Showing 159001 words to 162000 words out of 325849 words
bane, wallahi sai nace wani d'an Allah bani ne kai, sakarai kawai.*"
Wata marainiyar dariya ya mata tare da k'ok'arin mayar da hawayen da suka cika idonshi taf, gyara tsayuwa yayi ya shirya dan ya fad'a mata abinda har ta mutu bata mantawa, sai dai kuma kafin ya fad'a Hajia ta juyo ta kalli Ummy tace "Sa'ada kina jin rashin mutumcin da d'an ki ke shuka min ko? Wallahi idan bai kiyayeni ya kusa barin gidan nan."
Daga inda take tsaye ta wurgo masa da harara kafin ta kalli Hajia tace "Kiyi hak'uri Hajia, ni kaina al'amarin shi ya fara bani tsoro, hakan yasa ma nake ganin da k'yar in aljanu basu shafe shi ba, dan a yanzun ni kaina barinshi gidan nan ne kad'ai kwanciyar hankali na."
Wani shak'iyin murmushi Hajia tayi ta kalleshi tace "Kaji ko? Uwarka ma data haifeka tana so kayi nesa da ita, bare kuma ni da ban haifeka ba, dan haka ka kiyaye."
Tunda Ummy ta fara magana Zeituna dake nesa da ita ta k'ura mata ido, jin furucinta akan Ammar ba sabon abu bane a wurinta, amma ta rasa dalilin da yasa yau taji babu dad'i, a zuciyarta take fad'an "Akan me Ummy zata fad'i haka akan d'an data haifa? Meye ga Ammar d'in da har ya dace da wannan furucin?" Ita kam bata gani ba sai ma zunzurutun soyayyarta da yake d'awainiya da ita, soyayyar da har ta isa ta sashi ya ma mahaifinshi kashedi akan ta, amma ace ita tana fad'in haka akan shi, gaskiya har ranta ba taji dad'i ba. Lieutenant kam kallonta yayi kawai ya tako ya zo gaban Hajia ya gaisheta, duk lokacin Ammar na tsaye da Amar a bayanshi, kawar da kanshi gefe yayi ya d'anyi murmushi mai nuna k'unar zuciya da takaici, lokaci d'aya kuma ya kalli Ummy yana wannan murmushin yace "Ina da shafar aljanu kam, na tuna muku idan kun manta, mufa duk aljanunmu na gado ne, sai dai bansan daga ina ne muka gadosu ba, daga b'angaren uwa ne ko kuma uba, ni kuma aljanin daya shafeni sunanshi *ifritu*, shiyasa muke kama da shi a halayya."
Juyawa yayi ya bar falon lieutenant ya bishi da kallon jin haushi, sai lokacin Zeituna ta tako cikin mutuwar jiki dan dama ga ciwon jikin da ubansu Ammar ya saka mata, ga kuma al'amarin wannan gidan data gama fahimta ba'a zaman lafiya, tana zuwa kusan Hajia ta zube gwiwoyinta k'asa ba tare data had'a ido da ita ba tace "Ina kwana Hajia."
Wani banzan kallo Hajia ta mata ta yamutsa fuska tace "Mik'e."
Jiki na rawa Zeituna ta mik'e tsaye kamar yanda Hajia tace, sake kafeta tayi da ido tace "Wuce ki zauna." Ta fad'a tana nuna mata kujerar dake fuskantarta, rintse ido tayi ta fara takawa da k'yar har ta isa kujerar ta zauna, tana zaman ta d'an gyara zamanta kamar zata zame daga kan kujerar saboda rad'ad'in da take ji, tab'e baki Hajia tayi ta kalli lieutenant tace "Hassan dan Allah ko kunya baka ji ba? Yanzu k'azamar yarinyar nan ce daga kawota jiya shine har ka kusanceta, ashe dama kai ma kana sonta munafurcine kawai irin naku na maza."
Ummy na jin haka ta bar wurin tayi madafa kamar zatayi kuka, tunda ya rintse ido bai bud'e ba sai sanda kanshi da yayi k'asa ya kasa ko da motsin arzik'i, hararenshi tayi tace "Tashi dallah malam ka tafi inda zaka, ko kuma ba zaka fita ba yau zaka zauna wajen yar tsanar taka ne?"
