Showing 231001 words to 234000 words out of 325849 words

Chapter 78 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

568

Middle Ads

dai wanda take yi, haba ai wani abu taji ya zubo kamar kayan cikinta tare da wani irin gumi, kukan yaron da suka ji ne yasa Ammar saurin dawowa inda yaji kukan yaron ya sake bud'e k'afafun ta, bai tsaya saka safa ko wani abu ba kawai ya d'auki yaron da cibiya ta laulayeshi, cikin nutsuwa ya fara warware mishi da wani faffad'an murmushi a fuskarshi ganin yaronshi a hannunshi, Ummy ce ta matso tasa almakashi ta yanke cinbiyar, zata kai hannunta da niyar janyo uwa sai kawai Amna ta damk'i hannunta ta sake dank'aro wani nishin, fit sai ga wata santaleliyar budurwa ta fad'o ita ma sai wutsilniya take da kuka a hankali, kallon fuskar Amna yayi yace "Ke duniyata, ya kike neman kashe ni da farin ciki, daga farawa saiki fara min da bibbiyu."

Kallon Ummy yayi baki bud'e yace "Ummy biyu ne, wallahi yan biyu ne, wayyo Allahna dad'i, Amna nagode nagode kinji, Allah ya saka miki da alkairi."

Lumshe ido Amna tayi ta kwanta luf, Ummy ce ta kalleshi tace "Ka d'auko mana kayan haihuwarta."

"To Ummy." Ya fad'a yana nufa k'ofa rik'e da jinjirin, kallonshi Ummy tayi tace "Ina kuma zaka je dashi a haka?"

"Oh." Ya fad'a yana dawowa ya mik'a mata shi, aje shi tayi gefen Amna ta yanke cibiya ta fito mata da uwa, hannu tasa ta fito mata da gudan jini, kallonta tayi tace "Amna ci gaba da tausa ciki kina murzawa saboda jini ya fito."

Ido rufe tasa hannu tana murza ciki tana danna mararta tana ji jini na zubo mata. Yana fitowa ya ga duk iyayen tsaye Zeinabu ce kawai babu, cike da shak'iyanci ya fara taka rawa yana tafa hannaye yana juyawa, takon rawar a hankali mai birgewa, a haka kuma wak'a ya dinga rerawa ta godiya ga Allah wacce shi ya k'irk'ireta yanzun nan, lieutenant ko da yaga haka yasan ta haihu sai shima ya fara tapi yana biyar wak'ar yana gyad'a kai alamar yanayi da wak'ar sun masa dad'i, Hajia ce tace "Kai ta haihu ne?"

Girgiza kafad'u ya shiga yi yana kallon fuskarta ya kwaso shoki daga k'ololuwar k'asa yayi sama da ita ya wurgata fuskar Hajia yana fad'in "Hajia 'yan biyu ta haifa min, aradu mace da namiji ne Hajia, kai nima fa ashe jarumi ne."


Murmushi ta masa tace "Hakane, amma duk jarumtarka mijina dai ya fika, shi uku yake haifa."

Alhaji dake tsaye rik'e da carbi kunya yaji ta kamasa, su lieutenant da Labaran kuma dariya sukayi cike da jin kunya, shafa kumatunta yayi yace "Bari na dawo Hajia Allah yau sai kin taka rawar jin dad'i."

Da gudu kamar yaro ya nufi hanyar b'angarensu, da sauri ya d'auko kayan ya kawowa Ummy, Ummy da kanta ta gyara yaran ta bashi ya kawo musu, yana dawowa ya samu tana dannawa Amna mararta da jini ke ta fitowa, tana kallonshi tace "Zare nake so zan mata d'inki."

Kallon Amna yayi ya matsa kusa da ita yace "Wayyo duniyata yarana sun k'ara ki ko, sannu kinji, insha Allahu ladar ta tabbata gareki."

Rufe idonta tayi a ranta tace "Kai da kan ka ma ka k'ara ni bare su, ai kamar uba kamar 'ya'yansa ne."

Da kanshi ya had'awa Ummy zaren ya bata kafin ta fito, namijin dake hannun lieutenant ya lek'a fuskarshi yana wasar masa baki yana fad'in "Kai wanene wannan? Kai yaron babanshi ne, d'an albarka ne, yaron Ammar ne wannan."

๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚ *Allah ya kyauta.*

Soueiba ce ta kalleshi galala tace "Ammar yaron da ko ido bai bud'e ba kake ma wasa?"

