Showing 24001 words to 27000 words out of 325849 words

Chapter 9 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

504

Middle Ads

da tausayi Sameera tace "Allah sarki, a gaskiya Harira na tausaya miki, amma meya shafi matsalar iyayenki da aurenki kuma?"

Kallonta tayi tace "Sameera kinfi kowa sanin halin mutanen k'auye, abu k'ank'ane suke mayar dashi babba, da k'yar akayi aurena saboda kafewa da dangin mijina sukayi wai ba zai aureni ba, da k'yar akayi auren amma da nasan abinda zai faru a gidan aurena kenan da banyi auren ba ma, tun bayan aurenmu nake fuskantar matsi da takura a wajen iyayen mijina, ina hak'uri sosai wajen zama dasu tare da hak'urin da mijina ke bani, ko shekara bamuyi suka saka shi dole ya k'ara aure saboda cewa ban haihu ba, matsala ta sake rub'anya ne daga lokacin da amaryarshi ta zo, ita ma matarshi d'orawa tayi daga inda yan uwanshi suke min rashin mutunci, kullum habaici da k'ananan maganganu da zagin iyayena suke, a shekara d'aya ta haihu ni kuma shiru har lokacin, a haka na d'auki tsawon shekara hud'u ina wannan rayuwar har ranar da Allah ya kawo k'arshen zamana a gidan, kuma hakan ta faru ne sakamakon fad'an da mukayi da amaryarshi saboda ta zagi iyayena, nan ya goyi bayanta ya fad'a min magana sannan ya sake ni, kinji abinda ya faru Sameera, yanzu haka muna zaune tare da k'anwar mahaifiyarmu ce wacce mijinta ya rasu da kuma 'ya'yanta, wallahi ba zamu tab'a cewa muna jin dad'in zama da ita ba, saboda babu abinda take taimaka mana da shi duk da cewar tana sana'a."

Kuka sosai take saida Sameera ta koma kan kujerar da take ta dinga rarrashinta, kallon Adamu tayi tace "Adamu kuyi hak'uri dan Allah, naji uzurinku kuma na tausaya muku sosai, amma ku sani ko Dadyn mamana (Abbas) bana jin yana da hurumin da zai iya fito da iyayenku, dalili kuwa shine an kamasu da laifin dumu-dumu kuma su da kansu sun amsa, hukunci ne aka yanke musu wanda dole sai su gama wa'adinsu, kunga kenan bana jin akwai taimakon da zamu iya yi muku akan maganar nan, yanzu hukuma ce ke da wannan hakk'in amma bamu ba, amma dan Allah kuyi hak'uri, amma a shirye nake da na muku wani taimakon idan kuna buk'ata."

Adamu ne yace "Yanzu kenan babu abinda zaku iya yi mana?"

Jinjina kai ta d'anyi tace "I think so." Kallon idonta yayi duk da haibar matar na mishi kwarjini amma haka ya daure yace "Amma idan kuka janye k'arar tare da yafe musu laifinsu ai ina ganin za'a sake su."

D'an murmushin gefen labb'a tayi tace "Adamu kenan, magana ake fa akan wad'anda aka yankewa hukuncin."

Ajiyar zuciya ya sauke yace "Kuma fa hakane, to yanzu meye abunyi dan Allah? Muna neman taimakonki Hajia, nasan idan kila saka baki zai iya yin wani abu akai."

Dafa kafad'ar Harira ta kumayi tana kallonta tace "Harira ku nemi wani taimakon, amma maganar gaskiya Dadyn mamana ko maganar da zata tuno mishi da baya baya so anayi."

Kallon kallo sukayi tsakaninsu kafin Harira tace "To in wannan ba zai samu ba Sameera ki taimaka min da ko shara ce ko wanke-wanken a gidan nan, ko na samu abinda zan dinga samarwa k'annan mu abinci."

Adamu ne yace "A'a Harira, bake ke da wannan hakk'in ba, nine ya kamata na nemi aiki dan na ciyar da ku."

Murmushi Sameera tayi tace "To ai ko dukanku kuka samu abinyi farin cikinku ne, dan haka wannan ba matsala bace Harira, in dai aikine kin samu a gidan nan ko da babu abinda zakiyi."

Da farin ciki ta kalleta tace "Da gaske zaki d'auke ni aiki Sameera?"

