Showing 318001 words to 321000 words out of 325849 words

Chapter 107 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

565

Middle Ads

biyar wak'ar wani film wai ita *madubin dubawa* wacce Ali Nuhu da Rahama Hassan sukayi play roll d'in, yana biya kamar abun gaske, amma daga jin baitin da jarumar ta fad'a ya kalli Hamna yace "Kinji wai ta sauke farashi, yo shi ba dan ma ana so a bada maza ba wane farashi ne har mace zata kallemu tace ta sauke, ke baki ga inda muke tsada ba ma ku ne ke biyanmu sadakin."

Shiru ta masa tana d'aura kallabinta kafin ya sake cewa "Kuma fa ita ba wata kyakyawa ba banda dai Allah ya taimake ta tana da manyan kaya."

Kallonshi tayi ta harareshi sama da k'asa tayi k'wafa, kallonta yayi yace "Me ye na hararata ke kuma?"

Saida ta gyara d'an kwalin tace "Inba gulma ba da sa ido har ka mata kallon k'waf ka gane manyan kaya ne da ita ko?"

"To makaho ne ni?" Ya fad'a yana kallonta, a hassale ta kalleshi tace "Ba mahako bane, amma idan na cire maka su zaka dawo makahon."

Wani kallo ya mata yace "Wai ke mayya ce?"

"Eh." Ta fad'a tana kumbura, tab'e baki yayi yace "Wai ma me ye farashin da take magana akai?"

Kallonshi tayi tace "Ka tambaye ta mana."

Tab'e baki yayi yace "Wai haushi kike ji saboda naga ita ma k'atuwa ce kamar ke? To naje na ce a dafani a cinye."

Wani kallo ta masa bata sake cewa komai ba har suka isa.

Yau fa akayi ta kam a wajen d'aurin aure, bayan an d'aura ya shigo da ango har cikin gidan, har d'akin Ummy inda amarya take ya zaunar dasu, hud'uba ya musu sosai mai ratsa jiki, saida ya gama kamar abun arzik'i sai kuma ya kalli Huda yace "Kina ji na? Duk sanda ya guma miki laifi ki zo ki same ni, sai kin fad'i yanda kike so na miki dashi, in na dafa miki shi da fatar jikinshi ne, ko kuma sai an cire fatar a dafa sai kin zab'a."

Ango dai murmushi ya saki inda ya kalleshi shima yace "Kai ma kuma idan ta b'ata maka, ka zo ka same ni zan fad'a maka yanda zakayi da ita."

Kud'in hannunshi ya mik'a ma Huda yace "Karb'i nan sadakin ki ne."

Cikin lullub'inta na dara tace "Abba ka rik'e kawai, ni babu abinda zanyi dashi."

Kallonsu Ummy dasu Zeinabu yayi yana dariya yace "Kunji wai Abba, yanzu nan fa ya ce na aurar, kai Allah nagode maka, yanzu nan da yan shekaru kad'an Amnata ma zan aurar da ita."

Kallon Huda yayi ya kamo hannunta ya damk'a mata kud'in yana fad'in "Wannan sadakinki ne, kamar yanda mijinki ne kad'ai ke da wani muhimmin hurumi akan ki yanzun, haka wannan kud'in ma ke ya dace ki rik'e abinki, lada ce ta wani muhimmin abu da zaki rasa a jikinki."

Sautin kukanta ta k'ara hakan yasa shi dafa kanta yana fad'in "Kar kiyi kuka mana, ni ma saiki saka ni kuka."

_(Allah ya bar mana kai kakanmu Tahir, ka iya wakilci)_

Saida ya kai k'ofa zai fita ya kalli Zeituna yace "Uwa wai me yasa amare ke kuka ne? Wani abu suke tsoro ko kuma fargaba ne?"

Da kunya ta shiga rarraba ido ta kalli Ummy tace "Aunty ce zata fad'a maka."

Da sauri ta bar wajen Ummy na fad'in "Ke dawo ke zaki iya da kayanki, ai ba ni ya tambaya ba."

Murmushi ya saki yana kallonta yace "Ummy na ma gane, to amma naga ai daga baya kuma idan kuka saba kun ma fimu zak'ewa."

Da k'arfi ta dafe k'irji tace "Mu kuma?"

