Showing 114001 words to 117000 words out of 325849 words

Chapter 39 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

553

Middle Ads

yayi akan gadon marasa lafiya dake tsakiyar d'akin ya duk'ar da kai k'asa ya rik'e hannun dake fitar jini, har yanzu ya kasa tsayar da hawayen dake zubo mishi, tafarfasa kawai zuciyarshi keyi na k'una da k'unci, iyayen da suka haife ni, amma kullum babu kalma mai dad'i tsakani na dasu, tun ina yaro na fahimci me kalmar d'an iska take nufi, menayi da suka tsaneni tun ina yaron da bansan daidai da rashin daidai ba? Mena aikata gare su haka dayasa suka k'ini? Shin na zo musu ba yanda suka so bane? Ko kuma guda suka so haihuwa sai ni na fara fad'owa duniyar? Ko kuma dai ni wani sirri ne tare dani da yasa kowa na gidan nan ya tsane ni? Menene shi? Wa zai fad'a min dalilin tsanar da suka min? Iyaye na su hantare ni, kakanta ta zageni ta koreni daga wajenta, da irin haka suka raine ni a gidan nan, babu wanda ya tab'a rarrashi na, babu wanda ya tab'a tambayata damuwa ta ko matsalata, akan me? Akan me! Ya fad'a da k'arfi har da saka k'afa ya ture doguwar kujerar dake gaban gadon saida tayi baya.

Saukowa yayi ya d'auki alcohol ya bud'e ya rintse ido sosai ya dararawa hannun, wani rad'ad'i ne ya ziyarce shi amma a hankali ya bud'a ido ya kalli hannun yace "Wannan rad'ad'in bai kai rabin wanda nake ji a zuciyata ba a duk sanda suka kira ni da d'an iska."

Wasu hawaye ne suka sake taho mishi hakan yasa shi fad'awa kan gadon ya zaune yasa bandeji yana laulaye hannun yana fad'in "Kuna kirana d'an iska a kullum, shin baku tunanin na zama d'an iskan ? Namiji ne fa ni, ina da sha'awa da son jin dad'i, ba kwa tunanin tasirin addu'arku wata rana ya kaini ga aikata b'arna? Idan haka ta faru shima saik ku sake kirana d'an iska?"

Amar na tsaye k'ofar d'akin ya gagara shiga, yasan halin kayanshi ba zai tab'a bari ya rarrashe shi ba, abinda yaji kuma sai yaji kawai bari ya bashi wuri ya fad'i abinda ke ranshi ko yaji sauk'i, dan haka ya bar wurin cike da tausayin d'an uwanshi da kuma jin lallai iyayensu basa kyautawa.


➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️

Suna tafiya kawu Mamu ya tattaro kud'i ya shigo gidan afujajen kamar wanda zaho ya koro ya shiga bukkarshi, kud'in ya aje ya fito yana k'wala kiran Zeituna, ita ko tana can wajen yan bisashen da ake kiwo a gidan tana d'aure su, da sauri ta zo ta sunkuya gabanshi cikin fulatanci tace "Kawu gani."

Shima a fulatanci yace "Me kikeyi?"

Kallonshi tayi tace "Ina d'aure bisashe ne."

Juyawa yayi ya kalli Jumma dake cin tuwo yace "Innar Jumare, daga yau Zeituna karta sake aikin komai a gidan nan, ko da d'auke kara ne daga nan zuwa can, aikinta a gidan nan karya wuce yin wanka ta ci abinci ta zauna ta huta, kinji ko? Har wurin aiki ma surukinta yace karta koma zuwa."

Ya fad'a yana kama kunnenshi alamar taji, shek'ek'e Jumma ta kalleshi cikin k'warewa a harshenta tace "To me kenen zatayi idan batayi aiki ba? Ko mu bayinta ne da zamu dinga mata bauta?"

Cikin d'aga murya yace "To sai me idan kun mata bautar? Ku shekara nawa ta d'auka tana muku bautar? Ke bari kiji wallahi, tuwon ma idan har tana buk'ata a saka mata shi a baki to sai an saka mata ko da hakan na nufin zan biya kud'in hakan ne, idan kuma kika bari na kamata a gidan nan kin sakata aiki, to wallahi zan iya sakinki saki har uku, in yaso in auro yar birni ke kuma ki koma rigarku."

