Showing 78001 words to 81000 words out of 325849 words
dubashi, kunsan dai halin kayan gidan Suley sai kuwa tace babu inda zata je, wannan karan bud'e mata ido yayi yace wallahi ko a kai ne saiya d'auketa, hakan ne yasa ta shiryawa suka tafi tare da dare, wata atamfa ce a jikinta wacce a wannan zamani sai wane da wane mai sunan *ABC* a jikinta, hak'ik'a tasan mijinta namiji ne na gaske, dan duk abinda zai shigo dashi garin nan komai tsadarshi saiya fara kawo mata shi kafin ya fara siyarwa a gari, d'inkin riga da zane ne aka mata wacce rigar aka mata tattara da robo take ja sosai, kallabin daya kamata ta d'aura shi ta d'aura a k'ugu (wanda kowa yasan a zamanin iyayenmu da kakaninmu wannan ba wani abu bane dan mace ta fita kai sake, musamman idan aka ce ma anyiwa kan gyara), dama kuma ba kasafai aka cika saka gyale ba, sai dai a yafa zanin atamfar a mazaunin gyalen, maimakon ta d'ora zanin ta rufe kanta sai kawai ta ninkeshi gida biyu ta d'ora saman kafad'a, takalminta ta saka bak'ak'e k'afa ciki masu tudu sosai, inda kuma kanta ya ci uban gyara (coiffure) sai k'amshi yake da walk'iya, a haka fa suka jero suka zo har gidan duk da babu nisa, tunda suka shigo matan gidan da yara ke kallonta, hak'ik'a fa ta had'u sosai, sai dai bak'in ciki kawai da hassada ya hanaka fad'an hakan, Suley kawai ke gaisawa da su suna amsawa sama sama yana tambayar mai jiki, saida ya gama tsaf kafin Zeeya ta kalli Ramma cikin ido tace "Ya mai jikin?"
Ita ma kamar yanda ta tambaya haka ta mayar mata da "Mai jiki da sauk'i."
K'ala ba tace ba dan ita ma ba k'aunar su take ba kamar yanda basa k'aunar ta da kuma mijinta da yaranta, tun a labarin daya bata da kuma yanda yanzu suke zaune anan shekara kusan tara kenan ta fahimci haka, ita kuma duk wanda baya k'aunar mijinta da zuri'arta ita ce baya so, dan ita fa tana mugun bala'in son Suley, kawai dai tuna yanda aurensu ya kasance ne da irin zaman da sukayi yasa take jin ba zata iya neman sulhu ba ko ta kyautata mishi, mik'ewa sukayi zasu tafi tana gaba Suley ya ciro kud'i masu yawa ya aje gaban shinfid'ar Innusa yace a siya mishi magani, kullum idan ya zo ya bayar suna karb'a, amma yau Innusa daya kalli matar Suley ya ga ta take nashi matan har biyu, ga uban shirin da tayi sai ranshi ya b'ace, d'aukar kud'in yayi ya watso mishi yana fad'in "D'auki tsiyarka bana so, da can kai kake siya min maganin, ni zaka wa birgar mata, to bana son alfarmarka, dan wannan kud'in ganinsu nake kamar alfarma ce daga gareka, ni kuma duk wata alfarma da zata fito daga wajenka bana buk'atar ta a gidan duniyar nan, Suley babu ni babu kai wallahi na tsaneka."
Zeeya da tunda ya fara magana ta dawo ta tsaya take kallonshi , kallon Suley tayi taga sai doka murmushi take yana girgiza kai, a hankali yace "Allah ya baka lafiya kai dai, nasan zafin ciwo ne."
Haushi ne yasa taji kamar ta mare shi, dan haka ita ta kalli Innusa tace "Ka ce baka son alfarma kowace iri ce indai daga *Suleyy* ta fito?"
Kallonta Suley yayi saboda wani bala'in dad'i da yaji sunanshi yayi a bakinta, bai tab'a jin sunan cikin nutsuwa ba kamar yau, Innusa ne yace "Eh haka nace, ke ba tashi ma kaf zuri'ar shi da zuri'ata ba ma buk'ata, kuma ko bayan raina ban lamunce wani daga cikin tsatsona ya nemi alfarma ko taimakon zuri'ar Suley ba."
