Showing 162001 words to 165000 words out of 325849 words

Chapter 55 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

573

Middle Ads

ba, sannan ita kuma Ummy da take da yara biyu d'ayan kawai ta damu da shi, amma Ammar dake babban d'an ta bata nuna kulawa a kanshi ba, kuma ta tabbatar yana gidan dan ya riga sauran ma zuwa gidan, hakan yasa taji ba dad'i sosai ta mik'e daga kujerar ta nufi madafa, wani kwano ta samu madaidaici mai kyau ta zuba dambun ciki sannan ta samu k'aramin shi ta zuba had'in nik'akk'en naman da petit poit sannan ta fito, kai tsaye hanyar waje ta nufa ta kuma sa'ar had'uwa da Kamal ya dawo, kwanon ta bashi tace "Kamal, ka kaiwa yah Ammar kaji."

Kallonta yayi yace "Aunty Zeituna, har yanzu yah Ammar zaki ci gaba da kiranshi?"

Dariya tayi tace "To ya kake so na kirashi? Ai yayana ne a zahiri, ka je ka kai masa ka dawo."

"To." Ya fad'a yana juyawa ya koma b'angarensu, yana zuwa wata sallamar ya sake yi ya shiga, kai tsaye d'akin Ammar ya nufa har Amar na fad'in "Autan Ummy ina zaka je?"

"Wajen babban yaya." Ya fad'a ko juyowa baiyi ba, k'wank'wasa k'ofar d'akin yayi tare da turawa ya shiga, kwance yake yana kallon sama yayi nisa a tunani, har ya tsaya gabanshi ya aje kwanon k'asa bai kalleshi ba saida yace "Yah Ammar ga abincinka nan."

A hankali ya kalleshi ya tashi zaune, kallon kwanon yayi ya sake kallon Kamal yace "Abinci na kuma?"

"Eh." Kamal yace ya juya da niyyar fita, sake cewa yayi "Abinci fa? Wa yace ka kawo min?"

Juyowa yayi yace "Aunty Zeituna ce, amaryar Abba."

Bushewa yayi da dariya kamar mahaukaci sabon kamu, irin dariyar da yake yi ce yasa Kamal cewa "Yah Ammar lafiya?"

Tsayawa yayi ta kalleshi yace "Ko da nace, ni nasan inba bak'o ba babu wanda zai aiko min da abinci, to naga dai ko uwar data haifeni bata damu da ci na ba bare kuma wanda suke kewaye da ita."

Jinjina kai yayi yace "Amaryar Abba, amma me yasa zata aiko min da abinci?" Kamal ne yace "Ni ma ban sani ba."

Da mamaki Kamal yace "Zaka ci kenan?"

K'uri ya masa da ido yana kallo hakan yasa ya fita ya rufe mishi d'akin, yana ganin fitarshi ya shafa cikin da har kukan yunwa yake masa amma kasala ta hana shi fita ya je ya ci abinci, murmushi yayi yace "Zan ci mana Kamal, har na manta kalar d'and'anon abincin gidan mu, ina ma Ummy ce ta aikoka da abincin nan, da na ci da farin ciki da kuma karsashi ko da bana yanayin cin abincin, amma gashi matar data shigo gidan nan jiya wacce nayi mata kashedi akan uwata ita ce ta zubo abinci wai akawo min, duk da bansan manufarta na yin haka ba amma dai hakan yasa na ji kamar an kula dani ne."

D'auko kwanon yayi ya bud'a, take yaji yawunshi sun tsinke, tashi yayi yaje ban d'aki ya wanko hanayyenshi ya fito, saida yayi bismillah tare da fad'in "A'u'zu bikalmatillahi tammat-min sharri ma kalaq." Duk yayi hakane dan aniyarta ta koma mata wai idan ma abinda ya mata jiya ne zaisa ta fara gaggawar d'aukar mataki akan shi.

*A gurguje*

Da magribar wannan ranar aka kawo kayan Amar ma, shi ma dai kamar yanda Ammar yayi haka ya kawo, sai dai ba shine ya kawo ba, wasu daga cikin yan uwa na dangin mahaifinsu da kuma abokan lieutenant ne suka kawo, anan kuma take kafin su tafi Hajia ta shaida musu nan da kwana goma sha hud'u sati biyu kenan za ayi bikin, dan haka a shirya da kyau kafin lokacin, da haka labari ya riski kowa inda aka shiga shirya ma wannan rana.

