Showing 228001 words to 231000 words out of 325849 words
wani jami'i yayi yana d'an taka k'afarshi da k'yar yasa suka matsa mishi suka tafi, kafin a duba shi k'afar tayi sumtum bata takuwa, saida ya kalli mai motar d'aya wanda duk ciki shine baida gaskiya yace "Kai dai Allah ya saka min wallahi."
D'aya daga cikin jami'an ne yayi dariya sai mai motar dake zazzare ido yace "Ayi hak'uri yallab'ai, tsautsayi ne."
"Na gidan uban wa? Karka wani d'orawa tsautsayi kaji, ganganci ne da hauka."
Duk yayi maganar ne yana danna wayarshi, Jibril ya kira dan a lokacin yasan shine ke da k'arancin abunyi, yana d'aukar wayar ya kara a kunne yace "Ka zo *Clinik katsina* ka same ni."
Jibril ne yace "Katsina kuma? Me kake..." Bai barshi ya fad'a ba kawai ya datse kiran, juya akalar motarshi kawai yayi ya d'auki hanyar, bai d'auki lokaci ba ya isa can, tun a k'ofar asibitin ya ga motarshi, hankalinshi ne ya tashi ganin yanda murfin dake b'angaren mazaunin yayi, yana cikin kallo da mamaki yana shiga asibitin wayarshi ta sake k'ara, d'auka yayi inda mahaifinshi yace ya zo gida ya same shi, a cewar Jibril "To Abba ina zuwa, yanzu haka ma ina asibiti ne Ammar ya kirani."
"Asibiti kuma? Wace asibitin ta su?"
Cikin rashin tabbas yace "A'a Abba, ina ga fa hatsari yayi, dan ga motarshi can a waje ta bugu sosai daga wajen zaman matuk'i, amma dai bari na shiga ciki na gani."
Cikin tashin hankali shima yace "Subhanallah, Ammar d'in?"
"Abba ina zuwa." Ya fad'a yana kashe wayar ganin Ammar da yayi zaune jami'ai biyu tsaye a kansu, yana zuwa yace "Subahanallah, Ammar hatsari kayi?"
Mik'a masa hannunshi yayi yace "Ba surutu nake so, muje kawai ka kaini wajen duniyata, baiwar Allah yau saura kad'an wannan hamagon ya kashe mata ni."
Wani galala mutumin ya kalleshi, shima kallonshi yayi yace "Eh na fad'a, kayi hak'uri in zakayi in kuma ba zakayi ba ka mutu, ba zan iya b'oyewa bane har na tafi da magana a bakina kuma wacce ta shafeka."
Kallon jami'an yayi yace "Sai anjimanku."
Kamashi Jibril yayi sun fara tafiya kuma ya fizge hannunshi yace "Kai sakar min hannu bana so, dama dan jami'an su gane ya bigeni ne sosai ko sun ci tararshi dayawa, d'an banza ya ban haushi wallahi."
Jibril kam kecewa yayi da dariya yace "Sharri kamar mace."
Hararanshi yayi yace "Idan ba mace ce bani ai na mata ne, mace ta haifeni, mace ta haifi uba na da uwata, mace ce mahutata kuma insha Allahu a yaran da zan haifa akwai mace, to meya rage min kuma?"
Jinjina kai yayi yace "Na ga ranar da bakinka zai rufe."
Ba tare daya kalleshi ba yace "Sai ranar da k'asa ta rufe min ido." Da suka fita saida ya jira makanikenshi ya zo ya d'auki motarshi sannan suka d'auki hanyar gida.
Labaran na jin Jibril ya katse kiran saiya kira lieutenant, shima yana d'auka abinda ya fad'a masa kenan, cikin tashin hankali ya kira Ummy dan yaji ko tana asibiti, cikin rashin fahimtar tambayarshi tace "A'a, lafiya meya faru? Ko jikin Hajia ne?"
Cikin tashin hankali yace "A'a ba Hajia bace, wai Ammar ne yayi hatsari, Jibril yaje ya duba asibiti."
Ummy dake tattara kayanta tana sawa cikin jaka zata tafi gida tana jin haka ta saki jakar tace "Me? Ammar? To ya yake dan Allah? Yaji ciwo ne?"
Lieutenant ne yace "Ban sani ba nima."
Cikin d'aga murya tace "To ka kira ka tambaya mana kaji, ya zaka ce min baka sani ba."
