Showing 135001 words to 138000 words out of 325849 words
ka ba?"
Girgiza kai yayi yace "Yanzu kenan ba zaki saurare ni ba, shin kinsan ma wacece wannan yarinyar? Meerah daga had'uwar mu da ita har abinda ya faru tsakaninmu duk shiri ne, shine da suka shirya dan ruguza mana rayuwa, shiri ne dan tarwatsa rayuwata da kuma taki data yaranmu, idan kin tuna fa washe garin ranar da abun nan ya faru aka nemeta aka rasa, shin kinsan nawa ta nema a hannu na tana blackmailn d'ina? Ki farka daga bacci Sam, idan ba haka ba sunyi nasara a kanmu a karo na biyu."
Mik'ewa tayi tace "Ban damu nasan wacece ita ba, abinda na sani kawai shine ita ce wacce ta kwanta da mijin da nake ganin kamar nawa ne ni kad'ai, Abbas a tunani na na d'auka ko aure kayi matarka ta sunna zakaji kunyar kwanciya da ita a gidan nan, saboda ina tunanin kana so na kuma na gama maka komai ta yanda zakaji kunyar kusantar wata mace, ashe ba haka bane, da karuwa ma zaka iya wulak'anta ni, ashe kasan abinda kake aikatawa kenan shiyasa ka d'aga hankalinka daga ganin hoton Raihan wanda ita nata mai sauk'i ne ma akan naka, haka ka dinga shirgar min 'ya kamar ka samu jakarka duk dan kana tsoron kar tayi abinda kayi, kasa mun aurar da ita a gaggauce ko mak'wabtanmu ba duka suka san da aurenta ba kamar wata marar gata, ka had'a ta da wanda baka san halinshi ba kuma tayi nesa damu, duk dan kana so ka b'oye laifinka."
Juyowa yayi zaiyi magana a lokacin su Abba suka shigo a hargitse, tsayawa sukayi suna kallonsu da mamaki, Abba ne ya iya cewa "Abbas lafiya? Me yake faruwa ne haka?"
Murmushi Abbas yayi ya d'an dafe ciwonka da duk taji mishi yace "Ba komai Abba, kawai dai..."
Shiru yayi hakan yasa Sameera mik'ewa ta kalli Abba tace "Abba ba gaskiya bane, baya so ya fad'a ne saboda abun kunyar daya aikata ba k'arami bane, amma ni zan fad'a maka."
Matsowa ta sake yi inda Abba da Khalifa suke kallonta da ido, Abbas kuma matsowa yayi kusanta yana so ta bud'a bakin zatayi magana ya dakatar, dan ba zai lamunci ta fad'i abin nan ba a gaban d'an shi na cikin shi, sam ba zai jura ba ko da hakan na nufin ya mata dukan da zai sumar da ita ne, kallon idon Abba tayi ta kalli Abbas tace "...
πππ
25/06/2020 Γ 11:27 - Ummulkhairi: π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
π _*MASOYA NA*_π
_Bismillahir rahamanir rahim_
π³πͺ *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```
_13_
Yana isa ya sameta a ciki tsaye bakin wata bishiya da lemu a hannunta tana sha, inda Harira ke binshi cikin iya takonka ba tare daya sani ba, yana zuwa ya tattare babbar rigarshi kamar zaiyi dambe da ita cikin fad'a yace " Meye kuma yanzu? Meyasa kika ce na zo nan? Ko kin manta da na biyaki kud'in da kika nema?"
Kallonshi tayi tana murmushi tace "Dady..."
Yanda ya nunata da yatsa yasa tayi shiru, ido ya zaro mata yace "Karki sake bakinki ya sake kirana da ubanki, ni ba ubanki bane."
Ita dai murmushi take kafin ta fito da wayarta ta rik'e a hannu tana jujjuyata tace "Ok, dama nace ka zo mu had'u ne saboda wani tunani da nayi, na fahimci waccen farashin nayi maka sauk'i sosai, shiyasa yanzu na zo dan na fad'a maka ina buk'atar wasu kud'in."
