Showing 267001 words to 270000 words out of 325849 words

Chapter 90 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

507

Middle Ads

son haka wallahi ko kad'an, wai kai kake da aljanna ne da zaka saka ni a ciki? Ko so kake Allah ya k'ona ni."

Bai saketa ba bai kuma tashi ba saida Ummy ta shigo dubata saboda Hamna data fita tana kuka kuma ta k'i magana, da sauri ta fita ta d'auko allura ta zo ta mata, ba jimawa bacci ya d'auketa kad'ai ya sake ta.

*Kullum* haka Amna take tunda ta haihu, mai saurin kuka da tausayi baya iya tsayawa kusanta saboda maganganunta masu karyar da zuciya ne, indai idonta biyu ba bacci take ba to maganganu ne zatayi ta sakowa, duk wanda zai zo ganinta saita mishi nasiha, ka kula da yaranka kn kana da su, ka kula da mijinka in kana da shi, ka dage wajen karatunka in mai karatu ne, hakan ne yasa duk wanda yaje ganinta sai dai ya dawo yana zubar da hawaye, a cikin k'ank'anin lokaci kowa maganarta yake. Yaro kam ko da ta haife shi dama aka d'orashi kan madara, da fari anyi hakane saboda ganin jikinta, amma yanzu abinda ya tabbatar ma kowa tana jin jiki shine, duk yanda yaron zaiyi kuka a kawo mata shi ta bashi nono saita k'i, haka zata dage ita ba zata bashi nono ba, sai manya suka fara tunanin ko iska ne dan babu abinda basa yi, addu'a aka dage da mata amma babu abinda ke sauyawa, wani lokacin tana bacci haka zaka ga hawaye na bin fuskarta, data farka sai dai ta tashi da kuka, to fa zata iya yin awa goma ba tace um bare um um ba, haka suka kwashi kwana *bakwai* a asibiti, sallamarta akayi suka koma gida dan sun ce ciwonta bana asibiti bane.

*Ranar da* suka dawo gida...


*Alhamdulillah*
14/10/2020 ร  00:58 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

๐Ÿ’ซโœจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐ŸŒŸ
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_๐Ÿค

โ˜† *[ T.M.N.A]* โ˜† ๐Ÿ“–๐Ÿ–Š๏ธ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_62_


*A ranar da* suka dawo gida kuma wani ikon Allah sai abun yayi sauk'i, ta ci abinci sosai tayi wanka ta gyara kanta sosai, kowa yayi farin ciki da faruwar hakan, musamman Hamna tafi kowa farin ciki, har yamma dai babu wata matsalar komai, yaro dai ne tana saka shi a nono zata cire shi ta aje, an idar da sallah magriba Ummy ta kalli Hamna tace "Hamna ki taimaka ki siyo mana kayan sanyin da za'a saka mishi mana, dan da alama garin akwai hadari."

Amsawa tayi da "To Ummy."

Mik'ewa Ummy tayi tana fad'in "Bari na d'auko miki kud'in."

Da sauri tace "A'a Ummy ki barshi ma akwai a hannu na."

Da sauri Amna dake zaune k'afafu mik'e ta d'aga rigarta inda aka mata aiki tace "Kin gani ko Ummy, zata kula dasu ko bayan ba raina."

Hararanta Hamna tayi tace "Uwarki zan ci kika sake mana maganar mutuwa."

Da sauri tasa hannu ta rufe baki tace "Nayi shiru to, yi hak'uri tafi Hajia."

Murmushi Hamna tayi ta tashi ta fita, a farfajiyar ta had'u da Shureim da gudu ya tareta, dafa shi tayi tace "Daga ina kake?"

Cikin muryarshi ta yara yace "K'ofar gida ni da yaya Ammar da Appa."

Kallonshi kawai tayi da ido, wanda ya kamata ya kira Appa shi ya kira da yaya, wanda ke mazaunin kakanshi kuma ya kira da Appa, wannan wace irin *BADAK'ALA* ce? Cikin tunani bata san ta fara tafiya ba saida taji ya rik'e hannunta yana fad'in "Aunty ina zaki je? Ina zuwa."

Kallonshi tayi tace "To muje mu siyowa sabon bebynmu kaya ko."