Sululu ya mik'e ya nufi k'ofa bai yarda ya had'a ido da kowa ba, yana daf da isa bakin k'ofa tace "Sakarai kawai, wannan ma har mace ce."
Saida ya shiga mota ya zauna ya waro idonshi da kyau, take a wurin yaji wata siririyar k'walla ta gangaro mishi a gefen idonshi, yatsa yasa ya share kafin ya tayar da motar ya bar gidan. Ammar ma na fitowa daga nan d'akinshi ya koma ya kwanta zuciyarshi babu dad'i. Haka ma Zeituna daga nan wurin kasa tashi tayi saida Hajia ta kalleta cike da k'yama tace "Kinga yarinya, kada kiga anyi auren nan har d'ana ya sanki 'ya mace ki d'auka wai kin samu wurin zama kenan, ba zaki tab'a jin dad'in zaman nan ba indai ina raye, nafi kowa saninku ku talakawan nan, na tabbatar akwai abinda kika wa Alhaji da yasa ya aura sa d'an shi ke, watak'ila ma shi Alhajin kika so samu."
Da sauri Zeituna ta d'ago kanta ta kalleta, amma kwarjininta yasa ta kuma sadda kanta k'asa, ci gaba tayi da cewa "Amma da kika ga babu wuri a gidan da zaisa ki samu sunan kishiyata shiyasa kika samu babban d'an mu, to duk da haka baki tsira daga kaidi na ba, dan nasan kinsan ni ke mulki a gidan *Suley Gaga*, abinda na fad'a dashi ake aiki ko ba'a so, ba wai 'ya'yana ba, har shi kanshi mijin nawa da kuma jikoki na ni ke juya al'amuransu, dan haka ki kiyayeni wallahi."
Saida ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya ta nuna mata k'ofar madafa tace "Malama tashi ki shiga sahun masu aiki, karki d'auka kinyi aure a cikin gidan nan ne dan ki samu hutu daga waccen bautar da kike, ina! Ba haka bane? Yanzu ma bauta ta fara, dan zaki min kuma ki ma mijinki da 'ya'yan danginshi, dan haka tashi ki fara tun yanzu dan ba hutu ya kawoki ba."
Ai da sauri Zeituna ta mik'e ta nufi madafar ta ma manta da ciwon dake jikinta, tana shiga dukansu suka juyo kallonta, Zeinabu kallonta take tana murmushin mugunta wai an ma Sa'ada kishiya, cike da izgilanci tace "Lah! Amarya, meya kawoki madafa yanzu? Dan Allah ki koma karki ja mana magana, mu ma ba girki mukeyi ba kawai dai muna taya su Nana ne."
Cikin rashin sakin jiki Zeituna tace "Ina kwananku aunty."
Soueiba ce ta amsa mata da "Lafiya lau Zeituna, antashi lafiya?"
A hankali ta amsa da "Lafiya lau." Soueiba ce ta sake cewa "Ya kwanan bak'unta kuma?"
Shiru tayi wannan karan sai Sa'ada da tace "Kije ki zauna zamu k'arasa."
Zatayi magana suka ji muryar Hajia a bayansu tace "Duk wannan yawon naku amma girki ya kasa kammala sama da awa d'aya?"
Kowa a tsorace ya juyo uwa uba Zeituna da taji kamar tayi fitsari, cikin i'ina Nana tace "Kiyi hak'uri Hajia, saura kad'an ya k'arasa nuna ne."
Zeinabu ma wurk'il wurk'il tayi da ido tace "Bari naje ni na gyara wurin cin abincin kafin ku ida"
Fita tayi Hajia ta bita da harara kafin ta kalli Nana tace "Na baki minti biyar naga komai a gabana, idan ba haka ba kin dai san akwai masu neman aiki dake jiran samun irin damarki."
Tana fad'a ta juya ta fita, da sauri Nana ta sake bud'a tukunyar dan duba perper soup d'in kayan cikin ragon, amma abun mamaki da al'ajabi yana nan kamar dai yanda ta sakashi, a hakan ma wai dan ta silalasu tun jiya ta aje, amma yanzu kama daga kayan miyan zuwa naman komai na nan da ranshi yanda ta zuba, idonta cike da hawaye ta kalli Ummy tace "Aunty, wallahi har yanzu ko alamar dahuwa baiyi ba, bansan ya zanyi ba, gashi Hajia ta bani k'ank'anin lokaci, nasan lokacin barina gidan nan ne yayi."
