Showing 279001 words to 282000 words out of 325849 words
ta kakinshi, ko da ta ga zai b'alla botira tayi saurin matsawa zata taimaka masa, baya yaja tare da k'ara had'e fuska a cikin mak'oshi yace "Um um."
Kallonshi tayi tare da sauke hannayenta k'asa tace "Magana na zo muyi idan kana da lokaci?"
Shiru ya mata ya ci gaba da shirinshi kamar baisan da zamanta a d'akin ba, zaune yayi kan kujera yana d'aura d'amarar takalminshi, hakan ne ya bata damar matsowa tace "Magana nake."
K'asan mak'oshi sosai yace "Aiki ya min yawa yanzu bana da lokaci kaina ma, ki gaggauta fad'in abinda ya kawo ki."
Saida ta gyara tsayuwarta sosai sannan tace "Tunda abun nan ya faru ka canza min, na baka hak'uri har na gaji, Hajia da su Hajiar Jibril ma duk sun tayani baka hak'uri, amma abinda na fahita shine baka hak'ura ba har yanzu, a gaskiya na fara gajiya da irin halin ko in kular da kake nuna min, shine nake so ka fad'a min a me kake kallo na ne? Sannan me ye matsayi na a wurinka yanzun?"
Cike da nuna rashin damuwa kan maganar ya d'auki hularshi ya saita zamanta yana fad'in "Duk irin zaman da kike tunanin kina yi shi kike yi."
Jakarshi ya d'auka zai fita tayi saurin tare da gabanshi tace "Wannan wace irin magana ce? Abban Ammar ka tsaya muyi magana."
Kallon fuskarta yayi cikin yanayin firgitarwa yace "Na gama magana ni ba zan b'ata lokaci na anan ba."
Zai fita ta rik'e hannunshi tace "Nima ina so na kawo k'arshen abun ne, dama zamanka na ke a gidan nan, idan ka juya min baya banga anfanin zaman nawa ba."
Shiru tayi ta ja numfashi sosai sannan ta ci gaba da cewa "Ina so ka min magana d'aya kuma tsayayya, idan ka gaji da zama dani ne to na san inda dare ya min? Tunda kafi kowa sanin inda ka d'auko ni ai."
Ba tare daya kalleta ba yayi murmushi mai ciwo yace "Ni kuwa nasan inda na d'auko ki, da kai tsaye kika fito kika fad'a min abinda kike so, amma..."
K'ofa ya nuna mata yace "Hanya a bud'e take ban rik'e miki k'afa ba, zaki iya tafiya ko yanzu ma."
Zai wuce ta sake rik'oshi da k'arfin da Allah ya hore mata tace "Ba zan tafi ba tare da shaidar komai ba, tunda haka ka ce to ka ban takardar da zan nuna ta zama hujjar tafiyata kenan, dan in na tafi ma bana son dawowa."
Kallonta yayi yace "Kije zan aika miki da ita, yanzu bana da lokacin tsayawa rubutu."
π *Maza mutanen mu, mu ke shayar daku amma in kuka labta mana wata tsiyar...hummm*
Da sauri tace "Zan tafi yanzu, amma ka sani ina jiran takardata gobe goben nan."
Wucewa yayi yana fad'in "Anfanin me ma zata miki yanzu ko an baki? Ina ce zaki koma gidan nan da ki ci gaba da kulawa da yan uwanki."
Da kallo ta bishi tace "Ita ce lasisin fara zawarci na."
Duk da bai tsaya ba saida ya juyo ya kalleta ya kuma ci gaba da tafiya, zawarci? Matarshi ta shekara arba'in ba kad'an? Tayi zawarci har ta auri wani? Maganar fa ta soke shi sosai, ba dan baya son kulata ba da saiya buge bakinta, tunda dai har yanzu yana son abarsa kawai kuskurenta ne zai nuna mata, dan har ranshi yayi rantsuwa daya san abinda ya faru a lokacin *wallahi da sai Ammar yaje gidan maza* kan abinda ya aikata, yanzun ma wuri bai k'ure ba sai dai wacce zata zama tsayayyar shaidar ita ce Hamna, kuma yana tsoron shak'uwa ta yan uwantaka da jinin shi dake yawo a jinin jikin d'anta yasa ta basu kunya, shiyasa yayi fatali da maganar Ammar kawai.
