Showing 66001 words to 69000 words out of 325849 words
da lema (para-pluie) wacce zan dinga kare wannan katob'arar fa, dan wani abun idan ya murguzo kasa duk'ewa nake.*
Lieutenant da yake son fita amma Hajia tace babu inda zashi sai yaran sun dawo taji daga inda suke, yana jin k'arar motar ya fito ya duba, ai kuwa a lokacin da Amma ke tafiya zai bud'e k'ofar b'angaren su suka ji yace "To ku wuce muke ciki."
Take suka fara rarraba ido suna kallon kallo, kamar wanda k'wai ya fashe ma a ciki haka suka fara tafiya, murmushi Amar yayi yace "Abba barka da dare."
Dak'uwa ๐๏ธ ya watso mishi tare da nuna musu hanya su wuce gaba, Ammar dake kallon abinda ke faruwa baida niyyar tahowa, lieutenant ne yace "To ubana, sai nayi magana ko?"
Wani farrrr yayi da ido kamar mace na son karb'ar kud'i hannun mai gida kafin ya taho ciki takun k'arfi, saida ya kawo daf dashi zai wuce lieutenant ya d'aga hannu da nufin bugunshi a k'eya, da sauri ya duk'e tare da ja baya ya d'ago yana kallonshi yace "Abba wai sau nawa zan fad'a maka ka daina sarar dukana a kai? Kayi karatu fa, ko dai ka manta abinda ka karanta ne a cikin aji game da abubuwan dake cikin kai?"
A hassale lieutenant yayi kanshi ya zura hannu zai shak'o wuyanshi ya sake zillewa, tsaye yayi yace "To wai yanzu dukana ne kake so kayi ko me? Kasan dai na wuce wannan matakin ko?"
Saida ya nuna shi da yatsa yace "Dan Allah ka zo nan ka gani idan ban dake ba, Ammar ni zaka raina ka mayar wani mahaukaci."
Saida yayi nesa dashi ya ya wuce ya nufi falon Hajia yana fad'in "So ne kawai yake a kafa min mugayen hak'ora, ya bini a guje ya fad'i shikenan ace na kashe ubana, haba, tsofi sai jaraba bakinsu ko ciwo baya yi."
Yana dosowa falon ya canza salon tafiya da yanayin fuska irin ba magana kuma ba wasa bare dariya, yana shiga ya samu su Junaid sunyi cirko cirko zaune a k'asa kowa kanshi k'asa, gefenshi ya kalla inda Ummy, Soueiba da Zeinabu suke zaune, sai gefe guda su Amna ne da Umaima ke ta latsar wayar amma banda Hamna dake shan kankana da cokali mai yatsu, "Wato dan raini a gaban yaran nan za'a musu fad'a? Kai ba zai yiwu ba gaskiya."
Kallonsu yake yana so su kalleshi ko zasu fahimci kallon amma rashin sa'a babu wacce ta kalle shi har kankanar ma, a hankali ya cire takalmi ya k'arasa kusansu Junaid, amma saboda iko sai yayi zaune akan kujera yana kallonsu su dake k'asa kamar sun zo d'aukar karatu, Ummy ya kalla wacce idonta ke kanshi kamar ta zundumo mishi zagi, kallon Husseina yayi dake zaune kujera d'aya da Labaran da kuma Alhaji, hannu ya d'aga musu ba alamar fara'a yace "Barkanku da dare."
Husseina dake ta doka uban murmushi ce ta amsa mishi da "Barka Ammar."
Hajia ya kalla wacce bata da niyyar magana har yanzu, a ranshi yake fad'in "Wannan indai ba shanye Alhaji kikayi ba me zaisa gashi zaune amma ke ce mai zartar da hukunci, Allah ya sawak'e miki."
Ganin har yanzu shiru yasa ya kalli mutanen d'akin "Idan an gama karatun saimu rufe da salatin annabi ko?"
Su Amar dake kusa dashi duk rik'e dariyarsu sukayi, hakan ya hassala Hajia ta mik'e tsaye da fad'in "Kaiiiii."
