Showing 249001 words to 252000 words out of 325849 words

Chapter 84 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

589

Middle Ads

duk d'aya, amma Hajia ta damu sosai da rashin dawowar har ta fara fad'a tana cewa akwai abinda aka masa, kullum ya kirata sai dai ya mata shirmenshi ya mata kalaman soyayya yace mata zai zo idan lokaci yayi, ana haka Alhaji ya wayi gari babu lafiya, mutumin da bai tab'a ciwo ba, hakan yasa yanzu ko da ya kwanta sai abun ya masa kwaf yayi yawa, dan farko ma da aka d'aukeshi aka kaishi asibiti baisan halin da yake ciki ba, a ranar hankalin kowa ba kwance ba, asibiti kuma sun ce ayi gaggawar kaishi Niamey, Gambo ne ya turo jirgi musamman tare da lieutenant da Hajia suka tafi dashi, sai colonel da suka samu acan garin, saida aka kwana biyu Ammar yasan abinda ke faruwa, a ranar shima ya shirya ya taho hankali a tashe.

Asibiti ya wuce kai tsaye a taxi, colonel kad'ai ya iya kallonsa yace "Ammar kai ne? Yanzu ka shigo garin?"

Idonshi akan Alhaji dake kwance ido rufe duk jikinshi na'ura ce yace "Eh kawu, ya jikinshi? Me ya same shi ne?"

Kafin yayi magana Hajia ta fad'a kan kafad'arshi tana kuka, hannunshi ya d'ora bayanta yana shafata yana fad'in "Ya isa Hajia ta, ban sanki da raguwar zuciya ba fa, ko kin manta ke ce kakata?"

D'agowa tayi tana share hawaye da gyalenta tace "Tsoro nake ji Ammar, mutuwa karta rabani da Alhaji na, har yanzu ban nemi gafararsa ba."

Kallon lieutenant yayi da colonel sai kawai suka mishi alamar ya fita da ita, a hankali yana rumgume da ita ya jata suka bar d'akin, a k'ofar d'akin suka zauna kan kujera ta k'arfe mai sulb'i kamar zaiba, rik'e yake da hannayenta yace "Hajiata, kiyi shiru ki daina kukan to, babu abinda zai same shi zai tashi, taya ma zai tafi ya barki bayan shekarun da kuka d'auka, ai ke dashi mutu ka raba ne."

Kallonshi tayi cikin wani kukan tace "Kana cewa ba zai barni ba kuma gashi kace sai mutuwa ce zata raba mu, to idan fa lokacinta ne yayi?"

Saida ya k'ara matse hannunta sosai yana kallon k'wayar idonta yace "Hajia, ke da Alhaji kun ci nasarar rayuwa, kun zo duniya kun rayu tare da iyayenku, kun girma kuka rayu da 'ya'yanku cikin gata da kulawa, sannan yanzu kuna tare da jikoki da yaran jikokinku, kun ci ribar rayuwa sosai, ku godewa Allah daya baku arzik'i na gidan duniya, wasu sun rayu da kud'i babu 'ya'ya, wasu sun rayu da yara babu kud'i sanadiyar talauci yasa yaran fad'awa mummunan rayuwa, wasu kuma ya basu komai kamar ku, Hajiata, a familynki babu irin mai matsayin da babu, colonel na soja, kina da lieutenant na douanes, kina da babban k'usa a cikin siyasa, kina da babban professeur da da likita, kina da ma'aikacin ga wanda yake karantar shari'a, ga k'anwarmu dake son zama yar sanda, ga mai kwalliya ga yar kassuwa ga wacce ke son fitowa a alk'ali, sannan ga k'aramin k'ananmu wanda tun yanzu ya zama ustaz kuma yake burin zama babban malami da dai sauransu Hajia, kuma duk k'ok'arinku ne ya janyo hakan, ni kam Hajia me zaisa kuyi bak'in ciki ne a sanda zaku bar duniyar nan wacce ko ba dad'e ko ba jima dai sai an barta."

Kallon idonshi tayi sai kayi ta saki murmushi, ita ma rik'e hannunshi tayi sosai tace "In fad'a maka gaskiya Ammar?"

Kai ya d'aga mata alamar eh, cikin rad'a tace "A gaskiya da bana son mutuwa ko kad'an, amma yanzu daka tunasar dani yawan zuri'ata da kuma matakai na rayuwa da suka taka a rayuwarsu sai naji ko yanzu na mutu banda damuwa, saboda nasan ko ba dukanku ba dole zan samu tsirarun da zasu bini da addu'a ta alkairi."