Ai kuwa Ummy da gaske take, ko da ta shiga d'aki kayanta ta had'a a jaka ta fita a gidan ko Hajia bata san da fitarta ba.
Lieutenant kuma ya d'an jima d'akin Zeituna hakan ne yasa ko da ya fito ya samu d'an uwanshi ya zo da kuma Hadiza zaune suna gaisawa, Hadiza ce ta kalleshi cikin girmamawa tace "Ban ga Sa'ada ba ni ko har ta tafi aiki ne?"
Juya akalar zancen yayi da cewa "Ina mutumen ne (Ahmad)?"
Da murmushi tace "Ai ina zuwa uwarshi ta karb'eshi, tace ta tafi ta kaisu wajen Abbansu amma yanzu zata dawo."
Jinjna kai yayi sai Hajia data sake cewa "Babba ina Sa'ada? Yau kamar ba ranar aikinta ba ai?"
"Ta tafi." Yanda ya fad'a fuska a gimtse yasa Gambo kallonshi yace "Asibiti?"
Shirin daya musu ya tabbatarwa da Hajia ba lafiya ba, dan haka tace "Ina? Tana ina Babba?"
Cikin sanyin murya yace "Hajia ta tafi, nima ban sani ba."
"Kamar ya baka sani? Babba zauna."
Zaune yayi ya aje jakarshi gefe ya kalleta, cikin rashin son wasa tace "Fad'a min ina taje da safiyar nan? Ni dai banga sanda ta fita ba."
Ba tare daya had'a ido da ita ba yace "Hajia ta tafi, akan abinda ya faru ne, ita ce mai laifi ma amma har ta tsaya gabana tana fad'in idan na gaji da ita ta tafiyarta."
"Sai ka ce mata me?" Cewar Hajia, saida ya waina kanshi yace "Shine ta tafiyarta, tace na aika mata da takardarta."
Da k'arfi Hajia tace "Babba, kana da hankali kuwa? Yanzu kai baka ji kunyar fad'ar maganar nan ba? Matar ta ka?"
Gambo dake kallonshi da mamaki ne yace "Wai me ya faru ne haka da zafi? d'an uwa a sani na daku baku tab'a samun sab'anin da yasa tayi ko da yaji ba, me yayi zafi haka da girmanku da komai kuna fad'an yara."
Kallon Hajia yayi ranshi a b'ace yace "Hajia ni zan tafi."
Mik'ewa yayi zai fita Hajia tace "Ban gama magana da kai ba zaka mik'e min a kai Hassan, zauna min kaji malam."
Muryar da tayi magana da ita ta waccen Hajiar ce, dole ya dawo ya zauna yana sunkuyar da kai, Hadiza kam mik'ewa tayi ta kalli Hajia tace "Hajia zan jira a waje, akwai buk'atar ku tattauna."
Cikin mutumtawa Hajia tace "Zauna Hadiza, ai ke ma har yanzu iyalin gidan nan ce."
Murmushi tayi tace "Ban k'i ta taki ba Hajia, amma duk da haka akwai buk'atar kuyi magana tsakaninku."
"Hadiza karki manta fa yara biyu ne dake wanda kika samu a gidan nan, sannan abinda ke faruwa yanzun yana da alak'a da d'aya daga cikin ya'yan naki, ki zauna dan Allah sai muyi magana."
Komawa tayi ta zauna gabanta na fad'uwa kan abinda Hajiar tace, kallon lieutenant tayi tace "Kira min Sa'ada ka ce inji ni duk inda take yanzu ta zo ina nemanta."
Wallahi wannan Hajiarsu ce ta baya mai magana d'ayan nan, in yayi wasa zai sha ashar yanzu dan haka da sauri yace "To."
Wayar shi ya fiddo ya shiga neman lambarta, Gambo ta kalla tace "Ka kira min Ammar ka ce ya zo."
"To." Ya fad'a yana ciro wayarshi a aljijun balaluwarshi, yana gama magana dashi a lokacin har ya fita da yaran, sake umartarshi tayi daya kira Hamna sannan ta kalli Hadiza tace "Husseina na ciki, ki ce ta fito zamuyi magana."
"To Hajia." Ita ma ta fad'a ta nufi d'akin jikinta har rawa rawa yake na tunanin abinda ya faru tsakanin Ammar da Hamna daya har yasa Ummy suke k'ok'arin rabuwa da lieutenant.