Soueiba da ummy6ne suka matsa suka duba tukunyar, da tsantsar mamaki Soueiba tace "Amma ya ci ace abun nan ya dahu duba da ko da na sameki madafar nan har kin soya miyarki."
Ummy ce tace "Gaskiya kam, dan ko ni da na zo daga baya na samu tana shirin tsayar da ruwan miyar, da shigowata kuma yanzu a k'alla na d'auki minti kusan talatin, amma ace bai dahu ba? Abun kam da mamaki."
"Yanzu ya zamuyi? Wallahi a tsorace nake, Hajia ta turo ni ne dan na kama aiki, kar ta d'ora min laifin." Cewar Zeituna a matuk'ar razane. Matsawa Ummy tayi ta sake bud'ewa tukunyar wuta tana motsawa ta ga ko ya fara d'aukar hanyar dahuwa, babu wannan alama dan haka ta rufe tukunyar tace "Mu bashi minti biyar d'in shima muga ko zaiyi."
Baya suka ja wasu daga ciki suka zauna kan kujerun da suka k'awata madafar suka buga tagumi, dan kowa yana da tabbacin ba zai sha ba inhar basu gama kan lokacin da aka basu ba. Lokacin da aka basu na cika Ummy tayi saurin bud'a tukunyar, amma juya iya yau babu abinda ya sauya, abun mamaki ne wannan matuk'a, dukansu babu wacce bata nuna alamar wannan mamakin ba, Ummy ce tace "Anya kuwa? Ko dai..."
Sai kuma tayi shiru sai Soueiba ce tace " 'Yan biyu?"
Ba tare data kalleta ba tace "Bani da tabbas, amma kuma ai basu da k'ohi yanzu."
"Kada muyi saurin yanke hukunci, amma wannan abunda yake faruwa yafi kama da aikin 'yan biyun gidan nan." Cewar Soueiba, girgiza kai Ummy tayi tace "Ko hakane ma sai dai aikin Amna, dan tafi 'yer uwarta mugunta tun suna yara haka nasha wahalarsu."
Ajiyar zuciya Soueiba ta sauke tace "Sai kiji ki lallab'a mana ita mu samu mu ida girkin nan."
Murmushi Ummy tayi tace "In dai har Amna ce, to ba zata hak'ura ba sai dai kawai wanda ya rabasu jiya yanzun ma ya bata hak'urin, dan nasan tana fushi ne saboda an kirashi ya tilasta ta ko kuma dai dan tabawa yar uwarta hak'uri."
Soueiba ce tace "To kiyi magana da Ammar d'in mana shi ya rarrasar mana ita."
"Ba zan iya ba, ke kije." Ta fad'a kai tsaye. Kallonta Zeituna tayi sai Soueiba data kalli Nana tace "Kinga Nana, tun kafin Hajia ta dawo ki hanzarta b'angarensu Ammar ki kira shi, dan naga motar shi har yanzu tana nan alamar bai fita ba."
"To." Nana ta fad'a tana fita daga madafar, a hankali ta bi ta bayan Hajia ta sulale ta bar d'akin ta je b'angarensu Ammar, babu kowa a falon amma kuma k'ofar bud'e, ita kuma har ga Allah tana shakka da tsoron halin Ammar data shiga dan ta bubbuga k'ofar shi, dan haka ta juyo ta zab'i ta gaya musu su suje da kansu, tana dawowa kuma Ammar ya d'auki makullan mota ya bar gidan wanda yayi daidai da fitowar Soueiba dan ta mishi magana, amma kash har ya fita daga gidan sai komawa tayi.
Sanda Hajia taji meke faruwa da kanta ta samu Amna har d'aki tana gaggawar shiryawa zata tafi makaranta wajen jarabawa, tatas ta mata ta zageta uwa da uba sannan tace in har abincinta bi dahu ba zata kuma ci mata uwa, haka Amna ta fita rai a b'ace akan motonta dan Hamna ta jima da tafiya, amma tayi niyyar yau Hajia ba zata ci abincin ba ko da na rana ma tunda bata iya bayar da hak'uri ba.