Yana jin haka saiya jingina a kujera ya d'ora hannunshi a matangalin kujera yana shafar k'ulun hallitar dake mak'ogwaronshi wanda bak'in gashi mai silb'i ya rufe shi, kallon yan k'asa tayi dan sunfi dama dama tace "Daga ina kuke?"
Shiru ne ya d'an ratsa wurin yayin da Junaid ke ganin ba zai yarda a d'ora musu laifi ba, dan haka ya d'ago ya kalleta yace "Daga Goure."
Yatsina fuska tayi ta kallesu da kyau tace "Me kuka je yi a Goure? Wa ma ya aike ku?"
Junaid dake jin wani sanyi na ratsa zuciyarsa babu fargaba yace "Munje sulhunta tsakanin Maryama ne da iyayenta, sannan na gabatar da kaina a matsayin mai son aurenta, kuma sun amince."
"Wacece hakanan kuma?" Hajia ta tambaya cike da rainin wayo, shiru ya d'anyi dan haka ta kalli Zeinabu dake kallon Junaid da mamaki tace "Ke kinsan wacece hakanan?"
Cike da ladabi tace "Umma ita ce yarinyar da yace yana..."
Bata bari ta k'arasa ba tace "Ku ce min karuwa, wai karuwa kake nufi? Neman aurenta kaje kenan ko me?"
Shiru dukansu sukayi, cikin taushin murya tace "Shalele, har da kai da nake ganin kamar kana da hankali? Ya zaka biye musu wajen yin wannan d'anyan aikin? Halan wani ne ya tilastaka?"
Ta fad'i hakane tana kallon Ammar da shima yana jin haka ya kalleta, dan yasan shi take nufi, d'auke idonshi yayi dan haka Amar yace "Babu wanda ya tilasta ni, kawai naga yan uwana zasu tafi ne ni kuma na tafi tare da su."
D'aga kai tayi sama cikin gadara tace "Hakan na nufin kenan kun girma? Kun isa ku yanke hukuncin daya shafi rayuwarku ba tare da sanin kowa ba, hakan na nufin zaku iya ji da al'amari komai girmanshi idan ya taso muku ba tare da shawarar ko da iyayenku ba, to da kyau, amma ku saurare ni kuji."
Fuskantarsu tayi da kyau tace "A gidan nan ba ayi ba ba kuma za ayi wanda zai taka min doka ba ya kwana lafiya, matuk'ar ina raye banga wanda ya isa a gidan ya dinga juya rayuwarshi yanda yake so ba, dan haka tunda kun nuna min zaku ja dani, ni kuma zan dakatar da al'amarin yanzun nan."
Juyawa tayi ta koma inda take ta zauna ta d'ora gwiwoyin hannunta a saman cinyarta kafin tace "Hutun makaranta da za'a bayar na kwana goma nan da sati uku, ku shirya mishi da kyau, dan aurenku za ayi."
Da sauri suka d'ago suka kalleta inda Ammar ya dakatar da shafar gemun da take yana mata kallon mai bisa ruwa, jinjina kai tayi da yake nuna tabbas babu fashi tare da d'orawa da " *Shalele* zaka auri 'yar uwarka *Umaima*, *Junaid* zaka auri 'yar uwarka *Hamna*, kai uban sarkin marasa kunya zan had'a ka da wacce baka isa kace ta maka laifi ba bare harka zalinceta ( *Ammar*), za'a d'aura aurenka da *Amna*."
Juyawa tayi ta kalli Jamila sannan ta kalli Jibril, ita dai badan tana so ba zata had'a tsatsonta dana Husseina, amma idan ba tayi ba yanzu tsohon na zai kawo mata cikas a lamarinta, dan haka tace "Kai kuma *Jibril* zaka auri Jamila, wannan shine hukunci na, da wani mai ja."
Ta fad'a tana kallon iyayen duka, amma cikinsu sai kowa ya girgiza kai harda arhar murmushi da suke mata ana fad'in ai duk gida ne dan haka abun farin ciki ne, da murmushin k'asaita tace "Ku tashi ku bani wuri."
Mik'ewa sukayi kamar babu lakka a jikinsu, amma Ammar ko niyyar tashi ma baiyi ba, sun fara tafiya tace "Shalele."
