Showing 90001 words to 93000 words out of 325849 words

Chapter 31 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

556

Middle Ads

a wurin tayi kamar ta suma amma tana jin duk abinda zai faru, jakar kayan dake hannunta ce ta fad'i gefe, inda d'an kwalinta kuma ya rufe mata fuska, cikin tashin hankali Abbas ya fito tare da Abdul suna salati da sallalami, suna zuwa gaban budurwar da ke kwance suka ganta kamar babu rai, amma kuma babu alamar rauni a jikinta ko d'aya, a hankali Abdul ya sunkuya yana kiran " Baiwar Allah, baiwar Allah kinji ciwo ne?"

Jin shiru yasa Abbas d'agowa ya kalli Abdul sukayi ido hud'u yace "Ko dai ta mutu ne?"

Ido waje Abdul yace "Ban sani ba Dady, mu kaita asibiti to."

Da sauri ya d'ago ya juya ya ga babu alamar mutane a wurin dan unguwar silent ce, dan haka ya tak'ark'are zai kamata yace wa Abdul "Help me mu sata mota."

Da sauri suka kamata suka nufi mota da ita zasu saka ta gidan baya, k'aramin kallabinta ya fad'i k'asa fuskarta ta bayyana, dammm! Abbas yaji gabanshi ya fad'i saboda kallon fuskarta da yayi, har suka sakata a ciki Abdul ya d'auko jakarta Abbas bai daina kallonta ba, tabbas babu kama a fuska, amma dai yana jin kamar zai tuna wani abu a game da yarinyar, wani yanayi yake ji da bai iya fad'in takamaimai abinda yake ji ba lokaci gida, har Abdul ya saka jakarta bayan inda take zaune ya rufe Abbas na tsaye, Abdul ne yace "Dady ko ka santa ne?"

Da d'an sauri ya kalleshi, maimaita tambayar yayi a ranshi *ko na santa?* to a ina? Ya tambayi kanshi, cikin sanyin jiki da rashin kuzari ya rufe motar hakan yasa Ma'arufa farkawa, a zabure, saida ta juya da k'arfi ta ganta a mota sai kawai ta fashe da kuka da k'ok'arin bud'e motar tana fad'in "Wayyo Allah na shiga uku, dan Allah ku rabu dani karku cutar dani, dan Allah kuyi hak'uri kunji ku sauke ni anan, zan koma gidanmu ma."

Jin ta bud'e motar yasa su zagayawa wajenta da sauri suna son suji akan su wa take magana, fitowa tayi amma saboda iya shege saita durk'ushe alamar k'afar ta ba zata taku ba, Abbas ne yace "Kinga baiwar Allah, ki nutsu ki kwantar da hankalinki, babu abinda zamu miki, asibiti ne zamu kaiki kinji."

Sake mik'ewa tayi tana kuka tace "A'a wallahi bana so, dan Allah ku barni na tafi kafin su riskeni a hanyata, wannan ba komai bane a wajena, nasha wahalar da tafi wannan ma kuma ban mutu ba."

Zata taka k'afar ta sake cijewa ta d'yangasa ta da k'yar tana cije baki, lura da hakan da Abbas yayi yasa yace "Saurare ni baiwar Allah, da alama k'afar ki ta bugu sosai, ki zo mu kaiki asibiti daga nan saiki fad'a mana inda zaki je sai mu kaiki."

Kamar gaske cikin kuka mai ban tausayi tace "A'a ba zanje ba, dan Allah ku barni na tafiya ta, na so ace had'arin nan da mukayi da ku ya zama silar mutuwa ta, amma gashi har ita kanta mutuwar ma bata son d'auka ta, ya Allah! Sai yaushe ne wannan azabar zata yaye?"

Yanda take magana da kuma yanda take rera kukan yasa jikinsu duk yin sanyin, a hankali Abbas yace "Baiwar Allah yanzu ina zaki je?"

Girgiza kai tayi tace "Ban sani ba."

Abdul ne yace "To ina ne gidanku?"

Kallonshi tayi cikin share hawaye tace "Da nisa, ni ba 'yar garin nan bace."

Abdul ne ya sake cewa "Kuma kin tabbatar baki san inda zaki je ba?"

