Showing 282001 words to 285000 words out of 325849 words
Ammar, dan Allah muna nema mata alfarma kayi hak'uri ka dawo da ita, tayi hakane saboda 'ya'yanka, idan zaka nutsu kayi tunani zaka fahimci da a lokacin kowa yasan abinda ya faru, kayi tunanin irin abinda zai faru marar kyau, sannan kayi duba da shekarun da kuka d'auka ba tare da kun samu sab'ani irin haka ba, kayi hak'uri dan Allah, mu ma wallahi mun yafe babu komai, Allah ya yafe mana baki d'aya."
Gambo ne ya kalle shi yace "Ku daina bashi hak'uri ma dan Allah, yanzu zai tura dreba ya d'aukota ya dawo da ita."
Wani kallon ban son iskanci lieutenant ya mishi, shi ma hararanshi yayi yace "Allah sai kayi ko baka so, ba dan ma raini ba matar taka ta shekaru zaka yarda ta bar gidanta a wannan lokacin, to ina kake so taje? Ko kunya abun ba zai baka ba ace ta tafi gidansu, da yaranku da jikoki ku tsaya kuna abu kamar yara."
Had'e fuska yayi yace "Gambo, kayi shiru da bakinka kafin ranka ya b'ace."
Shi ma ba alamar wasa yace "Ya b'ace d'in mana, an fad'a maka ina jin tsoro ne."
Tasowa lieutenant yana fad'in "Zan tosheka kuwa yaro."
Da sauri Gambo ya tashi yayi baya yana dariya yana cewa "Ni ne yaron? Ni kake kalla ka kira ni yaro? Haba."
Hajia ce tace "Karka tab'a min auta wallahi, inba haka ba ranka zai b'ace."
Dawowa Lieutenant yayi ya zauna yana murmushi, Hadiza kam banda k'yalk'yata dariya ba abinda take, komawa yayi shi ma ya zauna yana dariya, Hajia ce tace "Dole zaka tura a d'aukota, kuma ba dreba kad'ai nake so ba, har da kai ma zaka tafi."
Kallonta yayi yace "Haj..." Bata barshi ya k'arasa ba tace "Bana son jin wata magana, abinda ka mata zaisa taji kamar ba a bakin komai take a wurinka ba, ba zan lamunci haka ba gaskiya, matar data k'arar da shekarun rayuwarta a tare damu, ta maka biyayya ni kuma ta min bauta, haka kawai yau ka wulak'anta ta."
Cikin marairaicewa yace "Shikenan Hajia zan tafi, amma ki min uzuri dan Allah har zuwa gobe, wallahi yau ina da muhimmin aiki a gaba sosai."
Fuska a d'aure tace "Shikenan, kaje Allah ya bada sa'a."
Da farin ciki ya amsa da "Ameen nagode."
Tashi yayi ya kallesu yace "Sai anjima."
Husseina ve tace "Allah ya tsare."
Sada ya fita Gambo ma yace zai fita ya dawo kafin Hadiza ta shiga d'aki ta samu Hamna, kwance ta same ta gefenta farantin kankana amma da alama bata sha ba, zaune tayi tana kallonta tace "Tashi zaune zamuyi magana."
Cikin muryar kuka tace "Dan Allah Mama in akan maganar nan ne kawai ki barta, ba zan iya ba wallahi."
Ajiyar zuciya ta sauke tace "Tashi Hamna, c'est trรจs important."
Tashi tayi ta zauna tana ci gaba da share hawaye kuma wasu na bin wasu, kallon basira ta mata kallon fahimta tace "Hamna, me yasa kika ce ba zaki iya auren Ammar ba?"
Da sauri tace "Mama je ne peut pas, ba zan iya auren mijin yer uwata ba, kuma ni bana son shi ko kad'an."
Saida ta karanci yanayinta kafin tace "Corrections, mijin yer uwarki data rasu zaki ce, sannan Hamna zaki iya aurenshi ko da baki son shi, kinsan me yasa?"
Da ido ta kalleta hakan yasa tace "Saboda shine uban d'anki Shureim."