Juyowa yayi tace "Idan kayi wanka ka ci abinci ka same ni d'aki na."
"To." Kawai ya fad'a suka bar falon, kallon Ammar tayi tace "Ko saina tasheka ne kai kuma?"
Saida ya d'an harareta na wucen gadi kafin ya mik'e ita kuma tsaf ta gane hararenta yayi, dan haka ma tace "To ko da magana ne?"
Cikin takonshi na isa yace "Ke ma kisan ai idan da maganar zan fad'a, dan bana tashi da kwananniyar magana a baki na."
Hamna ce ta saki cokalin hannunta saboda wani abu da taji, juyowar da Hajia tayi ne tasa ta saurin d'aukar cokalin, mik'ewa tayi ta aje farantin kankanar ta fita farfajiyar gida, Amna kuma Inna lillahi kawai take maimaitawa, wai da gaske ita ce aka had'a da Ammar? Tab', lallai sunanta margayiya daga yau, to ita ta ina zata iya da auren Ammar? Mutumin da idan ya fad'a maka wata maganar sai kayi sati kana kuka, shine zatayi zaman aure dashi? Umaima kuma har cikin ranta zab'in ya mata, dan dama Amar na masifar birgeta, haka ma Jamila sam bata ji a ranta wai an tauye ta ba, sai dai ta d'auka zata fara shan bikin yayunta ne dan ita ce k'arama a duk cikinsu, to amma haka Allah ya so sai fatan alkairi kawai.
Suna shiga b'angaren su kowa wanka ya shiga cikin matuk'ar sanyin jiki, amma banda Ammar da shi sam baiji wani abun bak'in ciki ba, hasalima yace Amna dai ce ta shigo d'akin shi a matsayin mata, Allah yasa ta mata shirin da zata uya zama da shi, duk ranar daya samu wacce zuciyarshi ke *so* to ko a yau Amna ta zo gidan saiya fad'a kuma saiya aureta babu mai hanawa.
*WAIWAYE*
_(ADON TAFIYA)_
*Suley Hassan Gaga*
05/06/2020 ร 20:32 - Ummulkhairi: ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*BADAK'ALA*
๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*Labarin gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ _*AHALI NA*_๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
_Allah ba dan mu ba ka yafe mana zunubanmu, Allah ba dan halayenmu ba ka gafarta mana kurakurenmu, Allah dan rahamarka ka jik'anmu ka mana gafara, *Astagfirullah wa atubu ilaikh*._
๐ณ๐ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya madaurinki d'aya)```
_Bismillahir rahamanir rahim_
_10_
*Suley Hassan Gaga*
Haifaffen garin *Marad'i* dake jamhuriyar Niger, a wata unguwa da ake kira *d'an gulbi*, mahaifinshi Alhaji Hassan yana da mata biyu, ta farko ita ce *Rumanatu* wacce suke kira da Ramma, tana da 'ya'ya uku, babban shine *Innusa* (Yunus), sai k'anwar shi *Barira*, sai kuma k'aramar *Rahmatu*, sai matarshi ta biyu *Saratu* wacce ita ce mahaifiyar Suley da 'yan uwanshi mata 'yan biyu masu sunan *Hassana* da *Husseina*, iyalin Hassan Allah ya musu baiwar haihuwar yan biyu, hakan yasa a ahalin nasu suke da yan biyu masu yawa maza da mata, Ramma na da 'ya'ya uku namiji d'aya da mata biyu, sai dai kasancewarta shu'umar mace yasa ita ke juya gidan da mutanen cikin shi.
Hassan yana da tarin arzik'i kama daga shanu zuwa tumaki da gonaki, a zamaninshi yana d'aya daga cikin masu kud'in da ake lissafawa a garin maradi da kewayenshi, amma dayake ya samu hatsabibiyar mata data riga ta gama mallakeshi da sihiri saiya zamana dashi da talaka duk d'aya, domin kuwa gidanshi ma ba'a cin abinci mai kyau bare suruta, tunda Saratu ta shigo gidan take fuskantar matsi daga gareta inda ta mayar da ita kamar baiwa a gidan mijinta, duk wahalar gidan ita ce har lokacin da rabon 'ya'yansu ya koka suma suka durmiya cikin wahalar, duk da kasancewar Suleymane babba kuma namiji amma haka ya zama kamar d'an daudu dan duk wani aikin gida na mata babu wanda bai iya ba, haka suke wannan rayuwar kamar bayin da aka siyo da kud'i dan babu wanda zasu fad'a ma ya taimakesu, duk da lokuta da dama Husseina na basu matsala dan ita ce marar hak'uri, amma haka zatayi saboda uwar na tausarta da cewa tayi hak'uri wata rana sai labari.