Cikin b'acin rai da hassala ya shak'i wuyanta da duka hannayenshi biyu ya had'a ta da jikin bishiyar cikin d'aga murya yace "Me kike nufi? Me kike so ki mayar da ni? D'an iska ko me? To ba zan bayar ba, kije kiyi duk abinda zakiyi, abun kunya ba'a kaina aka fara ba."
Ma'arufa da tunda ya shak'eta ta saki waya da jaka da lemun hannunta ta fara kakarin numfashi, sai dai a wannan d'an tsakanin kuma sai wani ciwon ciki daya taso mata na ajali, dafe cikinta tayi tana matsawa tana so ma tayi kuka da ihu amma Abbas ya shak'eta sosai, shi kuma duk a ganinshi wahalar shak'ar daya mata ce, ganin jini ya fito ta hancinta ne yasa shi sakinta sai kuma ta fad'i gabanshi, juya mata baya yayi yana huci da son saisaita nutsuwarsa suyi magana, juyowa yayi da k'arfi zaiyi magana sai kuma ya ga har yanzu bata tashi ba, baya ya ja yace "Ki mik'e, we need to talk."
Shiru ko motsi ba tayi ba hakan yasa ya d'an sunkuya ya daddab'a kafad'arta yace "Dake nake magana."
Shiru babu amsa daga Ma'arufa, turata ya d'an yi hakan yasa fuskarta ta fito tayi rairai tana kallon sama, ganin idonta a kakkafe bakinta bud'e daga yanda take neman numfashi ga kuma jini a hanci, tsoratar da yayi yasa shi wajen yayi baya da k'arfi harya fad'i zaune a wurin, tabbas gawa ce wannan, na kasheta ko me? Da sauri ya rarrafo ya fara jijjigata yana fad'in "Dan Allah Ma'arufa, karki mutua wannan halin kuma a hanu na, kar zunubin ya min yawa mana, please ki tashi Ma'arufa."
A tak'aice ya d'auki minti talatin a wannan halin yana tausa k'irjin ta da nufin numfashinta ya dawo, amma shiru babu labari, haka kawai ya fara hawaye da sambatu barkatai yana ji kamar ya kashe kanshi, tunani ya shiga yi na mafita kafin daga bisani zuciyarshi ta yanke miki kawai ya jefar da gawarta, yana gamsuwa da haka ya mik'e ya cire balaluwarsa ya jefata cikin mota, sam ya manta da wayarta da kuma lemun da take sha, ita da jakarta kawai ya d'auka yasa a boot ya fizgi mota ya bar gidan gonar.
Harira da har fitsari ya kusa sub'uce mata a wando saida taga fitarshi ta fito, idonta akan wayar tasa hannu ta d'auka, dama kuma Ma'arufa ba tsaro take sawa a wayar ba, tana ja sama taga ta bud'e kuma abun mamaki akan wannan banzan video ne wanda ita taga zahirinshi ma, tsaki tayi ta sunkuya zata aje wayar sai kuma tayi cak kamar an tsikareta, tsaye tayi tana kallon wuri d'aya tana tunani, wani murmushi tayi jin wani tunani daya zo mata, sai kawai tasa wayar a jakarta ta juya dan barin gidan.
Ko da Ammie ta fad'awa Sameera d'aurin auren Raihan da wani tayi fad'a har bakinta ya fara kumfa, tana ganin kawai yana neman maraba da ita ne shiyasa ya had'ata da wanda bai san halayenshi ba, kuma wai yace gobe Alhaji Khamis zai tafi da ita Maradi, jibi kuma an gama mata visarta saita wuce Maroc, saida Abba tace tayi wa mutane shiru kad'ai taja baki tayi shiru tana gunguni.
Tafiya yayi kamar zai bar gari duk inda ya gani sai yaga kamar za'a kama shi, kuma har wannan lokacin yana tunanin anya kuwa abinda zakayi daidai ne? Da k'yar ya isa wata doguwar hanya da babu mutane sosai, nan kawai zuciyarshi ta yanke mishi ya ajeta bakin titi ko ta samu taimako a mata sutura daga wasu bayin Allah, haka kuwa yayi saida ya tabbatar babu kowa ya fito da ita ya aje tare da jakarta da d'an kwalinta kafin ya juya ya bar wurin zuciyarshi cunkushe jikinshi na rawa na rashin saboda da tsintar kai cikin gagarumin tashin hankali, daga nan gida ya nufa da tunani iri iri.
