Showing 75001 words to 78000 words out of 325849 words
yayanta sun samu rabonsu inda saratu aka bata abinda ko kashi d'aya na mace d'aya bai kai ba, wannan bak'in cikin da k'uncin yasa Saratu ita ma cewa ga garinku nan, haka ita ma akayi na ta makokin inda abinda aka basu ya zama k'ark'ashin kulawar Hassana.
*Duk* abin nan dake faruwa Husseina na cikin garin, inda gaba d'aya ta lalace ta zama karuwa mai lasisi, duk da ba kowane lokaci take zaune garin maradi ba, dan wasu lokuta mawak'a suna d'aukarsu su tafi dasu wani gari dake nigeria da ake kira *hirji*, cikin jikinta kuma magajiya uwar karuwai ta so a zubar dashi amma tace a'a, da haka ta dinga rainon cikin kusan a wannan lokacin ita ce karuwar da wasu suka fi nema suna bayar da kud'i masu yawa dan su kwanta da ita saboda tana da ciki, saida cikinta ya tsufa ta aje harkar na d'an lokaci har saida ta haihu, namiji ta haifa wanda mata masu zaman kansu sukayi babban bidiri, mawak'a suka baje nasu kolin daga ciki harda irinsu margayi *Sa'adou bori*, ranar suna an kwana ana cashewa daga k'arshe dai yaro ya ci sunan *Labaran* a cewar Husseina shi yafi kowa bawa gidan karuwan tallafi, dan haka ya cancanci a mishi takwara, (duk wannan fa abun ya faru),duk da a lokacin ta samu labarin mutuwar mahaifinta amma sai tace "Allah raka taki gona."
Rasuwar mahaifiyarta kad'ai ta girgiza ta data samu labari, amma duk da haka bata je gidan ba saboda tace bata son sake ganin unguwar ma, haka ma wajen Suley tafiya kawai yake yi, yunwa na ci k'ishin ruwa na ci, domin duk abinda yake samu yasa a cikinshi ba isarshi yake ba, hasalima ba komai ne yake samu mai kyau ya ci ba, haka yake tafiya ba um ba um um, ya galabaita sosai ya jikkata ta yanda ya fita hayyacinshi, haka Suley ya d'auki tsawon lokaci yana tafiya ba tare da yasan inda yake saka k'afar sa ba har tsawon *wata biyu*, a cikin tafiyarshi ne Allah ya had'a shi da wani mutum mai kirki d'an kasuwa mai sunan *Alghabit*, mutumin *Agadez* ne kuma hamshak'in mai kud'i, yana kan rak'uminshi ya ga Suley na tafiya kamar gunki, kallo d'aya ya masa ya tabbatar yana tare da k'ishin ruwa da kuma yunwa dama gajiya, dan kuwa har k'afafun shi sun kumbura kamar na mai tsohon ciki saboda tafiya, tsayar da rak'umin yayi dan a wannan lokacin shine abun hawan kuma mai daraja garesu, duk da akwai mota a lokacin amma dai bata damesu ba kamar rak'umi ko kuma moto, saida rak'umin ya durk'usa har k'asa ya sauka ya tunkari Suley, tare gabanshi yayi yana mishi magana da gurb'atacciyar hausarshi daya d'an kama wajen yawon kasuwancinshi a bakin hausawan, ganin kallonshi kawai yake ya tabbatar ba lafiya yake ba, hannunshi ya kamo ya zo kusa da rak'uminshi ya d'auki aglami (buzun sallah) da gorar ruwa da kuma wani d'aurin abu a cikin fata, gefe suka koma k'ark'ashin wata bishiya ya shinfid'a aglamin ya zaunar da Suley, ruwan ya fara bashi ai ko da sauri ya fizga daga hannunshi ya kifa baki bai sauke ba saida ya shanye, da mamaki da kuma tausayinshi ya zauna kusa da shi ya bud'e wannan d'aurin ashe akushi ne a ciki da abinci, nan ma abincin nan ya ci sosai kafin ya sake bulbulo mishi ruwa a yar babbar jarkar da ke d'aure da rak'umin. Tare ya tafi da shi a d'ora shi akan rak'umin, idan dare yayi su yada zango da safe su ci gaba, kwana goma sha bakwai suka d'auka kafin suka isa garin agadez.