Saratu dama marainiya ce ba uwa ba uba, k'anin mahaifinta ya bayar da aurenta ne saboda dukiyar Alhaji Hassan, hakan ne yasa babu wanda suke kaiwa kukansu ma bare su saka ran za'a share musu, a cikin wannan bautar da k'ask'anci tafiya tayi nisa yara duk suka mallaki hankalin kansu, 'yan matan sun zama cikakkun 'yan mata da suka isa aure, haka shima Suley ya girma sosai, sai dai matan kamar mujiya suke a cikin tsuntsaye saboda bak'in jini, domin kuwa babu mai kallonsu da sunan so ko k'auna, abun duba kuma shine gasu kyakyawa saboda sunyi kama da mahaifiyarsu wacce ita d'in asalin *babarbara* ce ta *Diffa*, amma haka suke ba mashinshina sai wahalar gidan ubansu kamar zata kashesu, a cikin haka Hajia Ramma ta aurar da yaranta mata, aurensu kamar samun wani kasone daga 'yancin Saratu da 'ya'yanta, dan dama da suna gidan har wankin kayansu su keyi, duk wani abu da zaisa su motsa jiki to saidai susa su musu, dan haka wahalarsu ta ragu da sukayi aure.
Shekaru sun kuma ja dayawa amma su Hassana har yanzu babu ma-nemin aure, hakan ya fara damun Saratu fiye da zato ta yanda har ta kan zubar da hawaye idan ta gansu masha Allah sunata yawo a tsakar gida, sai dai bata san meye matsalar ba kuma, wannan ne yasa wata rana wata mak'wabciyarsu mai sunan *Delu* suna daka a tsakar gidan saboda Ramma bata nan take fad'a mata ta tashi tsaye akan yaranta, dan ko shakka babu akwai sihiri a jikinsu daya hana su aure, bud'ar bakin Saratu cewa tayi "To yanzu Delu meye abunyi? Wallahi lamarin yaran yana damuna sosai, kawai dan banda abokin shawara ne."
Da sauri Delu tace "Haba ke kuwa Saratu, ai mun zama d'aya, damuwarki damuwata ce, akwai abunyi kam in zaki yarda."
Cike da damuwa tace "Zan yarda mana Delu, idan ban samu mafita ba zan saka yaran a gabane na dinga gatsarsu ina ci? Kawai ki fad'a min kedai."
"Yawwa Sarai, kina ji ko." Ta fad'a tana yin k'asa da muryarta ta ci gaba da cewa "Akwai wani malami dana sani can bayan gidan sarki idan kin gangara tudun nan, wallahi yana bada taimako sosai dan aikinshi kamar yankar wuk'a ne, to ina tabbatar miki da zaki same shi da matsalarki wallahi zata zama tarihi."
Jim ta d'anyi kafin tace "Da gaske Delu? To amma ai matsalar ita ce ni ba komai gareni ba kinsani kema, ko abinci mai kyau ba samunshi muke a gidan nan ba, to taya zan samu kud'in da zan bayar a matsayin sadakar aikin da za'a mana?"
Dafa kafad'ar ta tayi tace "Haba Saratu, ni da ke fa yanzu mun zama d'aya, idan da ba zan taimaka miki ba aida ba zan fara fad'a miki maganar malamin nan ba ma, dan haka ki kwantar da hankalinki, insha Allahu zan rakaku idan kun tashi tafiya, kuma ni nan zan sayar da d'aya daga cikin awakina dan ganin yaran nan sun samu mijin aure."
Cikin farin ciki Saratu tace "Da gaske Delu? Kai amma naji dad'i da wannan taimakon da kika mana, Allah ya biyaki da gidan aljanna."