Hamna ma ko da kiranshi ya shigo wayarta tana k'ofar gidan, saida hancin motar ta ya shigo sannan ta d'auki wayar, shi kuma yana hangenta ma saiya kashe kawai.
_Kuyi hak'uri da wannan, yau ne sai a slow._
*Alhamdulillah*
04/11/2020 Γ 14:38 - Ummulkhairi: π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨
*BADAK'ALA*
π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
π¨βπ©βπ§βπ¦ _*AHALI NA*_π¨βπ©βπ§βπ¦
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
_66_
Husseina ta fito ta samu wuri ta zauna, tunda sauran matan suka fahimci zaman ba dasu bane kowace tayi d'akinta, sai lieutenant dake kiran Ummy, k'in d'aukar kiranshi tayi tunaninta hak'uri zai bata, Hajia ya kalla yace "Hajia ta k'i d'auka fa."
Wayarta ta lalubo a bayanta tana fad'in "Ban ga laifinta ba mana."
Kallon Hajiar yayi da mamaki, wai duk abinda tayi bata ganin laifinta? Kiran Hajia kad'ai ta d'auka cikin ladabi tace "Hajia."
Kai tsaye tace "Kina ina Sa'ada? Maza ki zo gida ina son ganinki."
Cikin rarrabawa tace "Hajia..ina..kan hanyar...zuwa gida ne."
"Wane gida? Sa'ada kina da gidan daya wuce nan ne? Kina da hankali kuwa? Ke yanzu dan Allah idan kika je ki ce me? Yaji kikayi? Kiyi sauri ina jiranki yanzu."
Cikin ladabi tace "Wallahi Hajia da gaske na ke, ina cikin bus d'in da zata tafi *Arlit*, yanzu haka mun wuce *Tessaoua*."
Shiru Hajia tayi tana kallon lieutenant da shima yake kallonta yana sauraren abinda take fad'a, sunkuyar da kanshi yayi k'asa ita kuma ta harare shi, wata shawarar ta yanke kawai bari ta barta yaje har can ya dawo da ita, kashe wayar tayi cikin fad'a tace masa "Ka shirya tafiya yin bikonta gobe goben nan, babu ruwa na da iskanci kaji na fad'a maka, kai in ba'a hak'uri da ko haihuwarku nayi a gidan ubanku ma."
K'wafa tayi mai k'arfin gaske dake nuna ranta ya b'ace sosai, kafin wani yayi magana Hamna ta shigo tare da Ahmad, da mamakin ganin mahaifinta taje gabanshi ta zauna tana fad'in "Abba? Yaushe ka zo?"
Kallonta yayi yace "Banjour."
Lab'e baki tayi tace "Pardon Abba, bonjour."
Gaisawa sukayi sosai inda take kallon mahaifiyarta da mahaifinta tana jin kamar ace babu aure kan mamanta ta sake had'a aurensu, ba wai sai iyayenka sun mutu ba wani lokacin kake zama maraya, su kansu akwai abubuwa dayawa wanda sukayi musu manquΓ© musamman daga mahaifi, lallai Ummy ta kai su kirata uwa dan ta musu abinda ta cancanci hakan, amma duk da haka uwa uwa ce, ko hakk'in rayuwa a cikinta kad'ai ya ishi d'awainiya dasu.
Sallamarshi tasa ta gyara zamanta ta tank'washe k'afafu ta matsa daf da k'afafun mahaifinta, yaran duk wurin Gambo suka nufa ya sumbaci kowane kafin yace suje sama suyi wasa zai zo ya ba kowa tsarabarsa, saida suka haye sannan Hajia ta kalli kowa tace "Abinda yasa na tara mu anan dama akan maganar yaran nan ne."
Yanda ta k'arashe maganar da nuna Ammar da Hamna da hannu yasa su k'ura mata ido, dukansu kallo ne suke mata suna tunanin hannun da zasu iya begeta dashi daga lokacin data tona musu asiri, ba tare data damu da kallon da suke mata ba tace "A gani na tunda Hamna har yanzu bata da wani tsayayye me zai hana mu had'asu aure da Ammar?"
Kallon kallo aka shiga yi sai dai wasu na su kallon farin ciki da al'ajabain maganar ne, Ammar Hamna kuma a d'an birkice suka fahimci abun, Gambo ne yace "Masha Allah, gaskiya Hajia wannan tunani ne mai kyau."
