Showing 186001 words to 189000 words out of 325849 words

Chapter 63 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

586

Middle Ads

kusa da ita, a k'wayar idon Ummy ta hangi abinda ta kasa fahimta, shin tana son tafiyarta ne ko kuma a'a, rashin sanin amsa yasa ta kalli Hajia ta sunkuyar da kai tace "Ni ban fad'a mata ba, ina so na tafi tare da Abba."

Kallon mamaki da takaici Amna ta mata, me yasa za tayi haka? Cikin jin haushi tace "Amma ai ni nasan ba kya son tafiyar, kuma idan kin manta na tuna miki, kina shirye shiryen tafiyarki koyon kwalliya ne."

Idan har ba bak'ar magana ta fad'a mata ba tasan ba zata rabu da ita cikin sauk'i ba, dan haka tace "Ni bana son koyon wata kwalliya, wajen mahaifina zan koma da zama."

Murmushin rainin hankali Hajia ta bisu da shi tace "To kinji abinda ta fad'a da bakinta, dan haka ki barta ta tafi can, idan da rabo ma ta samu miji acan aure zan mata, sai dai kawai kije bikinta idan da hali."

Da k'arfi ya kalleta, *miji*? kuma *aure*? acan d'in? Hummm! Juyawa yayi da sauri ya nufi hanyar barin d'akin, da sauri Amna ba tabi bayanshi dan bata ga abinda zata zauna tayi ba, kai tsaye b'angarensu suka koma.

Kallonta Hajia tayi tace "Ki d'auko kayanki ki zo ku wuce."

Juyawa tayi ta koma sama, ba b'ata lokaci ta d'auko ta sauko k'asa, tana zuwa Gombo ya mik'e yana wa mutanen wajen sallama, tafiya sula fara yi suna barin falon, anan Ummy ta samu damar fad'awa Hamna cewa "Karki damu Hamna, ki tafi dasu yanzu, tunda Hajia ta yanke hukuncin nan babu mai hanawa, amma ina so duk abinda kike ji a jikinki karki bari kowa ya sani, ki kira ki fad'a min zansan abun yi, kafin lokaci mai tsayi kuma nasan ta hak'ura tasa a dawo dake."

Jinjina kai kawai tayi suka fita, a farfajiya daidai k'ofar fita suka samu an saita hancin motocin, anan suka samu Aissata tsaye tana amsa waya da harshen zarma, saida ta gama wayar kafin ta kallesu cike da izza da d'aga kai sama tace "Sai anjima."

Zeituna da Zeinabu ne suka amsa da "Sai anjima, Allah ya kiyaye hanya."

Mai aikin data taho da ita ce ta bud'e mata k'ofa zata shiga, tsayawa tayi ganin Hamna na shirin shiga motar gabansu ansa jakarta a but d'in motar, da mamaki tace "A'a! Me wannan kuma take yi ne haka? Ina zata je ne?"

Mai aikin ce ta girgiza tace alamar bata sani ba ita ma, Gambo ne ya tsaya daga shirin shiga motar yana kallonta yace "Tare zamu tafi da ita."

Yamutsa fuska tayi tace "Ban gane tare zamu tafi ba? Tare muka zo da ita ne?"

"Umarnin Hajia ne, dole haka za ayi madame." Cewar Zeinabu, rai a b'ace ta juya ta kalli Gambo, kallon kiyi hak'uri mana har muje gidan ya mata, saida ta matse baki alamar akwai magana kafin ta shiga motar, tasan kawai dan Hajia ta muzguna mata ne ta had'a su tafiya da Hamna, amma inba haka ba meye na sawa a tafi da ita, yaran da ko da k'uruciya basu tafi ba bare yanzu da girmansu, suna kallo suka ja motoci suka fita daga gidan anata jiniya, basu zame ko ina ba sai filin jirgi, daga nan kuma suka d'aga zuwa Niamey.

D'akinshi ya shiga ya rufe zauna kan gado, tunanin abinda ya faru yake yi, yaji zafi sosai, ba wai marin data masa bane ya b'ata masa rai, marinshi da tayi a gaban wacce zai iya kira da matarshi, ta d'aga hannu ta dalla mishi mari, jin bugun zuciyarshi ya fara canzawa yasa shi mik'ewa da sauri ya fito daga d'akin yana fad'in "Ina! Ba zan tab'a bari damuwarku ta sa min ciwon zuciya ba, idan na mutu ma ba ciwo zakuji ba."