Da gudu ya rigata k'arasawa wajen motar, bud'ewa tayi ta shigar dashi sannan ta shiga, mai gadi na bud'e mata k'ofar anan ta ganshi tsaye tare da Abba da Labaran, sauke gilashin tayi tare "Abba barkanku."

"Ina zaki je?" Ita ce tambayar daya jefo mata, cikin ladabi tace "Ummy ce ta aike ni na siyowa bรฉbรฉ kayan sanyi, amma yanzu mun dawo dan tace akwai hadari a gari."

Cikin sakin fuska yace "Shikenan sai kin dawo."

Kallon Shureim yayi yace "Hein ba magana?"

Ammar kawai ya kalla yace "Yaya na tafi."

Murmushi ya masa yace "Saika dawo, ka kula da kanka."

Wucewa tayi suka d'auki hanya, sun bar nan kenan Amie ta zo yin barka, gaishesu tayi suka amsa ta tambayi Ammar ya mai jiki da bรฉbรฉ, cikin amon muryar da yake nuna babu wasa ya amsa mata, ciki ta shiga kai tsaye b'angare Amna ta nufa, nan ta samu Ummy suka gaisa, saida suka gama gaisawa fa Amna sannan tace "Ummy ina Hamna take?"

Cikin sakin fuska tace "Hamna ko bata jima da fita ba, amma yanzu zata dawo nasan ba zata kai ko kasuwa ba."

Hira suka fara tab'awa da Amna sai Ummy data bar musu falon, ba jimawa da fitar Ummy kuma Hamna ta dawo, Zeituna ta ci karo da ita saita fad'a mata yanzu Ummy ta shiga ciki, dan haka saita shiga kawai inda Shureim ke mata rigimar ta koma yawo dashi, kai tsaye d'akinta suka shiga ta same ta tana duba wasu kaya, kallonta tayi tace "Har kun dawo wai?"

"Wallahi Ummy, kinga kayan." Ta fad'a tana mik'a mata ledar, bud'ewa tayi tana dubawa sai Shureim dake kamo hannunta da k'arfi yana fad'in "Ki bani ni, ki bani."

Umly ce ta kalleshi tace "Wai me za'a baka?"

Dan kar Ummy ta dakeshi yasa Hamna sakar masa makullin, yana jin ta sake masa saiya fita a guje ta bishi da kallo, tana juyowa suka had'a da Ummy dake murmushi, cikin taushin murya tace "Ki k'ara hak'uri Hamna, insha Allahu komai ya kusa zuwa k'arshe, tunda a
mahaifin yaron nan ya canza al'amuran gidan nake son fad'a ma Hajia, matsalar d'aya ita ce ta yanda zan fara fad'a, amma nasan ko da na fad'a rai ba zai b'ace ba kamar zamanin baya."

Cike da damuwa Hamna ta kalleta tace "Ummy ni kaina tsoro nake ji, wallahi kullum tunanin al'amarin gigita k'walwata yake, duk da yanzu dai abubuwa sun canza, amma muyi kallon abun ta b'angaren yer uwata da kuma Abba, Ummy ya zasu ji idan suka ji maganar nan, ya yer uwata zata kalleni taji wai Shureim d'ana ne, d'an nawa ma wanda na haifa tare da mijinta, duk da dai kafin aurensu ne amma abun akwai gigitarwa, sannan Abba da yake mishi kallon d'an shi shima ya zaiji Ummy?"

Jinjina kai Ummy tayi tace "Wallahi Hamna karki so ki tona raina kiji yanda a kowace rana nake bacci da fargaban nan, ni kaina nasan wannan abune mai matuk'ar d'aure ne, abune da ko da ya tab'a faruwa to ba dai a k'asar hausa ko kuma anan kusa ba, k'anwata Gaishata da bana b'oye ma komai, amma sai gashi wannan karan har alk'awarin fad'a mata da nayi bai cika ba, Hamna tun tana tambayata na fad'a mata har ta kai ta gaji ta daina, ni kaina bansan ta inda zan fara kawo k'arshen labarin nan da nine na fara shi ba tun farko."

Cikin jimami tace "Kawai Ummy mu jira Amna ta samu lafiya a gama sabgar nan, kukan kura kawai zamuyi mu fad'a, in ya so ayita ta k'are kawai ko mun huta mu ma."

Jinjina kai tayi tace "Allah ya shige mana gaba."