Ita ma dariya tayi tace "Me kuwa zai hana Harira, insha Allahu zaki fara aiki duk ranar da kika shirya."

"To wane irin aiki zanyi? Dan naga akwai ma'aikata a gidan."

Saida ta tashi daga kujerarta ta koma inda take ta kalleta tace "Um, gaskiya kam babu abinda babu wanda baya yinshi, amma idan zaki iya saiki zauna a b'angare na kina taimakawa ko da yara wajen shirin makarantar da kuma abinda ba za'a rasa ba."

"Shikenan wai abinda zanyi?" Cewar Harira, murmushi kawai ta mata mai tsadar gaske, Adamu ne yace "Wannan ma da kika mana mun gode sosai Hajia, Allah ya saka da alkairi."

"Ba komai." Ta fad'a a tak'aice, Harira ce tace "Yanzu yaushe zan fara aikin?"

"Duk ranar da kike so Harira." Cewar Sameera, da azama tace "Ko gobe ma zan iya dawowa?"

Dariya Sameera tayi tace "To da wannan me zai hana ki bari har jibi, lokacin munyi magana da Dadyn yara."

"To shikenan, hakan ma yayi, Allah ya nuna mana jibi, mu zamu koma Hajia, mun gode sosai Allah ya saka da alkairi." Harira ta fad'a suna mik'ewa, itama mik'ewa tayi tace "Ina zuwa ko."

D'akinta ta shiga kusan mintuna ta d'auka kafin daga bisani ta fito rik'e da leda babba a hannunta, tana zuwa ta mik'awa Harira tare da kud'i har dubu biyar tace su shiga mota, sai kuma Adamu data bawa kud'i shima har dubu arba'in tace "Ga wannan ka fara juyawa ko kafin muga yanda abubuwa zasu tafi."

Har k'asa ya duk'a yana mata godiya ita kam kunya ce ma ta isheta saboda ya na gaba dasu, da haka suka juyo suka taho suna godiya sosai, tun a hanyarsu ta komawa Harira ta fara sak'awa zuciyarta wasu abubuwa na daban, tabbas ganin Sameera a wannan halin yasa ta ji tana hassadarta, abun takaici wai har su nemi alfarmarta ta kasa yi musu, wannan shine dalilinta na neman aiki gidan, saboda tana so ta cimma wani buri da yau ne ta kitsashi a zuciyarta, inda Adamu kuma yake ganin taimakon data musu ma yafi wanda sukaje nema mahimmanci, koba komai iyayensu sune masu laifi, laifinsu ya shafesu ta yanda shi kanshi harya rasa aikin lebarancin da yake ciyar da iyalinshi dashi, amma yanzu gashi ta bashi jarin da zai iya tsayawa da k'afar sa k'am, da wannan tunanin suka isa k'auyen su, tun a hanya suka rabu inda shi ya nufi gidanshi ita ma ta nufi gida.

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Bayan tafiyar su da kamar minti ashiri *Bilkisu* ta shigo gidan tare da *Imranatu* dake d'auke da yaronta, kamar dai yanda suka saba kullum yanzu ma da sallama suka shigo Sameera ta amsa musu, kai tsaye Bilkisu kitchen ta nufa tana fad'in "Matar Abbas nasan dai ba kya rasa abin dad'i a gidanki, dan haka bara na samo abin tab'awa."

Imranatu ce dake shirin zama ta aje yaronta tace "Ke dai wallahi anyi acici, ke ba kya da aiki sai ki kai bakinki."

Tana kusa da shiga ta juyo tace "Lafiya ce ta kawo haka, da babu lafiya sai kun dinga lallab'a ta akan na ci."

Dariya Sameera tayi tace "Gaskiya ta fad'a kuma, amma kuma abin mamakin bata tashi ciye-ciyenta sai ta zo nan gidan, bansan me ya sa ba?"

Imranatu ce tace "Baki ji tace ba kya rasa kayan dad'i ba, ai da wannan ne kika rabamu da mazajenmu ta yanda basa iya cin abinci idan ba nan ba."

Cike da murmushi tace "Kuma na samu kan mijina ba, kuma ai idan kuka so zaku iya rik'e su gidanku du dinga cin abinci."

Hannu ta mik'awa yaron daya fara zagaya tsakiyar falon da rarrafe tace "Oya *Muhsin*, come on beby."