A tak'aice dai ๐ Hajajju sai yan dubaru tayi, yara ma haka aka musu dubaru aka tura su makaranta, Ummy ma haka dubarar tayi kafin ta wuce asibiti inda ta samu Ammar yau ya rigata zuwa, amarya Zeituna ma a d'akinta ta samu madara da cornflakes ta mishi had'in kauri tasha ta kwanta tana tunanin ahalin gaga. Da rana sam Nana ba tayi tunanin komai ba ta gyara shinkafa ta bayar aka b'arzota ta d'ora tukunyar dambu, ba b'ata lokaci tukunya ta taso aka fara yamutsa dambu, ana gama gyara komai aka d'ora a madambaci aka rufe, nan Nana ta shiga sarrafa mahad'in dambu, 'yar k'aramar sauce ce mai nik'akk'en nama da albassa mai yawa, saida ta fuskanci yanzu dambunta ya isa ta dubashi ta tunkari tukunyar, tana bud'awa bud'e baki tayi kamar zata k'urma ihu tare da d'ora hannu d'aya bisa kai tace "Na shiga uku, yanzun ma?"
Da sauri Zeinabu data shigo tace "...
*Alhamdulillah*๐
09/09/2020 ร 17:58 - Ummulkhairi: ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*BADAK'ALA*
๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ _*AHALI NA*_๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
๐ณ๐ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```
_Bismillahir rahamanir rahim_
_30_
"Mun shiga uku! Kar dai ki ce har yanzu ma ba zamu ci abinci ba?"
Cike da tabbatarwa tace "Ai kuwa dai wallahi da alama."
Juyawa tayi ta fita tana fad'in "A'a wallahi ba zai yiwu ba, bari na d'auko wayata na kira Sa'ada ta zo ta sa Amna ta sakar mana tukunya, yau ni naga ikon Allah."
Tana daf da kaiwa d'akinta lieutenant ya shigo, wanda ya kasa zama ya matsu ya ga halin da Zeituna take ciki, sunkuyar da kai tayi tace "Ina wuni Abban Ammar."
Cikin sakin fuska ya amsa da "Lafiya lau, ya gidan?"
Ba b'ata lokaci tace "To da sauk'i dai gaskiya." Da mamaki ya kalleta yace "Lafiya dai ko? Ko wani abun ya faru ne?"
Cikin sunkuyar da kai ta fad'a mishi duk abinda ke faruwa, murmushi taga yayi yace "To ku samu ku lallab'a ta mana, kunsan dai fad'a da zagi ba zaisa ta huce ba."
"Eh hakane, yanzu ma zan d'auko waya ne na kira Sa'ada saita lallasar mana ita."
Da 'yar dariya lieutenant yace "To ke ba zaki lallab'ata ba?"
"To ai ni bansan ta inda zan fara bane, ita kuma ta saba da rigimar bibbiyu dama."
Dariya ya sake yi yace "Da gaskiyarki kuma, tana ina Amnar?"
Nuna sama tayi tace "Tana sama dai a tunani na."
"Bari na jaraba na gani ko zan iya." Ya fad'a yana wucewa d'akinsu dake sama, zaune tayi falo ta jira shi ya fito taji ya suka k'are, yana zuwa saida ya k'wank'wasa k'ofar d'akin yayi sallama, kusan a tare Hamna da Amna suka amsa wanda kowace ke kan gadonta babu mai kallon wata, saida kowace ta gyara zaman tufafinta kafin Amna da gadonta ne farko ta taso ta bud'e k'ofar, gaishe shi tayi ya amsa cikin sakin fuska tare da dafa kanta, murmushi yayi kafin yace "Amnata baki jin yunwa ne?"
Da sauri ta d'aga matsakaitan idonta ta kalleshi sai kuma tayi k'asa da su tana jujjuyasu, jin shiru yasa yace " 'Yata, yunwa nake ji, kuma na zo gida an fad'a min wai kin rik'e tukunyar girkin, shine nace bara na zo na rok'i alfarma, ko baki saketa dan ni ba ki saki dan k'annanki da kuma angonki Alhaji, wanda kinsan basa juriyar yunwa, da safe ma ance basu ci wani abun kirki ba."
Ganin tayi shiru yasa ya sake dafa kanta yace "A taimaka mana kinji, kiyi hak'uri komai ya wuce."