Kallonshi tayi tace "To wai meya faru ne? Akan me zaka ce zaka sakeni akan wannan mayyar yarinyar?"

Cikin karsashi yace "Saboda aure zan mata nan da kwana uku, yarinya mai k'ashin arzik'i ce, yau ma daga babban gidan da take aiki ne aka zo neman aurenta."

Tunda ya ambaci aure Zeituna gabanta ya fad'i ta d'aga kai ta kalleshi tace "Aure kuma kawu?"

Yanda yaga firgici tare da ita yasa yace "Ke kwantar da hankalinki, ba zan had'a ki da wanda ba kya so ba, zab'inki ne zan had'a ko da shi wanda yake sonki kuma kike son shi, ni ban damu da tsufanshi ba tunda dai kina son shi."

Kalamanshi sun k'ara sakata a duhun kai, Jumma kuma cewa tayi "Hum! Ayi dai mu gani Baffan Jumare, wurin son kud'in ka saika kaita inda za'a halakata."

Da k'arfi yace "To ba bakinki ba, yarinya dai mai goshi ce wallahi, ke kinma san waye zai aureta? To Alhaji Hassan ne, babban d'an Alhaji Suley Gaga, nan gaba kad'an nima zakiji na zama Alhaji."

Zeituna tsaye ta mik'e ta dafe k'irji tace "Kawu lieutenant?"

Kallonta kawu yayi yace "Ke ba lantanan ba nace Hassan, tare da babanshi suka zo suka nemi aurenki, ke har ma na amshi sadakinki mun tsayar da ranar juma'a za'a d'aura auren."

Sam ta kasa fahimta komai a zancen, lieutenant kuma? Ya zo neman aurenta? Anya kuwa! Me yake shirin sake faruwa kuma? Jin tana neman fad'uwa a wurin yasa ta juya ta shiga bukkarsu, Jumma kam dariya ta dinga yi tana fad'in "Ikon Allah, yanzu kuma abun ga tsoho ya kuma? To Allah ya kyauta maka."

K'wafa yayi irinta haba dai zaki gama dariyarki ne idan kika ga na shigo gari nima, juyawa yayi ya bar gidan shima zuciyarshi fes saboda yana da kud'i aje a d'aki, sam ya manta da maganar wani Jano, yau ma Zeituna yanda taga safiyar nan haka taga wannan dare bata rintsa ba, tambayoyi ne birjik a ranta amma babu mai amsawa, gashi ma ance kar taje wurin aiki bare tasan abinda ke faruwa, ta rasa me zatayi da jin labarin nan, farin ciki? To akan me domin kuwa bata da tabbas, har yanzu gani take mafarki take ko kuma kawunta ne ya shiga shuhuba, bak'in ciki? To shima akan me? Da haka har asuba tayi mata bata rintsa ba saida tayi sallah bacci ya d'auke ta.


*Washe gari* sammako sosai Ammar yayi ya tafi d'aurin auren Abdullahi, ana idar da d'aurin auren kuma ya d'auki hanya sai Madarunfa, awa d'aya ta kaishi a hakan ma dan baya gudu sosai ne, kamar haifaffen garin haka ya ratsa har ya isa gidan daya saba zuwa, paka motar yayi kai tsaye kuma ya shiga gidan yana sallama, matar dake k'ulla ruwa zaune bakin panpo ta amsa da farin ciki dan ta gane ko waye, mik'ewa tayi ta nufi wajen kujera ta d'auko tana fad'in "Ammar yau kaine da safiya haka? Amma dai sammako kayi sosai?"

Murmushi yayi ya k'arasa yana karb'an kujerar data d'auko ya aje ya zauna yana fad'in "Aunty daga wurin d'aurin aure ne kawai na wuce."

Zaune tayi kan kujerar data tashi ta kalleshi tace "Ina kwana."

Bai amsa ba shima yace da ita "Ina kwana aunty."

Sosai suka gaisa kafin ta sake mik'ewa ta bud'a fridge d'in dake cikin runfa ta sana'arta ta d'auko ruwa da lemu, kawo masa tayi ta aje ta juya ta d'auko faranti ta azo kwanonin abinci da duk abinda ya dace ta zo ta aje, saida ta zauna ta kalleshi tace "Ammar ga abinci ko, nasan dai ba lallai ka karya ka fito ba."