Falon ya dawo ya nufi wajen fridge ya bud'a ya d'auki ruwa, saida yasha sosai sannan ya dawo ya zauna kan kujera, tv ya kunna yana kallo sai kuma ya tuna da Amna, tunda ya nufi d'akinshi ita ma tabi bayanshi, amma kallon daya mata yasa ta shiga d'akin ta ita ma. Mik'ewa yayi ya shig d'akin, kwance take kan gado tayi ruf da ciki, k'arasawa yayi ya zauna kusa da ita yana ci gaba da kallonta, sai dai yafi mayar da hankalinshi kan hannunta na hagu wanda ta mik'ar dashi, ta kifa hannun ta mik'e yatsunta wanda ke rufe da jan lalle, amma yatsanta manuniya sai bubbugashi take akan katifar da sauri sauri kamar tana bubbugashi akan tebur, shafa hannun nata yayi hakan yasa ta tashi zaune tana kallonshi, sunkuyar da kanta tayi sanda taji wasu hawaye sun taho mata, da alamar damuwa ya kalleta yace "Kuka ne kike? To me akayi kuma yanzu? Amna bana son kuka fa ko da na yaro ne."

Abinda ya fad'a ne yasa ta rushewa da kuka ta d'ora kanta akan kafad'arshi, cikin kuka take fad'in "Yah Ammar bana jin dad'i, zuciyata kamar zata fashe, yer uwata yau tayi nesa dani, sannan Ummy ta mare mijina a gabana, banji dad'i ba ko kad'an, kawai dan babu yanda zanyi ne."

Murmushi yayi duk da bata kallon fuskarshi, cikin wata k'asaitacciyar murya yace "Hakan na nufin zaki iya tsayawa sosai akan kare min mutumci na?"

D'agowa tayi ta kalli k'wayar idonshi abinda ta jima ba tayi ba tace "Yah Ammar kai fa mijina ne, zan iya yin komai akan kare mutumcinka."

Wani murmushin ya kuma yi tare da jawota ya rumgume, shafa yake yi a hankali yana fad'in "Dama na fad'a miki Amna, ina so ki zama farin ciki na da kwanciyar hankali na."

Da sauri ta sake d'agowa tace "Zan zama, zan zama yah Ammar, ka kwantar da hankalinka."

Sake dawo da ita yayi jikinshi ya sauke k'akk'arfar ajiyar zuciya har iskan bakinshi ya sauka kanta kafin yace "Allah na gode maka, ka bani uwa ta gari da fari yanzu kuma ka ban mata wacce zata kula dani."

Ummy na shiga d'akinta Zeituna tabi bayanta, tana shiga ta same ta tsaye tana kai da kawowa da alama hankalinta ba kwance ba, k'arasawa tayi da girmamawa tace "Ummyn Ammar dan Allah zamu iya yin magana idan ba damuwa?"

Babu alamar sakin fuska a tare da ita ta tsaya wuri d'aya ta kalleta tace "Ina jinki."

Saida ta numfasa ta d'an kalleta tace "Aunty akan abinda ya faru ne yanzun dama, sai nake ganin kamar kinyi saurin marin yah Ammar, shi fa yanzu ba yaro bane, ya mallaki hankalin kanshi sannan yana da iyali, ko kamar Kamal yanzu a wannan zamanin duka baya gyara shi bare kuma kamar yah Ammar, ina ganin zaifi kyau idan kika jawo shi jikinshi, idan kikayi haka zaku fahimce shi da kyau kusan matsalarshi, dan na fahimci daga ke har Alhaji babu wanda yake nuna damuwarsa akan shi, wallahi wani lokacin sai kuyi kamar ba iyayenshi ba."

Tunda ta fara maganar Ummy ta rumgume hannaye tana mata wani kallo, saida ta dasa aya cikin mamakin k'arfin halinta tace "Zeituna wacece ke? Meye ruwanki da sabgar data shafi ni da d'ana? Me kike ji dashi da har zaki tare ni da maganar nan? In haifi d'an a ciki na ki nemi ki koya min yanda zan tafiyar da al'amarin daya shafi tsakani na da shi? Akan wane dalili?"