Murmushi tayi tace "Ni kuma Zeeya'atu muddin ina numfashi a doran k'asa sai na saka neman alfarmar Suley, idan haka bata faru ba to ka sani zuri'ar ka zata nemi taimakon zuri'ar Suley da ikon Allah, ka rubuta wannan ka aje ka kuma d'auka yanzu fad'an tsakani na da kai ne ba da mijina ba, dan shi yafi k'arfin ajinka yanzu."
Tana fad'a ta juya ta kama hannun Suley kamar yaro suka fita, kallonta kawai yake yana mamakinta, shin abinda aka mishi ne ya b'ata mata rai? To meyasa? Saboda tana sona? To meyasa bata nuna min soyayyar? Da haka suka k'arasa gida har ciki d'aki kafin ta saki hannunshi, ganin kallon da yake mata yasa ta fara cire shirin jikinta dan ta rage ma kanta nauyi, Suley na ganin haka saiya durmiya da ita duniyar maji dad'i daya jima har ya manta rabon da yaje can d'in, ita kanta fa ta gane tayi kewarshi sosai, *wannan rana*, *wannan dare*, shine ya shiga cikin tarihin rayuwar aurensu da ba zasu tab'a mantawa ba, kwana sukayi suna fad'awa juna kalamai masu taushi, kwana sukayi suna gajiyar da junansu da nuna yanda sukayi kewar juna, yan uku ma sai d'akin Husseina suka kwana da sukaji iyayen na su sun k'i bud'e musu k'ofa.
*Abu* kamar ya canza ashe ba haka bane, dan tunda gari ya waye Suley ya fahimci hakan, har yanzu dai ba wata girmamawa tsakaninsu, sai dai duk wannan billin rashin mutumcin da d'aga mishi murya ta daina, abinci ma yanzu har na safiya kawo mishi take ko ta aika cikin yaran wani ya kai mishi, idan an kwana biyu kuma ta kan ziyarce shi har d'akin shi ya d'an samu nutsuwa, kuma duk da haka tana nan tana tunanin hanyar da zata saka Innusa neman alfarma ko taimako wata rana, tana ji a jikinta zamani zai zo da komai zai zama ko dai d'an kud'i ko kuma alfarma, da wannan harta samu tsayayyar magana ta kuma tsaya a kanta.
A cikin shekaru *goma sha biyu* Zeeya bata sake haihuwa ba sai b'ari data dinga yi har sau biyar, hakan yasa tace ma Suley ta hak'ura da haihuwar kawai Allah ya raya mata ukun ma, tuni kuma lokacin ta juya akalar burin kowa izuwa nata burin, tun farko data nuna ga aikin da take su suyi basuyi mata musu ba, dan dama ita ce mala'ikan gidan mai horo, dan Abbansu babu ruwanshi tsakaninsu dashi wasa da dariya ne, amma ita babu wannan sai had'e fuska kamar sojiya,π Hassan ya duk'ufa nashi karatun inda yana kammalawa kafin ya samu aiki tace ai dole yayi aure, har Suley yace mata da son samu ne a aurar dasu baki d'aya, amma gudun kar ya kawo mata zab'inshi wacce zata zo ta sauya mata ra'ayin yara daga yanda suke mata biyayya yasa ta k'i yarda, haka yaran suka nunawa mahaifinshi ya rabu da ita kawai zasu mata biyayya, kuma kullum dama idan ya so mata magana akan tsaurin da take musu su ke nuna babu komai, saiya zab'i yayi shiru dan kar yaran su fahimci akwai rashin jituwa tsakaninsu da har zai saka su dinga saka bakinsu a al'amarinsu, *Sa'ada* yar aminiyarta ce wacce ke Agadez ita ma, sanin babu ruwanta ita da yarinyar tana musu kallon kidahumai yasa ta nema mishi aurenta, duk ba'a b'ata lokaci ba akayi komai aka gama, kasancewar tana karatu yasa bayan