Kallon dattijuwar yayi cike da k'aunarta, hak'ik'a yana son mahaifiyar su Hamna, baiji dad'in rabuwarsu da kawunshi ba amma k'addara ce, ita kad'ai ce suke fahimtar junansu kuma harya fad'a mata wani abinda ya shafe shi, tun yana yaro idan an hattareshi ia ke tarairayarshi tana bashi hak'uri, shiyasa har yanzu bai manta da ita ba duk da tana gidan wani amma yana ziyartar lokaci lokaci, wani lokacin ma idan ranshi ya b'ace ne ko kanshi yayi zafi yake zuwa ta bashi shawara da rarrashinshi, bai mata musu ba domin kuwa kamar gida ya d'auki nan, har mijinta zai iya yin hira dashi hirar da bata tab'a shiga tsakaninshi da mahaifinshi ba, da kanshi ya zuba abinci yana ci suna hira ta duniya harya gama.

Su colonel ma sammako sukayi zuwa Goure, kuma cikin hukuncin ubangiji suka isa da wuri kai tsaye gidan suka nufa dan tare suke da Junaid da kuma Labaran, gidansu Maryama sun sha tarba sosai, kamar dai tarba da ita kanta Maryama ta gani zuwansu jiya tare da 'yarta da k'awarta, nan suka k'arasa gidan malam Rabi'u inda dama ansan da zuwansu domin su gabatar da abinda ya kawosu, suna zuwa can ma tarba suka samu inda suka samu maza uku bayan malam Rabi'u, tunda Labaran ya kalli tsohon yaji fad'uwar gaban da bai tab'a jin irinshi ba, haka suka zauna suka sake gaisawa sannan malam Rabi'u yace "...


👏👏👏
22/06/2020 à 17:26 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

💞 _*MASOYA NA*_💕


_Bismillahir rahamanir rahim_

🇳🇪 *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_11_

"Nasan zaka gane muryata cikin sauk'i, dan haka ba zan bawa kaina wahala wajen sanar da kai wacece ba."

Jin Sameera a bayanshi yasa shi juyawa ya kalleta wacce ita ma ke kallonshi saboda son sanin abinda ke faruwa, matsawa yayi sosai nesa da ita amma ita da bata fahimta ba saida ta sake bin bayanshi, domin kuwa jikinta na bata wannan wayar nada nasaba da halin da mijinta ke ciki, ganin bata daina biyarshi ba yasa shi fita daga falon ya rufe k'ofa, yana fita yace "Meyasa kika kira ni?"

Murmushi tayi wanda saida yaji sautinsa kafin tace "Jiya mun rabu babu sallama baka kuma biyani kud'in aikina ba, shiyasa na kira dan na tuna maka karka manta da kud'i na."

A k'ufule yace "Karki raina min wayo Nasmat, kiyi gaggawar sanar dani abinda yasa kika kirani, idan kuma dan wannan maganar ne to kiji da kyau, karki sake gigin kiran wayata, idan kuma ba haka ba wallahi zansa rayuwarki a had'arin da kaf danginki sai sunyi nadamar kasancewarsu yan uwa a gareki."

Wata dariya tayi tace "K'arfin halinka na birgeni sosai, amma naga alama ba zaka saurare ni, shiyasa ma na tura maka da muhimmin sak'o a WhatsApp d'inka, zaka iya dubawa saika kirani muyi magana idan har kana son tsira da mutuncinka dana iyalinka."

Kashe wayar tayi inda shi kuma cikin rawar jiki ya fara dubawa WhatsApp d'in, yana bud'e vidéon nan saida ya saki wayar bai sani ba tsabar firgita, da sauri ya sunkuya ya d'auki wayar ya sake kallon abinda ke ciki, take yaji jikinshi ya d'auki rawa, ya ilahi! Meyasa banyi tunanin haka ba? Ita ce tambayar daya wa kansa, da sauri ya nemi lambarta ya kira tana d'auka yace "Me kike so?"