Cikin i'ina yace "A'a ina nufin su, su matan."

Ficewa yayi ta bishi da kallo, ko data hange shi tsaye kan Hamna dake shirya yaransu da suka kwana anan tace "Allah fidda *A'i* daga rogo."


*Badak'ala na ban kwana insha Allah*


*Alhamdulillah*
04/11/2020 Γ  14:40 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_79_


Ana ta cashewa a wajen bikin Hamna na zaune k'ofar gida tare da wata k'anwar Soueiba, ta baza mata hajar kayan mata tana dubawa inda Ameera ke kusanta tsaye, Ummy ce zata shiga cikin gidan ta kalli Ameera tace "Wai ke yaushe zaki girma ne? Kina nan k'ugunta ba zaki je cikin yara kuyi wasa ba."

D'agowa Hamna tayi ta k'ara mannata a jikinta tana fad'in "Ummy ki barta dan Allah, ni kaina bana so tana min nisa ai, mace ce dole ina buk'atar tafi sabawa dani fiye da kowa."

Tab'e baki Ummy tayi tace "Amma kuma bata sakewa cikin yara taya za tayi wayo da fasaha?"

Turo baki Hamna tayi tana kallon Ummy har ta wuce, kallon Ameera tayi ta manna mata sumba a kumatu tana fad'in "Ai kina da wayo ko?"

Kallonta tayi tana mak'ala hannayenta a wuyan Hamna tana dariya da fad'in "Ummy, in fad'a miki wani abu?"

Kallonta tayi tace "Fad'a min mana yer uwata."

Saida ta kalli k'anwar Soueiba dake ta mik'owa Hamna magani tana karb'a tana dubawa, cikin kunne ta rad'a mata magana, bud'e baki tayi da dariya a fuskarta ta kalleta tace "Da gaske? Haka yace miki?"

Cikin jin kunya ta rufe fuskarta da kallabin Hamna, jinjina kai tayi tana fad'in "Ina ga fa za ayi yar gida ce ko?"

Dariya suka saka gaba d'aya, tana cikin dubawa ta ga motar Ammar ta paka, da sauri ta shiga tattara kayan tana fad'in "Taimaka b'oye kayan nan kar mutumin nan ya sauke min kwadon tsiya a wurin nan."

A tsorace matar ta shiha tattarewa tana fad'in "Baya so kina aiki dasu?"

Saida ta gyara zamanta tana kallon motar tace "Ba haka bane, bana so ya sani ne kawai zai min tsiya wallahi."

Suna kallo ya fito ya canza kaya bana safe bane jikinshi, a hankali Ameera ta tarbeshi inda ya kamo hannunta suka k'araso, yana zuwa ya dangwari kan Hamna yana fad'in "Kankana me kike fad'a ma 'yarki naga kuna ta dariya?"

Matar na kallonshi tana musu dariya sai Hamna data dafe kanta tace "Yaushe?"

Kallonta yayi yace "Ke ni ba makaho bane ina gani, me kike fad'a mata?"

Turo baki tayi tace "To wai banda ikon da zanyi magana da "yata ne? Sirri mukeyi mana kai ma kaje ka kama naka yaran mana."

Tab'e baki yayi yace "Ke dai kika sani, yanzu tashi shiga cikin gida."

Da sauri ta mik'e tana fad'in "To yallab'ai." Kallon mai maganin tayi ta k'yabta mata ido ta shiga ciki tare da Ameera, a baya ya bisu yana fad'in "Yau ma ana bikin ba zaku rabu ba? Wai ke wace jaraba ce kika koyawa yarinyar?"

Gum tayi da baki dan ta fahimci me yake nufi, tayi magana ne ya fara tayar mata da hankali cikin mutane, rik'o mayafinta yayi hakan yasa ta juyowa tana kallonshi, kallonta yayi yace "Yunwa nake ji."

Wani kallo ta masa tace "To ya zan maka kenan?"

Shima wani kallon ya mata yace "Ya rage naki."

Wucewa yayi tana kallo har yayi bayan gidan, tasan kuwa d'akin lieutenant zai je ya zauna jiranta, girgiza kai tayi suka wuce ciki, inda ake girki taje ta samu an idar amma ana so ayi sallah la'asar sai a raba, plate ta samu ta zuba masa taje ta kai masa, har zata fita daga d'akin yace "Ke."