Cikin kuka tace "Kwana na hud'u a garin nan ina yawo bansan inda zan nufa ba."

Abbas ne yace "To amma baki kowa anan ne?"

"Bana da." Ta fad'a a tausashe, da mamaki yace "Amma kinsan baki da kowa me yasa kika zo nan?"

"Bani ce na zo ba, k'addara ce ta kawo ni nan."

Ajiyar zuciya Abbas ya sauke yana tunanin abinyi, ya d'an jima a haka har Ma'arufa ta jawo jakarta tace "Sai anjimanku."

Ta fara tafiya da k'yar tana d'yangasa k'afa Abbas yace "Dakata baiwar Allah." Tsayawa tayi ta juyo shi kuma yace "Idan ba damuwa ki zo muje gidana, saina kira dr ya duba ki tunda kin k'i yarda muje asibiti."

Shiru tayi tana jin wani farin ciki na shigarta na samun nasara, dan a yanda suka shirya dama shiga gidan ne zai musu wahala, amma tana shiga babu abinda zai tsayar da ita aikin daya kaita kawai zata fara, jin shirun yayi yawa hakan yasa Abdul cewa "Ki zo muje kinji, kar kiji tsoro, Abbanmu mutumin kirki ne, ki d'auka daga yanzu har zuwa lokacin da zaki bar fadarshi zaki kasance cikin aminci ne."

Jim ta sake yi alamar tsoro kafin tace "Na yarda zan biku, Allah yasa va zaku cutar dani ba kamar yanda wanda na zo domin shi garin nan ya nemi cutar dani."

Tabbas akwai labari mai ban tausayi a cikin rayuwarta, amma kuma ba yanzu ne lokacin da zasu sani ba, dan haka ta taho ta shiga da k'yar kafin suma suka shiga suka tayar, bata fi tafiyar minti biyu ba suka tsaya k'ofar gidan, horn yayi mai gadi ya bud'e mishi k'ofa tare da musu barka da zuwa, suna ratsawa suka shiga Ma'arufa ta saki baki tana kallon gidan, cab'! Ashe dama wannan masarautar ya gina ya shiga shi da iyalinshi? Gaskiya gurguwar nan ta cuce mu da bata bari wannan ya zama ubanmu ba, da wannan tunanin da take taji motar ta tsaya sun fita, fitowa tayi ita ma inda tabi bayansu tana sake k'are ma gidan kallo, kai kasan maganar ma ace an kashe kud'i a wurin b'ata yawun baki ne, dan ko a k'asashen waje ka gida wannan gida dole asan ka tara masu gidan rana, ji tayi kamar zata fad'i a daidai lokacin da ta taka k'afarta a teress d'in falon, ga wani masifaffen sanyi da k'amshi daya daketa, a lokacin suna kan dinning suna cin abinci dan haka suka zarce can, a tak'aice dai ta samu tarba sosai a gurin kowa da kuma sakin fuska banda Abba wanda har yanzu ranshi a b'ace yake, abincin ma ya fito ci ne saboda yaran karsu damu da damuwarshi tunda haka aka saba, nan Ma'arufa ta zauna aka yi serving d'in ta ita ma tana ji kamar tace wayyo ta wayyo kanta, abincin dare d'aya amma kai kace wata walima ce tasa aka shirya, nan suka ci abinci aka gama sai cewa tayi zata tafi, duk yanda suka so da ita ta bari a kira likita ta k'i, aka suka hak'ura Ammie tace bai kamata ta tafi ba tunda dare yayi kuma tace bata san kowa ba, a haka Ma'arufa ta samu yanda take so ma'ana masauki a gidan.

D'aki ne dake k'asa kuma babu tazara tsakaninshi dana Sameera, babu abinda babu a ciki dan Sameera ce ke kula da shi saboda saukar bak'i idan sun zo daga basraba, duk da wani lokaci idan ta b'atawa Abbas rai yana cewa kishiya zai mata kuma ya sakata a d'akin, amma sai tace ai babu mai k'arar kwanan da zata yarda ta shigo mata gida, ko shi saita k'ona shi da ranshi idan yayi wasa, to fa anan Ma'arufa ta sauka ta samu tayi wanka ta canza kaya, kafin ta kwanta Ammie ta turo Raudat da magani wai ta shafa a k'afar ta ko taji dama dama, har Raudat zata fita Ma'arufa tace "Ya sunanki?"