Wani ikon Allah kuma tun daga wannan ranar kullum akayi abinci na rana da dare sai Zeituna ta fitarwa da Ammar, duk yaron daya tarbi gabanta shi take bawa yana kai mishi, lokacin da lieutenant ya fahimci haka kuma sai yace ta rabu dashi mana shi fa ba yaro bane, akan me ma zata damu da shi ne? Dariya kawai tayi tace tana yi ne saboda Allah, kuma taga shi bai damu da ya zo ya karb'a ba, Hajia ma baida habaici da cewa neman gurin zama ne babu abinda take fad'a mata, haka ma Ummy gani take wahala ce take ba kanta, indai Ammar ne wata rana ya gwasaleta, wannan shine abinda take fad'a, Ammar kuma kuma yanzu ya daina cin abincin waje inba na safe ba, ya sakankance yana cin wanda Zeituna ke aika musu, dan lokuta da dama tare da duka sauran yan uwan take aika musu musamman da dare lokacin duka sun dawo, Ummy da kanta ta shirya tare dasu Amna suka je madarunfa aka kaiwa Hadiza kayan Amna ta gani tasa albarka, data tambayi Ummy abinda za ayi ko ya rage sai tace babu komai da suke buk'ata daga wurinta, alfarma kawai ta nema na ta zo ran damu taga d'akin yarta hakan zaisa taji dad'i, a haka kuma ake ta shirye shiryen biki dan lokacin ya taho sosai.

Wajen amare ma sun gama jarabawarsu sosai aka zage ana ta gyaransu kamar hauka, dan Hajia da kanta tasa ake musu gyaran, da farko suna zuwa ne a musu, amma daya rage sati d'aya sai mai musu gyaran take zuwa gida tana musu, kuma a haka yaran zamanin suma amaren suke k'arawa kansu wani had'in wanda suka koya, Ummy ma haka ta zage tana dafa musu kaji tunda ta ga sauran sati d'aya, da haka har aka riski daren da za'a saka amare lalle.

Duk iyayen na zaune akan teburin cin abinci suna ci suna hira, kuma hakan ya faru ne saboda Alhaji na wurin, ba dan haka ba babu wanda ya isa ya cika Hajia da surutu alhalin tana cin abinci, Amar ne ya shigo tare da Ammar kamar wasu zakuna, Amar ne yayi sallama suka nufi kan teburin yana gaishe da mutanen wurin, Ammar na zuwa hannu ya zura gaban Hajia ya d'auki robar ruwan da take sha ya kifa bakinshi yasha sosai, kowa kallonshi yake har da ita kanta Hajiar, saida ya sauke robar ya kalli kowa dake wurin shima yana murmushi, lokacin da kallonshi ya sauka kan Zeituna wacce kanta ke k'asa ne ya fad'ad'a murmushin shi yace "Ina wuni."

Da sauri ta d'ago kanta lokaci d'aya kuma ta mayar dashi k'asa dan bata zaton da ita yake, duk wanda ke gurin kallonshi sukayi da matuk'ar mamaki, *yau Ammar ne ke gaishe da wani?* gaisuwar ma ga wacce ba'a tsammanin zai iya gaisheta, ganin irin kallon da suke mishi yasa ya sake kallon Zeituna yace " Dake fa nake, *uwa*."

Sake d'agowa tayi cike da tsoron abinda zai iya fad'a mata, suna had'a ido bata san lokacinda tace "Yah Ammar ina wuni."

Murmushi ya mata yace "A'a uwa, ki kira ni Ammar kawai, ko kuma ki kirani da *d'an ki*, tunda ke ma uwata ce."

Wata irin dariyar rainin hankali Hajia ta bushe da ita har da gaggab'awa take, wani kallo Ammar ya mata kafin ya kalli Ummy yace "Ummy ina amaryata take? Ina so zamuyi magana ne."

Hararan sama da k'asa ta masa taja dogon tsaki, mayar da kallonshi yayi kan Zeituna yace "uwa dan Allah zaki iya fad'a min inda take?"