Kallonta Zeituna tayi a wannan karan babu wani girmamawa tace "Kawai dai ina so na ankarar dake ne da wuri kafin lokacin nadama ya zo muku, dan n..."

Tsawa Ummy ta mata ta hanyar fad'in "Shiru."

Shirun tayi tana kallon babu alamar jin tsoro ko makamancin haka, d'orawa tayi da "Bari kiji Zeituna, wannan ba abinda ya shafeki bane, ki fita a harkata tsakanina da yaro na, idan kuma ba haka ba zaki ga wata Sa'ada wacce baki tab'a tunanin zaki santa ba."

Girgiza kai tayi tace "Allah ya baki hak'uri, Allah yasa ku gane gaskiya." Tana fad'a ta juya ta bar d'akin, da harara ta bi ta dan dama ranta a b'ace yake, zaune tayi bakin gado ta soma tunanin abunyi na gaba tunda Hajia ta wargaza musu shirinsu.

*Zuwa* magrib duk wani bak'o daya zo bikin nan ya koma garinsu, ana sallah magriba lieutenant ya d'auki Zeituna suka tafi ganin kawu Mamu, a k'ofar gidan ya tsaya ita ta shiga ciki da sallama, babu wanda ya amsa sallamarta sai Jumma dake cikin garken awaki da tace "Wake sallama?"

Saida ta zagaya inda taji muryarta tace "Inna Jumare nice."

Duk da ta d'auki muryarta saida tace "Ke ce wa?"

"Zeituna." Ta bata amsa, da sauri ta saki k'afar akuyar da zata d'aure ta taho da sauri tana gyara d'aurin k'irjinta tana fad'in "Yawwa sannu da zuwa, naji dad'in zuwanki, kamar kinsan ina nemanki dama."

Tsaye tayi tana kallonta inda ita kuma ta fara masifa cikin fulatanci tana fad'in "Zeituna wane rashin mutumci ne wannan? Daga an aiki yarinya gidanki sai yaron gida ya mareta, me ta mishi to? Kuma ke a gabanki amma babu abinda kikayi, dama had'a baki kukayi dan a ci mutumcinta ko, ke tunda muke dake a gidan nan kin tab'a ganin ni ko ubanta wani ya d'aga hannu ya daketa? Sai wani d'an k'ato kawai kamar ya samu jaka ya marar min yarinya."

Masifar da take yi ce tasa kawu Mamu fitowa daga d'aki, yana ganin Zeituna shima ya d'ora tashi masifar har da cewa "To ki fad'a min d'an uban waye shi a gidan? Wallahi sai naje har gidan da kaina na rama mata marinta, ke a gaban uwarshi da ubanshi ma zan rama mata dan ya gane tana da gata, dan ba zai kumbura min fuskar yarinya kuma ya tafi a banza ba."

Ita dai kallonsu kawai take, saida kawu ya gama sannan tace "Kawu ya jikin naka? Da sauk'i?"

Cike da tijara yace "Wane jiki kuma? Ni dama lafiyata lau, kawai nace ta fad'a miki hakane dan na samu kud'i a hannunki, dan naga baki damu da mu ba tunda kikayi auren nan, yanzu gashi wannan shegen Janu (Jano) yake ko uban wa ya saka ni gaba akan kud'in shi har yana ikrarin cewa zai rufe ni, to ba dole na samu kud'i ko ta halin yaya ba na biyashi kafin ya rufe ni."

Cikin rashin jin dad'i tace "Kawu har nawa yake biyanka ne?"

"To ni na sani ne? Kawai ba dai ya bani kud'in na karb'a ba a lokacin ina jin dad'in ganinsu, amma dai nasan zasu kai jaka d'ari biyu."

D'an zaro ido tayi tace "Kawu d'ari biyu?" Jumma ce tace "Eh, sunyi yawa ne? Ke yanzu a matsayin da kike ai wannan kud'in ba komai bane a wurink."

Kallonta tayi cike da damuwa tace "Inna Jumare wallahi bana da wannan kud'in, ina zan samu d'ari biyu ni kuma?"

Kallon sama da k'asa ta mata tace "Kiji tsoron Allah Zeituna, dubi kayan jikinki fa, dubi sark'a da d'an kunnen dake jikinki, dubi jakarki ma abar kallo ce, kuma kice baki da wannan kud'in?"

