Showing 48001 words to 51000 words out of 325849 words
komai kamar yanda kika ce."
Ganin ta jingina a bayan kujerar yasan ta gama magana kenan, cikin girmamawa yace "Ni zan tafi uwar d'aki, sai kin jini."
K'ala ba tace mishi ba har saida ya kai k'ofa tana kallonshi, cikin dubara yayi kamar labulen d'akin ne ya sark'afe shi harya samu ya d'auki wayar ya fice, yana fita ya shigar da d'aukar da yayi ya fara tsare tsaren abinyi.
*Da rana*
A falonsu Ammie suke zaune bayan sunyi sallah sun ci abinci, suna tsaka da hira téléphone d'in dake kan wani k'aramin teburi dake tsakiyar kujeru yayi k'ara, Rauda ce ta d'auka ta kara a kunne, jim ta d'an yi kafin ta kalli Sameera tace "Ammie kina da bak'o a waje."
Juyowa tayi ta kalleta tace "Who is that?"
D'auke wayar tayi a kunnenta tace "Saleem, k'anin uncle Abbakar."
Da murmushi a fuskarta tace "Ok, ki ce ya barshi ya shigo."
A wayar ta sanarwa da mai gadi ya barshi ya shigo, baifi minti biyar ba sai ga Saleem ya shigo da fara'a a fuskarshi, Sameera da murna tace "Saleem, dama kana gari? Kwana biyu ka b'uya."
Saida ya k'araso ya zauna kujerar da Jabir ya tashi ya bashi kusa da Abdul yana murmushi yace "Aunty ina nan wallahi, abubuwa ne sai a hankali."
Murmushi tayi tace "Good, ina Abbakar da jiki kuma?"
Saida yanayin fuskarshi ya canja kafin yace "Jikinshi da sauk'i."
Hannu ya bawa Abdul suka gaisa da Jabir, har Khalifa da Usman ma, Diya'u ne ya taso yana turo baki yace "Ni baka gaisa dani ba, dan ban girma ba ne?"
Dariya Saleem yayi ya bashi hannun yana fad'in "Sorry my Man, ai kai ma babba."
Khalifa ne yace "Kaji yaron da ko gemu bai fara ba zai ce ba'a gaisa da shi ba."
Ammie ce ta rik'e baki tace "Ikon Allah Khalifa, to kuma ita gaisuwar dole sai mutum yayi gemu?"
Imranatu ce tace "To Ammie ki fara tambayarshi ma shi ina nashi yake?"
Cike da kuri Khalifa yace "Ai naga man da Dadyna yake anfani da shi gemunshi na k'ara yawa, da nace zan shafa yace na bari zai soyo min wanda suka fi na shi zama original."
Juyawa Sameera tayi saida ta kalli duk ' yan matan d'akin tace "Yanzu dukaninku babu mai wayon da zata kawowa bak'o ruwa? Yaushe kuka zama marowata haka?"
Raihan ce tayi saurin mik'ewa saboda shakkar uwar da take tana fad'in "Sorry Ammie."
Da harara ta bita harta shiga kitchen d'in su Ammie ta d'auko ruwa da lemu har kala uku, tunda ta tashi Saleem ya bi bayanta da kallo, a ranshi yace "Tabbas ke ce *target* d'ina."
Su Bilkis ne suka ce mishi sannu dan shi ba niyyar gaishe da su yake ba saboda hankalinshi baya nan, cike da kunya ya gaishesu har Raihan ta dawo ta dire farantin gabanshi, tunda ya d'ora idonshi a kanta ya kasa d'aukewa, har ta zuba mishi lemun ta mik'a mishi ta mik'e ta koma inda take ta zauna yana kallonta, Fadila ce ta lura da kallon dan haka a ranta taji ita da zai so Raihan d'in ma ya taimaka mata saita samu Abdul ita kad'ai, yana d'an kurb'a lemun ya aje ya mik'e yace zai tafi, godiya Sameera ta masa tace ya gaishe da Abbakar da jiki, kuma insha Allahu zataje ta duboshi dan ta jima rabonta da can, Abdul ne ya mik'e ya d'an taka mishi har k'ofar gida ya shiga motarshi kafin ya bar unguwar.
