki rainawa wayo Hamna, tun a waccen lokacin naga alamun ciki a tare dake, kwanciyar hankalin Ummy kawai yasa nayi shiru, amma yau ba zan barki ba sai kin fad'a min gidan uban da kika kai min ciki na."
Yanzu kam kuka ta fara na k'warai sosai har hawayen na shiga bakinta sun jik'e leb'enta sharkaf, ganin bata da niyyar magana yasa shi sakinta ya kuma dukan sitiyarin motar da k'arfi har wata razananniyar oda ta fito, k'amewa ta sakeyi ya kalleta cikin jin haushi yace " Hamna bana son dukanki, ke kad'ai ce bana jurar ganin cutuwarki, ki taimaka ki fad'a min ya kikayi da cikin nan Hamna, idan kuma kin zubar dashi ne kamar yanda nake tunani ki fad'a min."
Kallonshi tayi cikin kuka jin ya fad'a mata mafitarta, sunkuyar da kai tayi tace "Kayi hak'uri yah Ammar."
Lumshe ido yayi a k'alla tsawon minti biyar yana saita nutsuwarsa, saida ya daidaita kansa ya kalleta yace "Nayi hak'uri da me? Da cikin nawa da kika zubar?"
Da sauri ta d'aga masa kai alamar eh, rintse ido yayi ya yamutse fuska kamar zaiyi kuka, ya d'an jima a haka kafin ya bud'e ido yana sauke ajiyar zuciya ya kalleta yace "Hamna kinsan me zai hana ni sake miki wani cikin a yanzun nan?"
Fik'i-fik'i ta masa da ido ta kuma kallon titi ba tace komai ba, d'orawa yayi da cewa "Saboda yer uwarki ne, wallahi ba dan Amna ba da saina miki wani cikin naga abinda zai faru, ke ko da zaki zubar dashi ne saina k'ara miki wani sai dai mu tabbata a haka, amma..."
Kallon titin shima yayi cikin nutsuwa ya ci gaba da cewa "Ina ganin mutumcinta sosai, ina girmama al'amarin Amna har zuciyata, ina ganin k'imarta da darajarta a idona, ta kasance wacce tafi kowa kusanci dani, ta zauna dani sanda kowa ke kirana mahaukaci da ganin rashin tarbiyata, ta zauna dani ta fahimce ni ta shanye komai daga gareni, ta juri dukana ta shanye bak'ar maganata tayi dariya ga fitsarata, duk sanda na zalinceta bata tab'a fitar da k'walla a idonta ba sai dai tayi kukan da babu hawaye, duk sanda nayi niyyar dukanta bata guduwa sai dai ta tsaya wurin ta shiga bani hak'uri, wannan haukan nata na birge matuk'a. Ki sani yau kinci albarkacin yer uwarki, ba dan haka ba da sai kin gane kurenki na zubar min da ciki da kikayi, amma ko yanzu ma zaki gane kuren naki."
K'wafa yayi mai k'arfin gaske tare da tayar da motar ya fara ja, suna tafiya ya juya ya kalleta, ganin har yanzu bata saki jikinta ba sai share hawaye take, wani uban rank'washi ya gaura mata akai yana fad'in "Shegiya 'yar bak'in cikin tsiya, wai yaron ne da zaki haifo min kike jin haushi da hassada, a ganinki da ki haifo min shi gwara kin min asararshi, to Allah ya isa Allah saiya saka min wallahi dan ba yafe miki zanyi ba, mai bak'ar zuciya kawai."
Tunda ya rank'washeta ta baje baki tana kuka, cikin jin haushi ya sake shirga mata k'ulli a baya yana fad'in "Dan ubanki rufe min baki, Allah kinci sa'a bana son dukanki da saina karya k'asusuwanki yau a garin nan."
Hamna dai da yake muguwa ce k'ala ba tace masa saida suka isa gida tana wannan kuka kamar an mata mutuwa, a k'ofar gida ya tsayar da motar ya bud'a zai fito ita mata fito fuska rufe da hijabi, nufa yayi wajensu Junaid dake zaune suna hira suna aikin daya sa su, saida ta bud'e k'aramar k'ofa zata shiga dama wandon bacci ne gareta ta kalleshi tace "Ammar mugu Ammar azzalumi mai bak'ar zuciya, Allah ya isa Allah ya saka min duk cut..."
Da gudun bala'i ta k'arasa shiga ciki kamar zaki ya biyota ta haye sama, Ammar daya bita da kallo su Amar ne suka kwashe da dariya, kallonsu yayi a k'ufule yace "In ban muku wanka da tafasashen shayin nan ba ku ce ba namiji bane ni."