A tak'aice tace "Kud'i, kasan ku masu kud'in nan ba kwa tunanin talakawa da gajiyayyu, duk da kai kana k'ok'ari, to amma kasan dambu idan yayi yawa baya jin mai, kuma karka d'auka talauci ne yasa nayi abinda nayi."

Cike da k'aguwa yace "Ki gaggauta fad'a min nawa kike so bana da lokacin b'atawa a tare dake."

Cike da iko tace "Maganar nan ba zata yiwu a waya ba, mu had'u kawai."

"A ina?" Cewa tayi "Ni ko a titi zan iya had'uwa da kai, bansan ba kai."

Cikin jin haushi yace "Ba zan iya had'uwa da karya irinki a titi ba, zan turo miki da adresse d'in guest house d'ina ki sameni acan."

Dariya tayi tace "Zan so duk inda zaka gayyace ni domin kuwa wannan videon ya shiga hannun d'an uwana."

Tsaki kawai yayi ya kashe wayar ya tura mata adresse d'in ya shiga motarshi, hangen motarshi da tayi yasa ta fitowa da sauri tana so tayi magana, cike da damuwa ta bishi da kallo tace "Ya Allah, meke damunshi ne?"

Saida yayi jiran minti kusan ashirin kafin ta iso, tana k'wank'wasa k'ofar yayi gaggawar bud'ewa ta shigo, kallon juna sukayi inda yaji zuciyarshi na raya mishi kamar ya mata dukan mutuwa, tana shirin zama yace "Fad'a min nawa kike so na baki da zaisa ki goge wannan d'aukar ba'a iya wayarki kad'ai ba har da k'wak'walwarki ma?"

Tsayawa tayi daga shirin zaman ta kalleshi tace "Ko gaisawa ma ba zaka bari muyi ba?"

A fusace yace "Bana ciki da shirme, karki b'ata min lokaci ke nake sauraro."

Tsaye tayi da kyau tana kallonshi tace "Ina buk'atar naira million arba'in, yau ba sai gobe ba."

Da k'arfi yace "What!"

Matsowa yayi daf da ita ya galleta da wani mari saida ta fad'a kan kujerar da tayi niyyar zama ya nuna kanshi yace "Yanzu dama akan naira million arba'in ne kika sa na aikata zina? Akan wannan banzan kud'in kika saka na aikata abinda ban tab'a aikatawa ba tsawon rayuwa ta? Naira million arba'in kike so kika kasa fitowa ki fad'a min na baki? Nasmat kin cutar dani da rayuwata, ba zan tab'a yafe miki ba har abada."

Mik'ewa tayi tana share hawayen wahalar da suka zubo mata tayi murmushin mugunta tace "Naji, ka tura min kud'in a wannan account d'in yanzu, ba zaka sake gani ba."

Fizgar takardar data mik'o mishi yayi ya nuna mata k'ofa yace "Get out."

Murmushi ta sake mishi ta nufi k'ofa, saida ta bud'e k'ofar zata fita ta juyo da murmushi tace "Mahaifiyata, tana gaisheka, baka canza a yanda muka sanka ba, saidai ka k'ara zafi sosai, kayi sukuwa akan mahaifiyata kamar doki tun zamanin k'uruciya, yau gashi 'yar daka raina kamar 'yar daka haifa a cikinka ita ma kayi sukuwa akanta, a gaskiya da zan samu namiji kamarka da zanji dad'in rayuwa dashi, dan ka zo min a yanda nake son namiji ya kasance min, see u *Dady*."

Tunda ta fara maganar nan kanshi ya fara wani bala'in nauyi, mahaifiyarta, yar daya raina kamar yarsa, wa kenan? Yar daya raina har ya mata aure ita ce *Husna* yayarsu Abdul, to amma ai ba komai tsakaninshi da mahaifiyarsu Safeena, sai dai ko...

Cak yaji tunaninshi ya tsaya kanshi ya kulle, sunan da zuciyarshi ta ambata ne yayi barazanar tafiya da numfashinshi, da k'yar ya iya had'a sunan Sss... al..m...a, k'ara waro ido yayi yace "Kenan Ma'arufa ce? Na shiga uku ni Abbas mena aikata haka?"