Yana fita wayar Sameera tayi k'ara, d'auka tayi ta duba sunan taga sarki Imran ne, d'auka tayi tana murmushi da zolaya tace "Allah ya taimaki sarkin Basraba, k'anena ya kake?"
D'aga b'angaren Imran ne yace "Yarinyar nan fa kin gama raina ni, shekara uku na baki amma har kike kirana da k'aninki."
Cikin dariya tace "Amma dai kasan k'anwata kake aure ko?"
Saida ya kalli Ameera wacce ke mik'o mishi smootie d'in ayaba yace "And so what? Ni kuma yayanki ne."
Cikin dariya tace "To ya garin na ka mai martaba?"
Imran ne yace "Muguwa, ban sani ba to, kina son sanin yanda garin yake da aka ce za'a baki mulkinshi kika ce ba kya so? Gashi kinsa duk an takura ni ta ko ina."
Tunda ya fara magana take dariya saida ya tsaya tace " Ai na fad'a muku ba zan iya mulki ba, amma ko yanzu bata b'ace ba ai, idan ka samu labarin wata masarautar zata kawowa taku hari to kayi gaggawar sanar dani dan mu shirya dakaru ni kuma zan jagoranci yak'in."
Murmushi Imran yayi yace "Ke 'yar bala'i ko? To bama fatan tashin hankali mu.
Kafin tace wani abu yace "Ina mamana take da yarana?"
Saida ta kalli Ammie tace "Duka lafiyarsu k'alau, ina yaran nawa da yar uwata?"
Katseta yayi da fad'in "Dakata dallah ki saurare ni, serious magana fa na kiraki muyi."
Mik'ewa tayi daga wurin ta shiga bedroom d'in Ammie ta zauna bakin gado tace "What's the matter?"
Nan ya kwashe komai ya fad'a mata duk yanda ake ciki kafin ya d'ora da "Yanzu haka ban fad'awa Umma ba, dan nasan halinta ba wani farin ciki zatayi da zab'in na takawa ba, haka ma sistern ki ban san ta yanda zan fara fad'a mata ba, please Sam tell me what do i do now, wallahi i'm confuse."
Dariya Sameera tayi tace "Hey! What trouble in this issue? Listen to me brother, maganar nan babu wata matsala ko tashin hankali, ka samu aunty ka fad'a mata komai dake faruwa, sannan ka jira abinda uncle da liman zasu tattauna, idan har maganar ta fad'a shine saika samu Ameera ka fad'a mata, i hope zata fahimce ka d'ari bisa d'ari."
Ajiyar zuciya ya sauke yana hangen Ameera dake gyaran kayanshi yace "Ok, yanzu zanyi abinda kika ce, but make me sure k'anwarki ba zata d'aga min hankali ba."
Dariya tayi tace "I'm verry sure, kai dallah rago wallahi ka cika tsoro, kamar dai ba jinin *Ali zaki (Haidar)*."
Wata sayayyar ajiyar zuciya ya sake saukewa yace "Babu abinda ke kayar min da gaba a duniyar nan kamar idonki dana Ameera, sometimes bana iya kallon k'wayar idonku na fad'a muku abinda ke raina."
Tashi tayi zata fito tace "Matsoraci, u know me ai tha's why u scrad me."
Daga inda yake yace "God forbid na ji tsoronki, kema duk iskancin ki ai kina shakkar wannan yaron."
Zaro ido tayi tace "La la la la, mijin nawa ne yaro? Kai amma sarkin nan baka da mutumci aradu, amma ba komai kai da yallab'ai ne, zai sameka har Basraba dan kayi repeatn abinda ka fad'a."
Yasan tsaf Abbas zai titsiyeshi kan ya maimaita kamar yanda tace, shiyasa yace "In dai kina k'aunar iyayenmu karki fad'a masa, abinda ma a daren nan jirgi na zai tashi zuwa Belgium (ya fad'i hakane dan tayi tunanin zai bar garin)."
Dariya tayi tace "Fad'uwa ta zo daidai da seat kenan, ai shi tuni ya rigaka isa can."
Da sauri yace "No wonder yau mukayi magana dake perfect, banji yana ta min iskanci ba ko yana shinshinarki yana kissing d'inki ba, ashe jarababben baya gari."