Murmushi yayi sosai tare da sakin hannayenta yace "Bari na duba jikin Alhajin."

Jinjina kai tayi ya shiga ciki, Alhamdulillah kam jikin a lokacin yayi dama, sai dai dukansu babu mai tunanin su bar wurin nan da Alhaji, dan kuwa su manya ne sun san komai shi kuma Ammar likita ne yasan yanayin, yanda suka ga Alhaji yayi yasa duk suka sare da al'amarin, tubarkallah wani kyau ne aka zubo mishi yayi jawur dashi, ga kumburi da k'afafunsa sukayi, haka dai daya farka suka sha hira shi da Ammar har da dariya sukeyi, da dare iyayen sun fita sai Ammar da Hajia zaune, da hannunshi ya bashi abinci yana idawa ya aje plate d'in, har zai kwantar dashi sai kuma yace "Alhaji zauna ka ci gaba da kallon Hajiarka, na yau dai kawai na danne kishina."

Dukansu murmushi sukayi sai Alhaji daya kamo hannunshi yana sauke numfashi, saida ya saisaita nutsuwarsa da numfashinshi kafin yace "Ammar, dan Allah ku kula da kanku sannan ku rik'e zumunci, kai ne babba a yaran nan ka zama mai tsayawa kan lamuransu, Ammar ka rage zuciya da saurin hushi, sannan ka ci gaba da biyayya wa iyayenka, sannan ka..."

Sai kuma yayi shiru, dukansu ido suka sakar masa hakan yasa yayi dariya ya kalli Hajia yace "Ka kula min da Hajia Zeeya'atu na, kakar nan taka babu wanda ya iyata sama dani, ni ne mijinta anan kuma ni zan zama mijinta a lahira ma, ta dace dani, nima kuma na dace da kayata."

Cike da tabbatarwa yace "Insha Allah zanyi Alhaji."

Yanda ya k'arashe yana dariya yasa Hajia fashewa da kuka, d'ora kanta tayi kan k'afafunshi dake mik'e, dafa kanta yayi yace "Bana son ganin kukanki Zeeya'atu, ki daina kinji karki sani kuka nima."

Ba tare data d'ago ba cikin kuka tace "Tun bayan rasuwar iyayena a bakinka kad'ai nake jin sunan Zeeya'atu, Alhaji bana so na daina jin sautin nan, ka ci gaba da kirana haka dan Allah, hakan zaisa naji a raina akwai mutum d'aya daya isa dani kuma yake da iko a kaina."

Kallon Ammar yayi sukayi murmushi, k'ara shafa kanta yayi yana fad'in "Zeeya'atu na, Zeeya'atu na ki daina kuka kinji, bana son ganin hawayenki Zeeya'atu."

D'agowa tayi ta kalli tace "Zan iya yanzu Ammar?"

Fahimtar inda maganarta ta dosa yasa shi d'aga mata kai yace "Yanzu ne lokacin daya dace Hajia."

Jinjina masa kai tayi sannan ta kalli Alhaji, a hankali ta mik'e daga kan kujerar ta tureta baya, *me zai faru? Wace rana ce yau? Wane babban tarihi ne haka?* Hajia Zeeya'atu da kanta ce k'asa akan gwiyoyinta biyu a gaban Alhaji Suley, ko kuma nace muku Suley, hawaye a idonta cikin nadama da neman yafiya ta k'ara fashewa da kuka tace "Ka yafe min Alhaji na, ka yafe min dan Allah ba dan halina ba, in dan halina ne wallahi ko kallo ban isheka ba, na muzguna maka a rayuwa, na cutar da kai fiye da kima, na wulak'antaka na tozarta darajarka ta d'an adam, na ci zarafinka tare da yaga rigar mutumcinka, na yi wasar kura da rayuwarka, na..."

Hannunta ya rik'o da sauri yace "Zeeya'atu, ya isa haka kinji, na yafe miki duniya da lahira, Zeeya'atu ban tab'a rik'eki duk abinda kike min ba, da farko ina miki uziri da d'aga miki k'afa saboda hallacin mahaifinki gare ni, amma daga sanda na bud'a idona naga duk girman gidan nan a cike yake da mutane, kuma kaso biyu daga cikin uku duk ke ce tushen samuwarsu sai kawai naji na k'ara k'aunarki, sannan naji na yafe miki komai da kika min, dan haka karki damu kan wannan Zeeya."

