Showing 246001 words to 249000 words out of 325849 words
iya yin komai."
Tsabar neman fitina saiya rufe ido yace "Amna ni? Mahaukaci dama kike kallona ban sani ba, eh lallai yau ta tabbata kowa mahaukaci yake d'aukata."
Cikin zubo da hawaye ta girgiza masa kai alamar a'a, k'wafa yayi ya juya zai fita ta sake rik'e hannunshi, fizgewa yayi da k'arfi zai bar d'akin ta tare gabansa da gudu, rufe k'ofar tayi cikin kuka tace "Wallahi babu inda zaka je, nasan halinka yah Ammar in dai har ka fita yanzu saika nemi wani da masifa, ka bigeshi ko ya bigeka shine burinka, dan haka na zab'i ka zauna tare dani in ya so ni ka kashe ni, amma hankali ba zai kwanta ba dan bansan da wa zakayi rigima ba."
Belt d'inshi ya fara zagewa yana fad'in "Shikenan, bari na fara miki laga-laga sai na bi ta kanki na wuce."
Matsowar da yayi kusanta da sauri yasa tayi saurin duk'ewa tayi k'asa tana jingina a jikin k'ofar, yana ganin ya saki d'amarar cike da tausayinta ya sunkuya ya kamota, bud'a ido tayi ta kalleshi saiya rumgumeta yace "Amna baki da hankali ko kad'an."
Saida ta rumgume shi sosai tace "Na sani yah Ammar, shiyasa nake so ka dinga saita ni."
Tallabo kanta yayi ya had'e bakinshi da nata ya shiga tsutsa, shiru komai ya kwanta aka shiga wata duniya, ta d'auka an bar maganar tafiya ashe ko kad'an, cikin muryar bayar da umarni ya nuna ta yace "Ki tabbatar kin had'a kayanki dana yaran nan."
Kallonshi tayi, ba zata iya magana ba yanzu kam dan zasu sake samun matsala, sai kawai ta bishi da to da niyyar yin sun tafi ta lallab'a shi tasan meya faru haka.
*Washe gari* da sanyin safiya suka fito a shirye, ko falon Hajia bai shiga ba yace Amna dai taje ta fad'a musu zasuyi tafiya dan kar aga basu nan, haka ta shiga jiki a sanyaye bayan ta gaishesu ta fad'a musu, kowa yayi mamaki amma tunda tace tare dashi ne sai aka bisu da addu'a kawai, tare da Hamna suka fito suka tsaya farfajiyar gida inda suke iya hangenshi tare da yaran a mota yana jiranta, tsaye suke suna sallama inda Hamna ke d'agawa yaran hannu, idonshi na kanta ya fito da wayarshi, sak'o ya rubuta ya turo mata yana ci gaba da kallon fuskarta.
Tana jin wayarta tayi k'ara ta fito da ita ta duba, kallonshi tayi ta kuma kallon wayar, sak'o ne ba mai tsayi ba, amma ma'anarshi da abinda yake nufi da kuma yanda ita ta fahimci sak'on yayi kusa ya tsayar da tafiyar jinin jikinta, kad'an ne ya rage bata iya nuna abinda ke ranta ba, kafe wayar tayi da ido tana sake maimaita karanta sak'on mai d'auke da wasu tsirarun kalmomin kamar haka _"Bansan me yasa ke da Ummy kuka tsane ni ba, amma zan tafi nayi nesa daku dan na hutar da zukatank'u."_
Suka tsaneshi fa yace, shin yasan me take ji a zuciyarshishi a game da shi kuwa? Bai sani ba, Amna dake kallonta ne tace "Yer uwa ko zamu tafi tare ne dan kar kiyi kewata?"
Cikin gigita, cikin rashin sanin madafa, cikin hargagi da son fitar da abinda ke ranta, cikin yanayin da bata san tayi magana dashi ba, yanayin da bata tab'a ma yer uwarta magana ba sai gashi yau dalilin *namiji* ta mata, tsawa ce mai ban tsoro ta mata ta hanyar fad'in "Ba zanje ba malama ki rabu dani, kiyi rayuwarki nayi tawa, duk ke ce silar komai."