*Basraba*
Gidan sarauta gaba d'aya ya hargitse da hidima na walima da aka shirya, sosai aka ci aka sha kafin yamma tayi aka fara shirin tarban amare kamar yanda uwar d'aki ta buk'ata, yamma tayi rana tayi sanyi gidan ya k'ara yamutsewa ta ko ina saboda bak'i da suka fara shigowa da amaren, nan hadimai da bayi suka fara kai da kawowa suna nuna musu masaukinsu, haka aka dinga shiga da amaren suna gaishe da uwar d'aki da kuma sauran matan da kuma uwar gidansu gimbiya Ameera kafin aka wuce dasu nasu masaukin.
*A gurguje*
Da dare bayan jakadu sun shirya Jawahir wacce ita ta fara isowa gidan kafin Safiyya, hakan kuma na nufin ita ce gaba da Safiyya yau ita ke da sarki, sarki ma da kanshi ya tarasu su ukun ya nuna musu mahimmanci da darajar uwar gidanshi, sannan ya nuna musu yana son zaman lafiya da kuma had'a kansu, yana gamawa ya sallami kowace ya koma bed d'in shi.
Uwar d'aki da kanta ta turo jakadiyarta ta taimakawa sauran bayin aka shirya Jawahir cikin shiga ta alfarma kafin ta kamota har falon sarki tayi wa sarki magana sannan ta koma, izinin shiga ya mata bed d'in, cikin nutsuwa da jin kunya ta shiga kanta k'asa, kan gado ya nuna mata ta zauna shima ya zauna kusanta yana kallonta, ba laifi kam kyakyawa ce ga kuma kunya, saidai akwai k'ananan shekaru gareta da gani, ganin ta k'i d'agowa ta kalleshi yasa ya kalli hannayenta da suka sha lalle, sake kallonta yayi yace "Jawahir."
Har zata d'ago kanta kuma saita tuna yana daf da ita dan haka ta k'i d'agowa ta amsa da "Na'a."
Murmushi yayi dan ta birgeshi data kasa kallonshi hakan yasa ya mik'e ya kama hannunta yace "Muje muyi alwala muyi sallah."
Mik'ewa tayi tabi bayanshi har toilet, saida ta d'aga ido ta kalli toilet d'in ganin ban d'aki kamar d'akin kwanan wani, tare sukayi alwala suka fito sukayi sallah, bayan sun kammala ne ya mata tambayoyi kan addininta musamman yanda zatayi wankan tsarki da kuma yanda take sallahrta, abun mamaki shine amsa wasu tambayoyin da tayi ba daidai ba, bai wani nuna mata k'yama ko wani abu ba sai kawai ya bar abun a ranshi da d'aura niyyar d'ora mata a hankali harta fahimta, a nutse ya kalleta yace "Kina buk'atar wani abu ne da zaki ci?"
Kai ta girgiza alamar a'a, mik'ewa yayi tana kallo yayi shirin baccinshi tana zaune, ba zato ba tsammani taji ya kamo hannunta ya zaunar akan gadon ya koma ya kashe hasken d'akin sannan ya dawo, kwantar da ita yayi kamar wata beby ya kwanta gefenta, a hankali cikin nutsuwa da dabara ya samu ya lallab'a ta har ta zama cikakkiyar mace a wannan daren.
Kamar yanda mahaifanta suka rad'a mata tun kafin auren hakane ta kasance, a lokacin daya shiga ban d'aki dan tsarkake jikinshi cike da k'arfin halin duk da bata iya wa haka ta mik'e ta ta saka kayanta tayi sauri ta yaye wannan zanin gadon ta tura k'ark'ashin gado sannan ta zauna bakin gadon, yana fitowa ya kalleta da mamaki ya k'araso yana fad'in "Jawahir, ya zaki takura kanki haka? Kije kiyi wanka kinji."