Kallonshi tayi sai yace "Tashi dan Allah kar yaran nan su shigo su ganki haka, sai kisa su d'aureni na gurfanar musu da uwa, kinsan fa babu muk'amin da babu a 'ya'ya da jikokinki."

Cikin turo baki na shagwab'a ta mik'e tana fad'in "Ai da kai da kaya duk mallakar wuya ne, kuma sun samu matsayin da suka samu ne saboda samun jajirtaccen uba kamar ka."

Saida ta zauna ta kalli Ammar tace "Na fad'a maka dama shi d'in na musamman ne, hak'uri ne dashi kamar damo."

Dariya sukayi sai Alhaji daya mata wani kallo yace "Ke kuma akwai hauka a kanki Zeeya."

Dariya Ammar yayi yace "Hum! Ashe gado nayi, shiyasa har matata ke min kallon mahaukaci."

Dariya Alhaji yayi sai Hajia data mishi dak'uwa, hannu Alhaji ya mik'awa Ammar ya rik'e gam yana murmushi yace "Ko mutuwa ta zo min yanzu babu sauran k'unci a tattare da zuciya ta, kana tare dani ka min alk'awarin kula da yan uwanka, sannan yau Hajia ta nemi affuwata, alamu ne na ta d'auki hanyar gyara halayenta marasa kyau, hakan ya sani farin ciki, zan tafi gidana na gaskuya ba tare da tunanin zata ci gaba da takura kowa ba, ta mulki yaran kuma tana so ta mulki jikoki, abu ne ba mai yiwu ba, shiyasa ina jiye mata ranar da zata fara kuka kan rashin cikar burin da wani baiyi ba, Alhamdulillah Allah."

*Da asuba* mazan duk sun tafi masallaci sai Hajia a d'akin tayi sallah, a hankali ta d'ago kai ta kalleshi kwance ido rufe, ta d'anyi mamaki jin bai nemi ta taimakasa ya tashi yayi alwala ba, dan ko ranar da suka zo jikin ma babu dad'i saida aka tayar dadhi yayi sallah, ci gaba tayi da jan carbinta har zuwa wani lokacin, da sauri ta juya jin n'aurar nan ta canza k'ara daga yi d'aya bayan d'aya zuwa da sauri babu k'akk'auci, sam sai bata damu ba kawai ta ci gaba da abinda take, suna shigowa suka shiga kallon n'aurar suna kallon juna, Ammar daya kafe shi da ido ne ya d'an matsa kusan gadon, wani kallon tsoro ne yake masa har saida ya kamo wuyan hannunsa ya rik'e yana sauraran harbawar jijiyarshi, da sauri ya juyo ya kallesu ya musu alama da su fitar da Hajia waje, colonel ne ya d'an fita saiya lek'o yace "Hajia ana magana."

Tashi tayi ta fita sai Ammar daya shiga duba Alhaji yana kallon n'aurar dake haska bugun zuciya dana numfashi, dafe hannayenshi yayi kan gadon yana sauke numfashi, lieutenant ya matso yace "Ammar."

Saida ya sake furzar da iska ya d'ago idonshi sunyi ja ya kalleshi, cikin amon murya mai gindayarwa yace "Bari na dubo likitocin."

Ya taka da niyyar fita saiga docteur ya shigo d'akin, zaune yayi yana kallonshi shima yana duba shi, a hankali kuma saiya shiga cire mishi duk wasu wayoyi da abinda aka mak'ala mishi.


*Alhamdulillah*
14/10/2020 Γ  00:58 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_57_


Mutuwa mai raba tsakani, sun d'auka Hajia zata iya ja musu matsala ita ma, amma sai tayi juriyar da basuyi tunaninta ba, kasancewar Alhaji babban mutum yasa cikin k'ank'anin lokaci mutuwarshi ta zaga garuruwa da dama, an shirya kaishi gidanshi na gaskiya a Maradi, dangi sun jijjiga anyi kuka kamar ba za'a tsagaita ba, magana d'aya ce ke fita daga bakin kowa ita ce "Alhaji akwai hak'uri, ga faran faran da kowa, ga hira idan kuka zauna dashi babu ruwanshi sannan ga alkairi."