Kashe wayar tayi da gudu gudu duk da goyon Shureim a gabanta haka ta fita ta shiga mota, a kid'ime ta zo gida ko zaman motar bata gyara ba ta fito da sauri ta shigo falon, a lokacin ba kowa ke falon ba daga Hamna sai kuma sauran yara da Zeituna Soueiba da Husseina, yanda suka ga ta shigo a firgice yasa Hamna kallonta tace "Ummy sannu da zuwa, lafiya dai?"
Kusan saida ta kalli kowa cikin rud'u tace "Ammar basu zo ba?"
Soueiba ce tace "A'a bai shigo ba, wani abu ne ya faru dashi?"
Kamar zata fashe da kuka tace "Eh, ance yayi hatsari a hanya, kuma babu wanda yasan halin da yake ciki har yanzu."
Da k'arfi ta mik'e tsaye kamar girgizar k'asa ce ta d'aga ta sama, dafe take da k'irjinta da taji kamar zai tsage zuciyarta ta fito, take taji hawaye sun kawo a idonta, cikin yanayin dake nuna damuwa da mai mahimmanci a rayuwarka tace "Ummy wace asibiti yake? Bai kamata mu zauna haka ba muna jiran tsammani."
Kallonta duk sukayi, anya kuwa! To ai ba zaune suke ba da zata fad'i haka, Ummy ce tace "Ban sani ba nima Hamna, kuma yanzu daga asibiti nake ba can suka je ba."
Karaf ta fizgi makullin motar Ummy ta nufi k'ofa tana fad'in "Zan duba duk asibitin dake garin nan."
Bayanta Ummy tabi da sauri haka ma Zeituna, suna fita daga farfajiyar motarsu ta shigo gidan, tsayawa duka sukayi suna kallonsu, anan Jibril ya tsaya Ammar ya fito yana rintse ido da takawa da k'yar, tana ganinshi ta taka da sauri tana dudduba jikinshi, k'ura mata ido yayi yana kallo saida ta gama dubawa ta d'ago suka had'a ido, hannu tasa ta share yar k'wallar data taho mata ta kalleshi tace "Kana lafiya?"
Saida ya d'an sunkuyo da kanshi kusanta yace "Kankana duk damuwa ne a kaina ta saki zubar da hawaye?"
Kallonshi tayi sai taji haushin kanta da kunyar kanta sun kamata, saida ta d'an kalli gefenta taga Jibril ya sakar mata ido yana kallo, bata yarda ta juya ta kalli su Ummy ba kawai ta ruga a guje tayi b'angaren Amna, saida ta b'acewa ganinshi sannan ya kalli gabanshi, ido cikin ido suka kalli juna shi da Ummy, ga damuwa da tashin hankali da kuma soyayyarshi fal idonta, amma ba zata iya matsowa inda yake ba, Zeituna ce ta matso tace "Yah Ammar ya jikin? Hatsari kukayi?"
Murmushi ya mata yace "Uwata karki damu kinji, ba wani babban abu bane ai, k'afata ce kawai ta d'an bugu, gashi ma da kaina na zo gida."
"Allah ya k'ara kiyayewa to." Murmushi ya mata yace "Nagode, zan shiga ciki."
B'angarensu ya nufa shima, su Zeituna na komawa suka fad'a ma su Husseina, nan suka fito suka nufi nasu b'angaren, yana shiga Amna na zaune kan kujera tana kallon Hamna data shigo mata a gigice ta ganshi yana d'angyasawa, da sauri ta taso tana fad'in "Duniyata lafiya? Meya sameka?"
Rumgumeta yayi jikinshi wanda hakan yasa ya kalli Hamna dake bayansu zaune, murmushi ya mata inda yace "Kwantar da hankalinki me ni, d'an k'aramin ciwo ne karki sa min kanki a damuwa, ina lafiya."
Ganin su Husseina sun shigo yasa ta raba kanta dashi ta taimaka mishi ya zauna, suma zaune sukayi inda suke jajata mishi suna tambayar ba'asi, nan ma wani zagin ya dinga zunduma ma mai motar nan su kam banda dariya babu abinda suke, sai Hamna dake kallonshi da mamakin irin halinshi, tana so ta tashi ta bar wurin amma ta rasa me yasa bata son yin nesa da wajen, Husseina ce tace ma Amna "Ki samu ruwan zafi saiki gasa masa k'afar, idan kin kamalla sai ki shafa masa rob ko victago."
Mik'ewa Amna tayi kamar ba mai rumk'umemen ciki ba tana fad'in "To."