D'agowa tayi ta kalleshi tayi murmushi tace "Ba komai Abbanmu, nima ba'a son raina bane haka ta faru."
Murmushi ya mata yace "Nagode 'yata, Allah miki albarka."
Da murmushi ta masa da "Ameen Abbanmu."
Juyawa yayi ya samu Zeinabu zaune yace "To ku tashi ku duba tukunyar ku gani."
Yanda yayi maganar yasa ita ma tayi dariya tace "Yaran nan, mun gode Allah da yasa basu da k'ohi, da ina ga zuwa yanzu duk mun kamu da ciwon yunwa."
Dariya yayi yace "To wai ya akayi ma haka ta faru bayan kuma basu da k'ohi? Abun da mamaki fa."
"Wallahi nima ya ban mamaki." Madafa ta wuce shima ya shige d'akin Zeituna, kwance ya sameta akan sallaya ta idar da sallah, yanzu ma doguwar riga ce jikinta da hijab, sululu ta mik'e zaune cike da kunya tace "Sannu da zuwa, ina wuni."
Yaji dad'in gaisuwar data mishi dan haka ma ya saki murmushi ya sunkuya ya d'agota ta mik'e tsaye, saida suka k'arasa bakin gado ya zauna sannan ya zaunar da ita kan cinyarshi yana kallon fuskarta, yanda take sunkuyar da kai kamar zata nitse k'asa, d'ago hab'arta yayi ya juyo da kallonta kanshi yace "Wai ke yaushe kunyar nan zata k'are ne? Ba zan iya tuna ranar da muka had'a ido dake ba fa? Ya kamata ace ance yanzu kin saba ko dan igiyar data d'aure mu wuri guda ni dake."
Zeituna dai k'ala ba tace ba sai sunkuyar da kai da take, ba tare daya daina mata kallon nan ba yace " Na zo duba jikinki ne fa, to ya kike ji yanzu? Ba kya jin ciwon komai?"
Da sauri tasa tafukan hannayenta ta rufe fuskarta saboda tsananin kunyar data kamata, dariya yayi tare da k'amk'ame ta sosai a jikinshi yana sumbatar ta, (Harkar fa ta manya ce, nayi nan ni dai๐โโ๏ธ).
Zeinabu na zuwa suka duba tukunya sai suka ga har dambun ya fara rusuna alamar zai d'auki dahuwa, ajiyar zuciya ta sauke tace "Ikon Allah, duk da ana cewa a daina yarda da canfi amma wani abun idan ka ganshi dole ka amince, to Allah ka gafarta mana."
Lieutenant bai jima ba ya sake fita dan baya son Hajia ta saka masa na jiyamu, fitarshi kuma ta bawa Zeituna damar zuwa madafa aka k'arasa sauran aiki da ita, suna cikin jera kwanukan abincin Ummy ta dawo, wanka tayi ta fito lokacin har Hajia ta ci nata abincin ita kad'ai akan makeken teburin daya had'a kujera goma sha biyu, fitowar Ummy suma matan da su Hamna suka zauna suka ci na su abincin, a wurin ne Ummy ta dannawa Amar kira, bayan ya d'auka tace "Kana cikin gida ne?"
Daga b'angarensu ya amsa da "Eh Ummy, kin dawo ne?"
"Na dawo, ka jira yanzu za'a aiko miki da abinci." Amsawa yayi da "To Ummy."
Tana aje wayar ta kalli Kamal dake kusa da ita tace "Ka shiga madafa abincinsu na nan a kula ka kai musu."
Soueiba ce ta kalli Kamal tace "Daga nan ka duba ka gani ko Jibril yana nan sai su ci tare."
Da kai kawai ya mata alamar to, Zeinabu ce ta kalleta tace "Yana ciki ai, na ga shigowar motarshi kuma har yanzu tana nan, tare da Junaid ma suka shiga."
Soueiba ce tace "Ah to shikenan, ka kai musu kawai, kace idan ma bai ishesu ba sai su zo a k'ara musu, dan yau kowa ya wuni da yunwa saboda Amna yau ta hora mu."
Dariya suka kwashe da ita banda Zeituna da tayi shiru tsananin mamaki ya k'ara rufeta, sai yanzu ne data shigo gidan ta fara fahimtar wata b'oyayyar rayuwa da suke, kowa d'an shi kawai ya sani bai damu dana d'an uwa