Showing 270001 words to 273000 words out of 325849 words
maganarta yake kawai a sama, wata dariyar ta sake yi tace "Wai a haukanta cewa tayi kai da Ummy da yer uwata kuna cin amanata, kasan me ta fad'a min?"
Ajiyar zuciya ya sauke ba tare daya daina kallonta, jinjina kai tayi ta matso kusanshi cikin rad'a tace "Wai cewa tayi Shureim d'an ka ne, kaji fa mahaukaciyar, ta manta Ummy ce ta haife shi, to kuma ni ko wa ma ya haife shi ina son shi, inda yer uwar ta wa ta haife shi wallahi da naji dad'i."
Kallon fuskarshi tayi da kyau sai tayi dariya tace "Kai ma ka girgiza ko? Karka damu ci gaba da abinda kake."
Ko da ta fad'a ta juya a hankali ta bar d'akin, shi fa tunda ta fad'i haka gabanshi ya yanke ya fad'i, kawai bata aje hankalinta bane data fahimci tashin hankalin daya shiga jin wannan magana, ita dai ta d'auki abun wasa da k'arya da kuma hauka, amma shi baya da dalilin da zai k'aryata Amie, hasalima zai iya cewa ya yarda da abinda ta fad'a d'in, yana da gamsassun dalilai da hujojji.
Yanda ya zazzare ido haka ya zauna bakin gado, tunani ya durmiya yana tuna faruwar komai sala sala, tabbas bayan faruwar al'amarin ne cikin Ummy ya bayyana, lokacin daya ga canji a jikin Hamna har ya so fallasawa Ummy ta jijjiga sosai har ta mare shi, sannan ta matsa sosai har saida aka mata hanyar data shiga sahun masu tafiya France kuma ta k'ara kan lokacin daya kamata ta dawo, kuma ai Hamna bata nan a lokacin, to kenan taya haka ya faru? Girgiza kai ya shiga yi yana ta tunanin abubuwa da dama, ji da yayi kamar kanshi zaiyi bindiga yasa shi mik'ewa da sauri ya fito.
Har tsakiyar mutanen da take zauna ya ja hannunta inda hankalin kowa ya koma kansu, janta kawai yake ita kuma tambayarshi take ina zai kaita lafiya? Saida ya kaita kusan d'akin mai gadi ya tsaya ya saki hannunta, rik'e k'ugu yayi da duka hannayenshi yana kallon fuskarta kamar ba gobe, ajiyar zuciya ya sauke mai k'arfin gaske.
Cikin wata sanyayyar murya amma sautin ta zai nuna maka babu wasa a cikinta kuma mamallakin muryar zai iya yin komai a yanzun yace "...
*Alhamdulillah*
14/10/2020 ร 00:58 - Ummulkhairi: ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*BADAK'ALA*
๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ _*AHALI NA*_๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
๐ซโจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_๐ค
โ *[ T.M.N.A]* โ ๐๐๏ธ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
_63_
"Ummy, da gaske wai Shureim d'ana ne?"
A firgice ta kalleshi yayin da taji har ruwan jikinta na neman tsayawa, yanda ta zaro ido zai nuna maka bata da gaskiya, gudun kar ya fahimta sai tayi saurin b'atar da firgicin ta jawo mamaki ta dasa a fuskarta tace "Ammar, wace irin magana ce wannan? Wane Shureim d'in?"
Da hannu ya mata alamar ya isa haka tare da cewa "Ummy, kin sani na sani abinda ya faru, idan zan iya kawo miki hujojji na sai mu kwana anan ban gama ba, tun waccen lokacin ma nayi shiru ne saboda gudun b'acin ranki, Dan Allah Ummy inhar gaskiya ne abinda naji ki fad'a min."
Cikin fad'a tace "Ammar wace maganar banza ce wannan? Ya zaka tasa ni a gaba kana tambayata wai Shureim d'anka ne? Zargina kake da cin amanar mahaifinka ko me? Ni sam ban ma fahimci me kake nufi ba."
Matsawa yayi daf da ita murya k'asa k'asa yace "Ummy ba haka nake nufi ba, Shureim an ce d'ana ne dana haifa tare da Hamna, shine nake so naji gaskiyar."