Dariya tayi harta fito suna ci gaba da raharsu, cikin zolaya yace "Dallah ni bani uwata na kwashi albarka."
Saida ta k'araso kusan Ammie tace "What are u eaten na baka na following down? Gata in dai Ammie duk tsiyarka zaka bar min abata."
Ammie ta ba wayar suka gaisa harda su Imranatu ma da sauran yaran kafin daga bisani suyi sallama.
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Sai dare kad'ai Imran ya samu uwar d'aki ya fad'a mata abinda suka tattauna da takawa, ranta ya kai k'ololuwa wajen b'aci, ace d'an ta kuma babban d'anta wai ba zai iya fara sirri da ita ba, ba yabo ba fallasa ta nuna mishi ai ba komai kawai Allah yasa alkairi, dan tasan waziri zai lalata komai, shi kuma mamaki ne ya sa shi mik'ewa da k'yar ya mata sallama.
*Me waziri zaiyi? Wa sarki zai aura? Me zai samu takawa?*
_See u.✋_
03/06/2020 à 23:33 - Ummulkhairi: 👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*BADAK'ALA*
👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
👨👩👧👦 _*AHALI NA*_👨👩👧👦
🇳🇪 *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```
_Bismillahir rahamanir rahim_
_7_
"Dan Allah baiwar Allah ki tsaya, zo ki shiga mota saina kaiki duk inda zaki je."
Kasa had'a ido tayi da shi sai lumshe ido take kamar jiri zai deb'eta, jin ba tace komai ba sai k'ok'arin tafiya da take yasa ya sake tareta yace "Ki dubi girman Allah baiwar Allah ki saurare ni, ki zo na kaiki asibitin, zan taimakawa mahaifinki ya samu lafiya, karki d'auki abinda ya faru yanzun da son raina nima wall..."
Bai k'arasa saboda tafiya data fara yi, ji take kamar ta watsa mishi mari ko guda goma ne ko ta huce, amma kuma tsoronshi take ji, karta mareshi ranshi ya b'ace ya sake murk'usheta a wajen, dan ta fahimci sunyi hannun riga da imani, sake wucewa tayi ko kallonshi ba tayi ba bare ta saurare shi, shi kuma tausayin yarinyar ne ya kama shi sosai, juyawa yayi yana kallonta tana tafiya da k'yar waacce ya gani cikin karsashi wani lokaci daya wuce, wata zuciyar ce ta fad'a mishi "To me kenan kayi Jibril? Ka lalata rayuwar yarinyar daka had'u da ita yanzun nan? Yarinyar da ko sunanta baka sani ba, shin baka tunanin sanadiyar abinda ya faru ta rasa mijin aure? Ba ma wannan ba Jibril, shin kasan me zai iya biyowa baya sakamakon hakan? Kai tirr da wannan rayuwa taka."
Da gudu ya sake tare gabanta kamar zai rik'e ta saboda yanda ya bud'e hannayenshi a dole tareta zaiyi yana fad'in "Kinga baiwar Allah, dan Allah ki zo muje mota sai mu tafi tare, na amince ki kaini wajen iyayenki na taimaka miki, idan har mahaifinki ya samu lafiya na miki alk'awarin zan aure ki, ki zo muje dan Allah."
Wani kallo ta watso mishi dake nuna me ka d'auke ni? Amma ba tayi magana ba ta sake giftawa zata wuce, hijabinta ya rik'e tana juyowa suka had'a ido, ruwan dake sauka da k'arfi ne suka fara tsagaitawa a hankali, cikin raunin murya yace "Idan ba zaki aminta da ni ba dan Allah ki fad'a min sunanki da gidanku, zan zo, zan zo wajen iyayenki na nemi izinin aurenki."