"Amma Inna..." Kawu Mamu ne ya katse da fad'in "Ni ban damu da wannan ba, ba lallai sai ke zaki bayar ba ai, ba ga mijinki ba? Ki fad'a masa halin da nake ciki mana, shi da girmanshi da komai zai bari ne a d'aure sirikinshi a garin nan, kawai ki fad'a masa ke dai zaisan abunyi."

Iska ta furzar cike da damuwa da halinsu tana tunanin yanda zata fara tambayarsa kud'i masu yawa haka, sai yanzu ta fara nadamar k'in amsar kyautar da yake yawan yi mata lokuta da dama, yakan bata kud'i yace ko zatayi wani abun ba sai ta tambaye shi ba, tunda yer uwarta na zuwa aiki ita kuma bata damu ba, amma sai tace bata so bata buk'atar komai, idan ya matsata sai tace ya rik'e idan ta tashi zata tambaye shi. Yanzu gashi bukatar kud'in ta taso mata sai dai masu yawan da ba zata iya tambayarshi ba, ajiyar zuciya tasauke kallesu tace "Shikenan kawu, zan san abunyi dai."

"Da dai yafi." Cewar kawu Mamu, Jumma ce tace "Zeituna wai uban waye ya marar min yarinya?"

D'an murmushi Zeituna tayi tace "Inna Jumare d'an shi ne fa."

"D'an shi? Kuma shine baki rama mata ba saboda kina so ki nuna mishi ba kya k'aunarta."

Wani kallo Zeituna ta mata, na rama mata? Yah Ammar d'in zan mara? Lallai baki san waye shi ba, to ai ko ni har yanzu ban wuce ya galla min mari ba, wayarta ce tayi k'ara ta fito da ita daga jaka, saida ta ga sunan kad'ai ta iya tuna ashe fa tare suke, da sauri ta juyo dan fitowa ta same shi tana fad'in "Na manta ashe yana waje."

Kallon juna sukayi inda kawu Mamu yace "Kinji shiririta, tare suke ta baro shi waje."

Duk hayaniyar da suke a cikin gidan yana ji, sai dai rabi fulatanci ne rabi kuma hausa, hakanne yasa shi cabko matsalar da suke magana akai, sannan yaji sunan d'an shi ma ya fito da kuma ta'asar da yayi, dan haka ya kirata a waya dan da alama ta manta shi a k'ofar gidan. Tana zuwa ta marairaice tace "Alhaji kayi hak'uri dan Allah na barka k'ofar gida, wallahi su kawu ne suka rik'e ni da magana."

Babu alamar wasa a tare dashi yace "Me yake faruwa? waye zai rufe shi akan kud'i? Me kuma ya had'a Ammar da Jumare?"

Baki ta saki tana kallonshi da mamaki da kuma rashin jin dad'i, kenan ya ji komai? Oh Allah, cikin taushin murya tace "Ba komai."

Kafeta yayi da ido yace "Ya zaki ce ba komai, duk da ban ji komai ba amma ai na fahimci inda zancen ya dosa, fad'a min meke faruwa?"

Cike da rangaji tace "Idan mun koma gida zan fad'a maka, amma Abban Ammar ban so kayi hushi."

"Shikenan, yanzu ya mai jikin?" Dariya ce ta kubce mata ta rufe baki, dan ya bata dariya sosai data tambaya, hakan na nufin baiji abinda aka fad'a anan ba kam, klonta yayi yace "Meye?"

Girgiza kai kawai tayi ba tace komai ba tace "Shigo muje." Girgiza kai yayi da sauri yace "A'a, idan dai zasu iya ki fad'a musu ina waje, in kuma kwance suke kawai ki gaishe min su sai ki fito mu koma."

Kamar zata fashe da kuka tace "Lahh, na d'auka fa nan zaka barni da naga mun taho da wuri."

Hararanta yayi yace "Lafiya kike? A halin da kike ciki kulawa kike buk'ata, sannan hidimar da akayi duk kin gama wahalar min da kanki da baby na, dan haka ba zan barki ba, ki shiga ki fito mu koma daga baya kya dawo ganinsu."