Saida tayi jim saboda ta tsani ya kirata da ke, juyowa tayi tana kallonshi yace "Zauna ki bani a baki."

A marairaice ta kalleshi tace "Yallab'ai biki fa ake gidan nan, kar kasa a saka mana ido mana, dan Allah ka ci abincin kai ma ka fita kafin ayi sallah."

Wani kallo ya mata yace "Yanzu Hamna saboda bikin ne yasa ba zaki bani abinci a baki ba? Bikin ya fini mahimmanci kenan?"

Tahowa tayi a k'ufule ta zauna ta jawo plate d'in zata bashi, mik'ewa yayi yana kallonta yace "Ke ni ba d'an iska bane, kawai daga bani abinci a baki shikenan na miki laifi, to bana ci Hamna."

Har ya juya zai fita da sauri ta mik'e da niyyar taroshi ta bashi hak'uri, sai kuma ya juyo a hassale yace "Ki same ni a mota yanzu har ke ba zaki zauna a wajen bikin ba."

Juyawa yayi ya fita hakan yasa ta dukan cinyarta cikin jin haushi, kai da kawo ta fara a d'akin tana tunanin abinyi, da sauri ta zabura ta tafi da sauri zuwa fita kafin tayi wani laifin, haka ta ratsa mutane ta fita ta same shi.

Tunda ta shiga motar babu wanda ya kula wani har suka kai gida, ta riga shi fita ta nufi hanyar shiga cikin jiki a sanyaye, taji sanda ya rufe motar amma bata juyowa ba, sai ji kawai tayi ya fizgeta zuwa cikin gidan da sauri kamar zata kifa k'asa, saida ya tsaya zai bud'e k'ofar da makullanshi ta samu ta durk'usa kan gwiwoyinta ta rik'e k'afarshi tana fad'in "Dan Allah yah Ammar kayi hak'uri, ni wallahi raina bai b'ace ba."

Uwar d'aki ya shiga da ita ya shiga bata horo kan abinda ta masa, horon bala'i wanda ta wani fannin gwara duka dashi, ya gama gigitata tare da galabaitar da ita, zuwa ne na k'eta da bak'in ciki yake mata, saida ya gaji dan gaban kanshi kuma ya koma kimtsata da rarrashi wai tayi shiru ta yafe masa.

Haka Ummy tayi ta kiranta tana ina sai shi ya fad'a mata ai tana gida, a hassale Ummy tace "Uban me take gidan to bayan nan ana nemanta?"

Cikin rarrashi yace "Kiyi hak'uri Ummy zata dawo anjima."

Cikin fad'a tace "To me taje yi a gidan ne wai?"

Cikin nutsuwa yace "Ummy ibada ta zo, kuma ni da kaina na kawota."

Kashe wayar tayi ba tare data k'ara jan zancen ba, kallon Hamna yayi dake kusanshi ta zuba masa ido yace "Lafiyar kallona?"

Da sauri tayi k'asa da idonta, k'ura mata ido yayi shima yace "Kina lafiya?"

Ba tare data kalleshi ba tace "Bana jin dad'i k'asa, ka mayar dani gida ina so na ga Ummy."

Kamar daga sama kawai taji ya bud'e mata k'afafu ya zura hannu yana fad'in "Bari na duba ki watak'ila k'ari kikayi."

Rintse ido tayi tana jin zafi duk inda ya tab'a, saida taji ya ciro hannunshi ta bud'a ido, gani tayi ya kafeta da ido yana kallo, jawo kanta yayi cikin kunne ya rad'a mata "Kin fiye zak'i da d'and'ano ne, uwa uba ga ruwa."

Kamar yau ne haka ta fara faruwa kawai sai taji kunya ma ta rufe ta, sunkuyar da kai tayi hakan yasa ya sumbaci goshinta yana fad'in "Kankana ta uwar ruwa, a ci gaba da shan kankana ba d'aga k'afa, ni ma ba zan gaji da kawota ba, haka kuma ba zan gaji da tsotsar ruwana ba."

Mik'ewa yayi ya shiga d'akin daya ware na magunguna, ba jimawa ya fito sai ji tayi ya kwantar da ita yana gyara zare da allura, da sauri ta tashi tana fad'in "Me za kayi kuma?"