Cikin b'acin rai da d'aga murya ta rintse ido tace "Ammar bana son maganar banza, uwarka ce ya zaka sani gaba kana min wannan tambayar rashin mutumcin? Fad'a min wane d'an iskan ne yake son shiga tsakani na da kai da har ya fad'a maka wannan banzan shirmen?"
Cikin fitar hayyaci da b'acin rai da yanayin da shi kanshi baisan yayi magana dashi ba ya d'aga murya sama da ta ta yana fad'in "Ummy babu wani dake son shiga tsakani na dake, magana ce ta fito kuma ina so na sani nima, a matsayi na na d'anki ina da hakk'in da zan san haka."
Saida ya dasa aya ya iya jiyo sautin muryarsa can sama, dafe kanshi yayi da hannu biyu yana d'an murzashi a hankali, kallonta yayi ya rik'o hannayenta duka buyu yasa idonshi cikin nata yayin da take mishi kallon mamaki yace "Ummy ki daure ki fad'a min mana, da gaske d'ana ne ko kuma k'arya aka fad'a?"
Cikin zubo da hawayen da suke nuna ta k'are min ta kafe shi da ido tace "Ammar waya fad'a maka maganar nan? Wane d'an banzan ne?"
Kamar zai fashe d a kula yace "Ummy abinda nake so naji daban, abinda ke ma kike so kiji daban, amsar tana da sauk'i fa Ummy idan kikayi niyyar fad'a min, kawai zaki ce min eh ne ko kuma a'a."
K'yabta ido tayi tana kallon gefenshi, jinjina kai yayi yace "Zan tabbatarwa kaina."
Ko da ya fad'a ya wuce da k'arfi ya tunkari falon Hajia, da gudu gudu ta bi bayanshi tana fad'in "Ammar ina zaka je? Me kake shirin yi ne wai? Ammar..."
Bai tsaya ba har saida ya shige falon, shigarsu yayi daidai da fitowar Hajia daga d'akin tare da duk yan kuci-kucin yaran suna ta mata shirme, da sauri ya tunkareta inda ya ga Shureim, hannunshi ya kama ya juya zai fita dashi Ummy ta rik'e hannun Shureim ita ma, juyowa yayi yace "Ummy dan Allah sake shi."
Matsowa tayi kusanshi tace "Ammar baka da hankali ne wai? So kake ka min terere cikin mutane? Ina zaka kai shi?"
Gyara tsayuwa yayi yace "Asibiti zamu je."
Ko da taji yace asibiti tasan me zaiyi acan, sunkuyar da kai tayi k'asa sai Hajia data matso kusansu tana kallon kowane tace "Ku kuma lafiya? Meya faru ne haka?"
Kallon Hajia yayi yace "Hajia, Shureimmm..."
Yanda Ummy tayi saurin rufe masa baki yasa shi jan k'arshen sunan, kallonta Hajia tayi ta fahimci bata so taji, sai kawai ta kama hannun Ummyn da Ammar ta tura su d'akinta, Shureim ta kama hannunshi shima suka shiga ta mayar da k'ofar ta rufe, zaune tayi kan gado ta kallesu ta nuna musu kujerar dake d'akin mai kama data gwal tace "Ku zauna dan Allah."
Ummy na kallon Ammar ta tsoma mazaunanta kamar tace wayyo ita wayyo kanta, a nutse ta kallesu ta tattara hankalinta gaba d'aya kansu tace "Me yake faruwa Sa'ada?"
Cikin in'ina tace "Hha.jia, ba kommai..hajia."
Murmushi tayi ta kalli Ammar tace "Ammar lafiya? Me yake faruwa da kake d'aga murya fiye data mahaifiyarka?"
Ummy ya kalla ya sunkuyar da kai yace "Kiyi hak'uri Ummy ki yafe min, wallahi bansan na d'aga murya fiye da taki ba, kiyi hak'uri dan Allah."
Dan motsa kanta tayi wanda yake nuna tace ba komai, Hajia ya kalla yace "Hajia, in baki manta ba na fad'a miki abinda ya faru tsakani na da Hamna shekaru kusan biyar kenan."