Da fari zaro ido tayi tana kallonta a firgice, sai kuma ta fad'a kan k'afafunta tana kuka tace "Mama kiyi hak'uri ki yafe min dan Allah, wallahi ba laifi na bane shine ya tirsasa ni, Mama bana manta tunatarwarki a kanmu kullum, dan Allah kiyi hak'uri."
D'agota tana share mata hawaye tana ji kamar tayi kukan ita ma tace "Karki sani kuka Hamna, na riga dana yafe miki har da shi ma, bana so ki karyar min da zuciya kuma."
Sassautan kukan tayi sai ita data d'ora da cewa "Hamna a gani na ki amince da auren shi, sai nake gani kamar ba zaki samu wanda zai dace dake ba kamar shi, sannan Hamna duk wanda zai fito neman aurenki yanzu ya zama dole a sanar dashi kina da yaro, kina ganin zai amince ya aureki duk yanda yake son ki? Ba lallai bane gaskiya a wannan yanayin da ake ciki, amma kinga shi ba zai k'yamace ki ba, zai rik'e ki kuma ya rik'e d'anku hankali kwance."
Girgiza kai tayi tace "Mama zan samu amma ba dai Ammar ba, mutumin daya rabani da mutumci ne yaushe zan iya rayuwar aure dashi? Kuma shi ma fa kinji abinda yace yana da wacce yake so, to me zaisa na tusa kaina gare shi."
Murmushi Mama tayi tace "Wallahi baya da wata wacce yake so Hamna, kawai ya fad'a ne saboda kinsan shi ba rainin wayo yake so ba, nasan yanzu yana can yana bala'i kin kalle shi kince baki son shi."
Kallonta Hamna tayi tace "Mama kawai ko bar maganarshi, ni idan ma ban samu mijin aure ba zan zauna na ci gaba da kulawa da yara na."
Da sauri tace "To ba gashi ba, Hamna kina son yaran nan sosai kuma kin k'i yarda kowa ya kama miki kula dasu, indai kina son ki ci gaba da rayuwa da su dole ki auri mahaifinsu, amma ba zan takura miki ba ki zauna kiyi tunani sosai, duk abinda kika yanke ki kira ni ki fad'a min."
Tashi tayi zata fita tace "Mama ina zaki je."
Juyowa tayi tace "Zan je gida na dawo na d'auki Ahmad."
Fkta tayi inda Hamna ta shiga d'aukar kankanarta da d'aya d'aya tana sha tana kuma tunanin abinda Mama ta fad'a, lallai indai zata rayu da yaran da ko kukansu bata so dole ta bi shawarar Mama, amma kuma Ammar? Kai! Tana cikin wannan tunani wayarta ta shiga k'ara, d'auka tayi ta ga ko suna babu a lambar, d'auka tayi suka gaisa kafin ta tambaya wake magana, nan ya fad'a mata sunanshi tace bata gane ba, dan haka yace ta bashi izini ya zo zai ta ganshi ido da ido, burinta na son samun wanda ya dace yasa ta amince da ya zo anjima.
*Tsautsayi*
Bayan sallah isha'i ta gama shirinta cikin doguwar rigar shadda, duk da ba tayi kwalliya ba amma tayi kyau, wayarta ya kira ya shida mata ya zo, ko da ta aje wayar Imam ya shigo yana kuka wai Shureim ya dake shi, jawo shi tayi tana lallab'a shi ta bashi wayarta tace "Ka je kayi kallon abinda ka fi so karka bawa kowa, kuma zan ga Shureim d'in saiya gane kurensa."
Cikin jin dad'i ya karb'a ya fita, ita kuma saida ta shafa turare sannan ta d'auki gyale ta yafa tasa takalmi ta fito, su Zeinabu ta samu a falo ta fad'a musu tayi bak'o a waje zata shigo dashi ciki, fatan alkairi suka mata ta fice.
Tana fita ta shiga mamakin wanda ta gani, kusa da salon d'inta yake nan take ganinshi zaune a wata fada, da mamaki tace "Kai ne?"
Murmushi yayi "Kin gane ni ashe? Na d'auka yanzu ma saina kwatanta miki."
D'an murmushi tayi tace "Na gane ka mana."
Gyara tsayuwa yayi yace "To ya kike?"