Kallonta yayi yace "Ina so ya fara d'aukar sautin muryata ne kafin ta kowa."

Tab'e baki Hajia tayi tace "Duk tsiyarka kuma sai sun sun gane uwarsu kafin kai."

"Wannan ba matsala bane Hajia, ta cancanci haka ai, daga yanda naga ta canza d'in nan a yayin nak'udarsu na k'ara mik'o muku jinjinata."

Kalle kalle ya shiga yi kafin yace "Wai duk ina sauran mutanen gidan."

Husseina ce tace "Suna bacci mana, *12: 30* ce fa tayi na dare."

Zaro ido yayi yace "Wa? Bacci a lokacin da yan biyu na suka shigo duniya, ai Qur'ani basu isa ba, duk uban daya tsaya ma mutum ma saiya tashi, bari kuga yanda zan firgita nutsuwar kowa."

Labaran ne ya bishi da murmushi yace "Mun gode Allah da yasa ubannin gamu nan tsaye."

Dariya lieutenant yayi ya kalleshi yace "Kar ya baka wahala mana."

Suna kallonshi ya nufi wajen mai gadi kai tsaye ya fara bubbuga mishi k'ofa, yanda yaji buga k'ofar yasa shi fitowa da sauri da makullai a hannu yana tunanin fitar gaggawa ce, yana ganinshi ya tsaya yace "Alhaji k'arami wani ne ba lafiya? Bara a bud'e k'ofar."

"Kai tsaya dallah." Ya fad'a yana turashi baya, kallonshi yayi zuru da ido kafin yace " Ina bokitin nan naka da kake wanki?"

Saida ya had'e gira tsabar mamaki yace "Bokiti? Yana nan ciki?"

"D'auko min." Ya fad'a, shiga ciki yayi ya d'auko bokitin robar ya kawo mishi yana fad'in "Yallab'ai lafiya dai ko? Allah yasa ba laifi nayi ba."

Kallonshi yayi yace "Idan laifi kayi kuma shine sai a bokitinka zan huce saboda tsoronka nake ji."

Sunkuyar da kai yayi shi kuma ya juya zai tafi sai kuma ya tsaya ya juyo yace "Baka da wani mabugi haka kamar sanda ko icce?"

Shi kam mai gadi baya da dan ko shayi ko girki idan buk'atar yi ta kamashi k'aramin gas gare shi, dan haka yace "Babu yallab'ai, amma bari a samo maka."

Takalminshi yasa da niyyar fita nema sai Ammar yaga tsumagiya aje, d'auka yayi yace "Bari wannan ma yayi."

Juyowa yayi ya kalleshi yace "Yallab'ai da ka bari na samo maka wanda yafi wannan, ita ma ina ajiya ne saboda yara wani lokacin."

Kallonshi yayi saida ya kawo bokitin nan gaf da kunnenshi ya tak'ark'are ya had'a tsumagiyar nan da bokiti ya shiga bubbugawa da k'arfi kamar zamanin da ake shela da baki, rintse ido yayi sosai saboda yanda k'arar ke shiga hudar kunnenshi, saida yaji yayi shiru sannan ya bud'e ido ya kalleshi, shima kallonshi yayi yace "Har gari ya waye babu mai kwana a gidan nan, baiwar Allah na can tasha fama ta haifo min yara har biyu, biyu fa." Ya fad'a yana nuna mishi biyu da yatsunshi ya ci gaba da cewa "A lokaci d'aya, kuma kuma ku kuna baccin iya shege."

Juyawa yayi cikin takon k'arfi kamar zai shiga filin daga ya shiga falon Hajia, saida ya tsaya tsakiyar falon ya fara bubbuga bokitin yana ihu yana fad'in "Kowa ya fito, kowa ya tashi."

Har sama ya haura k'ofar kowane d'aki ya bubbuga yana shelar kowa ya fito, har yara masu nauyin bacci saida suka fito haka Zeinabu da Hamna take hangenshi daga sama, Kamal ne ya iya jarumtar cewa "Yah Ammar lafiya ka tashemu a bacci?"

Kallon duka yaran yayi yace "Kowa ya sauko k'asa."

Cikin turo baki da girmama jarabarshi kowa ya sauko rai a b'ace, kamar zai basu horan yak'i haka suke jera suna kallonshi, kallonsu shima yake yace "So nake ku fita farfajiyar gida kuyi murna kuyi tsalle kuyi ihu da hauka saboda murnar samun 'yan biyu da nayi, yan biyun ma ni duka jinsin aka had'a aka ban, dan haka ina so duk unguwar nan ta shaida anyi sabon *Ammar* da kuma k'anwarsa *Amna*."