Zeituna da ita dai al'amarin d'an mijin nata ke tsorata ta da sauri tace "Tana d'akin..." Da sauri Ummy ta katseta da cewa "A'a Zeituna, rabu dashi kawai, uwar me zai bata yanzun?"

Tab'e baki yayi ya kalli Zeituna yace "Uwa zan iya baki sak'o wurinta?"

Kamar sakarai haka take kallonshi baki bud'e ta jinjina masa kai alamar eh, da hannu ya mata alama yace " Zo to, sirri zamuyi."

Mik'ewa tayi tsaye zata tafi lieutenant ya daka mata wata harara yace "Wai ke me yake damunki ne? Kanki d'aya kuwa ko kuma ke ma irinshi ce?"

Alhaji ne yace "Babba, ka barta dan Allah."

Murmushi Ammar yayi yace "Abba kwantar da hankalinka mana, babu inda zan tafi maka da matarka, nima fa uwata ce."

Wata harara lieutenant ya wurga masa wanda tasa Ammar kwaso shoki, har zai sauketa akan idon lieutenant sai kuma ya juya ya kalli Amar dake gefenshi ya watsa mishi ita a fuska, Zeituna na zuwa kusa dashi saida ya k'ara matsawa kusa da ita ya juya baya suka bawa mutanen baya kafin ya sassauta murya yace "Uwa ki samu Amna a d'aki ki fad'a mata ta baki kayanta ki kawo min za'a d'auki awonta ne (mesure)."

Jin abinda ya fad'a yasa Zeituna sauke ajiyar zuciya ta kalleshi tace "Toh." Da sauri ta juya ta nufi d'akin Ummy inda amaren suke, tana shiga ta same su tare da wasu daga cikin k'awayensu, gabanta ta tsaya tace "Amna, sak'o daga angonki wai ki bado kayanki za'a d'auki awonki ne."

Kallonta tayi tace "Yah Ammar? D'inkin zai min?"

Da murmushi ta amsa mata da "Ni ma ban sani ba, tashi ki d'auko kawai."

Mik'ewa Amna tayi ta fito Zeituna na biye da ita a baya, d'auko mata kayan tayi ta bata ita ma ta juyo dan kawo masa, tana zuwa ta same shi tsaye kusan Hajia sai kallonta yake, ita kuma ta had'e fuska sai hararenshi take, Amar dai dariya yake musu har yace "Dan Allah Hajia ki ci abincinki kar ki biye masa, so fa kawai yake ki biye masa kuyi fad'a."

Tab'e baki tayi tace "To ai yanzu ni ya daina bani wahala shalele, ka rabu dashi zaiyi ya bari ne inya gaji."

Da wani murmushi a fuskarshi yace "Da gaske Hajia? To zan gani."

Zeituna na bashi kayan a leda ya karb'a ya matse ledar a hammata, ba zato ba tsammani ya daddage ya samu hak'ark'arin Hajia ya danna mata cakulkuli, ( Hajia mutan makka๐Ÿ˜‚), ai wata zabura Hajia tayi daga kan kujerar tare da sakin ihu har cokalin hannunta ya fad'i abincin cikin cokalin ya zube, haba wa ai sai Amar ya fashe da dariya tare da taimakon Alhaji da Husseina, Ummy kam da Zeinabu da Soueiba duk rufe bakinsu sukayi suna toshe dariyarsu, Ammar da tuni ya zura a guje shima dariyar yake, yana kaiwa bakin k'ofar fita daga gidan ya had'e da Hamna ta shigo tare da k'awar ta wacce ya amshi lambarta, tsayawa yayi suna kallon juna da ita b'angare d'aya kuma yana kallon Hamna da wutsiyar ido, washe baki tayi tace "Lah mai kyau, sai ganshi dai yau mun had'u, dama kuma ina son ganinka dan naji dalili da yasa baka kirani ba."

Yanda ta kafeshi da ido alamar tana jiran amsa yasa yayi murmushi ya kalli Hamna yace " Hum! Kinga ranar da kika bani lambar nan, saboda ina tuk'i daga na bawa k'awarki ta saka min sunanki akai, sai kawai tace min wai ta goge, to har yanzu ina so na sani ne gogewa lambar tayi ko kuma gogeta akayi, shine abinda na kasa fahimta."