Kowa kama bakinshi yayi kamar sun cika iska, ture Jibril yayi daga kan kujerarshi ya fad'i k'asa ya zauna yana fad'in "Zan kama ki ne yarinya, Allah zaki san ni kika tab'o yar banza mai zubin gwiwar daji."
Amar dake ta rik'e dariya ne ya kasa ya mik'e tsaye ya mik'o mishi d'an k'aramin bol d'in shayi na glas yace "Babban yaya ga shayinka, premier ( na farko) ne."
Lokacin kowa ya samu damar sakin dariyarsa har da masu rik'e ciki, kallonsu yayi da niyyar masifa sai kuma ya fashe da dariya shima yasa hannu ya karb'a ya kurb'a, saida ya kallesu ya sumbaci yatsunshi biyu ya jefa musu sumbar yace "Ina sonku k'annai na, kune rayuwata fa."
Jamil ne ya fito duk yayi gumi yana ganinshi yace "Yawwa Jamalun ya ake ciki? Waken ya dahu ne?"
Cikin jin haushi Jamil yace "Da k'yar na tashi Nana daga bacci ta bud'e min madafa, da k'yar na samu na d'ora ruwan, yana can zata k'arasa dafawa."
Girgiza kai kawai yayi suka ci gaba da zuk'ar shayinsu suna hira, wani abun daya fad'a kowa sai yaji abun wani iri, wani suyi dariya kamar cikinsu zai fashe wani kuma su girmama al'amarinshi, kamar yanda ya fad'a kam saida akayi sallah asuba kad'ai ya barsu suka koma cikin gida shima ya shiga ciki, wanka yayi ya canza kaya farare tas wanda rigar t-shirt ce sai wando 3 quater kafin yasha magani saboda k'afarsa da har ya manta akwai ciwo, kiran Ummy yayi ya tambayesu yanda suka tashi tare da neman a bashi Amna, sosai suka jima suna hira cikin nishad'i kafin suyi sallama yace sai ya zo d'aukarsu.
Misalin *06:30* na safe Hamna ma ta kirasu suka gaisa ta tambayi yara, saida suka gama waya har ta kashe Amna mijinta ya zo tunaninta, tunawa tayi da fa ciwo a k'afarsa, sannan mutum ne dake wasa da cikinsa, idan ya ga abinci ne zai ci idan kuma bai gani ba babu ruwansa, ita kanta wani lokacin sai tayi rarrashi yake ci kafin ya fita da safe, sake kiran Hamna tasa Ummy tayi ta bata wayar, tana d'auka tace "Na'am Ummy."
"Ni ce yer uwa." Ta fad'a murya k'asa k'asa, d'orawa tayi da "Dan Allah yer uwa wani taimako zaki min."
Daga b'angarenta ta amsa da "Wane irin taimako kuma Amna? Kin fara manta yanda muke ne?"
"A'a, amma nasan abu ne mai wuya a wajenki, ki min alk'awarin zaki min kafin na fad'a miki dan Allah."
Cikin rashin son wasa tace "Fad'a min ina jinki, nayi alk'awarin."
Cikin muryar rarrashi tace "Yer uwa taimaka min zakiyi dan Allah idan an kammala abin kari ki kaiwa yah Ammar, sannan idan kinje ki d'ora masa ruwan zafi ki ce masa ya gasa k'afarsa sosai sannan yasha magani, dan Allah." Ta k'arashe da sake kashe murya.
Wani mamaki ne ya kashe Hamna tare da tunanin taya zata je su had'u bayan abinda ya faru jiya? Gashi kuma tayi alk'awari, bayan alk'awarin kuma tasan halin Amna da rik'o zata iya yin hushi da ita akan haka, a hankali ta bud'a baki tace "Shikenan naji zanyi, tunda so kike ki mayar dashi kamar wani jariri."
Murmushi Amna tayi tace "Jariri ne mana, har yanzu baya iya kula da kanshi, Hamna yana buk'atar kulawa."
Tsaki Hamna tayi tace "Ki kular min da yarana ni, banda lokacin haukanki ke da mijin na ki."
Kashe wayar tayi ta aje ta sauko k'asa, madafa ta shiga su Zeituna na aiki ta kalleta tace "Aunty Zeituna idan kun kammala Amna tace a fitarwa mijinta da abincin saina kai mishi."
Cike da sakin fuska Zeituna tace "Kin ganshi nan zan fidda mishi kuwa, dan bana mantawa da babban d'an gidan nan, tunda yau babu mai girka masa."
Kallonta tayi tace "Amma kun gama da wuri yau aunty."
"Eh saboda za'a kaiwa yan asibiti ne." Saida ta d'auki wanda Zeituna ta nuna mata tace "Wa zai kai musu?"