Yanda ya fad'a haka suka fita duk sukayi inda suka ga su Hajia, d'aga kai yayi suka had'a ido, girgiza kai tayi a ranta tace "Allah ya shiryaka Ammar."

A zahiri kuma ce masa tayi "Saboda wannan ne ka d'aga mana hankali? Allah ya baka lafiya to."

Sake d'aga kai yayi yace "Ki sauko kema ko kuma na sauko dake yar bak'in ciki, hassada kike min na samu 'ya'ya biyu a lokaci d'aya."

Wani murmushi ta masa tace "Biyu ko uku?"

Dara daran idonshi ya sake kafewa kanta da mamaki yace "...

*Alhamdulillah*

*Wallahi rashin comment yasa duk rubutun ya fice min a rain, ba zan dakatar da rubutun ba amma zan iya daina turawa ko ina, idan kun canza na samu gamsuwa zaku ga wata page gobe insha Allah ba ma sai kun tambaya ba.*

_A kafta, yawan sharhi yawan rubutu._
14/10/2020 ร  00:58 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

๐Ÿ’ซโœจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐ŸŒŸ
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_๐Ÿค

โ˜† *[ T.M.N.A]* โ˜† ๐Ÿ“–๐Ÿ–Š๏ธ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_52_


"Yan uku kankana?"

Yawu ta had'e duk tayi alamar rashin gaskiya, ganin bai daina kallonta ba yasa ta juya zata koma d'akinta taji yace "Har d'akin zan sameki wallahi idan baki sauko ba."

Juyowa tayi ta kalleshi, yamutsa fuska tayi ita kam ba zata iya wannan tozarcin ba, hararanshi tayi tace "Hijabi zan d'auko to, saboda gidan nan ba tsaro gareshi ba, ta ko ina kuraye ke akwai ko ganye suka gani kallon nama suke mishi."

Da kallo kawai ya bita har ta fito, kallon saukowarta yake da dogon wando sai hijab daya rufe iya cinyarta, saita ta kawo daf da shi suka jera zasu fita yace "Duk kurar da take ma ganye kallon nama lallai lafiyayya ce, shiyasa fa har yanzu nake mamakin yanda akayi baki karb'i sak'on dana tura miki ba bayan kuma ina da tabbaci akan d'an aike na."

Hararanshi tayi ta murgud'a baki tace "Ta Allah ba taka ba, burinka kenan a kaina kuma ba zai cika ba."

Suna zuwa Ummy ta fito ta kalleshi tace "Malam muje dan Allah ka kaimu asibiti idan ka gama shiriritar."

Turo baki yayi gaba ya kalli mutanen dake wurin yace "Yanzu jama'a ba zan iya samun wanda zai kira ni ya danganta yaran nan dani ba?"

Alhaji ne yace "To uban..." Kallon yaran yayi yace "Da fari fad'a mana sunansu? Ko kuma ka bamu zab'i ne?" Da k'arfi tace "A'a Alhaji, haba dai kura da shan bugu gardi da kwashe kud'i, ai yanda nake ubansu haka zan saka musu suna."

Hamna ce ta kalli Ummy tace "Ummy ina Amna?"

Nuna mata d'akin tayi tace "Tana ciki." D'akin ta shiga dan ganin yar uwarta, shi kum saida ya gyara tsayuwa sannan yace "Namijin sunan *Ammar*, macen kuma domin nuna farin cikina ga uwarsu na mata takwara, dan haka ita ta ci *Amna*."

Kallon kallo aka shiga yi harda yaran, lieutenant ne yace "Meye na mayar musu da sunanku to kamar suna ya k'are?"

Murmushi yayi yace "Abba ai duka sunaye ne masu kyau, ina so jarumi na ya zama namiji marar tsoro da fargaba, ya zama babu shakka babu d'aga k'afa kuma zai iya fad'a ko a gaban waye, sannan ya zama wanda baya d'aukar raini, jarumata kuma zan so ta zamar ruwa masu aiki sannu kamar mahaifiyarta, hakan zaisa kowa ya so ta."

Lieutenant ne yace "Idan na fahimce ka kana so ka saka mishi sunanka saboda kana so yayi komai naka ko?"