Wasu hawayen takaici ne taji sun taho mata bata shirya ba, wai yau ita ce wani namiji da bata san shi ba kuma akan hanya ya mata fyad'e, kamar a film ko kuma tatsuniya, ko kuma kamar ana rayuwa a garin maguzawa, da k'arfi ta bige hannunshi ta sake juyawa tayi tafiyarta, baya da zab'in daya wuce ya shiga motarshi ya tayar ya bi bayanta, ba jimawa suka isa asibitin, tana zuwa a k'ofar d'akin da mahaifinta ke kwance ta samu duk dangi an fito sai sharar hawaye suke, mahaifiyarta da ke kuka sosai ta matsa kusanta tana tambayar lafiya, shirun da kowa ya mata ya tabbatar mata da mahaifinta ya rasu, Mari na gamsuwa da abinda zuciyarta ta fad'a mata sai lokacin ta ji wani azababben kuka na bak'in cikin mutuwar mahaifinta da abinda ya faru da ita yanzun, durk'ushewa tayi wajen ta fashe da kuka sosai kamar ranta zai fita, nan dangi har da kakarta suka dinga rarrashinta suna bata hak'uri, amma Mari ta zama kamar dutsi ko jinsu ba tayi sai kuka kawai, duk abin nan dake faruwa a idon Jibril dake hangensu daga nesa, lura da abinda ke faruwa yasa ya k'ara jin ba dad'i sosai, gyara tsayuwa yayi da niyyar ko zai kwana nan sai ya ga gidansu, amma rashin sa'a sai kiran gaggawa ya shigo wayarshi cewa ana nemanshi, dan a lokacin bai jima da fara aiki da wannan projetn ba, kawunshi Gambo ya shiga gaba har saida ya ga ya samu wannan aikin, dan haka baya da zab'in daya wuce ya shiga motar ya bar wajen.
Ko da ya isa inda suka sauka ya d'auka kira ne na ka zo yanzu ka koma, ashe a lokacin wani abu ne ya taso da dole za'a tura su wani garin, kuma shine zai wakilci tawagar, haka suka kama hanya zuciyarshi kamar zata fashe, ya rasa meke mishi dad'i a rayuwa, kamar ya fasa ihu yake ji ko zaiji sauk'in abinda ke ranshi.
Nan gawar mahaifinta ta kwana zuwa safe aka yi bisarshi, har lokacin Mari kuka take ga azabar ciwon kai da zazzab'i da suka tasota gaba, ta k'i ci ta k'i shan komai sai kuka kawai, kowa kuma tunanin shi kukan mutuwar mahaifinta ne dan haka sai dai ace kiyi hak'uri mana, duk mai rai mamaci ne, addu'ar ki yake buk'ata ba kuka ba, a kwana a tashi sai gashi sun kwashe *sati d'aya*, a ranar wanda suke haya gidanshi ya zo yace sai dai su tashi ya samu wanda zai zuba a gidanshi, dama kuma bashi ne a kansu sosai, da k'yar wani mak'wabcinsu ya bashi hak'uri yace shi zai dinga biyan kud'i har zuwa lokacin da mahaifiyarta zata gama takaba, dan d'akinta ya dace tayi wanka.
Haka suka ci gaba da rayuwa tare da kakar Mari a gidan, basu da matsalar abinci saboda lokacin zaman makoki an kawo musu, har lokacin kuma Mari ta k'i sakin jikinta, duk wani motsi da zata yi sai taga kamar suna kallonta kuma zasu fahimci abinda ya faru, dan haka kullum da hijabi a cikin gida, mahaifiyarta kuma tuni ta kafa mata na mujiya tana bin dindigin kowane motsinta dan tasan ba haka take ba, kwatsam sai aka kwashe *wata uku har da kwana sha biyar* Mari babu al'ada, abinda ya kusa tarwatsa zuciyar mahaifiyar ta.
Ta fito daga ban d'aki da hijabinta da bokiti a hannu mahaifiyar take kallonta tayi wani fes sai d'aukar ido take, cikin kallon nan tace "Zo nan Mari."
A hankali ta aje bokitin ta k'araso kusanta ta tsaya, hannu ta zura da nufin kama nata hannun ta duk'ar da ita sai kawai Mari da babu gaskiya ta zille, kallon mamaki ta mata tace "Meye? Mari kar dai abinda nake tunani ne ke shirin faruwa dake?"
Cije leb'e Mari tayi tuni ta fara sharar k'walla tana fik'i-fik'i da ido, dafe k'irji *D'iyar baba* (sunan da suke kiranta dashi kenan kasancewarta 'yar fari kuma kakanta ne yayi rainon ta) tace "Na shiga uku na lalace, Mari iskanci kike dama? Yaushe kika lalace ban sani ba?"