*A garguje*
Haka ya sauke Suley gidanshi da taimakon iyalinshi, inda ya samu limamin unguwarsu ya zo da shi har gidan ya nuna mishi Suley, daga lokacin aka d'ora shi akan magani da rok'on Allah, Allah maji rok'on bayinsa sai gashi cikin *wata biyu* Suley ya samu lafiya ya dawo kamar yanda yake, Alghabit dama 'ya'yanshi mata ne suka fi yawa, dan haka saiya rik'e Suley kamar d'an daya haifa, tunda jiki yayi kyau sai Suley ya d'aura d'amarar neman kud'i dan yaje ga ahlinshi ya tallafesu, hakan yasa duk safe ta Allah ya kan shirya ya fita kasuwa, lokuta da dama dakon kayan mutane yake ana biyanshi kud'i kad'an, wani lokacin kuma idan kayan manyan yan kasuwa sun zo sai su sauke kayan a biyasu, da irin wannan k'ok'arin na shi ya fara tara kud'in komawa gida, duk lokacin da zai fita idan Alghabit ya tambayeshi sai yace zaije zaga gari ne kawai, a haka wata rana Alghabit ya sake komawa fatauci, a lokacin ne Suley ya fahimci wani ha'inci da ake mishi idan baya nan kuma a cikin gidanshi, babbar 'yarsa *Zeeya'atu* wacce gaba d'aya shekarunta basu haura sha shida ba tana ganin ya bar garin ita ma zata fara na ta yawon dan jin dad'in rayuwarta, kuma mahaifiyarta *Zaha* iya ke d'aure mata gindi tana bata umarni, babban tashin hankalin shine wani lokaci har ta kan iya kwana ba gida ba, nan yayi niyyar sanar da mai gidan idan ya dawo, domin kuwa babu mai zarginta, dan idan ta tashi fitar ta kanyi shiga ta kammala sannan tayi nesa da gida.
Bayan Alghabit ya dawo tuni sauran yaran dake tayashi kasuwanci suka rigashi isowa tare da sauran rak'uman dake d'auke da kaya, dan haka kai tsaye ya wuce kasuwar garin dan a sauke wannan kayan a rabawa k'ananan yan kasuwa, a nan fa yayi kicib'us da Suley a cikin masu sauke kayan, wannan abu shi ya birgeshi a tare da yaron ya kuma ji ya yarda dashi ba ko kokonto, hakanne yasa ko da suka iso gida bai bawa Suley damar fad'in abinda yayi niyyar fad'a ba yace ya d'ora shi akan harkokinshi, yanzu ya zama kamar magajinshi zai dinga tafiyar da komai, wannan karamcin da wa suley ya sa bai iya fad'an komai ba saboda kunya, ba b'ata lokaci Suley ya durmiya cikin kasuwanci ya fara sarrafa dukiyar yanda ya kamata, sai Allah yayi wa Suley baiwa ta nasibi ta yanda duk abinda ya tab'a yakan hauhawa, cikin wata *uku* sai gashi shi kanshi alghabit na mamakin yanda dukiyar take bunk'asa, sai kawai ya sake yarda da shi ta yanda wata ranar *alhamis* ya shirya yace wa mutanen gidan zaiyi wata yar gajeriyar tafiya ya dawo, fatan alkairi suka mishi amma babu wanda tunaninshi ya bashi wani abu.
Sam Suley baya dawowa idan ya fita sai yamma, amma a ranar mantuwar da yayi tasa shi dawowa gidan lokacin da bai kamata, bai samu kowa a tsakar gidan ba dan haka ya shiga d'akin shi dake farkon shiga gidan, ya d'auko sak'on ya fito ya rufe d'aki zai juya kenan yaji sauti kamar kukan Zeeya'atu, A hankali ya dawo ya d'an daga k'afafun shi ya lek'o ta katangar data mishi shamaki da nasu d'akunan, ashe ciki ne da ita mahaifiyarta kuma ta amso mata maganin gargajiya dan cikin ya zube, ganin jini duk ya b'ata mata jiki ga bala'in kukan da take uwar na k'ok'arin shigar da ita d'aki yasa shi sukwanowa da nufin taimaka musu, yana daf da isa wurin su basu san da shi ba mahaifiyarta tace a harshen buzanci "Dangana mana Zeeya, ke da kin samu ma cikin zai zube."