Juyowa yayi cike da murna ya wangale baki ya taho da sauri, d'aukar shi tayi ta aza saman cinyarta ta ci gaba da hira da Imranatu, sai lokacin Bilkisu ta fito da k'aramin plate a hannunta d'aya hannun kuma da inibi tana sha, kamar jiran zamanta suke sai kuwa sallamar yara wasu da gudu wasu kuma a nutse, kasancewar yaran Imranatu dana Bilkisu duka tare suke karatu da yaran Sameera yasa gidan ya gauraye da hayaniya lokaci d'aya, gaishe da iyayen sukayi inda Raihan da kuma babbar 'yar Bilkisu *Fadila* da kuma 'yar Imranatu *Ma'awa* kasancewarsu yan wari ne yasa suka zaune akan kujerun suka fara cirewa k'annan su uniform, sai Abdul wanda har yanzu yake zuwa islamiyyar kafin hutunshi ya k'are, kallonshi sameera tayi da yayi zaune a kujera tace "Son an gaji ko? Ya karatun?"

Cike da nuna kasala yace "Ammie karatu yayi zafi kam."

A hankali cikin nutsuwa Raihan ta kalleshi inda Ma'awa ta amsa mishi da "Wallahi yah Abdul kai dai anyi rago, wai Ammie fa saboda yau ajinsu malaminsu bai zo ba shi aka wakilta a matsayin malamin shi ya sa yake fad'in haka."

Kallonta yayi yace "Au, ke kin d'auka koyarwar sauk'i gareta? To gobe ki jaraba koyarwar ki gani."

Bilkisu ce tace "Wannan ai ba zata iya ba, surutu zatayi ko karatu?"

Turo baki tayi cikin shagwab'a tace "Mama." Kallonta tayi tace "K'arya na fad'a kenan?"

Fadila da ke kallonsu kallon Abdul tayi cike da birgewa, cikin taushin murya tace "Yah Abdul ko zamu maka tausa ne?"

Murmushin gefen labb'a ya mata yace "Nagode k'anwata, ba sai kin wahala ba."

Cike da nutsuwa da sanyin jiki Raihan ta mik'e da kayan su *Diya'u* a hannu ta kalli Sameera tace "Ammie an gama abinci? Danni yunwa nake ji."

Murmushi Sameera tayi tace "Kowane tsuntsu kukan gidansu yake, kowa da abinda ya dame shi, to kije ki watsa masu ruwa sai ku sauko ku ci abinci."

Kama hannun Diya'u tayi tace "To Ammie kinsan fa yaron nan naki da iyayin tsiya wallahi kullum shi ke bani wahala wajen shirya shi."

Diya'u ne ya fizge hannu yace "To Ammie ni nace bana so ko zan dinga yi wa kaina wankan, ai yanzu na iya amma sai ace wata ce zata min."

Da kallo Sameera ta bishi kafin ta girgiza kai tace "Ki rabu da shi kawai tunda ya girma zai iya da kanshi."

Ba zato ba tsammani sukaji Ameer ya fashe da kuka, Sameera na waigawa taga shi da Khlifa ne, shiru tayi sai Raihan ce ta isa garesu ta shiga tsakani ta tambayi meya faru, Ameer ne ya fara fad'in abinda ya faru inda Khalifa yace "Ammie wato dan yana mai sunan Baba ne na daka shiyasa kikayi shiru."

Abdul ne ya kama hannun Khalifa yana fad'in "In banda abinka bros ai dukanku kun sanya mana uwa a tsakiya ne, kai Abban ta ne (mahaifin Abbas) shima kuma Ameer abban ta ne (mahaifinta), to yanzu a fad'an nan wa kake so ta shigarwa?"

Cike da wayo yaron yace "Ni mana, tunda ni surukine, kaga akwai kunya tsakaninmu."

Zasu wuce ne ta gaban Sameera ta daki mazaunanshi tace "Ya dai yau naga *aku na* ba karsashi haka?"

Kallonta yayi ya turo baki yace "Ammie kema parrot zaki kirani dashi kamar yanda tsofaffin can suke fad'a."

Janyo shi tayi ta rumgume a k'irjin ta tace "Ayya! Sorry Dady na, ba haka nake nufi ba, na ga dai ka shigo ba magana ne."

*Raudat* ce ta fashe da dariya tace "Ammie yunwa yake ji fa shiyasa."