auren aka nema mata gurbin karatu anan ta ci gaba, duk da babu soyayya tsakaninsu suna mutumta junansu da girmamawa, baifi wata d'aya da aurensu ba Allah ya bata cikin ' yan biyu, lokacin kuma Hussein ya dawo gida hutu shima aka fara maganar aure, sai dai tace bata ga yarinyar data dace da Hussein ba, tana buk'atar yarinya wacce bata da wayewa da zurfin ilimi ta yanda ba zata damu ko saka ma rayuwar d'an ta ido ba, sannan wacce bata da wani gata ta yanda ko ya daketa zai daki banza (π) dan ta sanshi da zuciya, yana da kwana biyar da zuwa ya tuk'a Hajia da kanshi ya kaita bikin 'yar k'awarta a Zinder, to fa anan ta had'u da *Zeinabu* a cikin k'awayen amarya take, duk yanda ta so ta kasance haka take, bugu da k'ari iyayenta sun rasu tana hannun kakarta ne *Inna* wacce ta haifi Babanta, su ma dai ba'a d'auki lokaci ba aka fara shirye shirye, su suna ganin zasu shiga babban gida ne, dan wannan lokacin *Alhaji Suleymane Hassan Gaga* ya zama d'an kasuwa lamba d'aya wanda ya zama komai da ruwanka, kampanin buga ledoji, kampanin sarrafa pliwa da sukari, kampanin sarrafa duk wani abu daya shafi roba irinsu robobi, bokiti tabarma da takalma na roba, gidajen mai wanda lokacin basuyi yawa sosai ba, baya ga shaguna ba adadi, da kuma kampaninshi na buga atamfofin dake garin *Niamey* , ya dai zama kicima shima, dan haka suke cewa kakarsu ya yanke sak'a, *(kuna musu kallon biri suna muku kallon bishiyar hawa)*, lokacin da aka saka ne ya bawa Hussein damar yin tafiya kafin lokacin, duka wata biyu yayi sai suka zo Zinder za ayi *18 DΓ©cembre* anan, bayan an kammala ana ta shirye shiryen komawa Hajia tace dole ya kira Zeinabu yaje ya sameta su gaisa karya yarda ya bar garin nan basu ga juna ba, Hussein ya kira Zeinabu da yar wayarta yace ta zo su gaisa kafin ya wuce dan shi ko gidansu bai sani ba saita waya dama suke gaisawa, Inna da rawar k'afa ita ta tayata shiryawa aka fesa mata turaruka sannan ta tafi a taxi, haka taje compagnie wajenshi babu mai tunanin faruwar wani abu a cikinsu, turarukan data fesa yasa hankalin Hussein tashi, hakan ya ingizashi har yayi abinda bai tab'a yi ba, duk da yaga Zeinabu kuma bata wani birgeshi ba, amma hakan ya kawar da budurcinta a wannan ranar, duk da ta so bijire masa amma daya tuna mata shine zai aureta sai tayi shiru ita ma, a wannan tarraya ne aka samu cikin *Junaid*.
Ana gobe d'aurin aure Inna taga laulayin Zeinabu yayi yawa, tana dubata ta gane ciki ne da ita, ko da ta tambayeta wane shegen ne? Ta fad'a mata wanda zata aura saida ta sauke ajiyar zuciya, nan tasa ta kirashi a waya wai yazo, ba tare da shakku ba yace idan ya zo me zai mata? Inna dai da taga yaron fitananne ne ba zai zo ba sai kawai ta amshi wayar ta fad'a mishi komai tare da cewa ita zata sanar ma da iyayenshi, nan fa hankalinshi ya tashi dan ba zai ce k'arya bane, sulhu ya nema anan ne fa Inna tace zata rufa asiri amma dole ya biyata, nan tace tunda dama ba mataimaki gareta ba to ya d'auke mata abinci da sutura, ba musu ya amince da hakan inda washe gari aka d'aura aure sukayi gum da bakinsu.
Bayan aurensu da wata uku Sa'ada ta haihu kuma 'yan biyu, *Ammar* da *Amar*, Hajia na d'ora ido a kansu Amar ne yafi shiga ranta, tana kallonshi kawai taji kamar yaranta ne take kallo lokacin data haihu, Ammar kuma daya cika asibitin da kuka sai take ta mishi sharri wanda mutane ke dariya ana ganin na kaka da jika ne, to fa da irin wannan hantarar ta gina rashin jituwa tsakaninta da Ammar, iyayensu ma da suka gane tafi k'aunar Amar sai suka fi mayar da hankalinsu kanshi, indai suna gabanta duk abinda Ammar zaiyi sai sun hantareshi da zaginshi dan jin dad'in ta, Amar kuma baya laifi a wajensu dan ko bata gidan babu mai dukanshi, dan tsaf zata gurza maka rashin mutumci ko uban daya haife shi ne, a wannan lokacin cikin Zeinabu na wata hud'u, Husseina ma sai tace Labaran yayi aure dan tunda yasan ta hanyar da aka haifeshi ya mayar da hankalinshi kan kasuwanci harya tsaya da kafarshi, da k'yar ya samu yarinya mai nutsuwa da hankali wato *Soueiba*, amma data amince tana son shi tsaf ya fad'a mata tarihinshi bayan ta mishi alk'awarin ba zata gujeshi ba, haka tace taji ta gani kuma daga shi har mahaifiyarshi babu mai laifi, girma da mutumcin Suley da ake gani a gari yasa iyayenta basu wani zurfafa bincike ba suka bashi aurenta, dan dayawa d'auka suke Husseina matar Suley ce saboda har wannan lokacin miji bai samu ba, suma anyi aure lafiya lau lokacin kuma aka haifi Junaid, kuma suna da wata tara da aure ta haihu, bayan watanni ma Soueiba ta haifi Jibril.
*Bayan shekaru biyar* Gambo data durmiyashi cikin siyasa ya samu nutsuwa, yana zuwa tace mishi ta mishi mata aure zaiyi, bai ja da maganar ba shima ya amince, *Hadiza*, ita ce yarinyar data zab'a mishi wacce anan unguwarsu take, sam Hadiza bata son shi dan tana da wanda take so, amma fin k'arfi da ganin matsayinshi yasa babu yanda ta iya, had'a kai 'yan uku sukayi suka had'a k'arfi da k'arfe suka gwangwaza sabon gini na gani na fad'a a wannan zamani, a *ADS* suka buga wannan gini tun lokacin unguwar babu mutane dayawa sai wane da wane, haka akayi tsari mai kyau a lokacin aka d'aura auren Gambo, tare suka dawo gidan dukansu harda su Labaran da suke jin ba zasu iya rayuwa da su ba dan sun zama d'aya, Zeeya tayi farin ciki da hura hanci da k'afafa ganin gidan da yaranta suka gina, sai dai bata ji dad'in tarewarsu tare da su Husseina ba sai taga kamar sun zamar mata k'arfen k'afa.