Tana gama fad'a ta taka da sauri ta nufi motar, ta tafi da niyyar yin wani abu daban, amma Ameer na lek'o kanshi ta mota ta sauke ido akan yaron sai taji ta rasa kuzari da k'arfin halin, sai kawai ta juya ta nufi inda motar ta take da sauri. Amna da tayi mutuwar tsaye odar daya mata ce ta farfad'o da ita daga doguwar sumar, da k'yar ta iya d'aga k'afarta ta shiga motar suka fita daga gidan, saida ta ga fitarsu da wasu mintuna kafin ta fita ita ma tana kuka.
*Alhamdulillah*
14/10/2020 ร 00:58 - Ummulkhairi: ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*BADAK'ALA*
๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ _*AHALI NA*_๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
๐ซโจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_๐ค
โ *[ T.M.N.A]* โ ๐๐๏ธ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
_56_
Ammar dai ya tafi tare da iyalinshi, inda suka kwana biyu a garin Niamey a masaukin da mahaifin Amna ya tanadar musu, a kwana na uku ya gama musu shirin komai har da allura saida aka musu na shiga wajen k'asarsu, ticket ya cirar musu ya aje motarshi anan gidan suka tafi *cotonou*, a kwanakin da sukayi saida yayi magana da abokinshi likita wanda ya yarda da k'warewarshi kan ya ci gaba da duba mishi Inussa, sannan duk abinda ake buk'ata a mishi magana zai bayar, sun isa lafiya kuma da yake harka ce ta dala ya samu masaukin daya dace da tsarinshi da kuma iyalinshi, sun fara rayuwarsu kamar yanda suke yi a gidan, amma anan kullum zai fita waje sai Amna tace ya kula kar ya ja musu rigimar da za'a k'onasu da ransu, shi kuma abinda yake fad'a mata shine "Amna ke ma mahaukaci kike d'aukata, amma ba komai zan kiyaye ko saboda ke."
*A gida* fa abubuwa sun shiga juyin waina inda komai ya fara tafiya a hargitse, Hajia da kanta tace ta amince da auren Junaid da Salma, sannan ta bawa Amar dama ya nemi auren Farisa, ta b'angaren Junaid anyi matuk'ar farin ciki ganin zumunci zai had'u tanan wajen, amma a b'angaren Amar tashin hankali ne ya kunno kai daga wajen Umaimah, dan kuwa ranar da taji labarin saida ta mata dukan tsiya har cikin falon uwarta, hakan ya b'ata ran Amar yace ta je gida kawai saiya neme ta, Alhaji ne ya bashi hak'uri yace ya lallab'ata kishi ne, Zeinabu ma hak'uri take bata dan ita yanzu ta nutsu tun abinda ya faru, amma Umaimah sai botsarewa take wai akan me zai mata kishiya kuma k'anwarta data yarda da ita har take shiga d'akin baccinshi. Saboda gudun matsala yasa Soueiba da Labaran cewa in akwai matsala kawai a bari, Hajia tace ai bata isa ba Umaimahr banza ko uwarta bata isa ta hana auren ba, Farisa aka tambaya idan tana so to babu fashi, abinda ta fad'a kawai shine "Ni karatu nake so nayi."
Hakan yasa Amar d'aukar alk'awarin barinta tayi karatunta har aiki ma udan tana so, magana ta kankama sosai har anyi komai an gama an saka rana.
Duk da akwai mutane a gidan kuma ana hayaniya, amma kowa ya tabbatarwa da kanshi akwai mutum d'aya da babu a gidan, babu nishad'i ko wata raha, Hajia Alhaji da Ummy abun yafi damunsu fiye da kowa, ko kiransu a waya bai cika yi ba saiya kwana biyu, yanzu Hajia saita wuni ta kwana a kujerar nan zaune bayan gaisuwa babu wanda zai tsokaneta ko ya sakata dariya ko nishad'i, idan abinci ake ci haka kowa zai gama ya tashi, inba tashin hankali ba na auren Amar ko kuma sab'ani na zaman tare baka jin komai a gidan, dan haka yanzu kowa ya zama shiru zaman d'aki yafi yawa, kowa saiya had'a kan yaranshi k'ananan ya shige d'aki ya zauna abinshi, har Zeituna ma dake da yarinya d'aya, sai dai ita suna waya da Ammar kullum dan yana girmamata sosai.