"Ni nake son tafiya tare da Abban Fatima." Cewar Zeituna, kallonta Hamna tayi da mamakin sunan data kirashi dashi, wato tunda ita ma yanzu ta haihu dashi ba buk'atar ta ci gaba da kiranshi da Abban Ammar? Abun ya birgeta sosai har taji ina ma tana da 'yancin kiran d'anta da sunan ubansa data kirashi da *Shureim Ammar* da babbar murya kowa yaji, karb'ar abincin tayi ta fito ta nufi b'angaren nasu, ta manta bata saka ko da mayafi ba bare hijab, wannan siket d'in na atamfa da rigarsa wanda suka kama jikinta suka zauna daram dam, ga k'ibar data k'ara yasa k'ugun ta ya sake sama ya zauna da kyau, d'aurin kallabin mai sauk'i ne wanda zamu iya kiransa da ture kaga tsiya, dan ya turo sosai gaban goshinta, ko kwalli babu a idonta haka ta bud'a k'ofar d'akin ba tare da tunanin zata same shi a bud'e ba, amma sai ji tayi ya bud'e a hankali ta shiga tana kallon yanayin d'akin shiru kuma babu wuta sai hasken safiya kawai, saida ta je gaban teburin nan ta aje kwanukan ta nufi hanyar madafa dan d'ora ruwan d'umin kawai tayi tafiyarta, ta taka d'aya biyu na uku taji wata tattausar murya a bayanta yace "Ba sallama, ba neman izinin shigowa bare ki gaishe da mutane?"
Tsayawa tayi sai jikinta da taji ya fara rawa rawa kamar zata kifa k'asa, had'e fuska tayi alamar bata son wargi sannu sannu ta juyo, inda taji maganar ta kalla sai taga ashe ya kishingid'a ne kan kujera yayi luf, turo baki tayi cikin shagwab'a tayi k'asa da kanta tace "Ina kwana."
Wani narkakken kallo ne yake mata inda yake jin abubuwa da dama na b'abb'akowa daga k'asa suna yin sama, ganinta a haka ba k'aramin gigita nutsuwarsa tayi ba, a hakan daya ganta ta tuna masa da duniyarsa, dan atamfar ma kala d'aya ce haka d'inkin, kuma ita ma haka suka amsheta a ranar daya fara ganinta dasu, lumshe ido yayi tare da buk'atuwar son ganin hak'oranta ko da ba ta sigar dariya bane, hakan zaisa ya yarda cewa ta daina hushi dashi, amma ganin fuskarta a had'e a haka zai rikita lissafinsa har ya kasa iya aiwatar da komai, bud'a idon yayi ya sauke kanta yace "Kunna fitilar."
Rintse ido tayi, har ga Allah tasan inta juya saiya kalleta, fuskantarshi tayi sai kawai ta dinga yin baya baya tana nufa wajen kunna hasken, murmushi ya dinga yi yana kallon fuskarta a ranshi yana godiya ga Allah data rufa masa asiri ta juya bayan, dan shi fa ko matarsa idan zata juya masa bayan nan sau dubu sai yaji buk'atarta sau dubun, kuma yana tsoron sake faruwar al'amarin a bisa wasu dalil...Hasken d'akin daya kawo ne ya katse masa tunaninsa ta hanyar kallonta.
Da kallo ya bita ta shige madafa, wayarsa ya fito yana dannawa yana jiran fitowarta ya sata dariya ko hankalinsa ya kwanta.
Ta d'an jima kafin ta fito rik'e da robar jiya da k'aramin towel, har gabansa ta aje masa ruwan kafin tace "Wai inji ta ka ci abinci ka gasa k'afarka sannan kasha magani."
Murmushin gefen labb'a ya mata yace "Ashe kema kina jin maganar zuciyarki akai na?"
Da sauri ta d'ago kai ta kalleshi da sauri kuma tayi k'asa da kanta saboda kallon da yake mata, ganin tayi k'asa da kanta yasa yace "Mai ladabin kunama, yanzu sai kin tashi zaki fita ki juyo ki ce min Allah ya isa ko?"
A hankali ta girgiza kai tace "A'a, me ka min da zan maka Allah ya isa?"
"Kinfi kowa sani." Yana kallonta, mik'ewa tayi zata fita yace "Baki k'arasa ladanki ba ai, ki zuba min abincin idan kin gama ki gasa min k'afar tawa, ko ba abinda tace kiyi ba kenan."
Yamutsa fuska tayi tace "Ni ce zan gasa maka k'afar? To ba haka tace nayi ba, wannan ma saida ta rok'e ni nayi."