Hadiza ma murmushi tayi tace "Gaskiya ne, Allah ya tabbatar mana da alkairi."
Lieutenant da fuskarsa ke had'e yana kallon Ammar ne yace "Amma Hajia ina ga da an ji ta bakinsu, tunda shi yayi rayuwar auren nan yasan komai dake cikinta, ita kuma bata tab'a ba dan haka da an tambaye su aji idan hakan ya musu."
Husseina ce tace "Hakane kuma, tunda babu yaro a cikinsu da za'a ma tilas."
Hajia ce ta kalli Hamna tace "Hamna kinji abinda aka ce, Me ye ra'ayinki? Ki fad'a mana abinda ke ranki dan ba za'a miki tilas ba."
Daram! Gabansu ya fad'i a tare, kallon juna sukayi kowa da abinda yake sak'awa a ranshi, Hamna a ganinta ba zata iya zama da tsohon mijin yer uwarta ba, taya ma zata iya auren yar uwarta saboda ta mutu? Mijin ma kuma Ammar wanda zata iya rantsewa da Allah ba zasu tab'a zama lafiya ba kamar yanda suka zauna da yer uwarta, gaskiya ba zata iya ba sai dai suyi hak'uri. Kallon da yake mata kallon son gane abinda ke ranta ne, bakinta yake kallo yana mai matuk'ar zak'uwa da son jin kalamanta, sanda kanta tayi k'asa tana wasa da yatsunta na hannu, Hadiza ce ta kalli fuskarta tace "Hamna kiyi magana mana, duka anan babu bak'onki."
Husseina ce tayi murmushi tace "Ai mace kunya ne da ita, shirun kuma shi ya bamu amsar tambayarmu."
Da sauri Hamna ta d'ago ta kalleta tace "A'a Hajia, gaskiya ni ina da saurayi, yanzu ma ni yake jira na bashi dama ya gabatar da kanshi."
Tana fad'a ta d'an kalle shi, da sauri ta d'auke idonta, ba zata iya yarda ta k'ara kallonshi ba, wannan kallon babu alamar arzik'i a ciki. Hajia da bata ji dad'in abinda ta fad'a bane tace "Amma Hamn..."
Ammar bai jira me zata ce ba yayi saurin cewa "Nima haka, ina da wacce nake so."
Ko da ya fad'a ya mik'e tsaye ya juya zai fita Gambo yace "Ammar dawo ka zauna."
Juyowa yayi cike da girmamawa yace "Dan Allah tonton, zan gabatar muku da ita nan da lokaci k'ank'ani."
Juyawa yayi ya fice ita ma a hankali ta mik'e zata shiga d'akinta, duk sai taji jikinta yayi sanyi da yace wai yana da wacce yake so, lallai ma mutumin nan! Kenan har ya manta da yer uwarta a wata shida kacal ya fara son wata? Tsaki tayi a zuciyarta tana fad'in "Allah ya tsine mata ma."
π€ *Wacece?*
Gambo ne ya katse mata tunaninta da tafiyarta ta hanyar fad'in "Ke."
Juyowa tayi ta dawo ta durk'usa gabanshi, cikin kakkausar murya da gargad'i yace "Tunda kince baki son d'an uwanki to ki turo mana wanda kika ce d'in, yau d'in nan ba zan bar garin nan ba sai nayi magana dashi."
A mugun tsorace ta kalleshi, me kenan ta jawo ma kanta? Ita fa ta fad'a ne dan abar maganar shi, amma bata da wani tsayayye yanzu ita in banda 'yan abi yarima asha kid'a, yanda ta kakkafeshi da idonta babu ko k'yabtawa yasa shi daka mata tsawa cikin jin haushi yace "Tashi ki bani wuri, kina girma kina cin k'asa har yanzu kin kasa sanin ciwon kanki."
Saida ta juya zata tafi taji wasu hawaye sun taho mata, bata san abunyi ba a yanzun gaskiya, Hadiza ma da bata ji dad'in k'in amincewarta ba tashi tayi tana fad'in "Kuyi hak'uri dan Allah zanyi magana da ita."
"Dawo zauna Hadiza." Cewar Hajia, komawa tayi ta zauna tana kallon Hajiar da tace "Watak'ila tana da dalilinta na k'in amincewa, karku matsa mata dan Allah ku barta ta zab'arwa kanta abinda take so."