*I β€ u true fan's*
10/06/2020 Γ 12:07 - Ummulkhairi: π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨
*BADAK'ALA*
π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
π¨βπ©βπ§βπ¦ _*AHALI NA*_π¨βπ©βπ§βπ¦
π³πͺ *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```
_Bismillahir rahamanir rahim_
_14_
Tunda Hadiza ta tare gidan ta fahimci sauran matan da ma mutanen gidan baki d'aya hak'uri suke da tsohuwar gidan, ita kuma sai take ganin ba zata iya ba gaskiya, domin kuwa ba zatayi hak'uri da tilasta mata da akayi ba ta auri d'an ta, sannan kuma tayi hak'uri da rashin mutumcin da uwarshi ke darzawa a gidan, duk da bata nuna mishi k'iyayya a zahiri amma dai da gani kasan ba wai dan tana so bane take zaune da shi, dan ko mu'amuma ta aure ya nemeta zakaga tana irin gani kayi yanda zakayi kawai na kama gabana take mishi, haka zaka ga tana wani kakkawar da kai tana gunguni da k'ananun tsaki da baya fitowa fili, ya jima da fahimtar hakan, shi kuma Allah ya san zuciyarshi baisan lokacin data shiga ta shi zuciyar ba, dan haka yake k'ok'ari sosai wajen faranta mata rai duk da bai cika zama tare da su ba, kulawar da yake nuna mata da kaffa-kaffa da rashin son b'acin ranta yasa Hajia lura da hakan, nan ita ma saita fara kafa mata k'ahon zuk'a ta hanyar nuna mata tsana a fili da cewa bata isa ta rabata da d'an ta ba ko da me ta shigo, sam bata kula ta saboda ko ba komai babba ce ita kuma ta haifi mijinta, sai dai ita kuma bata cika yin irin bautar da take saka Zeinabu da Soueiba ba da Sa'ada, ko sun fara aikin tare zata zame ta kawo na ta fi'ilin, a lokacin Sa'ada ita ma hak'uri take sosai, badan ma karatun ta data saka gaba ba wanda Hajiar ta so datseshi, amma da k'yar Hassan ya fad'awa Suley daya fahimci tana son karatun sannan suka shawo kan matsalar, duk da jimawar da tayi bata samu ciki ba hakan bai damu Hajia ba, dan ita a ganinta ma hakan daidai ne, dan yanda ita kad'ai ma ta mallake mata d'a ina ga ta haihu, saidai bata d'aga musu k'afa har zuwa lokacin, duk wata hidima ta gidan sune har da hidimar ita kanta, idan ka same su da rana zaka rantse masu aiki ne ba matan gidan ba, gashi kuma a lokacin Allah yasa duk mazajen nasu babu wanda bai samu k'arin matsayi ba, amma haka suke rayuwar k'ask'anci kamar bayi, ko fita zasuyi sai Hajia ta bada izini, dan haka tun kana jibi zaka fita kake sanar da ita dan ta baka lokacin data ke so, girman ciki ko tsufanshi baya sa ta sarara maka da aikin gida, saika haihu kawai kake da damar yin jego na sati d'aya shima saboda idon mutane, wani ikon Allah kuma har saida Hadiza ta shekara *shida* a gidan kafin Allah ya bata cikin su Hamna, ciki ne daya bata wahala sosai, hakan yasa fa Gambo ya rufe ido ya shirya sai kawai Hajia ganinshi tayi da kaya yace zai tafi da matarshi can ya samu k'wararrin likitoci da zasu dinga dubata, a lokacin Hajia bata iya cewa komai ba saboda Suley dake wurin kuma yace ba komai su tafi Allah ya tsare, daga lokacin ta sa k'afar wando d'aya da su dukansu, ko kiranta sukayi a waya dan su gaisheta sai dai ta kashe kiran, sam ta fita a lamarinsu ta zura musu ido, shi kuma yana can duk da yana damuwa sosai da hushin da Hajiar keyi amma baya hana shi kulawa da ita, sosai yake nuna mata soyayya, amma zuciyarta kamar ta shed'an sam ta k'i saduda ta so shi daidai da k'wayar zarra, suna haka har ta haihu ta samu *Hamna* da *Amna*, yara ne da za ace basuyi goshi ba a wajen Hajia, dan da suka dawo ma dan ayi suna anan ko kallon yaran batayi ba, hakan baya musu dad'i amma ya zasuyi daya wuce rarrashi harta yafe musu, abu ya k'i ci ya k'i cinyewa, sai Hadiza tayi anfani da wannan dama ta hanyar nuna mishi gwara ya rabu da ita danya shirya da mahaifiyarshi, tambayar daya jefa mata a lokacin tasa t saurin kallonshi, domin kuwa cewa yayi "Har yanzu na kasa samun shiga zuciyarki ko?"
Kame kame kawai ta dinga yi masa har yace ta fad'a mishi gaskiya tsakaninta da Allah tana son zama da shi ko bata so, ganin ba zata iya tauye kanta ba yasa ta fad'a mishi gaskiya hak'uri take amma bata sonshi har yanzu,