Saida ta shiga madafa Hamna ta mik'e zata bi bayanta ta kalleshi tace "Ya kamata ka fad'a musu rob ya k'ara tsada, ina ga yanzu zaka buk'aci likitan k'ashin nan."
Shigewa tayi su dai babu abinda suka gane, amma sai gani sukayi ya saki murmushi mai tsadar gaske, basu d'auki lokaci ba Amna ta fito ta nufi teburin abinci ta d'auko kwanuka ruwa da duk abun buk'ata, Hamna kuma na rik'e da roba d'auke da ruwan d'umi da k'aramin towel mai taushi sosai, a tare suka aje gabanshi sai Amna data shiga d'aki ta d'auko victago, cike da mugunta Hamna tace "Ban shi da kaina zan shafa mishi, yau zan gane k'aryar jarumtar da ake mana."
Su Zeituna ta kalla tace "Aunty ku duba mana idonshi idan kuka ga alamar hawaye to akwai buk'atar ku fara d'inka masa atamfa."
Rintse ido yayi, wannan magana ta k'arshe ba k'aramin tab'a shi tayi ba, shi Hamna zata ce a had'a da atamfa? Ma'ana fa ta mayar dashi d'an daudu, jar ubancen, shi kam da Hamna a matsayin matarsa take tayi wannan maganar daya mata luguden bulaliyarshi ko zata shiga hankalinta, dan ya fahimci duka ko zagi ba zai sata shakkarshi, tsayawa ya nuna mata mazantaka shine zaisa ta shiga hankalinta. Su Husseina dariya sukayi tare da tashi Zeituna na fad'in "Na yarda da jarumtar yah Ammar Hamna, ba zai bani kunya ba dan yana da uwa bafulatana, juriya da b'oye hawaye ba sabon abu bane ga fillo."
Tana kallon cikin idonshi tace "Zamu gani."
Husseina ma cewa tayi "Saida safenku." Kallonshi tayi tace "Ammarun Hajia yau fa gaka hannun 'yan biyun Ummynka, ya zata kasance gobe da safe kun bamu labari."
Dariya akayi suka fice, Amna abinci ta zubo ta zauna kusa dashi ta dinga bashi a baki cikin kwanciyar hankali, jimawar da sukayi yasa Hamna cewa "Ke dallah kiyi sauri ki gama bashi sai kace zai cinye abincin shi na k'arshe."
Kallonta tayi tana turo baki tace "Haba Hamna ke baki da imani ne, dubi fa yanda k'afarsa tayi ko motsi bayayi da kyau."
Sunkuyar da kanta tayi hakan yasa shi tallabo fuskarta, hawaye ne suka kwaranyo wanda yasa shi jin tausayinta, tunani dayawa ne ya zo masa a daidai lokacin, yanzu fa irin wannan da ace akwai k'arar kwana da ya zatayi? Gashi tana da tsohon ciki daga yanzu zuwa kowane lokaci zata iya haihuwa, sannan akwai wata kulalliya tsakaninshi da yer uwarta da yake buk'atar ta yafe masa ko da bata san da al'amarin ba. Share mata hawayen yayi yace "Karki zubar min da hawayenki kinji, kada ki karya min zuciyata nima nayi kuka."
Jinjina kai tayi tace "To na daina." Murmushi yayi yace "Yawwa to bani magani na nasha."
D'aukowa tayi ta bashi yasha kafin ta kalli Hamna tace "Mik'o min ruwan."
A daidai wannan lokacin sosai taji zafi zuciyarta, dan abun a bayyane yake cewa yar uwarta tafi iko da shi duk da ita ya fara sani, kuma bata da yanda zatayi daya wuce hak'uri, kasa tausar kanta tayi tana mik'a mata ta fice a d'akin da sauri har ta bar makullin motar Ummy anan, Amna bata kula da komai ba sai dai shi ya fahimci ranta bai mata dad'i ba, fuskar matarshi ya ci gaba da kallo tana gasa mishi k'afarshi wacce ke luf da bak'in gashi kwance kan jar fatarshi.
*Alhamdulillah*
14/10/2020 ร 00:58 - Ummulkhairi: ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*BADAK'ALA*
๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ _*AHALI NA*_๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐
*RAYUWAR RAYAM*
๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐
_*MY BK* INA TAYAKI MURNAR FARA SABON NOVEL D'IN KI, ALLAH YASA MU ANFANA DA DARASIN DAKE CIKI, ALLAH YASA YANDA KIKA FARA LAFIYA KI GAMA LAFIYA, ALLAH YA K'ARA MIKI LAFIYA MASOYIYA._
๐ฆฏ๐๐ฆฏ๐ฎโโ๏ธ *KUTKALE*๐ฎโโ๏ธ๐ฆฏ๐ ๐ฆฏ
*(PRISON)*
_MA SADIJA BARKA BARKA DA KAMMALA NOVEL D'INKI *KUTKALE*, ALLAH UBANGIJI YASA MU ANFANA DA DARASIN DAKE CIKI, ALLAH YA YAFE MIKI KURAKUREN DA KIKAYI A CIKI, ALLAH YA BAKI LADAR FADAK'ARWA, SAI MUN JIKI A NOVEL NA GABA INSHA ALLAH._
๐ *Sis Chappa*๐
_Barka da k'arin shekara 3 a duniya, Allah ya karo shekaru masu albarka, Allah ya baki lafiyar anfanarsu ta hanyar data dace, bรฉbรฉ Khalid yace yana tayaki murna._
๐ซโจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_๐ค
โ *[ T.M.N.A]* โ ๐๐๏ธ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
_51_
Ummy ta fito goye da Shureim zata tafi duba jikin Ammar Hajia ta fito daga d'akinta, tana ganinta tace "Ke kuma ina zaki je yanzu da dare da kika goya shi?"
Cikin ladabi tace "Hajia zan duba Ammar ne."
Da wani kallon rashin mutumci ta kalleta tace "Ban gane ba? Ammar d'in baya lafiya?"
"Eh Hajia, d'azu ne ya samu hatsari a hanya, amma da sauk'i sosai k'afarsa ce kawai ta bugu."
Cikin fad'a tace "Amma kuma shine banda darajar da wani zai shiga ya fad'a min halin da ake ciki."
Tsaki tayi ta nufi hanyar fita waje, Ummy kuma tunaninta ko dai ta d'auka Amar aka ce shalelenta, dan haka tace "Kiyi hak'uri Hajia, dan naga ba kya jin dad'i ne shiyasa."
Bata juyo tace komai ba sai ci gaba da tafiya da takeyi, ganin dai sun doshi b'angaren tare yasa Ummy cewa "Hajia Ammar ne fa."
Cak ta tsaya ta juyo tana kallonta tace "Ammar ne fa? Eh Ammar d'in, me kike tunani? To saurara kiji da kyau, na jima ina rayuwa cikin k'arya da yaudara, jiya zuwa yau ne kad'ai nasan masoyana na gaskiya, duk gidan nan babu mai k'aunata kamar shi Ammar d'in."
Juyawa tayi ta shiga ita ma tana biye da ita, babu sallama ta shiga ta samu Amna ta gama gasa masa k'afarsa, zaune tayi kan kujera kusa dashi tana kallon k'afarsa tace "Mijin ya jikin? Ashe takaba ka kusa sani, kaji yanda zuciyata ta buga, kada ka sake min irin haka gaskiya."
Yanda ta gama maganar da shagwab'a, dariya sukayi sai Ummy data saki baki tana kallon, me ya samu Hajia ne? Ammar ne fa ko ta manta? Yaushe haka ta fara faruwa? Cikin murmushi Ammar ya ja hancinta yana rera mata baitin wak'ar gari ya waye yace "Haba, na gwadaki ne kawai dan ramawa."
Cikin turo baki tace "Kuma duk gidan nan babu wanda ya iya fad'a min ma sai yanzu na sani."
Saida ya saci kallon Ummy sannan ya kalli Hajia yace "Ai Hajia sai munsha lahaula, dan soyayyata dake yanda zata jijjiga wasu zaisa a kafa mana na mujiya, dan tunaninsu yaushe ne kuma tayaya haka ta fara faruwa."
Wani kallo Ummy ta masa jin ya karanta mata tunaninta, dariya Hajia tayi ta mik'e tana dafe k'afarshi tace "Zan tafi saida safe zan zo muyi hira."
Murmushi yayi har ta juya zata tafi sai kuma ta juyo, ba zato ba tsammani ta rarumeshi ta rumgume tana fad'in "Nima na rama buru-ubar da kake min."
Sakinta tayi ta juya shi kuma yace "Ramuwa mai citta."
Fita tayi Ummy na kallo al'ajabi duk ya kasheta, kallonta yayi yace "Ummy zauna mana, kawo min shi dan Allah." Ya fad'a yana tara hannu ta bashi Shureim.