Hararan Raudat tayi tace "Ba fa nasan sharri kinji, Abba na k'arko ne da shi yunwa ba zata sa shi ya zama rago haka ba."

A kasalance ya kalli Sameera ya shafa cikinshi yace "Ammie yanzu dai bara na haura sama na sauko, idan na ci abinci zaki sha labari."

Bushewa akayi da dariya sai Raihan da ita dai murmushi ne nata dan sam yarinyar bata da hayaniya kuma bata son hargagi a rayuwarta, komai cikin nutsuwa da sanyi take yin shi.

Sama suka nufa haka ma Abdul da Jabir, Imranatu ce ta fito da makullin gida ta bawa Ma'awa tace "Kije ku canza kaya ku ci abinci, ki kula da kyau kar a hargitsa min lissafin gida bayan na gama gyara komai."

Sameera ce ta kalli yaran dake fita ta kalli su Imranatu tace "Jiya munyi magana da Abban Raihan akan maganar Abdul da Raihan d'in, yace yana tunanin yi musu baiko idan mun dawo daga bikin *Arfat* (yar kawu *Bakura* yaya ga iyayensu Sameera da Abbas), yace idan so samu ne yana so a d'aura musu aure saiya tafi da matarshi idan hutunshi ya k'ar."

Bilkisu ce tace "Kuma hakan ba wata matsala? Ni har yanzu gani nake Raihan yarinya ce wallahi."

Sameera ce tace "Ba wata matsala yar uwa, tunda dai ta balaga ta kai matakin da zata iya d'aukar namiji ai shikenan, zamu kiratada yarinya ne idan bata zama mace ba, amma kinga Raihan bana da shakku a kanta, na yarda da ita ta yanda zan iya kaita gidan mai mace biyu ma saboda nasan na bata horon da zata iya zama da kowa."

Bilkisu ce tace "Kuma gaskiya kika fad'a, to amma ya waccen maganar?"

Saida Sameera ta sake kallon yaran dake ta ficewa har yanzu sai Fadila data rage ita ma tana shirin fita tace "Maganar gwajin jinin da za'a mishi wannan ba matsala bane, tun farko ma yallab'ai ya b'ata lokaci ne saboda ganin rashin dacewar hakan."

Imranatu ce tace "Banga laifinshi ba gaskiya, haka kuma banga laifin su Ammie ba, amma haka zai daure yasan abunyi dan lokaci k'uracewa yake, yanzu ana fara maganar zasu ce ina sakamakon yake, amma kinga idan aka tabbatar da lafiyarshi ai mu kan mu hankalinmu a kwance yake, tunda wannan cutar ta *HIV* ana d'aukar ta, kuma akan iya haihuwar yaro da ita ma idan ba Allah ne ya kareshi ba."

Bilkisu ce tace "Oh Allah ka nuna mana wannan rana, ranar da alk'awarin nan zai cika na auren Raihan da Abdul."

Murmushi Imranatu tayi tace "Ameen ya Allah, Allah yasa muna cikin masu rai da lafiya."

Cak Fadila ta tsaya daga shirin fitar da take daga d'akin, sakin jakar hannunta tayi ta fad'i k'asa saboda jin wani abu ya daki zuciyarta da k'arfin gaske, kasa motsawa tayi daga wajen kamar wacce aka d'aure, take kuma hawaye suka cika mata ido har suna zarya a kumatunta, muryar Bilkisu ce ta katseta da cewa "Wai tsayuwar me kika wa mutane anan kuma? Kinsan dai *Farisa* (k'anwar ta) ba zata iya bud'e gidan ba ko."