Sakar masa duka giman idonshi yayi wanda hakan ya tsorata ta, ba shiri ta matso tace "Zan zuba to."
Durk'usawa tayi ta fara zuba abincin, yana kallonta cikin taushin murya da alamar gaskiya ya karkace kai yace "Kiyi hak'uri Hamna, ki yafe min kinji."
D'agowa tayi ta kalleshi babu alamar annuri a fuskarta tace "...
*Alhamdulillah*
14/10/2020 ร 00:58 - Ummulkhairi: ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*BADAK'ALA*
๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ _*AHALI NA*_๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
๐ซโจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_๐ค
โ *[ T.M.N.A]* โ ๐๐๏ธ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
_53_
"Akan me zan yafe maka?"
Cikin ladabi yace "Akan komai ma dana miki wanda ya tsaya miki a rai kike kallona da shi."
Wata dariyar ka raina min hankali tayi tace "Abubuwan fa dayawa, ba zan iya ba gaskiya."
Cikin wata siga yace "Yanzu kankana ba zaki iya yafe wa d'an uwanki ba? So kike mu tsaya gaban Allah ya mana hisabi? Ashe dama ba sona kike ba da kike so Allah ya k'ona ni, shikenan nagode."
Rumgume hannayenshi yayi ya turo baki gaba alamar yayi hushi, kallonshi tayi ido cikin ido tace "Bana so gaskiya."
"To ki yafe min." Ya fad'a da k'arfi yana gyara zama, girgiza kai tayi alamar a'a, dan haka ya d'ora gwiwar hannunshi kan cinyoyinshi yace "Saboda me?"
K'asa tayi da idonta tace "Saboda suna dayawa."
Cikin kafeta da ido yace "Fad'a min guda goma naji wanda suka tsaya miki a rai, ni kuma na miki alk'awarin duk'awa har k'asa na nemi affuwarki."
Saida ta aje masa abincin gabanshi ta
tsiyaya ruwa ta aje mishi sannan ta kalleshi tace _"Ranar da mukayi fad'a da Amna ka hukunta mu ta hanyar samu tsayuwar awa uku ba tare da mun motsa ba, a gaskiya ranar naji haushinka, saboda babu irin hak'uri da magiyar da bamuyi maka ba amma baka k'yale mu ba, sannan bana manta ranar daka sameni da saurayi na k'ofar gida kawai ka dinga zagina shima ka kore shi kace wai an min miji kuma mahaukaciya ce ni ya daina kula ni, har saida nayi kuka ranar fa."_
Cikin jin haushin ta ambaci saurayinta, wai saurayinta ko kunyarshi bata ji yace "Yanzu ma ashar d'in zan daddana miki idan kika kuma kallona kika fad'a min wai saurayinki."
Kallonshi tayi tana k'yabta ido yace "To naji ci gaba."
Cikin turo baki gaba tace "Shikenan ma kawai na yafe k'ananan laifukan amma ban yafe manyan laifukan ba."
Mamaki ne yasa shi bud'e baki yace "Wanene kika yafe to wanene baki yafe ba?"
Saida ta mik'e tsaye tana d'an jan siket d'inta sama alamar dakawa zatayi da gudu sannan tace "Kamar mari wanda ka min ba adadi, duka idan munyi laifi da zagi, sanda ka kusa sa min k'adangare a jiki, d'ora ni saman bishiya duk na yafe, amma ban yafe manyan ba har da keta min haddi na da kayi."
Juyawa tayi da k'arfi zata zuba a guje yace "Dawo nan, in kika fita Allah saina biki."
Tsayawa tayi ta juyo tana kallonshi kamar zatayi kuka, kujarar dake gefe ya nuna mata yace "Zauna nan."
A hankali ta lallab'a ta zauna tana satar kallonshi, saida ya fara cin abincin kamar ba zai kulata ba kafin ya kalleta yana tauna lomar bakinshi yana fad'in "Wai ke kika haifi barewa ne ko kuma ita ta haifeki da ba kya gajiya da gudu?"
Girgiza kai tayi ba tace komai ba, d'orawa yayi da "Zaki je asibiti ki taho tare dasu."
Wani irin kallo ta masa, ta d'auka fa zai sake jadadda neman afuwarshi ne, amma ya canza maganar zuwa wata daban, mik'ewa tayi saida ta kai k'ofa ta juyo, rik'e da cokali ta ganshi zaisa bakinshi amma bai kaita bakin ba yana kallonta yana jiran ta juyo ta fad'i abinda zata fad'a, ai kuwa saida ta shirya gudu sannan tace "Ai ba sai ka fad'a min zanje ba, yer uwata ce ita baka fini sanin abinda ya dace na mata ba."
Sakar mata ido kawai yayi yana