"Lafiya lau, mu shiga ciki ko, ba'a barinmu tsayawa kan hanya."
Gabanshi ne yaji ya fad'i sosai, tambaya ya wa kanshi to me ya kai na shiga ciki? Shi fa ba wata babbar magana bace ta kawo shi wajenta. Murmushin yak'e ya mata yace "Amma kafin nan mu gaisa ki san suna na, in ya so sai mu shiga ko."
"Amma ai duk zamu iya yi a ciki." Ta fad'a fuskarta a d'an had'e, kallonta yayi yace "Hakane, amma in d'an jin tsoro."
Wani irin kallo ta masa tace "Tsoron me kuma?"
Cikin rashin gaskiya yace "Eh to, kin gane? Kawai dai, gidan na ku ne, nasan mutanen cikinshi, akwai abokaina dayawa."
Wani kallo ta masa zatayi magana Imam ya fito daga cikin gidan da gudu yana kuka, tana ganinshi ta durk'usa ta rik'eshi tana fad'in "Imam me ye? Waya tab'a ka?"
Kafin yayi magana Shureim ya fito da wayarta a hannu ya zo ya tsaya yana fad'in "Aunty wai dan na ce ya bani nayi jeux (game) shine ya k'i."
Ranta a b'ace ta kalle shi tace "Shine ka fizga da k'arfi?"
Mik'ewa tayi tsaye ta kamo kunnenshi ta kwad'a masa mari tana fad'in "Shine zaka saka min yaro kuka? Dan ubanka ban hana ka tab'a min su? Wallahi ka sake karb'ar min a waya a hannun sai na ci ubanka a garin nan."
๐ *Hamna kin taro match fa, da kin duba bayanki kafin ki fad'i haka.*
*Ammar* da saida ya kusa kawowa gida motarsa ta tsaya, makanikenshi ya kira shi kuma ya k'araso k'asa saboda tafiyar ma na da anfani ga lafiya, tunda ya hangeta ya ganeta, k'ara hassala yayi dama a tafashe ya fita daga gidan, har yanzu yana nanata kalmar data fad'a ta *ina da saurayi*, ya rasa dalilin da yasa Hamna ta soka mishi wannan iskancin, a gaban iyayensu tace tana da saurayi kuma bata son auren shi. Sannan yazu ya dawo ya tarar da ita da saurayi a k'ofar gida tana hukunta masa yaro, wannan wace irin uk'uba ce? Bayan ta gaura masa mari kuma ta bishi da zagi, zagin ma ubanshi kawai take zaga, wato dan ta ga wani d'an iska a gabanta shine zata tsaya tana zaginshi, tunda dai ta zagi yaronshi ai da shi take.
Amma ba damuwa zaiyi maganin saurayin kafin ita, shi daya zauna yana kallo yana jin dad'i tana zagar masa yaro amma bai hanata ba, dan baisan darajar 'ya'ya ba saboda bai da su shi, da azama ya k'araso wajen ta bayansu ba tare da sun san da zuwanshi ba, saida ya tsaya da kyau ya toge sosai yasa k'afarsa ta dama a gaban k'afafun saurayin nan da ko sunanshi Hamna bata sani ba bare ta fad'a mana ya kwashi k'afafunsa.
Sai ji tayi kawai abu ya fad'i k'asa pamm, da sauri ta saki Shureim ta juya ta kalli ikon Rabb, bawan Allah bai san me ya faru ba, baisan wane shaid'anin bane a cikin shaid'anun, abinda ya sani kawai shine a cikin aljannun ma wannan gagararre ne, duk yanda akayi ko dai a gidansa ne suke tsaye ko kuma sun taka masa yara basu sani ba, amma wannan kwasa da aka masa ko jirgin sama yana shaida maka zai tashi ya d'aga ka daga kan k'afafunka bare kuma bil'adama.
Yana shirin bud'e idonshi daga k'asar da fuskarshi ta daduma yaji an tokara masa gwiwar k'afa a baya an hana shi tashi, bai yarda yayi gamo ba saida yaji an figi hannunshi ta baya anyi ciri dashi, yana jin sautin k'arar gotawar k'ashin shi sanda aka karya hannunshi, azaba ce tasa shi sakin k'arfinshi ya daka uwar ihu.