Wani marairaicewa yayi yace "Dan Allah budurwata ki tayani tambayarta ta fad'a min, na shiga damuwa sosai saboda rashin kiranki da banyi ba, da zaran na kwanta bacci ke nake gani a idona, idan ina wanka ma ke nake ji kamar kina goga min bay..."

Hamna ce ta fizgi hannunta tana fad'in "Dallah *Ami* wuce mu tafi, k'arshen marar kunya ne wannan yanzu saiya fad'a mana abinda kanmu ba zai iya d'auka ba."

Juyowa yayi ya bita da kallo yace "Kunya? Ai laifinku ne inma bana da kunyar, tunda sanda ake rabonta ina bacci kuma babu wanda ya tasheni."

Tsaki Hamna tayi wanda yasa ya juya da hanzari ya kamo k'aramin kallinta, duk da ta tsorata da yanda ya fizgota ya kuma kalleta da jajayen idonshi hakan bai hanata cewa ba "Dallah malam sake ni, ni yanzu sam bana son had'a hanya..."

Bai bata damar k'arasawa ba ya kama dogon hancinta yaja sosai, siririyar k'ara ta saki take idonta suka kawo ruwa saboda zafin da taji, k'ank'ance idonshi yayi yace "Na sake jin tsaki ya fito daga bakinki zuwa kaina wallahi zaki rasa hak'oranki."

Sakinta yayi ya juya zai fita Ami tace "Mai kyau."

Tsayawa yayi ya juyo a hankali ya kalleta, matsowa tayi tace "Nace ka kawo wayar taka saina saka maka lambar ko?"

Saida ya kalli Hamna yace "Ki barshi kawai, wacce ta goge lambar uta zata sake bani ita da kanta."

Yana fad'a ya juya ya fita ita kuma ta kalli Hamna tace "Dan Allah besty ki bashi lambar, wai ko dai ba kya so na auri yayanki ne?"

Dafe goshi Hamna tayi ta mata kallon sakarai tace "Ki farka idan ma bacci kike, nan da kwana uku za'a d'aura aurenshi da Amna."

"Me?" Ta fad'a da d'an k'arfi, kallon k'ofar daya fita tayi tace "Amma kuma alamunsa bai nuna haka ba."

"Shi wani irin mutum ne da ba'a gane gabanshi da bayanshi, k'ok'arin sanin asalin Ammar zai iya tarwatsa miki k'wak'walwa, dan haka ki fita a harkarshi kafin ya fad'a miki abinda zaisa kiyi nadamar sani na a rayuwa, dan ko kad'an bashi da tabbas." Jinjina kai kawai tayi suka shiga ciki.

*Da asuba*...


*Alhamdulillah*
09/09/2020 ร  17:58 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_31_


*Kubra* wacce take kamar 'ya ga Alhaji ce ta zo gidan dan shafe amare da angaye da lalle, d'aya bayan d'aya ta shafawa amaren kafin ta nufi b'angaren samari, d'akin Ammar ta fara turawa a hankali, cikin sa'a k'ofar ta bud'e ta shiga cikin sand'a, amma saita samu Ammar zaune akan sallaya ya tank'washe k'afafunshi, d'agowa yayi yana kallonta da mamakin shigo mishi d'aki a wannan lokaci, ita ma kallonshi take ganin bacci pal a idonshi alamar bai samu baccin ba, murmushi ta sakar mishi tare da matsawa kusanshi rik'e da robar lallanta tana fad'in "Ammar idonka biyu? Ai na d'auka zan samu kana bacci ne ta yanda zan wankeka da lalle."

Saida ya kashe mata kyawawan idanunshi kafin yace "Wanda bai ga annabi ba kuma ina shi ina bacci?"

Wani murmushin ta sake yi tace "Hakane, to naga hannunka."

Kallonta kawai yayi bai bata hannu ba hakan yasa ta d'ebo lallen ta nufeshi da nufin shafa mishi a kai, da sauri ya mik'e tsaye yana rik'e farar jallabiyarsa ya dakatar da ita yace "Tsaya aunty Kubra, kar muyi haka dake fa, me zaki min da wannan sai kace wani mata-maza?"