Hararanta ya shiga yi sama da k'asa yana fad'in "D'inki zan miki, kin k'aru Hajiata."

Girgiza kai ta shiga yi tana fad'in "A'a wallahi bana so, ni ka bari Ummy na zata min, bana so gaskiya."

Sake kwantar da ita yayi yana fad'in "Ni kuma ga mahaukaci kullum sai mu tsaya Ummy ce zata dinga d'inke b'arnar da d'anta ya aikata ko? Ai ko ban iya d'inkin ba kinsan na koye shi dan na dinga gyara kayana da kaina, bare kuma na iya har tiyatar zuciya na iya."

Tana kuka tana k'ari tana ihu tana bata so tana rirrik'e shi haka ya mata d'inki uku, saida aka gama ta yunk'ura da k'yar ta tashi zaune wai sai gani tayi yana share hawaye (D'an iska rairai neπŸ˜‚), da mamaki tace "Lafiya kake kuka kai kuma?"

Kawai fad'awa yayi kan k'afafunta har da jan majina yana fad'in "Wallahi tausaya miki nake, akwai zafi d'inkin nan, sai naji kamar a zuciyata nake soka allurar da zaren."

D'ago kanshi tayi tace "A kaina ne dama kake kukan?"

Turo baki yayi yace "Ina sonki sosai Hamna, duk abinda zan miki da zai cutar dake ba nayi shi dagangan bane, b'acin rai ne ke saka ni, ki yafe min kinji."

Jawo kanshi tayi ta manna a tsakiyar mamanta tana shafa kanshi tana fad'in "Kayi hak'uri ai nice mai laifi ni ce bana jin maganarka, kuma duk horon da kake min ina jin dad'i dan hakan yana nuna min ka isa dani ne, sannan ina d'aukarshi a matsayin horo na yaya da k'anwarsa, dan haka ka daina zubar min da hawayenka na cancanci wannan hukuncin, ko ba komai kaga gobe zan kiyaye fito da b'acin rai a fili yayin da ka saka ni aiki."

D'ago ido yayi ya kalleta cike da k'aunarta yace "Yunwa nake ji fa."

Hannu tasa a rigarta tana fito da nononta tana fad'in "To dama me ye anfanin nonon da har yanzu yake min zuba? Saboda kai dama nake ta ajiyarshi."

*Iko sai Rabba*, k'ato ya daddage a k'afafun yarinyar sai tsotsar nono yake, rayuwa kenan ta musu dad'i, komawar da bata yi ba kenan wajen bikin nan sai dare, a lokacin da suka je har an zo d'aukar amarya, ko da ya sauketa yace "Ki kula min da kanki Hamna."

Kallonshi tayi tace "Kaima ka kula da kanka, amma ana zaka jirani har mu dawo sai mu koma gida ko?"

Saida ya kalli gabanshi yace "A'a, daga nan majalisa zan tafi, akwai wad'anda na gayyata d'aurin aure kuma ban gansu ba, to zan je ne na shukawa kowa rashin mutumci, sannan su biyani katin d'aurin aurena dana basu, tunda 'ya'yan k'ananan mutane ne su."

Kafin tayi magana ya ja mota ya wuce, da kallo ta bi motar tana mamakin abinda zaije yayi, bata ankara taji an daketa a baya da sauri ta juyo ta ga Sayyada, hararanta tayi tana fad'in "To dad'i miji sai yanzu kika dawo?"

Murmushi ta mata tace "Kin fad'i daidai, mijina miji ne da zan iya kiranshi namiji gaban zaratan maza."

Dariya tayi tace "Ba sai kin fad'a ba ai, kowa ya ganshi zai gane hakan, shi yasa ma nake nan har yanzu banyi aure ba shi nake jira yayi ta biyu dani."

Wata harara ta galla mata tace "Sayyada rufawa kanki asiri wallahi, mijin nawa? Ai kuwa sai dai ki mutu babu aure."

Dariya tayi tace "Au ba'a aure ke ya aure ki?"

Kallonta tayi sosai tace "K'addararsa ce ni babu yanda zaiyi, ke baki ga yer uwata ba ma aka raba shi da ita saboda ni."

Yanda Sayyada taga duk tayi ne yasa ta daddab'a kafad'arta tana fad'in "Sai hak'uri Hamna, ki ci gaba da mata addu'a."