"Eh Abba." Ya fad'a cike da kuri, jinjina kai yayi yace "Har da fitsarar da rashin ta idon ma?"

Kwab'e fuska yayi alamar shagwab'a yace "Abba ni ne marar kunyar?"

Murmushi lieutenant ya masa yace "A'a d'an albarka."

Husseina ce tace "To wai akan me sai sunayenku za'a mayar ma da yaren kamar wad'anda suka mutu?"

Alhaji ne yace "Dan Allah ku barshi tunda haka yake so ai ya hallata, kawai mu dai ya fad'a mana wani sunan ko da alkunya ce da zamu dinga kiransu dashi, d'an ba zamu kiraku da sunanku ba kuma suma mu kirasu da sunanku."

Girgiza kai Hajia tayi ta kalleshi tace " *Shalele* na, fad'a mana alkunyarsu ko kuma na saka musu da kaina."

Kallon kallo aka shiga yi Hajia ta kirashi shalelenta, basarwa kawai tayi shi kuma saida yayi tsayuwar tata rashin mutumci yace "Eh to shi jarumin Ammar d'in zaku iya mishi lak'abi da *Abu Ahmad*, sunan da zai sawa d'anshi kenan insha Allah, jatumar tawa kuma saiku mata lak'abi da *Ummu Aysha*, idan kuma alkunyarsu kuke so saiku kirasu da *Ameer* *Ameera*, idan kuma a sauk'ak'e kuke so saiku ce *A.A*, ita ma kuma saiku ce mata *A.A*."

.Cike da k'aguwa Ummy tace "Ba zan iya sauraren wannan shirmen ba, yarinyar can asibiti take buk'ata a bata kulawar data dace, amma kun tsaya kuna maganar sunan yara tun yanzu."

Juyawa tayi cikin jin haushi ta shiga ciki, Hamna ta samu rik'e da hannun Amna cikin sanyin murya take fad'in "Yer uwa wallahi ban tab'a tsammanin haka haihuwa take ba, ta zo min da sauk'i fiye da tunaninki, sannan yah Ammar ya tsaya kaina har na haihu, gaskiya naji dad'in kulawarsa a kaina."

Murmushi Hamna ta mata tace "Yanzu ma gashi can sai hauka yake mana a gida wai shi yayi yara, ya hana kowa bacci fa."

Murmushi tayi tace "Ba hauka bane yer uwa, farin ciki yake ya d'ora idonshi akan 'ya'yansa."

Kamata Ummy tayi tana fad'in "A ganinki haka murna ce? Wannan ai hauka ne da shirme, kanshi aka fara haihuwa?"

"Ummy a gareshi shine na farko." Cewar Amna, da sauri Ummy ta kalli Hamna ita ma kuma ita ta kalla, kamata sukayi ta tashi Ummy ta mata durwa (k'unzugu) sannan suka fito, sun same su tsaye sai zuba musu haukan ko yake ta bakinsu, sunaye kawai yake zana musu idan basu iya fad'in wannan su fad'i waccen, rankaya sukayi zasu fita ya kalli Hamna ya cilla mata makulin mota yace " Ke b'ukekiya tuk'asu ina zuwa."

Hajia ce tace "Ina zaka je kuma?" Kallonta yayi yace "Ku dai ku tafi gani nan."

Hamna da bak'in ciki ke neman kasheta tsabar haushi kawai taji hawaye sun taho mata, lieutenant ne yayi sauri matsowa kusanta yace "Ke lafiya? Meya miki?"

Saida ta nuna Ammar tace "Abba na fad'a mishi bana so yana shammatar min jiki amma ya k'i dainawa, haka kawai kamar maye ya sa min ido."

Kallonta yayi da mamaki yace "Ke ni banda lokacinki, girma ya zo min yanzu na wuce ajinki wallahi."

Yana fad'a ya wuce b'angarensu, k'ofar Amar yaje kamar Allah ne ya aikoshi ya shiga jijjiga mishi k'ofa, cikin kasala ya taso ko baccin ma baiyi ba su gama tijara shi da Umaimah kan shinfid'ar gado da bata gyara masa ba, yana bud'ewa Ammar yace "Shege, wato ina can ina bud'ar baki dan murna ku kuna can kuna nanik'e tsakani k'ugu da k'irjin matanku, to fito kaje ka d'ora mana shayi a k'ofar gida zanje na tado sauran matsiyatan."

Da mamaki Amar yace "Ammar Amna ta haihu ne?"