Gambo ne yace "Amma Hajia ko ma menene dalilinta ai bata k'i d'an uwanta ba, ko dan marayunshi ai zata amince."
A hankali Hajia ta kalli lieutenant ta kuma kalli Husseina, kallon Gambo da Hadiza tayi tace "Magana ta gaskiya bai kamata mu ci gaba da b'oye muku ba, ku kuka haifi abarku ya kamata kusan komai dake faruwa kan 'yarku."
Gaban Hadiza ne ya sake fad'uwa dan ita tun farko tayi tsammanin jin wani mummunan abu, kallonta suke sosai kafin ta gyara zama tana fuskantarsu da kyau tace "Kuyi hak'uri dan Allah ku yafe mana dukanmu, sannan zan so ku nutsuwa kuyi duba na tsanake akan lamarin, karku yanke hukunci cikin hushi, hakan zai iya janwo mana dana sani."
Shiru tayo sai Hadiza da tace "Hajia ko me ya faru bai kamata ace kina neman afuwarmu ba, mu 'ya'yanki ne baki buk'atar wannan."
Gambo ne yace "Hakane, koma menene Hajia ai ba sai kin rok'e mu ba."
Numfasawa tayi cike da muryar rarrashi da nuna nadama tace "Shekara biyar da rabi kenan da wata mummunar k'addara ta fad'a kan Hamna, idan kaji ance tsautsayi to akwai ganganci a ciki, shi yasa na ce muku k'addara dan ku fahimta da kyau, k'addarar data tashi fad'a mata ma sai ta fito daga ruhin d'an uwanta Ammar, bayan abinda ya faru ya faru ciki ya shiga jikinta, hakan kuma ya tabbatar mana da lallai wannan abun daya faru rabon wannan yaron ne, dan da wani yayi k'ok'arin shiga tsakanin faruwar wannan al'amari, ko shakka babu wannan rabon zai iya ajalinshi, *Shureim*, shine yaron wanda Sa'ada a matsayinta na uwar yarinyar da kuma yaron tayi k'ok'arin b'oye wannan laifin dan kar mutumcin yaranta ya zube a idon duniya, bata so 'yarta ta rasa kimarta ta 'ya mace, ta d'auki zunubin da hannu bibbiyu ta d'ora akanta, tayi mana k'arya duk dan ta kare mutuncinsu, ta yaudari mijinta dan ta tseratar dasu a matsayinta na uwa, ta nuna mana zata iya yin komai akan 'ya'yanta, tabbas laifi ta aikata amma fa a dalilin soyayyar da take wa yaranta, muyi k'ok'ari mu fahimceta dan Allah, uwa takan iya yin komai ta kan iya tarar kowane bala'i saboda yaranta."
Ajiyar zuciya tayi tace "Da wannan nake nema mata alfarma a wajenku dan Allah ku yafe mata, kuma iyayen yaran nan ne, ku kamalta da idan kune abun ya faru a idonku me zakuyi? Nasan ko baki abinda tayi ba zakuyi makamancin shi."
Tirk'ashi! Yanzu abinda ya faru kenan da 'yarsu da kuma d'an su? Tambayar da suka ma kansu kenan? Sai dai Hajia ta gama sage musu gwiwa, ta gama dasu tunda tace k'addara, babu wanda ke kauce mata inda ta tashi fad'a masa, sannan ta k'ara d'auresu da tace tana nema mata alfarmarsu, uwa ce ita gare su sannan Ummy ta rik'e yaran kamar ita ta haifesu a cikinta, sun gamsu ba tayi haka bane dan ba ita ta haifeta ba, sai dai su ce kawai k'addarar da kuma sharrin shaid'an, bugu da k'ari ma abun ba yanzu ne ya faru ba, shekaru har biyar to wane fad'a zasuyi kuma da dama ya wuce suyi hak'urin? Cikin jinjina al'amarin Gambo ya kalli Hadiza ya kuma kalli lieutenant yace "Abinda ya shiga tsakaninku kenan har kuka samu sab'ani da matar da baku tab'a sab'awa ba?"
Ajiyar zuciya lieutenant ya sauke yace "Gaskiya raina ya b'ace sosai, matata uwar yarana ta ha'ince ni har haka? Mtsss."
Hadiza ma data gama sawa zuciyarta ruwan sanyi ta yanke hukunci taushe komai ta had'iye ya zama sakayyar da zata musu na kula da yaranta da sukayi ta kalle shi tace "Abban