Cike da dagiya ta murmusa kanta k'asa tace "Ba komai, dama zan canza zanin ne kuma bansan a ina zan samu ba, shiyasa..."
Maganar ta tace ta sark'e haka kawai dan haka ya kamata ya nufi toilet da ita yana fad'in "Ki barshi kawai, ni zan canza wani da kaina, yanzu ki samu ki kula da kanki kinji ko."
Yana fitowa ya fara k'ok'arin canza zanin, yana da niyyar idan ta fito ya tambayeta ina waccen zanin? Dan kar azo ta fita da shi sai kowa ya ga meya faru tunda akwai k'uruciya a tare da ita, amma jimawar da tayi tana kula da kanta da kuma kunyar fitowa yasa har bacci ya fara ridarshi saboda akwai gajiya a tare dashi, tana fitowa kuma jawota kawai yayi suka kwanta yana rumgume da ita a k'irjin shi kamar yar tsana.
*Abuja*
Cikin tsanani rud'u ya shigo gidan ya kuma zarce bed d'in shi, kile k'ofar yayi inda ya cire kayanshi ya shiga wanka, haka ya zauna ruwa na sauka a kanshi yana kuka kamar yaro k'arami, sam wunin ranar bai ma san ya akayi shi ba bare kuma yasan yanda ya gudanar da nashi, sanda Sameera ta ankara da motarshi taje d'akin dan suyi magana amma bai bud'e mata ba, haushi ne yasa ta baro k'ofar da niyyar ba zata sake komawa ba sai in ya fito dan kanshi, sam kamar ba gidan da aka d'aura aure ba, a haka har dare yayi yan mutanen da kenan ma suka watse, da dare kusan kowa ya kwanta amma banda Sameera dake tare da Raihan ana ta gyaran jiki, haka ma Abbas da abun duniya ya isheshi yake tunanin halin daya samu kanshi cikin d'an lokaci, sai kuma Harira data samu lambar Abbas d'in wurin Abdul raheem tana kwance kan k'aramin gadonta zata kira shi.
Yana kwance yana kallon sama kiran Harira ya doki kunnuwanshi, har ga Allah saida gabanshi ya fad'i kuma ya zabura ya tashi zaune, dan yanzu fa ya zama marar gaskiya ne kowane kira d'aukar shi yake wata matsalar ce, k'ara shiga damuwa yayi ganin bak'uwar lamba, amma wannan karan sai yayi saurin d'auka saboda maganin matsalar bai tsaya b'ata lokaci ba, shine ya fara cewa "Wake magana?"
Harira na jin muryarshi saida gabanta ita ma ya fad'i kafin ta daure tace "Harira ce."
Da d'an k'arfi yace "What! Harira kuma? Wacece hakanan kuma?"
Murmushi tayi tace "Harira dai yar k'auye mai aiki gidanka, na kira ne muyi magana idan kana da lokaci?"
"Bana da to." Ya fad'a a harzuk'e, dariya tayi dan tasan maganar yayi ne cikin jin haushi sannan tace "Dama wayar siyarwa ce gareni mai matuk'ar tsada wacce nake ganin da kai kad'ai zata dace, amma tunda kace baka da lokaci shikenan, saida safe, amma karka manta da abinda masu iya magana ke fad'a, *ko a k'ark'ashin k'asa ka shiga ka aikata abu to ka sani akwai ranar da zai fito*, bare kuma kai da a bayyane kayi komai naka ma, ka sani yanzu bana ganinka da wani sauran mutumci, tun ranar da nayi mugun gani, yallab'ai Abbas da karuwa a cikin gidanshi ba kunya ba tsoron Allah, tirr."
D'orawa tayi da "Ban tab'a tunanin zaka iya aikata zina ba, amma sai gashi naga ka aikata har kisan kai ma, hakan fa na nuna rashin imaninka yayi yawa."
Abbas da rigarshi tayi sharkaf da gumi yaji kanshi ya fara juyawa jikinshi ya fara kyarma ba tsayawa komai yace "Ke kuma nawa kike so?"