Yana jin k'ararshi ya sake cije leb'e yana fad'in "Au! Zaka iya ihu ashe."
Tsakiyar kanshi ya dafe ya rik'e hab'arshi da d'aya hannu da niyyar kawai ya juyar masa da wuya, an jima uban kowa bai mutu ba, Hamna data shiga firgici na abinda zai aikata bata san sanda ta rumgume shi ta baya ba ta rik'e hannayenshi gam ta fashe da kuka tana fad'in "Dan Allah Ammar sake shi baiyi komai ba, dan Allah karka kashe shi ka rufa mana asiri."
K'arfin tartsatsin da yaji kamar k'arfin dake cikin wutar lantarki ne, ba wai tsayawa ba daga masifa, hatta numfashin shi ma ta kusa sawa ya bar jikinsa, har jikinshi ma ya shida ita ta musamman ce, sannan dokinshi ma ya tabbatar da yana kewar mace, dan a take sak'on yaje ya kuma haifar da sakamako mai kyau. Sakinshi yayi tare da mik'ewa tsaye yana kallon mutumin, shi fa ko fuskarshi ba bai gani ba, tsabar fitina ce kawai da neman wanda za'a mutu tare, sai lokacin ta sake shi tana k'ok'arin su kalli juna sai kawai ya taka da sauri yaja hannun Imam da Shureim wanda dukansu sukayi shiru da kukansu suna kallon babbar harka, cikin gida ya shige dasu.
Cikin jin kunya ta kalleshi ya tashi zaune yana karkad'e k'asa a fuskarshi yana furzar data bakinshi, a hankali cikin taushin murya tace "Dan Allah kayi hak'uri kaji, kayi hak'uri da abinda ya maka, yayana ne."
Shi dai da har yanzu bai gama gane komai ba ga hannunshi dake zugin bala'i na karaya ko kallonta baiyi ba, ko da taga haka ta mik'e ta shige gida da gudu da niyyar yau saita kawo k'arshen wannan bura'ubar da yake mata a gidan nan. Shima yana ganin shigewarta ya fashe da kuka na gasken gaske yana birkid'awa yana rik'e hannunshi da yake jin kamar zai cire ya barshi, gashi ba zai iya tuk'a motar ba bare ya kai kanshi wajen magani, baida nutsuwar da zai iya kiran wani ya zo ya d'aukeshi, mai gadin gidan ne yaji kukan babban mutum a waje ya fito da gudu, da taimakonshi ko da ya duba hannun yace karaya ce, tsaf ya mishi magani yasa mishi magani yanata addua'r Allah ya sawak'e, saida aka gama yace mi shi "Amma ba kaine bak'on da ka zo wajen Hajia Hanne (Inji shi)?"
"A'a." Ya fad'a yana tashi tsaye, shima tsaye ya mik'e yace "Amma garin yaya ka karya hannu haka? Gashi kuma banga alamar hatsari ba."
Huyowa yayi ya kalleshi, hatsari? Hatsari ma yake cewa baiga alama ba, bayan abinda ya faru yafi karon babbar mota muni, juyawa yayi ya ci gaba da tafiya a hankali yana d'an sosa bayanshi inda ya daka mishi gwiwa, motar ya bud'a ya shiga ya tayar ya fara janta a hankali yana tuk'i da hannu d'aya, sai dai ya ci alhwashin ko ma uban waye wannan yayan nata wallahi saiya tara masa yaran nan na unguwarsu yan zaman kashe wando sun ciro masa jijiyar dake sadar da ji da ganinshi.
*Allah yaba mai rabo sa'a.*
*Ko da* ta shiga da masifa a falon ta same shi yana wa Shureim bala'i yana fad'in "Akan banzar waya zaka zauna ana zagin ubanka a gaban k'aton banza, me yasa baka buga wayar a k'asa ba ta b'are? Duk duniya idan ka cire ni ubanka da uwarka da kuma yan uwanka ban yarda ka d'auki raini a hannun kowa ba, kaji na fad'a maka."
Girgiza kai Shureim ya shiga yi yana sako da hawaye, tana bayanshi a hassale tace "Wannan har d'ab'ia ce kake jin kana koya masa to?"