Rintse ido tayi wasu hawaye masu zafi suka sake antayo mata, a hankali ta bud'e tare da had'e wani k'ululun abu da taji ya tokare mata mak'oshi, sunkuyawa tayi ta d'auki jakarta ta wuce ba tare da tasan ina take saka k'afar ta ba, tabbas yarinya ce ita kuma mai k'ananan shekar, sai dai tasan tana matuk'ar jin Abdul a zuciyarta fiye da yanda take jin komai, tana ji a duniya inhar za ta yi aure to Abdul ne zata aura, ta yarda wannan so d'in da suke jin ana labarinshi ya kamata, ta kuma tabbatar a yau d'in nan taji wani tafasashen kishi ya taso mata akanshi, da haka suka isa nasu gidajen wanda dama had'e suke waje d'aya, kamar yanda iyayen suka d'ora su akan turbar kula da k'annan su yanzu ma haka ce ta kasance, duka yan matan uku kowace ta taimakawa yan uwanta k'anana wajen yin wanka da canza kaya, saidai Fadila bata tare da walwala sam, haka ta shirya musu sahu sukayi sallah tana wannan halin, dan ko dinning ma da suka zauna cin abinci ita bata ci ba, ta dai zauna saboda kar ta gusa yaran suyi wata b'annar, saida suka gama taga sun mik'e zasu fita tasan ina kuma zasu je, saida ta je har k'ofar gidan taga shigarsu gidan kawun nasu (Abbas) kafin ta rufe gidan ta haura sama izuwa d'akin ta, tana shiga ta fad'a kan gado ta fashe da kuka dan shine kad'ai taji tana buk'atar tayi, ita kanta bata san ya akayi ba kuma yaushe ta fara son Abdul, ta dai san kawai yana birgeta tun farko har lokacin da take jin wasu abubuwa a game da shi d'in.

Ma'awa ce ta had'u da su Farisa ta tambaye su ina Fadila, Farisa ce tace "Tana gida bata fito ba."

Juya akalarta tayi ta nufi gidan, dan ya zama kamar ibada a wajensu tarewa gidansu Raihan a kowane lokaci su da iyayensu, ta jima tana bubbuga k'ofar falon amma shiru bata bud'e ba dan bata ma san tanayi ba saboda tana saman bene, haka ta gaji ta dawo gidan sai dai bata ji a ranta cewa wani abu ne ke faruwa ba, dan haka ma bata damu kanta ba, ko da ta shiga gidan kai tsaye wajen su Ammie ta nufa, kamar yanda ta sani kam ta same su duka a falon na su anata hira, inda Abba ya fito farfajiya tare da duka yara mazan, sai Khalifa dake rik'e da hannun Abban yana ta zuba mishi surutu, hakan ne yasa ya juyo ya kalleshi yace "Ka dubi Allah ka k'yale ni da zancen islamiyyarku nan, wai kai d'aukar rahoto ne ke kai ka makarantar? Saifa na je na fad'a wa malaman na ku su killace ka kai kad'ai tunda lek'en asiri ke kaika makarantar ba karatu ba."

*Usman* (mai sunan kakansu Abbas baba Ard'o) ne yace "Abba shi fa labari ne bai iya bayarwa ba, sai yace komai daya faru saiya fad'a."

Juyowa Khalifa yayi ya harare shi yace "To ina ruwanka, na sa da kai ne a maganata?"

Take ya mayar da kallonshi ga Abba yace "Kana ji ko aboki na, sai yaron ya..." Dakatar dashi Abba yayi jin zai ci gaba da bayar da labarinshi yace "Kunga wa zai min karatun da aka koyar da shi yau d'in nan na bashi kyauta?"

Da sauri Khalifa ya d'aga hannu sama yace "Ni ne, zanyi."

"To fara ina jinka." Cewar Abba, saida suka zauna a gardine akan kujeru sannan Khalifa ya fara rera kuratunshi tun farkon suratul *Mulk*, murmushi kawai Abba keyi saboda farin ciki, zai iya cewa suruntu da wayon yaron ne yasa yake da matuk'ar k'ok'ari ko a school ko islamiyya, saida ya kai k'arshe sannan ya tsaya yace a bashi kyautarshi, dole Abba ya bashi kyautarshi kad'ai ya rabu da shi.

*ZARIA*

*K'auyen Dabai*

*Salma* ce ta fito daga ban d'aki rik'e da buta a hannunta sai d'aya hannun dake rik'e da sandar dake taimaka mata wajen tafiya, da k'yar ta k'araso ta zauna akan tabarmar dake k'ofar d'akin ta, sai dai kuma wata masifaffiyar yunwa take ji wacce ke neman kaita gushewarta, dan har ta manta rabon data samu abinci mai kyau ta ci, tunda mahaifinta ya rasu tsananin rayuwarta a k'ara bunk'asa, dama kuma matar mahaifin nata ba k'aunar ta take ba, hasalima tana da hannu sosai a shigarta duniya, dan ita ce ta shanye mahaifinta ta yanda baya iya ja da maganarta, matsi da takura kuma suka sakata barin gidan gaba d'aya, yanzu

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login