Duk da bai iya komai a hausarsu ba amma yana jin d'aid'ai, a cikin hakane ma ya gane ta ambaci sunan ciki, da kuma zubewa amma sauran kam baiji komai ba sai dai kasancewar shi matashi mai matuk'ar basira da d'aukar duk abinda yaji yasa ya hardace kalaman data fad'a a buzancin, juyowa yayi ya fita ya barsu nan, yaje kasuwa ya kai sak'on yana cin abincinshi na rana tare da wani shi ma yaron Alghabit ne, da k'yar yaron ya fahimci abinda suley ya fad'a mishi yace yana son sanin fassarar , haka dai ya had'a haussar da k'yar ya fad'a mishi abinda ake nufi, sosai wannan al'amari ya girgiza shi ya kuma yi niyyar fad'awa mai gidanshi.
*K'addara ta riga fata*
Ko da ya samu alghabit dan sanar dashi sai ya katseshi tare da cewa ya kira mishi liman, bayan sun dawo tare da liman ya kira Zaha da Zeeya, bud'ar bakin Alghabit shine ya baiwa Suley 'yarshi Zeeya'atu wacce yafi so da k'auna, kuma baya buk'atar komai daga gare shi sadaki ma shine zai biya a matsayinshi na uban Suley, da sauri Suley ya kalleshi gabanshi na tsananta bugawa, juyawa yayi a hankali ya kalli Zeeya wacce take jin kamar ta mutu tsabar bak'in ciki, amma son nuna ita saliha ce yasa ko d'agowa ba tayi ba, zaha kuma kuma ba tace bata ji dad'i ba ba tace taji dad'i ba, kowa da abinda yake tunanin a zuciyarshi har Alghabit ya katsesu da cewa zai basu gidan da zasu zauna kuma gidan ya mallakawa Suley halak malak, sannan ya k'ara da cewa ya ware mishi jari mai yawa da zai tsaya da k'afar shi shima, wannan abun ne yasa Suley yin shiru ya karb'i auren Zeeya, gashi kuma Alghabit yace za'a d'aura auren juma'a ne ba b'ata lokaci.
*Allah ka gafarta mana.*
10/06/2020 ร 12:07 - Ummulkhairi: ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*BADAK'ALA*
๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ _*AHALI NA*_๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
๐ณ๐ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```
_Bismillahir rahamanir rahim_
_13_
Lafiya lau Suley ya zo maradi kuma wannan karan tafiyar tashi tayi goshi, domin kuwa da idonshi yaga k'anwar shi da irin mummunar rayuwar da take, wacce a lokacin take d'auke da yaronta Labaran daya ke da shekara d'aya da haihuwa, wani ikon ubangiji cikin sauk'i Suley ya shawo kanta suka dawo gida tare, amma bata yarda ta biyo shi gidan mahaifinsu ba saida ya tabbatar mata da yana da kud'i zai siye musu gida su zauna tare saiya kawo iyalinshi, kasancewar lokacin akwai albarkar rayuwa yasa ya siye lafiyayyen gida kuma a farashi mai sauk'i, gyara yasa aka ma gidan sosai tare da ware d'akuna uku, nashi, na Zeeya, na Husseina, saida aka gama gyaran gidan Husseina ta tare a ciki sannan ya juya ya koma agadez dan sanar da mutanen can halin da ake ciki tunda ba waya ke akwai ba a lokacin, nan Husseina ta ci gaba da zama a gidan tana jiran dawowarshi, babu wani abu da bai bar mata ba duk dan tsoron karta sake sub'uce musu, wanda wannan zaman da tayi kuma mutane aka sake d'ora mata ido, dan dama gidan daya siye ba nesa ne sosai da gidan nasu ba wanda yanzu daga Ramma sai Innusa a gidan da matanshi biyu, haka yaje gida lfy kuma tun a zuwanshi iyalinshi Zeeya ya fara yi wa magana akan komai, kuskuren da yayi shine sanar da ita da yayi halin da Husseina ke ciki tunda farkon abinda ya faru har k'arshe, sannan yace a matsayinshi n'a mijinta dole ta shirya su koma mahaifarshi tare.