*04:30* na yamma jirginsu ya sauka, a filin jirgin aka taresu daga can zuwa mak'abarta, a wannan rana kuma a wannan lokaci duk wanda ya fito da niyyar zuwa wani wurin kuma ya had'u da motocin yan rakiyar nan, to fa dole ya tsaya ya gyara zama dan in mai saurin bacci ne ma saika fara gyangyad'i kafin ka iya wuce, mutune dai ba wata tsiya ba kace duka garin ne aka taru, mutane har saida suka koma kallon al'ajabi ba wai jimamin mutuwar ba, babu motar da babu a taron nan, idan aka wuce sai kaji kamar k'asa na girgizawa saboda rubdugun mutane, ance alamun kyakwayan k'arshe ne jama'a ma, sai dai fatan dacewa kawai amma ta wannan b'angaren Alhaji ya cinyesu har ma da d'oriya akai, hakan ma dan wasu suna wasu garuruwa basu samu halarta bane.

Gidan mutuwa ya zama kamar gidan biki, wannan jimami daga sanda aka kwantar da bijimin sa aka yanka aka shiga kiciniyar sarrafa shi, sai ga mata sun d'ora guma guman tukane na d'ori tare da girke buhun albassa ana ta yankewa, abu fa yayi k'amari sam kamar ba mutuwa bace a kayi, jimamin dai anbar na kusa dashi suyi, amma hira ta b'arke tsakanin mutane hira kuma ta duniya, ko da rana tayi aka dinga raba abinci da nama har ka ci kayi guzuri dashi, b'angare d'aya kuma masu karb'ar gaisuwa suna karb'a. *Kwana tashi* sai gashi an kwashe kwana uku, Hamna dama tare da mahaifinta da tanti Aissata suka zo, sai Amna data addabi Ammar tana so ta zo, da yace ma zai tura mata kud'i su taho tace ita ya barsu tana da kawai zata taho, da ita akayi sadakar uku wacce ta zo da jimamin mutuwar, mutane kuma suna kallonta da magana kan yanda ta k'ara girgijewa ta zama hamshak'iyar mace, haka ma yaranta sun zama yaran gwarawaπŸ˜‚ dumur dumur dasu tubarkallah.

*A kwana na hud'u* tunda safe Hassana da Husseina da suka fi kowa jimamin rasa d'an uwansu d'aya daya rage musu suka kira lieutenant, Hassana ce take fad'a masa cewa "Dan Allah Alhaji maganar abincin nan yau dai kawai a canza, idan so samu ne a dafa wake na sadaka, dan ni abun ya fara damuwa wallahi, gidan rasuwa kamar gidan biki, wanda ya zo jiya shine zai dawo yau kuma ba zaka ji yayi addu'a ga mamacin ba, ba jimami babu rakashi da addu'a, shikenan dai shi daya tafi shi ya tafi kawai, ina ganin idan aka rage tukanen da canza abinci kaga wani abu ya sauya."

Cikin ladabi lieutenant yace "To Hajka ya za ayi kenan? Har munyi waya da wanda yake kawo mana shanun, yanzu nasan yana daf da kawowa kuma babu dad'i ace ya koma da ita."

Husseina ce ta kalleshi tace "To ai ba sai an yanka ba, za'a iya ajewa har wani lokacin."

Murmushi yayi ya kalleta yace "Hajia mu zamuyi kiyonta ne? Kawai ku hak'ura na yau kad'ai sai a dakata."

Shiru sukayi cikin rashin jin dad'i, fita yayi k'ofar gida sai Zeituna dake jinsu tana wankewa Fatima hannaye ta matso tace "Hajia indai kuna son a dakatar dashi yau to ba Abban Fatima zaku ma magana ba, dan ba zai iya ba shi."

Kallonta sukayi Husseina tace "To wa zamu fad'a ma? Shine babba yanzu kuma mai fad'a aji."

Dariya tayi tana kallon fuskokinsu tace "Ku ga Ammar, shine zai iya kawai, tsaf zai muku yanda kuke so, amma gaskiya nima abun ya fara hawa min kai na, wallahi idan ana cin abinci wani ya shigo yana addu'a ga mamacin amsawa da Ameen ma wahala yake."

Murmushi Husseina tayi tace "Kin ce wani abu kema, tabbas shi zai mana maganin al'amarin, amma akwai buk'atar mu rufe idonmu da kunnuwanmu kan abinda zai fad'a."

Daruya Zeituna tayi sai Hassana da tace "Kar mu musa ya ma mutane rashin kunya aje ana fad'armu da sharri."

Husseina ce tace "Zai aika, amma kuma Ammar yana aiki da ilimi ai, yana saka komai a muhallinsa ne."

Kafin su ce wani abu kam ya shigo gidan d'auke da Abba da yafu rigima sai Imam yana jaye dashi, kallonsu yayi yace "Hajiyoyi barkanku."

"Barka Ammar, zo." