Showing 165001 words to 168000 words out of 325849 words

Chapter 56 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

577

Middle Ads

anbayar a kaiwa 'yan uwanka babu mai cewa ku ci tare, shiyasa nake tunanin ko kai d'in irin mutanen nan ne da basu damu da cikinsu ba."

Take Ammar yaji hawaye na neman taho mishi saboda abinda ta fad'a, matar uba na! Matar dana rainawa k'ura wai ita ce ta damu da cikinshi har haka! Shi kam wai me yayi wa iyayenshi ne har haka da zafi? A k'alla ba'a k'asara ba yafi shekara d'aya da rabi rabon daya ci abincin gidan nan idan ka cire ruwa lemu, amma sau d'aya Ummy bata tab'a tambayarshi ya ci ko bai ci ba bare tace ya ci, sake kallonta yayi yana murmushi yace "Nagode Uwa."

Ita ma murmushin tayi duk da kanta na kallon k'asa tace "Ba komai."

Juyawa yayi zai fita har ya kai k'ofa ya dawo tare da cewa "Uwa zaki min wani taimako?"

Kallonshi kawai tayi alamar tana saurare kafin yace "Dama su Amar sun shirya zama ne a k'ofar gidan nan ranar biki, kuma sunce dole zamu gayyaci duka abokanan mu, har ma mun riga da mun had'a kud'in da zamu bayar a mana girki, shine nake so na ware nawa daban dan ni ba anan zan zauna ba, ko zaki iya mana girkin da zamu ci?"

Juyowa tayi sosai tana kallonshi da mamaki tace "Amma yah Ammar me yasa kai ma ba zaka zauna tare da 'yan uwanka ba? Ina ganin kamar hakan zaifi armashi tunda kai ma ka bayar da kud'in ka."

Murmushi yayi cike da nutsuwa yace "A'a, ina so na ware kaina ne."

Jinjina kai tayi tace "Shikenan, za ayi insha Allah."

Da farin ciki yace "Yawwa uwa, amma fa bana so kowa ya sani." Jinjina kai kawai tayi ta ci gaba da girkinta shi kuma ya fita.

Tunda Zeituna ta shiga madafa Hajia tayi tsaki tace "Aikin banza, ni bansan meye manufar yarinyar nan akan waccen yaron ba, Allah yasa dai ba jan hankalinshi take son yi ba suja min abun kunya."

Da sauri Husseina tace "A'u'zu billahi, haba Zeeya'atu, me yasa zaki fad'i haka kema kamar wata k'aramar yarinya? Dan Allah ki dinga kyautatawa mutane zato, kuma idan ita kince baki san halinta ba duk da shekarun data kwashe tana miki bauta, ai shi Ammar kinsan me zai iya yi da wanda ba zai iya yi ba."

Wani d'an iskan kallo ta mata tace "Ina ce dai bansa dake a maganata ba, to akan me zaki tsoma mi bakinki? Kuma da kike fad'in haka ke kinsan halin Ammar d'in ne? Yaron da rashin kunyarshi ta bunk'asa ta yanda har gaban iyayenshi zai iya fad'in abinda yake so, shine kike so na kyautatawa zaton? Ke zaki iya rantsewa cewa Ammar baisan 'ya mace ba?"

Girgiza kai tayi tace "Allah ya shiryaki, amma ni dai har zuciya ta na yarda da Ammar, shi kawai yaro ne mai k'iriniya mai kuma fad'in gaskiya duk a yanda ta zo, sai dai kar kowa yaji dad'i amma hakan bai dame shi ba."

Hararanta Hajia tayi ta mik'e ta nufi k'ofar fita tana fad'in "Shiyasa na tsani ina zaune a zo duk a cika min falo, inba sa ido ba ga d'akinki ki zauna mana."

Dreba ta samu ta bashi takardar da aka rubuta mata abun buk'atarsu tace "Ka samu Hassan zai baka kud'i ka siyo mana duk abinda ka gani rubuce anan."

Da ladabi ya amsa da "To Hajia, insha Allahu." Juyowa tayi shima ya juya ya fita dan isar da sak'onta.

*Zuwa yamma* gida ya fara nuna alamun ana hidima kuma babba, domin kuwa kujeru ne aka cika gidan dasu aka jerasu gwanin sha'awa, sannu sannu mutane suka fara hallara har gida ya fara batsewa, b'angare d'aya babbar redio ne aka kunna yana tashin kid'a, ana cikin haka amare suka dawo daga wurin wunin k'umshi, tubarkallah yanda gidan ya cika kai kace yau ne bikin, a haka kuma wankan amare ne kawai za ayi, kuma yawan mutanen ya samo asali ne saboda kowane b'angare da na shi dangi, dan haka gida ya cika mak'il har aka shirya amare aka tafi wurin wanka a gidaje daban daban, sai bayan magriba aka dawo da amare gida. Shiri na musamman aka musu kowace a cikin tsadadden leshe na gani na fad'a, Amna dake cikin leshenta kalar pink tayi masifar kyau, a haka aka fito dasu wajen bidirin bayan an turaresu da turaren jiki, duk da rincab'ewar da wurin yayi ana fitowa dasu kowa ya mayar da kallonshi kansu, Umaimah ce a gaba sai Jamila tsakiya, Amna na baya tare da Hamna wacce ita ma ke cikin leshe kalar na Amna sai dai d'inkin ya banbanta da kuma shirin, amma daga d'aurin kallabi da jaka da takalama sark'a da yan kunnai duk iri d'aya ne, amma kwalliyar fuskar Amna da kuma ashaokin dake kafad'ar ta ya banbantasu, Hamna kuma yanda d'inkin ya fito da ita da manyan d'uwawunta ga uwar atach d'in data gabza akai kamar tayi magana tasha kitso, d'aurin d'an kwalin kusan saman rabin kanta ne kawai yake, hakan yasa zaka iya gane kitson dake kanta da kuma kitso k'waya d'aya da alayi da kalar bleue d'in atach.

Akan kujeru aka zaunar dasu inda Hajia ke tsaye gabansu ta kalli su Zeinabu tace "Ku fito da yayanku."

Wani kallo Zeinabu ta mata a ranta tace "Kaji wai mu fito da yayanmu , mazan fa take nufi." A zahiri kuma jinjina kai tayi tace "To Hajia."

B'angaren samarin ta nufa ita kad'ai, tana zuwa ta shiga da sallama saboda k'ofar bud'e take da abokanansu ciki, tana shiga suka gaisheta kafin tace su fito, nan suka fito suna ta ihuce ihuce da tsokanar angayen irin dai rahar nan ta samari, suna zuwa Junaid ya tsaya ya turo Amar gaba yana fad'in "Ku wuce ku, ni ina nan tunda babu sarauniyar sai sarki kawai."

Gwalo Amar ya mishi yace "Gwauro kenan, mu dai munji dad'in mu."

Ammar dake bayansu ya k'urawa Hamna ido haushi na kashe shi a wurin, tambaya ya ma kanshi "Akan me Hamna zata fito haka babu mayafi? Me yasa za tayi shiri kamar amarya ita ma?"

Hajia ce ta juyo garesu tana musu kallon ku taho mana, dukansu k'arasawa sukayi suka zauna har da Junaid d'in dan har da kujerarshi a ciki, haka suka jera su bakwai a wurin masha Allah, kamar yanda Hamna ke bayan yar uwarta tsaye kamar wata mai tsaronta, hakanne yasa Ammar d'ago kanshi ya kalleta yace "Ke dan ubanki fita daga kaina, kin min wani k'arere dake a baya."

Amna da kanta ke k'asa a hankali ta saci kallonshi, masha Allah ta fad'a a ranta ganin wani kyau da yayi cikin chadda kalar ruwan k'asa, karin hular shi da yanda ta zauna mishi a kai sun masifar dacewa da fuskarshi, ga uwar k'asumbarshi dake ta k'yalli alamar tasha gyara, mayar da kanta k'asa tayi yayin da taji Hamna na fad'in "Malam babu ruwanka da tsayuwata anan, dan kai na tsaya ba dan yer uwata ne, idan zan tsaya anan dan kai ne wallahi sai dai dan na zama ajalinka ne."

Lumshe ido Amna tayi jin har yar tsamarsu ta kai haka, inda Ammar ya gumtse baki yana mata murmushin iya shege ya sake kallonta yace "Idan naje lahira zan siyo miki kankana, nasan ta can tafi tanan komai, asha a k'ara zak'i."

Kashe mata ido d'aya yayi tare da yi mata gwalo, haushi ne yasa Hamna tunzura ta zura hannu ta ture hular dake kanshi ta fad'i, da fari a hassale ya kalleta da niyyar aikomata ashar, amma ganin fuskarta a had'e sai kawai yayi niyyar yin maganinta cikin ruwan sanyi, Husseina ce tace "Ke Hamna lafiyarki kuwa, ya zaki ture hular ango?"

Hassana yar uwar Husseina ce ta d'auko hular zata saka mishi tana fad'in "Ai kinsan halinsu, in suka had'u kamar b'era da mage suke."

Da sauri ya janye kanshi yana wani shak'iyin murmushi yace "A'a Hajia bana so, tunda dai k'anwar matata tace hular nan bata min kyau ba to na hak'ura da ita."

Hassana ce ta kalli Hamna data saki baki tana kallonshi tace "Ke kuma ina ruwanki da shirinshi to? Kika sani ko ya ma amaryar ita?"

Ammar ne yace "To ai Hajia nasan ita ma bata mata ba, ko kin manta yan biyu ne? Zuciyarsu ma d'aya ce."

Tsaki Hajia tayi ta matso kusansu ta dungurar mishi kai tace "Shege uban surutu, a wajen hidimarku ma ba zaka rufewa mutane baki ba, idan ka b'ata min rai sai dai ka bar wurin nan ba tare da an maka wankan turaren ba."

Murmushi ya mata yana dafe da inda ta rank'washeshi yace " Babu fargaba a tare dani, a cikin dangina nake wanda nasan zasu iya yi min."

Wani tsakin ta kuma yi ya bi bakinta da kallo yace "Hajia, Allah ja-leb'en nan da kika shafa ya miki kyau, ki daure dan Allah ki sumbace ni ko sau d'aya ne, kar ya fita a banza baki sumbaci baki na ba."

Husseina da Hassana dariya suka saka hakan yasa ran Hajia b'acewa dan har yanzu ba k'aunarsu take ba, kwalaben turarukan dake hannunta masu matuk'ar tsada da k'amshi ta jefa mishi a k'irji ta juya da sauri ta bar wurin rai a b'ace, ganin haka da Ummy tayi ta tabbatar Ammar yayi halin, duk da bata ji me ya faru ba amma tasan aikinshi ne, girgiza kai tayi ta wurgo mishi da harara daga inda take, Hamna da har yanzu ke bayansu ce tace "Kaga bak'in halinka ya fara shafar yer uwata tun yanzu, gashi kasa Hajia ta tafiyarta bata fesa muku turarukan ba, anji sanyi dai wallahi."

Ba tare daya kalleta ba tace "To ai bana da bargon rufa ne, kuma kinga kune da jin takaici bani na ba, tunda babban abun kunya ne ace babban jikan Alhaji Suley baya da bargon rufa idan yana jin sanyi."

Hannun Amna ya kamo ya matse sosai yana murzawa ya kafeta da ido yace " Amna, nasan kinsan wanene ni, kuma a haka kika amince da zaki aure ni, hakan na nufin kenan zaki iya zama dani a duk yanda nake?"

Kallonshi Amna tayi yayin da take lumshe idonta a hankali wanda suka sha dogon gashin daya dace da idonta ganin sha'awa, wani sauk'akk'en murmushi tayi ta d'an gyad'a mishi kai alamar eh, murmushi ya mata wanda ya k'ara bayyanar da kyawunshi yace "Karki damu to, *insha Allahu da sannu zamu samu masu son mu a duk yanda muke*." Yana fad'a ya juya kanshi a hankali ya kalli inda Ummy ke tsaye, suna had'a ido ta kawar da kanta tana jan tsaki, murmushi yayi ya d'auke kanshi, duk abinda ya faru a idon Zeituna, da sauri ta matso ta d'auki turarukan da suka fad'i k'asa ta mik'awa Husseina tace "Hajia ke ki fesa musu mana tunda Hajia ta tafi."

Girgiza kai tayi tace "Aa 'yar nan rufa min asiri, a gaskiya ina so ayi bikin nan lafiya a gama lafiya, bana son abun magana."

Hassana ce tace "Kira Sa'ada mana saita fesa musu, ita ya dace ai dama."

Husseina ce tace "Ko kuma Zeinabu ba ko Soueiba."

Kallon inda su Zeinabu suke tayi ta taka da niyyar zuwa ta kai musu turarukan amma abun mamaki sai Zeinabu ta dakar da ita tace "A'a gaskiya, su Hajia ma sun saka bare kuma mu, auren 'ya'yanmu ne za ayi, gaskiya karki ja mana jarfa."

Tsayawa tayi da mamaki tana kallonsu, ya zatayi kenan? Muryar Ammar taji yace "Karki damu amaryata, ni wannan ba sabon abu bane a wurina, ke kawai nake so kema ki samu k'arfin gwiwar daurewa da shanye komai."

Tana jin haka ta juyo cike da jin haushin halayen yan gidan nan ta zo kusansu, tana zuwa ta fara bud'e kwalaben, fesa musun data fara yi yasa kowa kallonta da mamakin katsalandan irin nata, sai dai babu mai magana domin kuwa matar lieutenant ce, kallonta Amna tayi tana murmushi shima kuma Ammar haka, cikin taushin murya yace " *Uwa ita kad'ai ce mai tarar aradu da kai ko da me zai faru in dai akan 'ya'yanta ne, a ido na girmeki a shekaru, amma halayyarki da d'ab'iarki sun gama d'ad'ani a k'asa ta yanda dolena na d'auke ki a matsayin uwata*, mun gode da kulawa."

Hannu yasa ya karb'i turaren ya karb'a yace "Duk d'a na gari ba zai so ganin ana cin zarafin mahaifiyarshi ba, dan haka nima ba zan juri ganin waccen masassar cizon sauron tana miki ihu ba, ki barshi kawai mun gode."

Baki sake kowa ke kallonshi da mamakin sunan daya kira Hajia da ita, Jibrl wanda Jamila ta shiga tsakiyarsu ne ya zuro kai yace " Kai Ammar kaji tsoron Allah, yanzu Hajiar ce haka?"

Hassana ce tace "Wai dama Hajia yake nufi? Yanzu Ammar kakar taka ce kake kira da wannan sunan?"

Had'e fuska yayi yace "Hajia muna irin haka dake ne?"

Girgiza kai tayi tace "A'a." Sake cewa yayi "To kina so mu fara irin haka dake?"

Nan ma kai ta girgiza tace "A'a, Allah huci zuciyarka."

Mik'ewa yayi tsaye ya saita kwalbar turaren jikin Amna ya fara mata wanka dasu, Husseina dake rik'e da wani kaskon wuta mai kyau tana turaren wuta bata san sanda ta kai hannunta kan wutar ba saboda kallonshi da take, da sauri ta janye hannunta ba tare data daina kallonshi ba, saida ya mata sharkaf da turare kafin ya mik'awa Zeituna kwalaben ya juya ya bar wurin ko a jikinshi, Hamna ma dake tsaye har yanzu ce tana yamutsar fuska saboda a cikin turarukan daya fesa akwai wanda ya tayar mata da zuciya, juyawa tayi ita ma ta bar wurin, Ummy da duk wani motsin Hamna ke kanta tana ganin haka ta bi bayanta, a falo ta sameta ta zauna tana shan ruwa, zaune tayi ita ma tana kallon mutanen dake kai kawo a falon har zuwa farfajiyar gidan tace "Ya naga kin zo nan kin zauna kuma? Da wata matsala ne?"

Cikin yamutsa fuska tace "Ummy bana jin dad'i ne, gaba d'aya turaren da yah Ammar ya fesa ne ya tayar min da zuciya."

Take gaban Ummy ya fara fad'uwa taji zufa na neman karyo mata, haka ma fitsari ne taji kamar zai taho mata a guje, kallonta tayi yace "Baki da lafiya ne?"

"Lafiyata lau Ummy, amma d'azu muna wurin wankan nan jiri ne ya dinga kwasata wallahi, shiyasa ma na koma mota na zauna."

A firgice Ummy ta kalleta tace "Hamna! Yaushe rabon da kiga hannunki?"

Kallon Ummy tayi ba alamar damuwa tace "Watan daya wuce."

Cikin d'aga murya tace "To wannan fa?"

Da wani murmushi a fuskarta tace "Ban gani ba, amma dai..."

Tsawar da Ummy ta mata tana fad'in "Hamna shashashar ina ce ke?"

Hannunta ta kama da k'arfi suka nufi d'akin ta, suna shiga ta wurgata kan gado ta bud'a wata ma'ajiya ta d'auko wata k'aramar roba mai kyau fara mai murfi ta bata tace "Maza shiga ban d'aki ki bani fitsarinki."

Tsaye ta mik'e tana kallonta da alamar tambaya, da yatsa ta sake nuna mata k'ofar ban d'aki tace "Jiranki nake."

Wucewa tayi inda Ummy ta fara safa da marwa a falon tana sharar zufa, cikin sanyin jiki Hamna ta fito ta mik'awa Ummy robar, hannu tasa ta karb'a ta bud'e magwajin (Gtest) ta saka, mik'a mata robar tayi ta koma ban d'aki ta zubar, Ummy kam idonta na kan wannan abun gwaji addua'r ta d'aya shine kar ya nuna abunda take tunani, inhar ya nuna kam ta shiga uku ta lalace.


_Idan har kukayi comment sosai zaku sake ganin sabo zuwa gobe da yardar ubangiji._


*Alhamdulillah*
09/09/2020 ร  17:58 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

_Bismillahir rahamanir rahim_

_32_


*Jan layi biyu* shine abinda ya nuna, tana rintse ido taji hawaye sun kwaranyo mata, bud'e baki tayi tana so tayi salati kuma ta kasa, shiru d'akin ya d'auka inda Hamna ta k'ura mata ido tana karantar yanayinta, ganin sai zufa take yasa ta taka kusa da k'ofa ta kunna mata ac ta juyo ta dawo tace "Ummy lafiya? Me yake faruwa?"

Girgiza kai Ummy tayi ta bud'e idonta da k'yar wanda suka mata nauyi, gaba d'aya d'akin ne taga yana juya mata kamar zai kifata k'asa, hakan yasa tayi saurin matsawa jikin gado ta zauna tana dafe kai, ita ma zaunawa tayi ta dafata murya a raunane tace "Ummy dan Allah ki fad'a min meke faruwa?"

Saida ta sake lumshe ido tace "Hamna, ciki ne dake, ciki Hamna, cikin Ammar jikinki, Hamna na shiga uku na lalace, ban san ina zansa kaina ba, Hamna ki tayani rok'on mutuwa kafin lokacin da kowa zai san abinda ke faruwa..."

Kukan daya ci k'arfin ta yasa dole tayi shiru ta fara rizgar kuka, Hamna data daskare a wurin kamar an zuba mata ruwan sanyi, ta nema hawaye a idonta ta rasa, zuciyarta ta cunkushe ta yanda taji ta kasa maganar zuci ko tunanin abunyi, ta rasa fahimtar yanayin da take ciki, farin ciki? Ko bak'in ciki? a lokacin sai taji tafi tausayin Ummy ma fiye da ita kanta, dawowa tayi hayyacinta ta fara rarrashin Ummy tana fad'in "Ummy ki daina kuka, wannan *ita ce k'addarar mu*, mu rumgumeta hannu bibbiyu Ummy, mu mayar da al'amarin mu ga Allah shi zai mana mafita."

Kallonta Ummy tayi tace "Hamna na daina kuka fa kike cewa? To me zanyi inba kuka ba? Ciki fa nake fad'a miki kina da, ko dai ba kya fahimta ne? Cikin d'an mutum ne jikinki cikin haihuwa, wanda kika samu sanadiyar kwanciyar da Ammar yayi da ke, ki fahimci tashin hankalin da muke ciki mana."

Kawar da kai tayi tace "Tashin hankalinmu na yanzu ba shi zai hana mu shiga na gaba ba, zaifi kawai mu tanada kukanmu a tashin hankali na gaba."

Tsayawa tayi da kukanta ta kalleta, tabbas abinda ta fad'a hakane, to kenan ya zasuyi? Hajia kullum son ganin laifinta take ta yanda zata tozarta ta, a girman laifin data aikata ma

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login