Sororo Ummy ta kalle shi da wani fitinannan mamaki, ya fad'a mata? Yaushe akayi haka bata sani ba? Kuma shine Hajia bata nuna mata ta sani ba? Tana kallon bakinshi taji yace "Shine yanzu aka fad'a min Shureim d'ana ne, Hamna ce ta haife shi, kuma ina tambayar Ummy amma ta k'i fad'a min, Hajia ina so na sani d'ana ne ko kuwa."
Hajia ma mamaki ne ya bayyana a fuskarta, kallon Ummy take tace "Sa'ada."
D'ago kai tayi ta kalleta, d'orawa tayi da "Da gaske ne abind yake fad'a?"
Cikin sanyin jiki tayi shiru ta kasa cewa komai, ba zata yarda ta sake yin k'arya ba, tunda gashi wacce tati shekaru ma yau ta fito, sai dai kuma ba zata iya amsa kai tsaye da eh ba, ganin wannan shirun na ta yasa Ammar kallonta da mamaki yace "Ummy me yasa kika yi haka?"
Kallonshi tayi saita sake yin k'asa da kanta ta fara zubar da hawaye, girgiza kai yayi kamar zai yi kukan shima na tausayin mahaifiyarshi yace "Ummy me yasa kika aikata haka? Dama har soyayyar da kike min ta kai wannan matakin?"
Fashewa ta sake yi da kuka sai kawai yace "Ummy in kinyi hakane saboda ki kare mutumci na dana Hamna, ai da fad'a min kikayi saina tayaki kare wa har zuwa lokacin da kike so kowa ya ji, idan kuma kinyi ne saboda gudun abun kunya da kallon da mutane zasu mana, Ummy ai naga ba akai na aka fara abun kunya ba, a gidan nan bani ne farkon daya fara aikata irin wannan laifin ba, Ummy ina kika kai tonton Labaran? naga shima ba da aure aka same shi ba kuma yana rayuwarshi hankali kwance, hasalima ba tare daya tab'a ganin mahaifinshi ya taka wani babban matsayi na rayuwa."
Cikin nuna mata da hannu ya ci gaba da fad'in "Sannan ki dubi Huda, gata nan tana rayuwa cikin dangin mahaifinta ba tare da tsangwamar kowa ba, haka ma Junaid, rayuwarsa yake yi bai damu ba, kuma babu wanda yake iya d'aga ido ya kalleshi ya fad'a masa hanyar da aka same shi, Ummy sai ni ne dan na aje d'an gaba da fatiya za'a min zund'e da kinibibi, Ummy hakan ma ai tayar da lissafi ne yayi, kinga kenan zai zamana a kowane d'aki akwai shege."
Yanda ya fad'a da k'arfi yasa ta rintse ido, kallon Hajia yayi yace "Hajia, ki fad'a mata ko ta kwantar da hankalinta ta nuna wa yaro ubansa, ki fad'a mata abun kamar a jininmu yake."
Wani murmushin rainin hankali Hajia tayi ta kalli Ummy tace "Hakane Sa'ada, ki fad'a masa in dai har kinsan d'ansa, karki ji komai a game dani, kamar yanda ya fad'a ne a kowane d'aki akwai yaro irin Shureim, sannan ni kaina da kike gani fa sanda nake budurwa na tab'a yin cikin nan, ni na ma fisu laifi saboda zubarwa nayi, su kuma basu zubar ba sun haifi abinsu, to kika sani ko fantin dana shafawa kaina ne har yanzu yake biyar zuri'ata."
K'ara saita muryarta tayi ta dafa hannun Ummy tana kallon fuskarta tace "Sa'ada, ba zan manta sanda aka kawoki gidan nan ba, ni shaida ce Hassan ya same ki a tsarkake, haka ma Hadiza ina d'aya daga cikin wanda suka taimaka mata a daren farkonta, wannan duk ya isa ya zama hujjar da yaranku zasu k'auracewa zina, amma inda gizo ke sak'ar shine ni, ni d'in ne duk ni na gurb'ata muku iyali, ki dubi Alhaji bawan Allah wanda bai san hawa ba bare sauka, shi ya kamata ace yafi kowa damuwa, amma shi ma ido ya saka min yayi hak'uri dani har saida mai rabawa ta raba."
Numfasawa tayi tana ci gaba da kallonta tace "Sa'ada, ki dubi girman Allah ki fad'a masa gaskiya, Shureim d'an waye a cikin Ammar da Hassan?"