Hamna ma gaba d'aya ta canza kamar ba ita ba, jikin nan nata duk ya rage yanzu sai lalacewa take, tafi son zama wajen aikinta fiye da ko ina, idan ka ganta gidan nan da dare ne, kuma gari na wayewa zatayi sammako ta fita, hatta Shureim yanzu ta rage kusanci dashi kamar da, sai dai tana waya da Amna akai akai suna gaisawa, wani lokaci haka zata tashi tayi ta b'ata rai a banza, a haka ita ma rayuwar ta godewa Allah kawai zata ce.
*A kwana a tashi* ba wuya a wurin Allah, sai gashi an sake d'aura auren Junaid da Salma da kuma Amar da Farisa sai Jamil da amaryarsa *Zeinab* shima, amare sun tare sun fara rayuwarsu mai cike da jarabawa, tunda akayi bikin aka gama Umaimah ke hushi da Amar bata kula shi, har ranar girkinta ya zagayo da safe ina abin kari tace ai bata dafa dasu ba, banza ya mata ya fita da rana ma bai dawo gidan ba, da dare ma daya tambayi abinci tace yaje amaryarshi ta bashi, murmushi ya mata ya fita daga d'akin, yana zuwa ya samu amaryarshi kam ta mishi dubaru ya cika cikinshi, ko da ya dawo bai kulata ba ya kwanta shima. Washe gari ya bata kud'i haka ma Farisa yace tayi girki, lokacin da take aiki a madafa Umaimah ta dinga masifa akan me zata karb'e mata ranar girki, ita dai bata ce komai ba saboda tana tsoronta.
_Yan uwa rayuwa wata aba ce dake tattare da k'alubale da shubuha, wani lokacin zata iya zuwa maka yanda kake so, wani lokacin kuma ta zo da sab'anin haka, ka yarda ka karb'a ko kuma ka kafirce mata ya rage naka, so da dama mukan so abinda ba alkairi bane a gare mu, haka ma sau tari mukan fifita tsana ga wanda yake alkairi gare mu, shiyasa a kullum ya kamata kayi fatan zab'in Allah._
*Daren yau* duk suna zaune ana cin abinci Jamila ta shigo da gudu wai Umaimah suna fad'a da Farisa sai dukanta take, da gudu kowa yayi b'angaren nasu suka same su, tsaf tayi zaune kan yarinyar mutane tana mai k'aramin ciki tana bugu, ba tsayawa komai colonel ya d'auketa da mari, da k'arfi yasa k'afa ya turata tayi baya yana fad'in "Jaka kawai, yaushe haukan naki yayi tsanani har haka?"
Lieutenant ne ya rik'e shi yana fad'in "Ya isa dan Allah karka ji mata ciwo."
Tana mik'ewa Hajia ma ta kwad'a mata mari tana fad'in "Mahaukaciyar ina ce? Baki san halin da take ciki bane da zaki mata wannan dukan? Jaka ce aka kawo miki?"
Tsayuwar rashin mutumci tayi tana ta wani girgiza da gunguni, Ummy ce ta kama Farisa ta shiga d'aki da ita tana dubata, Hajia kuma kallon Umaimah tayi tace "Bari Amar d'in ya dawo kiga yanda zanyi dake, wallahi sai kin shiga taitayinki."
Wani par-par tayi da ido tana motsa baki tana fad'in "Ya dawo d'in a sa ya yanka ni sai me?"
Wani mari colenel ya sake datsa mata a kumatu wanda yayi sanadiyar gabcewar jini daga hancinta da bakinta, duk'ewa tayi rufe da bakinta ta fashe da kukan da ko sauti babu tsabar azabar marin, cikin bala'i yayi kanta zai sa mata k'afa yana fad'in "Dan ubanki uwar tawa kike fad'awa magana? Sa'arki ce Hajia ko nine kika raina?"