Juyowa tayi da fara'a tace "Raudat."

Murmushi ta mata kafin tace "Zo zauna muyi hira lil sis."

Dawowa tayi ta zauna tana kallonta ita kuma tace "Ina Ummynku take ne? Ko kuma mahaifiyarku ta rasu kamar ni? Dan na fahimci wacce kuke kira da Ammie kamar granny d'in ku ce ko?"

Bud'ar bakin Raudat sai cewa tayi "...

*Sub'ul da baka.*

👏
12/06/2020 à 11:49 - Ummulkhairi: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

💞 _*MASOYA NA*_💕


_Bismillahir rahamanir rahim_

🇳🇪 *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_9_


Tunda Allah ya halliceta take zaune shekara goma sha bakwai a matsayin matarsa bata tab'a sanin cewa baya k'aunar ta ba irin yau, to mana baya k'aunar ta, dan rashin imanin daya darza mata ko dabba kayiwa haka kasan sai dai a d'auki gawarta, tabbas tasan akwai fyad'e a duniya, domin kuwa ita ta hanyar fyad'en ma ya rabata da nata budurcin, amma sanin azabar dake tattare da haka bata sani ba kam sai yau, babu inda bata jin yana mata zafi a jikinta, kama daga labb'anta wanda har cizasu yake tsabar mugunta zuwa kan k'irjin ta daya dinga lindasu kamar yana wankin kayan da suka shekara ba wanki, k'asanta kam ko magana ma ba ayi, duk da uwa ce ita ta haihu amma gyara da kular da take bawa wurin yasa yake zam-zam, to a yau dai kam ta tabbatar ya gama wangaleta ta yanda ko d'inketa akayi ba zata sake birgeshi ba bare ya moreta, cikin wannan hali da take taji ya kasheta da wani tattausan mari wanda ita a wurinta wata azabar ce ya biyota da ita, mik'ewa yayi ya fad'a ban d'akin ta ya tsarkake kanshi, yana fitowa ma jakar daya jefar ya d'auka ya d'ora akan gado ya bud'e ya d'auki kayanshi ya saka, sai lokacin ya kunna hasken d'akin ya kalleta.

Sam baiyi dariya ba saboda baya so ta samu damar sauke mishi tijara, amma yasan yau kam mai rabasu sai Allah, ko bata zage shi ba saita dake shi, har zuciyarshi yasan tana buk'atar taimako, amma danya d'an fara bata tsoro idan yace tayi sau d'aya ba sai ya maimaita ba yasa ya k'are mata kallo ya fita a d'akin, tana ganin haka ta tattara k'arfinta ta mik'e zaune da k'yar, kallon kanta tayi ta madubin dake gefenta tace "Ni zai yi wa haka? Lallai ma mutumin nan."

Misalin *09:00* na dare suna zaune dukansu kan dinning table, sanye take da doguwar rigar material mai kyau da tsada bleue light da d'an kwalinta, babu komai a fuskarta data shafa idan ka cire mai da lips a bakinta, tana hango Ammie zaune ta sake sangarta tafiyarta cikin shagwab'a ta k'arasa ta rumgumeta ta baya ta fashe da kukan sangarta, da sauri Ammie ta fara tambayarta "Auta ta lafiya? Waya tab'a min ke?"

Abbas da tunda ta fito yake kallonta, maganar gaskiya kallo d'aya ya mata ya ga har tayi wata ramar k'arfi da yaji, hatta tafiyarta ma ta kasa daidaituwa da kyau duk jikinta ya saki, wani haushi ne ya tokare masa mak'oshi yaji kamar ya mareta, shin bata lura da bak'uwar dake wurin bane? Idan ma bata ganta ba ai tasan Abdul na wurin yaron dake shirin zama sirikinta, kasa amsawa tayi yayin da yaran duk suka k'ura mata ido har da Ma'arufa dake mamakin karuwanci Sameera, Ammie ce ta gyara zamanta kan kujerar da nufin zaunar da Sameera kan k'afafun ta, amma suna had'a ido da Abba taga kallon da yake ma Sameera tasan duk yanda za ayi zai iya d'aukar wuk'a yace zai gagara mata, dan haka ta mik'e tsaye tace "Auta zo muje d'aki na ki fad'a min meya sameki, naga duk kin canza kamar ba ke ba."