Jin motsin zasu fito yasa *Amie* barin wurin da sauri wacce data mik'e zata tafi Zeituna ta fad'a mata ai Hamnar ta dawo tana wajen Ummy, tana zuwa yayi daidai da jin wannan babban sirri da ake ta b'oyo, da sauri ta koma b'angaren Amna ta zauna sai ga Hamna sun shigo, kallonsu take tana ta sak'a da warwara, sai dai ta girgiza kai kawai tayi murmushi, sai taji ma ta kasa tashi ta bar gidan, Amna da Hamna take kallo tana hasaso Ammar a idonta, lallai duk cikin lamarin Amna aka rainwa hankali, to miye abun b'oye mata ana zalintarta, kai ba zai yiwu ba wallahi, *gwara komai ya fito uban kowa yaji duk a k'one tare*, haka ta ci gaba da zama har k'arfe *09:00* dare yayi.

Mutanen d'akin sun rage daga Amna da Hamna sai Amie, sai kuma Husseina wacce suke kwana tare amma tana nesa dasu sai gyangyad'i take, Hamna ce ta tashi ita ma tace "Besty bari na fad'awa Ummy saina aje ki gida."

"Ok besty." Ta fad'a tana binta da kallon yar rainin hankali, saida ta ga fitarta ta gyara zama ta kalli Amna da kyau tace "Amna ke fa yanzu nan baki san komai ba ko?"

Kallonta tayi tace "Komai kamar me fa?"

Girgiza kai tayi tace "Allah sarki, gaskiya Amna ana cutarki a gidan nan, mijinki, yar uwarki da kuka fito ciki d'aya, da kuma Ummy, sun taru suna raina miki hankali."

Duk mutanen da Amie ta ambata mutane ne da suka zama dunk'ulen rayuwarta, mutane ne masu matuk'ar mahimmanci a tattare da ita, dukansu zata iya sadaukar da rayuwarta akan su, dan haka a take taji wani haushinta da tsanarta sun dira a zuciyarta, sama da k'asa ta kalleta tace "Ni dai a sanin dana miki ban sanki da gulma da yarfe ba, bansan kuma yaushe kika koyesu ba?"

Murya k'asa k'asa tace "Amna wallahi maganar gaskiya nale fad'a miki, idan ma baki yarda ba to ki tambayesu kiji."

A kausashe tace "Na tambaye su me Amie? Wai dama gulma kika zo ba dubiya ba? To tashi ki fita."

Tab'e baki tayi ta mik'e tsaye ta kalleta tace "Dama ko a yan biyu akwai baud'add'e, ke kam ba zaki tab'a gane irin cutar da ake miki ba, amma idan mijin naki ya shigo ki tambayeshi waya
haifi Shureim? *Shi ko mahaifinshi*, inhar gaskiya zai fad'a zai ce miki shine, in kuma k'arya zai fad'a zai fad'a miki mahaifinshi ne."

Juyawa tayi tana fad'in "Sai anjima."

Zata fita Hamna ta shigo, juyawa tayi ita ma tace "Yawwa to yi sauri muje Hajia tace kar na jima."

Cikin wata irin murya Amna tace "Dakata."

Tsayawa sukayi suka juya suna kallonta, ba tare data tashi daga inda take ba ta kalli Hamna ido cikin ido babu yanayin wasa tace "Ki koma ciki babu inda zaki kaita."

Da mamaki Hamna tace "Me yasa?"

"Saboda munafuka ce." Ta fad'a kai tsaye, murmushi Hamna tayi a tunaninta jikin ne ya motsa tace "Kiyi hak'uri kinji yer uwa, ba jimawa zanyi ba yanzu zan dawo."

Da k'arfi tace "Hamna babu inda zaki kaita, in kuma baki yarda ba to kuje ga hanyar nan."

Kallon Amie Hamna tayi ta k'yabta mata ido alamar su mata wayo sai a zahiri da tace "Besty kawai ki tafi tunda yer uwata bata so ba zanje ba."

Jinjina kai Amie tayi ta fita, Hamna na ganin haka ta kalli Amna tace "Akwai abinda kike so na miki ne ko ka naje na kwanta? Bacci nale ji sosai."

Kallonta tayi tace "Kije ki kwanta saida safe."