"Ameen." Ta fad'a tana d'aga tab'aryarta sama suka ci gaba da daka, suna haka Ramma ta shigo gidan, saida ta k'are musu kallo kafin tace "Yanzu dan na fita daga gidan shine har da min gayyar tsiya a gidan nan, to yayi kyau bari Alhaji ya dawo gidan sai ki fad'a mi shi abinda matar nan take yi, dan na tabbatar gulma kukeyi tunda ai bata zuwa gidan idan ina nan."
Durk'usawa Sarai tayi har k'asa tana fad'in "Dan Allah Hajia kiyi hak'uri na tuba, wallahi ba zamu sake ba daga yau kiyi hak'uri ki min rai."
Delu ce tace "Kinga Saratu tashi, ni zan tafi kar na ja miki matsala ba da niyyar haka na shigo ba, amma dai ya kamata ki rage tsoron nan tunda miji ba shi ya hallice ki ba."
Da kallo kawai Sarai ta bita a zuciyarta kuma tana fad'in "Dan baki san bala'in shi bane Delu akan matar nan tashi, ke dai Allah ya mana tsari da irinsu Hajia kawai."
Dan kuwa tasan inhar ta fad'a mishi to fa ya mata k'aramin hukunci shine ya mata dukan tsiya bayan idon 'ya'yansu, shine ya mata gata kenan, masifa Ramma ta ci gaba da yi ai kawai munafurci ne ya kawo Delu tunda bata cika zuwa gidan ba musamman ma idan tana gidan, Husseina da Husseina suna d'akin Ramma d'aya na gyaran d'akin d'aya na shara, suma tana shiga ta balbalesu akan basu gama gyaran ba tun lokacin data bar gidan, nan fa ta had'e su ta zage son ranta, da magrib Sarai da 'yan biyu suna zaune a d'akin su sai fitar k'wai (aci balbal) dake bayar da haske, Sarari ce ta lek'o a hankali tsakar gidan taga babu kowa, dawowa tayi ta kalli Hassana tace "Husseina, kinga yi sauri kafin Babanku ya shigo ki tambayo min Delu ki ce nace yaushe ne tafiyar nan, idan ta fad'a miki sai ki ce nace ni ba zanje ba amma ku zaku tafi tare da ita."
"To." Kawai Husseina ta fad'a ta tashi ta fita tana waiwayen d'akin Ramma, tana fita Alhaji Hassan kuma ya danno kai cikin gidan, kamar kullum kai tsaye d'akin Ramma ya nufa, tana jin motsinshi ta fashe da kukan makurci, nan fa hankalinshi ya gama watsewa Ramma na kuka, bai samu nutsuwa ba har saida yaga tayi shiru ta fara zayyana masa abinda ya faru kamar haka "Gaskiya Alhaji na gaji, na gaji da irin cin mutumcin da Sarai ke min a gidan nan, wai daga nasa k'afa na fita shikenan saina tarar da Sarai da Delu a gidan nan sunata cin nama na, a k'arshe ma dana musu magana kar ka so kaga rashin mutumcin da suka min ba, da nace kuma idan ka zo zan fad'a maka dan ka shiga tsakani na da ita, amma wai sai Sarai ta bud'a baki tace ai kai miji ne kawai ba ubangiji ba, dan haka baka da wuta ko aljannar da zaka sakata, dan haka ni kawai ka rama min cin mutumcin da ta min gaban k'awar ta."
Wani huci yayi yace "Yanzu dama akan Saratu ne kike kuka haka? Me ya sa zaki tsaya ki bawa kanki wahala? Naga ai kina da damar dake kanki zaki hukunta ta ko bana nan, amma ba komai zata gae kurenta, wallahi zata san ta tab'a ki a gidan nan, yau zanga waya d'aure mata gindi a garin nan."
Fitowa yayi daga d'akin ta biyo bayanshi tana ci gaba da rera kukan iskanci, shi kam d'akin shi ya shiga ya d'auko bulalar fata ya nufi d'akin Saratu da ita, suna zaune ita da Husseina saiko ya fad'o d'akin kamar an turo shi yana fad'in "Ina kike marar mutumci, har ni zaki wa fitsara