Gumtse bakinta tayi tace "Lalle zan shafa maka, kuma dai kasan sai an shafa maka ne kad'ai zai baka damar angwancewa da yarinyata ko?"

"A al'adarku ba." Ya fad'a cike da gatsali kafin ya d'ora da "Nuna min ina ne za'a shafa sai ki ban na shafa da kaina, gaskiya bana so jikina ya b'ace da wannan abun."

Tab'e baki tayi tace "Naga yanda za kayi wanka da ruwan lalle kam."

Lallen ta d'ebo a hannu ta mik'o mishi, yamutsa fuska yayi kamar yaga kashi tare da saka yatsarsa manuniya ya lak'ato lallen ya kalleta yace "Ina zan shafa to?"

"A kai." Ta bashi amsa, a hankali ya d'an shafa shi a saman gashi tare da kallonta alamar tambayar sai ina, saida taja tsakin jin haushi kafin tace "Sa a tafukan hannayenka."

Shima juya idonshi yayi suka kalli sama cike da birgewa tare da cewa "Kamata yayi ace mata kawai ke wannan abun, amma maza abun ba tsari."

Wanda ya d'an rage a yatsarshi ya murje a tafukan hannayen yace "To aunty Kubra ni ma dai na shiga lalle, shikenan?"

Juyawa tayi ta fita tana fad'in "Amaryarka dai ta shiga, amma kai kam har yanzu da saura, in baka sake shafa lalle ba ko na wanke 'yar sai dai na kaita d'akin wani amma ba kai ba."

Murmushin gefen labb'a ya mata ya bita da cewa "Aunty Kubra kenan, idan ma kinyi haka da kanki ne zaki dawo da ita ai, dan sai nayi abinda da kanku zaku je ku d'auko ta ku dawo da ita hannu na." Tana fita ya fad'a ban d'aki ya wanke kanshi da hannayenshi ya fito ya rufe d'akin shi ya tafi masallaci.

Kasancewar yau ba zai fita da wuri ba yasa bai dawo daga masallaci da wuri ba, inda amare su kuma safiya na wayewa kowace ta shirya dreba ya kaisu gidan da zasuyi wunin k'umshi, da k'yar Ummy ta had'a kan Amna da Hamna suka tafi tare dan har yanzu ba wani shiri suke ba, kusan k'arfe *08:24* ya shigo gidan, kai tsaye falon Hajia ya nufi, Hajia na zaune Husseina gefenta sai Ummy dake rubuta duk abinda Hajia tace mata wanda zasu buk'ata saboda hidimar, shigowarshi tayi daidai da fitowar Zeituna daga madafa rik'e da robar yaghurt d'in da yasan Hajia kad'ai ke shan ta a gidan saboda rashin zak'inta, abun mamaki yau ma dai kai tsaye madafa ya nufa amma kuma yana fad'in "Uwa kin tashi lafiya?"

Cike da nutsuwa da kuma girmamashi ta amsa da "Ina kwana, antashi lafiya?"

"Lafiya lau." Ya fad'a yana shigewa madafar, Zeituna na zuwa ta sunkuya ta bawa Hajia madarar, tana karb'a ta juya ta nufi madafar ita ma, a cikin ma'ajiyar (store, mangaza) kayan abinci ta ji motsinshi dan haka saita shiga sarrafa indomie da k'wai, yana fitowa da carton d'in lemu a hannunshi dan ya saka a fridge ya ganta, kusanta ya matsa yace "Uwa girki ake yi?"

Ba tare data kalli k'wayar idonshi ba tace "Eh, na ga baka fita bane, shine zan d'ora maka indomie."

K'ura mata ido yayi yana kallo kamar mai tunani kafin yace "Uwa, meyasa kika damu da bani abinda zan ci ne? Alhalin ni ban buk'aci haka ba, kuma ina da wayon da zan iya nemawa kaina idan ina buk'ata? Meyasa?"

Har yanzu ma ba tare data had'a ido dashi ba saboda kwarjinin da yake mata tace "Yah Ammar ba saida wani dalili sannan zan kyautata maka ba, kawai naga kai baka neman abincin ne alhalin akwaishi, sannan kuma babu mai tambayarka ka ci ko baka ci ba, sannan ko da

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login