Da sauri ta girgiza kai sai rufe baki take da hijabi, cikin jin haushi D'iyar baba ta taso ta shak'o hijabin Mari, ita kam ana jawota saita fad'i k'asa ta fashe da kuka tana fad'in "Wallahi Ayya banyi ba, ba laifina bane, ki tsaya na fad'a miki abinda ya faru, shi ne fa ranar kawwww..."
Marin da D'iyar baba ta watsa mata yasa ta dafe kunci ta kwamtsa k'ara, kafin ta sake cewa wani abu D'iyar baba ta d'auki kujerar data mik'e a kai 'yar tsugunno ta maka mata a kai, wannan azababbiyar k'arar da tayi tasa kakarta dake shigowa saurin d'aga k'afa ta ida shigowa tana sallallami da tambayar kai lafiya? Ganin wacce ake jibga yasa ta zubar da ledar hannunta ta k'arasa ta rik'e ta cikin harshensu na barebari tana fad'in "Ke dube min yarinya, me tayi miki? Kamar kin samu jaka."
D'agowa D'iyar baba tayi ta nuna Mari cikin son d'aukewar numfashi tana fad'in "A..a...a..ta cu..ceni, cikin...sh..eg..e..."
Zubewa tayi wajen sumammiya, ai fa sai wani tashin hankalin ya samu kuma, take bakinta ya karkace saboda hawan jinin da take fama dashi, amma duk da haka nuna Mari take tana fad'in "Allah ya isa...Allah ya miki abinda kika min...bani ba ke Mari har abada." Duk da maganarta ba'a jin sosai amma Mari ta fahimci me take fad'a, ai kawai sai kakarta ta kifa mata wani marin ta fara masifa ita ma wai zata kashe mata 'ya har tana fad'in "Wallahi idan 'yata ta mutu dalilinki kema sai kin mutu, da ubanki *Muhammadu* yana raye kikayi wannan abun kunyar da shima ya tsine miki albarka".
_Masu karatu karfa ku manta babu kirkira a ciki, duk abinda ya faru ne da wasu mutanen nake rubutawa bayan an bani labarin._
Wannan yammaci Mari bata kwana gidansu ba, domin kuwa D'iyar baba tace ita ba yarta bace , kakarta kuma da zasu tafi asibiti saida ta watsowa Mari kayanta sannan ta rufe gidan, a daren nan duk inda Mari take tunanin samun taimako na yan uwa saida taje, amma da sunga yanayinta suka tambayeta lafiya ta k'i fad'a sai wasu suce ta koma gida zasu zo su ji meya faru sai a sasanta, har gidan *malam Rabi'u* taje a tunanin kamar kaka yake gareta saboda da shi da kakanta wanda ya haifi mahaifinsu uwa d'aya uba d'aya suke, sa'a da ta ci shine baya gari kasancewarshi malami ne na tsibbu, shiyasa ta baro gidan da tunanin da yana nan daya karb'e ta tunda malami ne shi.
A tak'aice dai Mari a gindin wata bishiya ta zauna ta rakub'e, kuka take da tunani barkatai na yanda lokaci d'aya komai ya canza mata, mahaifiyarta ta kasa tsayawa ta saurareta, yanzu ya zatayi kenan? Meye abunyi? Ina zata je? Wannan tambayoyin ta dinga jerawa kanya kafin daga bisani zuciyarta ta fad'a mata ta je gidan k'anwar mahaifinta *Khadi*, ta san matar kuma tana nuna mata soyayya saboda Maryama sunan mahaifiyarsu ne aka saka mata, ko rasuwar mahaifinta saida ta so ta tafi da ita amma dai ta jinkirta har wani lokacin, matsalar d'aya ita ce ba garin nan take ba, tana Maradi ne da aure, amma a yanda zuciyar Mari ke tafasa dole ta shirya ta kuma k'udira gari ya waye ta tafi can duk da bata da kud'in mota, a haka kuwa aka fara kiran sallah asuba, tashi tayi daga wurin ta samu wani masallaci tayi alwala da butar nan, gefe ta koma tayi sallah kafin ta d'auki hanyar zuwa gidan mota.
A k'ofar shiga gidan ta fara rarraba ido tunda ita dai ba kud'in mota gareta, haka ta