Da sauri lieutenant ya rik'eshi, jinjina kai Hajia tayi kawai ta fita a d'akin, bayanta suka bi sai ita da aka bari tana kuka, suna shiga falon akayi cirko cirko ana kallon Hajia data sunkuyar da kai, Alhaji dake zaune anan bai tafi ba dama ya tambaye su lafiya, kafin wani yace wani abu Hajia ta d'ago cikin dattako tace "Ba komai, zanyi maganinta."
Tana fad'a ta mik'e ta nufi kan teburin cin abinci ta zauna, kowa cikin nutsuwa ya je ya samu kujera ya zauna, Zeituna da Zeinabu ne suka zuba abincin suka aje ma kowa gabansa, amma abun shiru babu armashi kamar anyi mutuwa, Hajia ce ta d'ago kai ta kalli kowa sai kawai tayi murmushi ta tangale hab'arta da bayan hannunta tace "Hausawa sunyi gaskiya da suka ce *duk wanda ya tuna bara baiji dad'in bana ba*, tabbas mutum baya sanin abinda yake so sai ya rasa wanda yake hannunshi, *Ammar* yana raye amma yau ranar yabon ta zo, duk da wani mawak'i yace wai *kar Allah ya kawo ranar yabo*."
Nunfasawa tayi ta d'auke tagumin tace "Dukanmu anan mun sani da yana gidan nan a irin wannan lokacin da yanzu yasa kowa dariya koda kuwa tnda fad'in wata magana ne wacce mu zamu kalleta a rashin kunya ko fitsara, ko da bamuyi dariya ba akan shirmenshi zai zamana zuciyarmu bata tunanin damuwa, amma yanzu gashi rashin shi yasa kowa abinda ya ga dama yake yi."
Saida ta sake kallon kowa tana murmushi tace "Yana son kowa a gidan nan, yana tsayawa kan matsalar data shafi kowa, yana da kirki da kuma d'ab'iu masu kyau."
Dariya tayi ta kalli Alhaji da Husseina tace "Sai yanzu na fahimci dalilin da yasa tsofaffin gidan nan bamu da hawan jini, shine maganin ashe bamu fahimta ba tun wuri."
Dariya sukayi a hankali sai Alhaji da yace "Ni nasan wannan ranar tana zuwa, kune kuka kasa fahimtarshi, amma yanzu gashi kuna fad'a da bakinku."
Cikin sanyi murya tace "Kullum mukayi waya dashi ina tambayarshi yaushe zai dawo? Amma yanda na fahimta kamar bai saka ranar dawowa ba."
Kallon Ummy tayi a raunane tace "Sa'ada dan Allah ki kira shi ki ce masa ya dawo, ya zo ko naji dad'i."
Kallonta Ummy tayi tana tunani, sai kuma tayi murmushi tace "Hajia ke ma baiji maganarki ba ya dawo bare ni."
Murmushi Hajia tayi ta kalleta tace "Ko yaron da bai mallaki hankalinsa ba yasan Ammar yana fifita soyayyarki kan ta kowa, duk yanda zai rud'e ya birkice ya fara sababi idan kika masa magana yana ji, ko hankalinshi ya gushe saboda b'acin rai indai zaki masa magana to zai bari."
Kafe Hajia tayi da ido inda wasu kalamanshi suka dinga dawo mata a kai, da jimawa ya tab'a fad'a mata cewa "Ummy na so barin gidan nan tun a waccen lokacin, amma saboda tunanin halin da zaki shiga yasa ban tafi ba, ina tsoron na barki Hajia ta dinga takura miki."
Sai kuma ranarta ta k'arshe dashi da yace "Amma duk da haka duk ranar da kika buk'aci na gareki zan zo da sauri na, saboda ke mahaifiyata ce kuma ina sonki, ina sonki sosai Ummy."
Wannan tunanin data tafi yasa bata san har sun tashi daga zaman ba, Zeituna ce kawai ta rage a wurin tana kallonta, suna had'a ido suka sakarwa juna murmushi, cikin ladabi Zeituna tace "Gaskiya Hajia ta fad'a Ummyn Ammar, yana d'aukaka lamarinki fiye da komai, duk da rashin kulawar da kike nuna masa baisa ya tab'a yin hushi dake ba, duk yanda yake ganin darajata idan ya kirani kafin mu gaisa saiya fara tambayata ya Ummy take, saina tabbatar masa da kina lafiya kad'ai zai iya gaishe ni, aunty na fad'a miki a baya kuma yanzu ma zan maimaita miki, Ammar so da kulawarki kad'ai yake buk'ata, duk abinda yake yi wanda ba kya so kuna zama dashi cikin sauk'i zai daina."