Juyawa tayi ta nufi ciki har da buga k'afafu take tana kukan shagwab'a, da murmushin birgewa ya bita cike da k'aunar yarinyar. Tare suka fito da kawu Mamu suka gaisa sosai, da zai tafi ma wasu kud'in ya sake bashi, babu kunya babu kawaici ya karb'a yana godiya kafin ya koma ciki suma suka tafi.

Tun a hanya ya sake tambayarta abinda ke faruwa, tsaf ta fad'a mishi amma banda marin da Ammar ya wa Jumare, dan haka yace "To ita kuma Jumare da waccen ya mareta fa?"

Cikin turo baki tace "Jumare fa rashin kunya ta min shine ya hukunta ta."

Kallonta yayi yace "Ban gane ba? To shi shi ta wa da zai mareta? Ke fa naga alama kin d'aukeshi wani mutumin arzik'i."

Wani kallo ta mishi mai kama da na tsani kalmar daka fad'a, sake kallonta yayi sai yaga ta k'ura mishi ido tana kallo, d'aga mata gira yayi yace "Lafiya?"

Had'e rai tayi sosai alamar bata ji dad'i ba tare da kawar da kanta gefe, cikin d'an d'aga murya yace "Wai meye? Wani abu na fad'a daya b'ata miki rai ne?"

Juyowa tayi cikin tsananin masifa har ta manta dawa za tayi magana sai ta fara fulatanci tana fad'in "Gaskiya ni na baku kyautawa, d'an da kuka haifa a ciki kuna fad'a mishi duk abinda ya zo bakinku, yanzu meye na wani cewa wai ina ganinshi kamar mutumin arzik'i, to mutumin banza ne dama? Akan me zaka fad'i haka a kanshi?"

Tunda ta fara magana ya saki baki yana kallon nata bakin, yanda ko wane harafi ke fita na bakinta abun birgewa, masifa take amma kuma ta mata kyau, sai dai abun takaicin baiji komai data fad'a ba, bakinta kawai ya gani yana motsawa da sautin harrufan da take furtawa, kallon gabanshi yayi yace "Idan kin gama fad'an saiki fad'a min me kika ce ko."

Sak'e tayi ta kalleshi, wai dama ba da hausa tayi magana ba? Kawar da kanta kawai tayi ita ma har suka isa gida, katari kam suna shiga sun aje motarsu Ammar shi kuma zai shiga tashi motar, da mutuntawa ta kalli Zeituna yace "Uwa barka, daga pakarey ake?"

Murmushi tayi duk da bata san me yake nufi da pakarey d'in ba, kallon lieutenant yayi yace "Alhaji ya ake ciki?"

Banza yayi da shi zai wuce Zeituna ta d'an rik'o rigarshi, tsayawa yayi ya juyo ya kalleta da alamar tambayar lafiya, saida tayi kamar zata fad'a jikinshi ta kashe murya sosai tace "Magana fa yake maka, dan Allah ka amsa mishi, laifin me yayi maka?"

Cikin fad'a yace "Ke baki ji me yayi bane? Ina ubanshi zai wani ce min ya ake ciki, dallah rabu dani."

Fizge rigarshi yayi ya juya zai wuce, kukan shagwab'a ta saka tana fad'in "Shikenan nagode da abinda ka min."

Juyowa yayi yana ganinta ya dawo yana fad'in "Wai ke meye haka? Dan Allah wuce muje."

Juyawa tayi ta kalli Ammar daya ke daf da shiga mota sannan ta kalle shi tace "Babu inda zanje yau sai na gani da ido na kuma naji da kunnuwa na ka lokacin da zaka sa mishi albarka, inba haka ba kuma yanzun nan na koma inda muka je yanzun."

Yanda tayi maganar ya nuna rigima take ji, sai dai shi a wurin shi ba wani abu bane da ita take kambama shi har haka, turo baki yayi kamar yaro yace "Kira shi to."

Take murmushi ya maye gurbin fuskar shanun nan, sam farin ciki yasa ta manta sai ta k'walla kiran sunan Ammar daya shiga mota har ya tayar, bai ji kiran farko ba saida ta kura shi sau uku sannan ya fito daga motar, cike da takon k'asaita ya zo gabansu ya tsaya yana kallonsu.

Kallonshi lieutenant yayi babu annuri yace "...


*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*BADAK'ALA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*Labarin Gaske*

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login