Kutumar bala'i! Shine abinda Ummy ta fad'a a ranta, Hajia! Ciki? Lallai ma, idan ta fahimci inda zancen ya dosa duk ita ce ma silar komai, lallai su Hajia manya, k'warin gwiwa ta samu daga jin kalaman Hajia, sai kawai taji bari ta fad'a da alama ta samu sauk'i.
Ba tare data kallesu ba ta fara goge k'walla cikin muryar data sha kuka tace "Gaskiya ne, Hamna ce ta haife shi bani ba."
Hajia ce tace "Amma Sa'ada taya kika iya shirya lamarin nan ba tare da mijinki ma ya sani ba?"
Tsaf Ummy ta fad'a musu duk yanda akayi har haihuwarta, d'orawa tayi da "Wallahi a lokacin na tsorata ne sosai na rasa yanda zanyi, tunanin hukuncin da zaku d'auka akan shi ke da mahaifinshi ya k'ara tunzari muka ci gaba da b'oye, amma dan Allah kuyi hak'uri ku yafe min, ya lalata rayuwar yarinya ni kuma na taimaka masa, a idon doka da mutane duk mun aikata laifi."
Cikin kuka sosai tace "Na sani da ace wani daga waje na ya ci zarafinta, wallahi sai inda k'arfina ya k'are wajen bi mata hakk'inta, da nayi anfani da mahukuntan dake gidan nan da kud'i da muk'amin mahaifinta wajen ganin na kai ko d'an uban waye k'asa, amma daya zama d'ana ne saina kasa yin komai na lullub'eta tare da laifin ina ta hura mata wuta, banda fargaba idan aurenta ya tashi, na yarda da kaina da gyaran dana koya iyaye da kakanni, dole zata banbanta tsakaninta da budurwa, shiyasa kullum fatana Allah ya fito mata da miji tayi aure."
Kallonta duka suke sai kuma ya juya ya kalli Shureim dake tsaye gaban madubin Hajia yana kallon kwalaben turaren da suka d'auki hankalinshi saboda kyawunsu, kamo hannayenta yayi ya rumgume cikin muryar alhini yace "Yanzu Ummy wannan dalilin ne yasa kike ta nesanta ni dashi dama? Shiyasa ba kya so kiga muna kusantar juna sai kin raba mu?"
Kallonshi tayi tace "Kayi hak'uri Ammar, nasan yanda soyayyar jini d'aya take, duk yanda zan nisanta ku a cikin dubu zaku iya gane junanku, kawai dai ina nesanta ku ne bana son kuyi saurin gane junanku."
Sakin yaron yayi ya rumgumeta kamar zaiyi kuka yana fad'in "A da tunani na shine baki sona, idan kina hantarata da zagi na sai naga kamar baki damu dani bane, amma yau na gane babu wanda kike so sama dani Ummy, duk wannan kasadar saboda ni ne kika d'auketa, nagode Ummy, dan Allah ki yafe min komai dana mike."
K'ulli ta sakar mishi a baya tana fad'in "Shashashan banza, taya wai zaka ce bana son ka bayan a cikina na haife ka."
D'ago kai yayi yace "Hauka na ne ke nuna min haka Ummy."
Rank'washin shi tayi a kai tana murmushi tace "Kai fa na daban ne yarona, tashin hankalin da ka so min yanzu shine nayi gudu tun tuni yasa ban fad'a maka ba, nasan in ka sani zaka shelanta ne kowa yaji."
Dariya yayi yana sosa inda ta rank'washeshi yace "Kamar kin sani kuwa Ummy."
Wani kallo ta masa tace "Au! Kamar ma na sani ne? Wa ya fini saninka a duniyar nan."
Hajia dake dariya tana kallonsu ne tace "To ku bani hankalinku nan."
Juyawa sukayi suka kalleta cikin nutsuwa, saida ta kallesu tace "Maganar nan ba zata tsaya iya nan ba, dole akwai wad'anda zamu fad'a ma su san halin da ake ciki."
Kallon juna sukayi suka sake kallon a tare da mamaki Ummy tace "Hajia su wa kenan?"