Wata dariyar jin dad'i tayi tace "Da idona naga duka ta'asar da kayi, a yanzu haka kuma ina rik'e da wayar yarinyar daka kashe mai d'auke da vidΓ©on caskalenku, ni ba kud'i nake so sab'anin hankalinka ne, idan har kayi abinda nake so ni kuma zan rufa maka asiri har abada."
"Ki fad'a min kawai me kike so da gaggawa? Sannan ki min alk'awarin zaki bani wayar nan idan har nayi abinda kike so."
Saida ta gyara kwanciyarta kafin tace "Ina so ka aure ni, da ka amince ni kuma zan baka wayar tare da duka idanu na da sukaga abinda kayi."
Sauka yayi daga kan gadon yace " In aureki? Ke a wa? Ke tsaya kiji, halin da nake ciki fa bai haukatar da ni ba ta yanda zan iya had'a kaina dake ba bare kuma har na had'a ki da matata, dan haka ki canza wata buk'atar amma ba wannan ba."
Zaune tayi tace "Kana nufin ba zakayi na kenan?"
Kai tsaye yace "Eh, haka nake nufi."
Cike da gadara tace "Ai kuwa zuwa safiyar gobe mummunan sak'on nan zai sauka idon matarta ka."
Yasan barazana ce dan haka yace "And so what? Ki nuna mata mana, kin d'auka mahaukaciya irinki? Wallahi kina nuna mata ba zaki bar gabanta ba har sai kin rasa k'afa ko hannu ko kuma ki rasa fatar jikinki."
Jim tayi dan kuwa tasan gaskiya ya fad'a, to ai ita zata fad'awa wani wacece Sameera ba wai wani ya fad'a mata ba, dan haka tayi murmushi tace "Shikenan tunda haka kace, ni kuma zan nuna maka bana maganar banza."
Cikin jin haushi yace "Shikenan mu zuba mu gani."
Yana fad'a ya kashe wayar, dafe k'ugu yayi ya shiga zarya yana tunanin ta ina ita kuma ta shigo labarin? Ya akayi ta sani ko? Rasa amsa da jin haushi yasa shi buga wayar a bango take ta tarwatse, ganin haka yasa shi fad'awa kan gadon yana dafe da kanshi da hannaye biyu kamar ya kwamtsa ihu da iya k'arfin shi, tabbas yayi bacci amma baisan wane irin bacci bane, domin kuwa abubuwa ne fal a kanshi wanda yasa yake ji kamar ma a zahiri ne idonshi biyu.
*Washe gari*
Ko da Sameera suka tashi ta d'ora gyaran da suka tsaya jiya, da taimakon su Bilkisu aka had'awa Raihan kayan jikinta musamman kayan bacci wanda ake siyo mata duk jiya, wani abun kam saidai suyi godiyar Allah, ba dan akwai dalar ba antara ta cirewa kawai ake a account da sun d'ora hannu a kai, kasancewar Alhaji Khamis babban mutum ne yace amaryar kawai suke buk'ata, hakan yasa Sameera dan kar a raina mata 'ya ta kashe mata kud'i kamar ba gobe ta fannin sutura wacce zata saka a gani dai, sark'ok'i ma na milyoyin kud'i aka siya mata ga kuma bala'in gyaran da suka saka aka aiko musu daga mai duguri da kuma sokoto, haka ma daga Niger saida aka kawo musu sak'o duk na gyaran jiki a safiyar yau da yake harka da kud'i, misalin *09:00* motoci uku ne suka paka cikin gidan Alhaji Khamis ya turosu su d'auki amarya da masu rakiyarta, sai lokacin kad'ai Abbas ya fito daga d'aki cikin doguwar riga kana ganinshi kaga damuwa, su Ammie da Abba ne da kuma Sameera suka mata nasiha sosai, daga bisani kuma k'annan ta kuka Uka dinga yi na rabuwa da yar uwa wacce aurenta ba zasu shaida komai ba, Raudat taso taje amma haka Abbas ya murje ido yace ai mutum biyu kad'ai zasu