Cike da isa yace "Biyu, biyu yaro ta haifa min, a halin da ake ciki yanzu zan iya bada 'ya kuma nima za'a iya bani 'ya."

Wani mamakin ne ya sake lullub'e shi yace "Ban gane ba, kar dai yan biyu ta haifa maka mace da namiji?"

Sororo ya kalleshi yace "Ban gane kar dai ba? Bai kamata bane ko me kake nufi?"

Cike da damuwa yace "Kai sarkin masifa, ni ba haka nake nufi ba."

Hanyar b'angaren Junaid ya nufa yana fad'in "To maza kaje ka d'ora mana shayi."

Niyyar komawa ciki yayi yana fad'in "Ba uban da zan d'ora ma shayi yanzu ehe."

Shi dai baisan ya akayi ba saiji kawai yayi har ya shak'o wuyan rigarshi yana fad'in "Sai ni Ammar, ni zaka d'ora ma inba haka ba ubanka zaka ci Allah a cikin daren nan."

Cikin son k'wak'ule hannunshi yace "Naji to zan d'ora sake ni."

Sakinshi yayi da sauri ya shige ciki yana fad'in "Sai naga tsiya yanzu in zaka biyo ni ciki ne."

Saida ya rik'e k'ugu yace "Kai dai kafi kowa sanin waye d'an uwanka, kaine zaka bayar da labari na ba wai wani ya baka ba, k'arami ne a cikin k'ananun aikina na shiga ciki, to miye a ciki? Daga kai har Umaimah a gabana kuka girma, dukanku k'annai na ne to sai me."

Juyowa Amar yayi ya mayar da k'ofar ya rufe ya tunkari inda yake jin k'arar motoci yana fad'in "Naji dan Allah zan d'ora, je taso sauran."

A wurin Junaid ma haka abun yake bayan ya gama kiranshi gwauro sannan ya iza k'eyarshi gaba, Jibril ma haka taso shi gaba yayi har da Jamil ma bai bari a baya ba, yana dawowa k'ofar gida ya same su mai gadi na kunna musu wuta a mangal, Jibril ne yayi wata doguwar hamma yana fad'in "Allah gamu gareka, wannan lamari sai kace a mulkin mallaka."

Junaid ne yace "Muyi fata kawai d'ora shayin nan ba kullum zai ce sai mun d'ora ba, dan in kullum ne akwai matsala wallahi."

"Shawara mai kyau." Ammar ya fad'a daga bayansu, saida ya k'araso yace "Yanzu ku haihuwar da aka min ita ce ba zaku iya tayani farin ciki ba duk kuke k'ananan maganganu, sai yaran sun girma kuma kuce zaku dakesu wai sunyi ba daidai ba, to duk uban da bai tayani murna yanzu ba yace zai dakar min yara Allah shari'a ni dashi daga nan har tahatas-sara."

Junaid ne yace "Allah ya baka hak'uri duniyar Amna, farin ciki mu ai mun fika dan mu aka ma haihuwa."

Kallon jamil yayi yace "Jamalun (rak'umi๐Ÿ˜‚, amma ya cuceka) shiga ciki ka samo k'atuwar tukunya da wake da shinkafa ka d'ora mana, zanje yanzu a samo mai yanda zai ishi kowa har ayi wanka dashi."

Jamil take ya b'ata rai kamar zaiyi kuka, shi kuma meya had'ashi da dafa wake da babbar tukunya? A ransa yayi tsaki ya shige cikin gidan kamar ya kwamtsa ihu, kallonsu yayi su kuma yace "Kuyi da jiki mana kuna abu kamar yan mata."

Amar ne ya kallesa a ransa yace "Yau ni naga ikon Allah, kuma ba damar magana wannan jaraba."

Hannu ya tara musu yace "Mai makullin mota ya ban."

Junaid da makullinshi ke tare dana d'aki ne ya mik'a mishi yace "Dan Allah yanda na baka motar nan lafiya ka dawo min da ita lafiya, kar kaje ka ja min jarfa ka sani zuwa ofishin yan sanda ko gendarmerie."

Hararanshi yayi yace "Wato ga Ammar masifaffe jarababbe d'an masifa d'an bala'i wanda aka haifa ana tsaka da yak'in duniya na farko."

K'wafa yayi ya shiga gidan Amar yace "To me ya rabaka da abinda ka fad'a d'in."

Yana d'aukar motar ya fito da gudu da gangan yayi kansu hakan yasa su

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login