Juyawa tayi ta fita tana zuwa ta ja mota ta fita ta d'auki Amie, hak'uri ta bata kan abinda ya faru tace ba komai. Tana fita Amna ta bita da kallo, murmushi tayi tace "Ko yaushe Amie ta haukace kuma? Su yanzu nan mutane kallon mai hankali suke mata? Lallai ma Allah ya bata lafiya."

Daga nan zaune ta saki wannan maganar kamar anyi rubutu a saman ruwa, jikinta ya bata Hamna ta tafi ta kai Amie gida ne, k'wafa tayi tace "Haba, kuje d'in mu gani."

Saida sukayi nisa da gida kuma basu kai ko rabin gidansu Amie ba mota ta tsaya cak, ko da Hamna ta duba wajen dake bayyana idan mai ne babu taga tanki cike yake, nan ta shiga tayar wa amma mota shiru, tsayawa tayi tana girgiza kai tana murmushi a hankali take fad'in "Amna, Amna, amma zan ci uwarki, ni zaki wa iskanci."

K'wafa tayi ta kalli Amie tace "K'awata, hak'uri zakiyi ki samu adaidaita ki hau, in dai ina tare dake to babu inda zan gusa."

Da mamaki ta kalleta tace "Me yasa? Wani abun ne ya faru?"

Murmushi ta mata tace "Ba zaki gane ba, kawai ki samu adaidaita."

Bud'e motar tayi ta fita ta kalleta tace "To ke ya zakiyi?"

Saida ta kalli titi tace "Karki damu, idan ma bata tashi ba zan kira a zo a d'auke ni."

"Ok, ki kula da kanki."

Jinjina kai tayi tace "Ok, saida safe."

Nan ta samu adaidaita ta tafi, tun a hanya data shiga WhatsApp d'inta ta kasa hak'uri ta tab'o sauran k'awayenta su biyu, gulma ajali inji yan magana, haka suka jima suna tattaunawa suna fad'in ashe ta ma fisu iskanci, shine in taga suna rayuwarsu saita dinga nuna tana k'yamar abun, ashe ita har shege ma gare ta kuma da mijin yar uwarta.

Saida ta ga tafiyar Amie ta kira Amna a waya, har ta kusa tsinkewa sannan ta d'auka tace "Lafiya? Har kin kaita d'in?"

Dariya Hamna tayi dan su rabu lafiya kar ta jawa motarta kwana akan titi, cikin muryar rarrashi tace "Dan Allah yar k'anwata taimaka min ina so na koma gida kinji, dare kayi kar Abba ya min fad'a."

Cikin kumburo baki Amna tace "Na k'i d'in, bani kika rainawa hankali ba?"

Sake mak'ale murya tayi tace "Dan Allah fa nace."

"To shinenan, ki bani hak'uri yanzu." Cewar Amna.

Saida ta gyara murya tace "To aunty Amna kiyi hak'uri."

Murmushi Amna tayi tace "Shikenan to kiyi sauri ki dawo gida kar wani ya sace min ke."

Dariya tayi tana wa motar key tace "An gama zuciyata."

Ko da ta kunna ta kama tana murmushi tayi baya baya ta d'auki hanyar komawa gida.

*Da safe* Hamna na ta kai da kawon gyara falon an gama ma bรฉbรฉ wanka, duk inda tayi sai Amna tabi ta da kallo, tun bata lura ba har ta ankare, tun abun bai tsaya mata akai ba har ta fara tsarguwa da kallon, tsayawa tayi tana kallonta tace"Wai ke lafiya?"

Sai kawai ta bushe da dariya kamar mahaukaciya, kallon mamaki Hamna ta bita dashi ta girgiza kai ta ci gaba da aikinta, Ummy na shigowa cikin shirin tafiya aiki da Shureim a hannunta, hannu ta tarawa Shureim tace "Zo nan."

Takawa yayi ya je wurinta ya tsaya, rik'e hannunshi tayi tana mishi wani kallo kamar yau ta fara ganinshi, sai kawai ta matso dashi kusanta ta sumbaci goshinshi, saida ta d'auke bakinta ta sake kallon fuskarshi sai tace "Kai ni fa sai naji na fi sonka da aka ce yar uwata ma ta haifeka."