Juyowa yayi ya kalleta, kallon jin haushi da zan iya miki komai, ganin bai tanka mata ba yasa tace "...
*Alhamdulillah*
04/11/2020 ร 14:38 - Ummulkhairi: ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*BADAK'ALA*
๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ _*AHALI NA*_๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
๐ซโจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_๐ค
โ *[ T.M.N.A]* โ ๐๐๏ธ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
_67_
Ammar me ye matsalarka da samari na? Akan wane dalili ne kullum ka ganni da saurayi saika wulak'anta ni a gabanshi ko kuma ka muzantashi? Me yasa? Ka fad'a min idan ba haka ba yau ni da kai a gidan nan wallahi sai dai duk mu babbake."
Da fari da kallonta yake yana tunanin hannun da idan ya bigeta dashi zata fi jin zafi, amma data ce wai duk su babbake sai ta bashi dariya, dariya ya shiga yi hankali kwance wanda hakan ya sake hassalata cikin d'aga murya ta kalli Hajia dake zaune tana kallonsu kamar tv tace "Hajia ki mana tsakani da bawan Allahn nan ya daina shiga tsakani na da samari na, tunda dai ba zamansa nake ba kuma ba aurenshi ne akai na da zai addabe ni ba."
A hankali Hajia ta d'an dafe kanta dan ciwon kai taji suna neman sanya mata, lallai da taso a had'a aurensu, amma yanzu tunaninta shine yanda wannan yara zasu zauna in aka aurar dasu, lallai gaskiyar Junaid ne gidan nan zai iya kamawa da wuta, ganin Hajia ma ta k'yalesu saita k'ara jin haushi tace "To Allah idan na sake tsayawa da saurayi ka min iskanci Ammar saina soke ka da wuk'a."
Hajia ta kalla tace "A matsayinki na kakarshi Hajia ki fara nema masa magani, dan wallahi ya gama kwancewa."
Sama da k'asa ta bishi da harara ta giftashi zata wuce d'akinta, cikin salon da ka rantse bashi yayi maganar ba yace "Nan gaba ma wuyansu zan fara takawa, kin k'waci kanki da rumgumar da kika min, amma kika sake gigin zagar min yaro sai jini ya fita a bakinki, dan abu d'aya dana lura dashi shine baki k'aunarshi, to ni ina son kayana ehee."
Tab'e baki tayi tace "Akan me zan k'aunace? Wannan d'in?"
Ta fad'a tana nuna Shureim, gyara tsayuwarsa yayi yace "Me yasa baka son shi? Shi ba d'a bane?"
Kawai dan ta b'ata masa rai tace "Saboda bai min ba."
Gabanta fad'uwa yake saboda kallon da yake mata, murya k'asa k'asa yace "Me yasa bai miki ba?"
Da sauri Hajia dan ta tsayar da maganar tace "Hamna wuce d'akinki bana son tashin hankali."
Har ta fara takawa sai kuma ta tsaya ta kalleshi, cikin gadara da isa da rashin tsoron abinda zai biyo baya tace "Saboda da kai na same shi."
Wucewa tayi ta barshi tsaye, had'e labb'anshi yayi yana lasarsu, har ga Allah baisan ta yanda zai fara fad'awa yarinyar baya son ya ga ana nuna masa k'iyayya ba, musamman ma daga mutane masu mahimmanci a gare shi, saboda bata son shine yasa ma bata k'aunar d'an data haifa dashi, to wace irin k'iyayya ce take masa?Wani shu'umin murmushi yayi dan har ya tsara abinda zai rama shi ma, juyawa yayi ya nufi d'akin Ummy sai Hajia da tace masa "Bata nan."
Tsayawa yayi ya juyo yana kallon agogon hannunshi, shi dai duk yau banga Ummy a asibiti ba, to kuma in bata gida tana ina kenan? Saida ya zo kusan Hajiar yace "Ina taje a wannan daren?"
Tsakiyar idonshi ta kalla yanda ba kowa da falon zaiji ba tace "Tana arlit yanzu, amma gobe Abbanka zai je ya taho da ita."
"Arlit kuma?"
Bata bashi amsa ba sai kallonshi da