Ita ma barin wurin tayi suka barta, ta jima nan zaune tana tunanin abunyi kafin ta koma d'akinta. Hajia ma na d'aki Hamna ta sallamo, amsa mata tayi ta bata izinin shigowa, cikin sanyin jiki ta k'araso cikin ladabi tace "Hajia dama na zo neman alfarmarki ne?"
Kallonta tayi ta aje wayarta gefe tace "Wace irin alfarma Hamna?"
Cikin nutsuwa tace "Hajia dama su aunty *Hana* ne (k'anwar mamansu) zasu tafi Niamey bikin *Abdu*, shine nace zan tambayeki idan kin amince ina so mu tafi tare dasu?"
Murmushi ta mata tace "Ba komai Hamna, kuje Allah ya tsare, a kula sosai kinji."
Saida ta sunkuya tace "Nagode Hajia, insha Allahu."
Da kallo ta bita har ta fita, har zuciyarta yanzu kam ta fara tausaya mata, sam babu maganar aure a sabgarta, samari da masu mata suna gosulo a k'ofar gidan akan ta, amma kowa sai tace bai mata ko ta kushe shi dole a rabu da ita, ita kuma bata so ta fitar mata da miji a yanda yanzu ta k'ara mallakar hankalinta take rik'akk'un shekaru ga kuma wayewa da karatu ba lallai ta yarda ba, sai dai kawai su ci gaba da addu'a Allah ya fito mata da miji ita ma tunda gashi har k'annan baya suna aure suna barinta. D'akin Ummy ta wuce ta fad'a mata zata tafi amma fa zata jima gaskiya, Allah ya tsare ita ma ta mata kafin ta fito, tsaf ta shirya kayanta wayewar gari kawai take jira.
Tsakanin mata da miji ance sai Allah, Amar da ake tunanin d'aukar mataki akan Umaimah shi kuma ko da yaga jinin da take zubarwa sai kawai tausayinta ya lullub'eshi, (๐ auren kenan) sai ga Amar ya rarrasheta kan tayi hak'uri dukan da tonton ya mata, ko nasiha bai mata ba na abinda tayi, saida ya gama ita ma amarya Farisa ya lallab'ata yace tayi hak'uri. Da safe saida aka had'asu aka ja kunnensu sosai tare da tsorata ta hanyar fad'a mishi inta sake yayi duk abinda ya dace.
*Bayan wata takwas*
Ko da ya kira gida cikin farin ciki ya sanar dasu Amna fa ta haihu, abun farin cikin kuma shine ta sake haihuwar 'yan biyu duka maza, duk da basu gari amma gidan haka aka dinga murna da farin ciki, dan dama ana cikin hidimar haihuwar Zeinab ne Farisa kuma har tana da sati biyu da haihuwa. Ranar suna ko da ya kira yace an yi wa Alhaji da Alhaji takwara, ma'ana *Suleiman* da kuma *Yunus*, wannan abu ya ma kowa dad'i na wannan iyali, babu wanda ya tab'a tunanin a familyn Hajia kuma Ammar zai iya saka sunan Alhaji Inussa, dangi daga masu kiransu da Alhaji sai mai kiransu Baba, amma shi ya musu alkunya da *Abba* da kuma *Imam*, daga Niamey Hamna ta kirasu ita ma tayi musu barka, wqcce ita ma har yanzu tana can bata dawo ba tayi zamanta, musamman data tafi da kayan aikinta hakan yasa acan ma bata zauna ba, babu inda bata zuwa yin kwalliyarta, dan shiga gidan yana wuya saboda tsaro.
*Shekara d'aya*
Rasuwar Alhaji Inussa ma bata dawo dashi ba, Zeituna ta haihu Jamila Umaimah duk sun sake haihuwa, lieutenant ma ya saka masa ido ya dawo ko ya zauna can