Wani yamutsawar hanji Ummy da Hamna suka ji a lokaci d'aya, Husseina dake karin kumallo kallonta tayi irin kallon anya kuwa Amna, da sauri suka kalli juna suna zazzaro ido na alamar tambayar me ke faruwa, kallonsu Amna tayi a tare saida ta gama kallonsu sai tayi dariya ta nuna Hamna da hannu tace "Sakarya, ji yanda kika zaro ido kamar mahaukaciya, ko ke ma kin haukace irin na k'awarki?"

Da sauri suka saisaita nutsuwarsu, sai Ummy data kalli Husseina tace "Anya Hajia kuwa lafiyarta k'alau?"

Cikin murya k'asa k'asa tace "Ni ma dai abinda nake tunani kenan."

Amna kam kallon Shureim ta sake yi tace "Baka tafi islamiyya ba kai?"

A hankali yace "Yanzu Ummy zata kaini."

Murmushi ta masa tace "Yawwa, kana ji ko? Ka dinga karatu sosai saboda ka zama babban malami, kana so ka zama kamar wannan kai ma?"

Ta fad'a tana d'aukar wayarta, wa'azin *ustaz Rayyadun* (Allah k'ara girma malaminmu) ta nuna masa na vidรฉo tace "Ka gani ko? Ka zama kamar wannan kaima, kana so?"

Kai kawai ya d'aga mata irin shi dai yana saurarenta, su dai kallonta suke har Ummy ta mik'e ta kama shi suka fita, hankalin Hamna ya kasa kwanciya duk a takure take jin kanta, ta k'i yarda su had'a ido da Amna wacce ita kuma take ta binta da kallo har yanzu, idan ta ga Hamna ta k'i kallonta sai ta bushe da dariya, duk wanda ya zo gidan haka zai iskota a wannan yanayin, gashi kuma Hamna babu damar da zata barta dan wani abun sai tace dole Hamna ce kawai zata mata, haka suka dinga wannan zama babu dad'i babu hira tsakaninsu, sai dai ita Amnar tayi ta nata maganganun masu kama dana mai shirin barin duniya.

*Kwana uku* yau da faruwar wannan lamari, shirin biki ake ta yi sai dai ba wani da karsashi ake yinshi saboda yanayin jikin mai jego, kullum cikin taka tsantsan ake kan d'inkinta, ana yawan kwakwafarta kan rage magana da dariya mai k'arfi, amma abun sai a hankali in tayi wani abun kamar dai k'walwarta ce ta fara samun matsala. Yanzu ma Ammar ne ya shigo da babbar leda a hannu, ko da ya gaishe da mutanen d'akin ya nufi nashi d'akin, kamar daga sama aka tsinci muryar Amna tace "Ammar."

Cak ya dakata ya juyo ya kalleta, *Ammar*? Tunda yake da ita daga k'uruciya har girmanta bai tab'a ji ta kama sunansa ba haka, dama dai waccen marar kunyar ce, su kansu mutane mamaki ne ya kama su jin yanda ta kira sunan nashi kamar sunan Ammar k'arami, shi kanshi Ammar k'arami saida ya juyo ya kalleta, har ya cire hannunshi daga abincin da yake ci zai taho tace "Ba kai ba zauna."

K'ok'arin mik'ewa ta shiga yi hakan yasa Ummy taimaka mata ta tashi, saida taje kusanshi ta kalle shi tace "Muje ciki."

Kallon Ummy yayi daga nesa, ita ma shi take kallo kallon nima bansan komai ba, wucewa yayi d'akin ta bishi a baya, sua shiga ta zauna kan gadonshi tana kallonshi tace "Kana ji ko? dan Allah ka kula min da yarana, ka dinga kaisu makaranta kan lokaci, kaji ko?"

Shi mamakin yanda take masa magana kamar wacce ta haife shi ne ma yake, ganin bai ce komai ba yasa ta amso ledar hannunshi tana fad'in "Kawo to, watak'ila kallon nan da kake min dan ban karb'a bane."

Aje ledar tayi kan gado ta mik'e zata fita sai kuma ta juyo ta kalleshi tace "Kasan wannan k'awar ta mu Amie?"

Kai kawai ya jinjina mata yana ci gaba da kafeta da ido, dariya tayi sosai tace "Baka san ta hauka ce ba? Kasan haukan data zo min dashi gidan nan?"

Kai ya girgiza mata kawai dan jin

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login