Kamar dai yanda yasan zai faru hakane kuwa, domin direwa tayi tace Allah ya tsareta da komawa garinshi ta bar na ta garin, kwana hud'u ya d'auka yana lallab'ata kan ta shirya su tafi amma tana botsarewa, dan haka k'arshe ya samu iyayenta ya fad'a musu komai da ake ciki, Allah sarki dattijon arziki Alghabit, nan ya rufe ido duk da son da yake mata ya mata tatas tare da bata umarnin ta had'a kayanta su tafi, sannan yace Suley zai iya siyar da gidan daya bashi saiya k'ara ya ci gaba da kasuwancinshi, haka kuwa akayi sai dai hakan ya d'auke shi kusan wata d'aya kafin suka d'auko hanya kuma suka zo da izinin ubangiji.
Duk da a lokacin ana ganin yara 'yan biyu, amma ganin 'yan uku kam ba'a cika samu ba, dan haka wannan yara na Suley sai suka samu farin jini a cikin unguwarsu fiye da kima, gasu kuma dama sak mahaifiyarsu suka d'auka buzuwa jawur da su kuma tub'ur tub'ur, hakan yasa mutanen sintiri cikin gidan ana duba yaran wasu ma har uwar kallonta suke suna son tayi magana suji harshenta da hausarta ke da ban sha'awa da dariya, sai dai ba anan gizo yake sak'ar ba, tunda suka zo ta ga d'akin daya fitar ma da Husseina ma had'e yake da nata saita mayar da ita kamar kishiyarta, wani haushinta take ji tare da k'yamarta, ita ma Husseina a lokacin da sauran d'anyan kai na rayuwar da tayi saiya zama babu ruwanta da harkar matar yayan nata, dan haka babu mai shiga shirgin kowa, hatta yaranta Zeeya bata bari ko da rarrafe suje d'akin ta, suna dosa zata taro su tana habaici da bak'ak'en maganganu a harshenta na buzanci, Husseina kuma tunda ta fahimci yayanta ma zaman hak'uri yake da ita kuma kullum yana cewa tayi hak'uri da halin Zeeya'atu sai kawai take ba banza ajiyarta, duk da zamansu gida d'aya baisa ta d'aga mishi k'afa ba na salon rashin mutumci, zai kawo abinci mai rai da lafiya ta sarrafa amma idan ta gama sai tace bata dafa da shi ba sai ita sai 'ya'yanta, shi kuma sai yace yaji dad'i tunda ma an dafa da 'ya'yan nashi, maganar saduwa kam shi har ma ya manta rabon daya kusanceta, dan tun kafin su fahimci tana da ciki, yanzu kuma daya nuna mata buk'atar shi sai tace ai ina, bata sake shirya haihuwar wasu yaran ba, idan ya isheta da magiya saita dinga cewa wai ai da karuwa a gidan yaje ya biya kud'in shi mana ya samu nutsuwa, hakan yana k'ona masa rai sosai, da wannan rayuwa har ya saba da shan jar kanwa da lemun tsami, Husseina kuma ta fad'awa yer uwarta Hassana wacce ke gidan aurenta ita ma halin da d'an uwansu ke ciki, shawartarshi sukayi yayi aure, kuma bai watsa musu k'asa a ido ba, sai dai Allah ya hukunta Zeeya ita ce matarshi ta har abada a duniya, watak'ila tanadin da ubangiji ya mishi ne mai girma a lahira, shiyasa duk yarinyar daya nema maganar bata zuwa ko ina sai a barta, harya gaji yace ya hak'ura ba zai zama kamar mane-min mata ba kullum a hanyar zuwa gidan yan mata, mutane kuma da 'yan uwa sun alak'anta hakan da Zeeya wacce take kallonsu tace eh tabbas ita ce, ba zai tab'a had'a ta da wata mata a duniya ba, kuma har ga Allah babu boka babu malam a lamarinta, kawai tana tauna tsakuwa ne dan aya taji tsoro, k'iyayyar Husseina ta sake hudawa ta shiga zuciyar Zeeya a sanda duk in ta k'i bashi abinci ita take bashi, ya zamana ma harda rana ita ke dafawa tana zuwa kasuwa da kanta tana kai mishi, hakan yasa take ganin ba tada maraba da kishiyarta, saidai duk masifar da take daga Suley har Husseina babu mai tanka mata.