Kujerar da tayi niyyar zama ta kalla sai taga makullin motar ta, takawa tayi ta d'auki makullin ta nuna masa tace "Dama shi na zo d'auka."
Juyawa tayi ta fita suka bita da kallo, murmushi kawai yayi ya mayar da hankalinsa kan Amna dake d'an ciccije leb'e, cikin kulawa yace "Lafiya dai?"
Cikin yamutsa fuska tace "Ciwo nake ji yah Ammar, bayana ke wani irin abu ba dad'i."
Cikin son gano abinda ke faruwa yace "Tashi ki d'anyi tafiya to ko haihuwa ce zata zo da sauk'i insha Allah."
Had'e labb'enta tayi ta yunk'ura ta tashi, rik'e take da bayanta tana ta safa da marwa a tsakiyar d'akin, ikon Allah da yake haihuwar na kusa bata jima da fara wannan sassarfa ba taji ciwo na tasowa sama, kallonta yake duk inda tayi yana lura da halin da take ciki da kuma yanayinta, da fari duk sanda wuyan k'aramar rigarta ya fad'i saita jashi sama ta mayar, amma yanzu yaga bata kula ba har rabin k'irjinta duk a fili, ga kuma wata uwar zufa dake ta tsatsafo mata a goshi da wuya, sannan idan ciwon ya turnuk'ota saita rabka sallalami da dafe duk abinda ke kusa da ita ko ta durk'ushe k'asa, yanzun ma durk'ushe tayi amma kuma tashin ya gagara, hannunta ta d'ora kan k'aramin teburin dake wurin ta rintse ido sosai take fad'in "La'ilaha ilallah, ya hayyu ya k'ayyum bi-rahmatika astagisu, la'ilaha..."
Da k'arfi ta kalleshi tace "Dan Allah ka kaini asibiti karna mutu, yah Ammar ka taimaka min mutuwa zanyi."
Da sauri ya taso yana taka k'afarshi da k'yar ya durk'usa kusanta shima yace "Kalleni Amna, kalli fuskata kinji."
Kai ta dinga girgizawa cikin rad'ad'i tana fad'in "Ba zan iya ba, ka kaini asibiti dan Allah, ka kira min Ummy, bayana ciwo yake kamar zai tsage."
Mik'ewa yayi tsaye ya dawo kan kujerar da yake ya d'auki makullin mota da wayarshi, dawowa yayi kusanta ya tallabota da nufin su fita, tana mik'ewa sai kuwa ta cakumo rigarshi tamau ta fasa ihun data shiga dodon kunnenshi, yanda yaga tana neman sulalewa k'asa yasa shi azamar tarota, ya fara takawa da ita sai yaji tayi wani irin nishi kamar dai wani abu ya tunkaro zai fito, tsayawa yayi ya kalleta da kyau sai yaga daga inda take durk'ushe har inda suke yanzu duk wasu ruwa ne suka b'ata wurin, dafe goshinshi yayi yace "Oh mon Dieu."
Da sauri ya fara latsa wayarshi ya danna kiran wayar Ummy, tunda taga kiranshi a wannan lokacin tasa a ranta cewa Amna ce ba lafiya, dan haka ma saida ta mik'e da sauri ta rarumi gyalenta kafin ta tashi lieutenant, tana d'aukar wayar yace "Ummy Amna ba lafiya, kiyi sauri ki zo."
"To gani nan." Ta fad'a ita ma da sauri, tare da lieutenant suka fito yana rik'e da Shureim, fita tayi shi kuma ya je d'akin Hajia ya sanar da ita, tare suka k'arasa a lokacin Ummy na shiga Ammar yace "Ummy haihuwarta kusa take, ki dubata in zaiyi mu kaita asibiti."
Kamata tayi ta kalleshi tace "Taimaka min da safa."
Ya juya da niyyar shiga d'aki Amna ta sake wani nishi mai k'arfin gaske tana rirrik'e da hannun Ummy, haba mantawa yayi da ciwon k'afarsa ya juyo da gudu, yana zuwa makullanshi ya cillawa Ummy yace "Ummy bud'e min d'akin magani na." Da sauri ta mik'e ta shiga gaba shi kuma kamar wata yar beby haka ya lailayeta da iya k'arfinshi ya bi bayan Ummy, suna shiga da ita d'akin ya kwantar da ita kan gadon dake wurin musamman na haihuwa, Ummy kuma safa ta sanya da sauri ta tunkarota zata duba ta, kafin ta ida k'arasawa kusanta ta sake d'an d'agowa ta danno wani nishin kamar