Hannunta Ammie ta kama zasu fice sai idonta ya sauka kan bak'uwar su, yanzun ma kamar ganin ta da ita na farko sai taji gabanta ya fad'i tare da jin haushin yarinyar, wani tunani ne ya d'arsu a zuciyarta take a wurin, shin idan fa k'addara tasa yarinyar ta aurar mata miji? Kanta ta bawa amsa ta hanyar fad'in "Ai kuwa babu abinda zai hanaki k'ona gidan nan kamar yanda kike fad'a masa."

Da haka suka tafi part d'in su Ammie suka zauna falo, cikin rarrashi Ammie tace "Auta fad'a min meya miki?"

Turo baki tayi gaba ta kwantar da kanta saman k'afafun Ammie tayi shiru, cire mata d'an kwalin tayi ta fara shafar kanta data ji shi a jik'e, take ta fahimci komai, dama ba kunya ce tsakaninsu ba dan haka Ammie tace "Auta halan hukuntaki yayi saboda baki taho tare da mu ba?"

D'agowa tayi ido taf da hawaye kamar zata fashe da kuka tace "Ammie hukuncin ma mai tsanani, wallahi bai tab'a min irin shi ba sai yau, bansan a ina ya koyi wannan muguntar ba, ni gaskiya Ammie daga yanzu d'akin ki zan kwana har saiya bani hak'uri."

Kwantar da kanta tayi tana daddab'ata b'angare d'aya tana toshe baki tana dariya, labari ta fara bawa Ammie yanda sukayi da matar waziri, dariya kawai Ammie take tana godewa Allah da abun ya tsaya iya mari kawai, suna haka sai ga Abbas ya shigo tak'im tak'im kamar wanda aka bawa sarauta, Ammie na ganinshi ta had'e rai tace "Kai kuma malam lafiya? Meya kawoka wajenta?"

Saida ya harari Sameera yace " Ni ba wurinta na zo ba."

Zaune yayi kan kujerar dake fuskantarsu ya kalli Sameera dake wurga masa harara yace "Ke tashi ki bamu wuri zamuyi magana da uwa ta."

Sake mak'alk'ale Ammie tayi tace "Ba zan je ko ina ba, ka fad'i duk abinda zaka fad'a ina gaban uwata."

Murtuke fuska ya sake yi, matsalarshi da ita daman kai tsaye zai bata umarni tace ita ba haka ba, kafeta yayi da ido kawai hakan yasa Ammie kallonta tace "Yarinyata, shiga d'aki na ki kwanta abinki gani nan zuwa yanzu, idan kin shiga ki duba a drower akwai kayan dad'i ki d'auka kinji."

Mik'ewa tayi a kasalance ta wuce ko d'an kwalin nata bata d'auka ba, da kallo ya bita kafin ya kalli Ammie wacce tace "To ina jinka, lafiya da zaka wani katsewa yata jin dad'in ta?"

Mik'ewa yayi yace "Ba komai, dama zan d'an fita."

Kafin tayi magana taga ya sa kai ya nufi d'akin nata kuma, girgiza kai tayi tace "Kaji da munafurcinka, da nace wurinta ka zo ai cewa kayi a'a."

Sameera na sunkuye zata d'auki chocolat taji saukar mari a mazaunanta, da sauri ta d'ago ta dafe kayanta tana fad'in "Washhhh."

Tana ganin yanayin shi sai kuma tayi shiru, cikin muryar shagwab'a tace "Dan Allah Abban Ameer ka daina wahalar dani haka, ya kamata fa ace yanzu na wuce ajin shan wahalarka, wacce na sha ma a baya lokacin da nake maka bauta ta isa haka."