Cikin kallon basira tace "Hassan, dole ya sani ko da bama so, da kuma Husseina wacce yanzu ni kaina nake girmamata, ita kwatankwacin Alhaji ce da baya nan a gidan nan, dan haka ita ma zata sani, sai kuma Amna amma bansan ku me zakuyi tunani a game da ita ba?"
Tashin hankalin Ummy da ma Hajia ce kuma gashi ta tsallake cikin sauk'i, dan haka yanzu ita bata damu ba duk wanda ma zai ji ya ji a shirye take, cikin ladabi tace "To Hajia ke me kike gani?"
Saida ta gyara zama tace "A gani na ni dai a fad'a mata, ba dan komai ba sai dan halin rayuwa."
Da sauri Ammar yace "A'a Hajia, kar a fad'a mata gaskiya ina jin tsoro."
A tare suka kalleshi da mamaki, Ummy ce tace "Tsoro? Ammar kai d'in? Lallai."
Hajia ce tayi murmushi tace "Ashe dai har abun ya zo inji me tsoron wanka, Ammar kai ne baka so a fad'i gaskiya, har kake cewa kana jin tsoro, tsoron ma matar aurenka."
Kallonta yayi yace "Hajia ko yanzu wallahi a shirye nake dana fad'awa duk duniya waye Shureim, ita dai ce kawai bana son ta sani."
"Saboda me to?" Cewar Ummy tana kallonshi.
Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Saboda tana d'aya daga cikin mata ukun dake kassara tunani na, tana d'aya daga cikin wanda tunanin al'amarinsu ma kad'ai yake firgita min nutsuwa ta, tana d'aya daga cikin sanyin idanu na, d'aya ce daga cikin ukun da bana son ganin tashin hankalinsu."
Kallon Ummy yayi yace "Taya zan so nutsuwarta ta bar gangar jikinta kan abinda na aikata, kwanciyar hankali na ce ita, taya zan so taji abinda nake da tabbacin zai gusar da hankalinta, idan kuma haka ta faru ni wa zai nemo min nawa hankalin, mallakina ce kuma babban rabon dana gada a gidan duniyar nan, idan zan misaltata da gona to bansan adadin girman ekar dake cikinta ba, daga ni har yarana ita ce duniyar mu."
Ummy da taji hawaye sun cika idonta ne tace "Bansan ya zata ji idan aka fad'a mata ba?"
Murmushi yayi yace "Ummy kunsan a ina naji kuwa?"
Girgiza kai tayi tana kallonshi har ya d'ora da "Ita ce ta fad'a min."
Hajia ce tayi saurin cewa "Ita wa?"
"Amna mana." Ya fad'a yana kallonta, zaro ido duka sukayi sai kuma Ummy tace "Amna? To ita a ina taji? Amma kuma banji tashin hankali ba?"
Murmushi ya sake yi yace "Ummy yarinyar nan tayi a rayuwa wallahi, ita ta fad'a min da kanta, amma abun tsoratarwa ta d'auki abun kamar tatsuniya, abun ma dariya yake bata sabodaa ganinta abu ne da ba zai tab'a faruwa ba, sannan tana da yarda akai na da kuma yar uwarta d'ari bisa d'ari."
Da mamaki tace "Amma a ina Amna taji maganar nan?"
Ammar ne yace "A wurin Amie k'awarsu."
Da wani mamakin tace "Amie kuma? A ina Amie taji to? Babu fa wanda yasan da maganar nan."
D'aga kafad'a yayi irin ohon nan yace "Ki tambayi *uwar Shureim*."
Wani galala Ummy ta kalleshi a ranta tace "Kaji wani wai uwar Shureim, to wannan ya ma bari har a gama fad'a ma wanda ya dacen kafin ya fara kiranta da wannan sunan?"
A fili kuma cewa tayi "A gaskiya bana tunanin zata fad'a mata, amma kuma abun da mamaki sosai."
Bud'ar bakinshi cewa yayi "Ummy karki ba kanki wahala wajen sanin yanda akayi taji, kawai share zancen."
Hajia ce tace "Kunga, hak'uri zamuyi mu daure a fad'a mata, kamar yanda na fad'a muku ko saboda halin rayuwa, abinda nake so ku fahimta shine idan yanzu bata sani ba a k'arshe kuma ta ji a wani wurin aka tabbatar mata da gaskiya, to fa ba