Saida ta goge k'walla tace "Allah ya jik'anta da rahama."

"Ameen ya Allah." Ta fad'a kafin ta d'ora da "Haka naji mutane na fad'a, ashe kema kin fahimci haka."

A nutse ta kalleta tace "Sayyada kullum na kalli Ameera sai na ga fuskar yar uwata a fuskarta, kuma kullum na ga haka saina tuna rayuwata da ita, haka zalika ina tuna cewa tsananin rabon haihuwar dake tsakani na da yah Ammar ne ya amshi rayuwarta."

Jinjina kai tayi tace "Hakane, kinsan shi rabo ba'a rantsewa akan shi, da wani yayi k'ok'arin shiga tsakaninku to sai dai ya mutu."

Kama hannunta tayi tana fad'in "Muje ciki na samu zagina a wurin Ummy tun yanzu, yau nasan har uwata sai Ummy ta ci."

Cike da raha tace "Ai ko ni zan kama mata, kina matar uban d'aurin aure ace anyi biki babu ke."

Bushewa sukayi da dariya inda Hamna tace "Kinsan kuwa mutumin naki ya tafi majalisarsu wai zaiwa duk wanda bai zo d'aurin auren ba rashin mutunci, sannan su biyashi katin d'aurin auren daya raba musu."

Girgiza tayi tana dariya tace "Yer uwa wannan mijin naki ki dinga tofa masa lahaula kowace safiya, sannan ki dinga binshi da ayatul kursiyu dan bai rasa shafar mutanen b'oye."

Hararanta tayi tace "Sayyada bana son iskanci fa, mijin nawa?"

Cikin dariya tace "Ai ni labarinku ma zaki ban wallahi ina da marubuciyar da zata rubuta min shi."

Dafe k'irji tayi tace "Ni? Rufa min asiri, idan ya gani babbaka ni zaiyi da raina."

"Ba wani nan, ni zanje har gidan na same shi sai ya yarda ko baya so."

Dariya tayi tace "Gaki gashi ne ai kar tasan kar."

*Ammar* na zuwa duk ya tashi hankalin bayin Allah, kububuwa ya dinga musu ai duk sai ya ci ubansu tunda basu je d'aurin auren fari daya fara ba, sannan su tattara mishi katinshi su bashi inba haka ba zasu ga tsiya, su uku ne a wurin da basu je ba su dai hak'uri suke bashi amma da yake sauran da suka je suna zuga shi saiya dinga botsarewa, fad'i yake ai basu da mutumci ne shiyasa suka mishi haka, kenan ko auren Amreerarsa ya tashi haka zasu mishi? K'arshe dai yace a bashi katinshi kad'ai zai hak'ura, biyu daga ciki har motarsu suka duba basu ga katin ba suka ce bari suje gida su d'auko.

Rigarsu ya rik'e yace "Yo ni saida naje gida na d'auko muku? Anan na baku nima anan zaku ban kayana."

D'aya ne yace "To ai shine zamu d'auko maka a gidan ko."

"Ban yarda ba, a bani yanzu kawai hankali ya kwanta, ko a biyani da kud'i."

Wani daga zaune dake ta musu dariya ne yace "Eh su biyaka da kud'i, kati fa yanzu tsada yake, kuma irin wanda kayi ma na manyan mutane ne mai tsadar gaske, ya kai jaka goma fa wannan."

Kallonsu yayi yace "To kunji dai da kunnenku, dan haka a fiddo a bani kud'i na yanzu."

D'aya da abun ya dame ni ya fiddo jaka gomar ya mik'a mishi yana fad'in "Allah ya rabaka da wannan jaraba Ammar, wallahi ni daga matata ta farko har ta biyu babu wacce ta tab'a titseni irin haka akan abu, yo ni naga jaraba da zafi zafinta."

Saida ya soka jaka gomar aljihu yace "Yo suma sakarkaru ne matan basu san yanda zasu amshi kud'i a hannunka bane."

Haka dukansu suka biyashi kud'in katinsu kafin ya rabu dasu, mik'ewa yayi yana fad'in "Sai anjimanku to."

D'aya daga ciki ne yace "Allah raka taki gona."

Saida ya kwaso

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login