Ya d'an jima a wannan halin yana tunanin da sam babu mafita, yana cikin haka yaji wani sak'on ya shigo wayarshi, da sauri ya duba dan a tsorace yake, yana dubawa kuma me zai gani? Sabuwar lamba ce ta turo mishi hotunan Raihan tsirara, zunbur ya tashi tsaye ya rufe ido ya dafe kanshi yana so ya samu kowace irin addu'a a baki amma ya kasa, a karo na biyu sake sakin wayarshi yayi ya fad'i kan lallausan carpet d'in, voice not d'in da aka turo ne yayi saurin d'auka ya bud'e, tattausar muryar Saleem ce yace "Shin da kake nan zaune gida ka tura 'yarka can kasan me take aikatawa ne? To wannan ma sanfuri ne, nan gaba zan turo maka da video yanda nake mu'amulantar ta."

Cikin matsanancin sauri ya nemi lambar Raihan, tana d'auka daga can b'angaren cikin muryar dake son yin kuka yace "Kiyi gaggawa ki shirya kije airport, ki hau duk jirgin da kika samu ki dawo gida *Raihan*."

Tabbas Raihan ta tsorata dan kuwa bata tab'a jin ya kama sunanta ba, cikin sauri kamar yanda yace ta tattaro kayanta ta nufi airport d'in, tayi sa'ar samun jirgin da zai tashi zuwa Abuja, dan haka ta hau aka juyo da ita babu shiri.

Suna gama yawa ya sake yin zaune yana matsa k'irjin shi da yaji ya mishi bala'in zafi, tunanin abinyi yake nema har saida yaji lambar nan ta sake turo mishi da sak'o kamar haka _"Kayi gaggawar aurar da ita, idan ba haka ba zan kafa mata tarihi kuma mummuna, idan bakayi abinda nace ba wannan hotunan zasuje inda baka tsammani ne, domin kuwa zan d'ora su a kafafen yanar gizo ta yanda kowa zaiga tsiraicin 'yarka, a haka ma zata rasa mijin da kuka zab'a mata."_

Had'a kanshi yayi da gwiwa ba tare daya shirya amsar da zai bawa mai turo sak'on ba, shi dai kawai yasan alhaki ne ya fara biyarshi tun yanzu, dama ance idan kayi da 'yar wani za ayi da taka kaima, a hakan kuma yana ganin ko da ace Raihan bata tab'a sanin d'a namiji ba to angama dashi tunda har akaga tsiraicinta, kai shi sam bai ma yarda da babu abinda ya faru ba, tayaya namiji zai samu hotonta haka babu kaya a jiki inhar ba wani abu ne ya shiga tsakaninsu ba? Yana tsaka da wannan tunanin wani sak'on ya sake shigowa cewa _"Tunda baka da lokaci na zanyi abinda ya dace, da fari zan fara tura hotan a wayar mahaifiyarta, daga nan kuma zan sake shi duniya ta gani, ni ba kud'i nake nema a wurinka ba, ka aurar da 'yarka kawai ga wanda ka zab'a mata."_

Sai lokacin ya kira lambar Saleem na d'auka ya canza murya Abbas kuma yace "Bansan ko waye kai ba, amma dai nasan baka nufi na da alkairi, dan Allah karka saki hotunan nan domin kar mutumcin 'yata ya zube, nasan gabarka ba zata wuce dani ba dan haka ka d'auki fansarka a kaina, dan Allah karta shafi iyalina."

Cike da izza yace "Ka fad'i gaskiya, amma ka sani ba zan huce ba har sai naga ka tara taron jama'a zasu shaida d'aurin auren 'yarka."

A tak'aice yace "Zanyi, zan d'aura mata aure da safiyar gobe da Abdul, ban buk'atar had'uwa da kai, amma dan Allah ka goge hotunan nan daga wayarka, ba mutumcin 'yata bace harda ni kaina."

Cike da dariyar iskanci ya amsa da "Saina gani idan kayi abinda nace."

Makullin mota ya zara tare da takardar da Ma'arufa ta bashi yayi gaba ya bar gidan, a hanya tunani kawai yake wanene kuma wannan? Shin tarbiyar daya bawa Raihan kenan? Meyasa haka ta fara faruwa dashi? Wayarshi ya d'auka ya duba takardar nan ya turawa Ma'arufa wannan kud'in, bayan kud'in sunje yana ganin tana kiranshi amma ya k'i dagawa harya isa

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login