Yana kallon k'aramin bakin har saida ta dasa aya sai kawai ya had'ata da bango ya had'e bakinsu, wani bala'in kiss ne yake mata mai matuk'ar zafi kamar zai cire mata labb'a, tuni idonta suka kawo ruwa ta rufe ido wasu hawaye masu zafi sirara suka shiga fitowa suna bin kumcinta, a gefen fuskarshi ne ya ji alamar lema hakan yasa ya tsaya yana kallonta, cikin wata irin murya ba tare daya matsa daga cikin jikinta ba tace "Sam ki dinga jin magana ta mana, bana so muna irin haka dake dan mun girma yanzu, ki ce zaki dinga ji duk abinda na fad'a miki, ni kuma ba zan sake bari ki zubar da hawaye ta dalili na ba."

Bud'a ido tayi cikin shashek'a tace "Zan dinga jin maganarka indai kayi alk'awarin ba zaka sake min irin muguntar nan ba ta yau?"

Yanda tayi maganar saiya k'ayatarda shi, bud'e mata hannayenshi yayi alamar ta taho, sake fashewa tayi da kukan da bata san dalilinshi ba ta fad'a cikin lafiyayyen k'irjin shi, matseta yayi sosai yace "Na miki alk'awarin ba zan sake ba indai nima zaki dinga jin duk abinda zan fad'a miki."

Cikin shashek'ar kuka tace "I promise u, please forgive me."

Cikin shafar tattausan bayanta yace "I forgive u my Meerata, i really love u."

Sake k'amk'ame shi tayi a haka suka fito falon tare, Ammie na ganinsu rumgume da juna sai ita taji kunya, dama kuma ba sabon abu bane a wurinta, kullum suka samu matsala saita tsaya bayan Sameera ko tasan ita ce bata da gaskiya, ba jimawa kuma sai ka gansu a had'e a jone.

➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️

Abbakar ne ya samu Saleem a d'akin shi yana waya da Fadila kamar sun jima da fahimtar junansu, yana ganin shigowarshi ya datse kiran yana fad'in "Yah Abbakar, kaine yanzu?"

A hankali ya k'araso cikin jan k'afar shi ya tsaya kusa da shi yana kallonshi yace "Saleem baka kwanta ba har yanzu?"

Murmushi yayi yace "Ban kwanta ba yah, amma kai ma ya akayi baka kwanta ba har yanzu?"

Shima murmushi yayi yace "Ina ta tunaninka ne Saleem."

Da mamaki yace "Tunani na kuma yah? Akan me? Ko dai tunanin Zeenat?"

Girgiza kai yayi yace "Tunaninka nake Saleem, tsoro kake bani, ina gudun kar kaje kayi abinda zai saka mu cikin matsala, shiyasa na gagara bacci har na zo na sameka, kwanan nan kana wayon fita kuma baka zama sosai a shago, sannan kashe kud'in ka ya k'aruda kaso goma, me kake yi da kud'i Saleem? Ina kake zuwa idan ka bar shago?"

Cike da nuna alamun rashin gaskiya ya fara shafar kai yana fad'in "Yah ba komai fa, ka yarda dani mana, ni fa yanzu ba k'aramin yaro bane, nasan abindake daidai da wanda ba daidai ba, so calm down bros."

Ajiyar zuciya ya sauke yace "Saleem kai ba yaro bane, amma dai kasan ina gaba da kai ko? Please Saleem ka fad'a min idan akwai wani abinda ke damunka, na maka alk'awari insha Allah zan taimaka wajen solven matsalarka, amma bana so kaje kayi abinda ya sab'awa shari'a da ma al'ada da mutuntaka ta d'an adam."

Shiru Saleem yayi baice komai ba, jin ba zaiyi magana ba yasa Abbakar cewa "Saleem idan kana da matsalar sha'awa ne ka fad'a min sai mu maka aure, amma karka jefa kanka a harkar neman mata, mummunan zane ne da zaka yiwa kanka na har abada."

Cike da k'aguwa ya kalleshi yace "Yah ba komai fa, dan Allah kaje ka kwanta, ba zan tab'a neman mata ba kai ka sani."

Cikin sanyin jiki ya juya ya bar d'akin inda Saleem yace "Har na fara jin k'amshin yanda zan kuntatawa rayuwarsu zaka zo min da wata magana, yanzu kana komawa d'akin ka hoton matsiyaciyar yarinyar

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login