Shekaru na ja duniya ana sake ci gaba zamani na k'ara shigowa, kai ya waye ta yanda kowane yaro akan saka shi makaranta dan yak'ar jahilci, sai dai ga wanda kan nasa bai waye ba kawai, a lokacin ana shiga ajin farko da shekara bakwai, haka Suley ya had'a duka yaran harda Labaran ma daya d'an fisu da watanni aka kaisu makaranta aka saka, takaici kamar zai kasheta dan bata so hakan ba, shiyasa har yaran saida suka shiga uku, dan dukansu take sosai tana cewa babu su babu d'an karuwar nan, amma abinka ga yaro yanzu yanzu ne zata sake ganin sun had'e wuri d'aya, musamman ma Hussein da yafi sauran zuciya, tana dukanshi zai koma bakin k'ofa yace anje anyi, shi kuma Labaran yaran sun shiga ranshi sosai, suna matuk'ar birgeshi sosai sosai, yana mamakin ganinsu su uku duk iri d'aya, haka zai saka su gaba ya tab'a hancin wannan ya duba yatsunsu ya ga kala d'aya, yace suyi dariya ya ga iri d'aya wannan yasa yake k'aunarsu sosai, haka suke zuwa makarantarsu tare suna dawowa, wani hukunci na Allah kuma sai Labaran ya zab'i zama kamar Suley ma'ana d'an kasuwa, cewa yake shi zai dinga binshi kasuwa ya daina zuwa makaranta, amma Suley yace yaje yayi karatu da hakane zai zama d'an kasuwa mai ilimi ba jahili ba, Hassan shima da abinda yake son zama, domin yaro ne mai son k'irk'irar abu da kanshi, haka ma Hussein yana son ya ga ya zama matuk'in jirgin sama wanda a lokacin idan ya wuce zakaga har babba ma ya d'aga kai sama ya kalla, Gambo kuma tunda ya samu Suley wata rana yana shan lemun tsami ya tambaya shi dalili yace cikinshi kawai ke ciwo, sai ya d'auri niyyar zama babban likita danya warkar da mahaifinshi, amma sakamakon wani abu daya shigo ya gifta ya musu shamaki da cikar burinsu wanda zasu iya kiranshi da k'addararsu sai kowa ya zama abinda bashi yake so ya zama ba, hakan kuma ya faru ne sanadiyar jiji da kan uwarsu da kuma son cika nata burin.
Innusa yayan Suley ne ya kwanta rashin lafiya mai tsanani, Suley na shiga gidan ya ganshi sai dai baya samun wani sakin fuska daga kan Ramma har shi Innusa, domin kuwa suna matuk'ar jin zafin ci gaban da yake samu a harkokinshi, dan Suley mutum ne mai k'wazo, duk abinda yasan zai samu riba a kai to ya kan siyoshi ya siyar, ya zama d'an kasuwa da ake ji da shi a wannan lokacin, sannan matarshi da suke gani buzuwa ce wanda a lokacin sun san auren buzuwa *jidali* ne kamar yanda wani mawak'i ya fad'a, har yan uku yaje dasu sun ga baffan nasu har Gambo yana cewa idan ya zama likita zai bashi magani ya warke, Zeeya ce bata je ba dan haka Suley yace taje ta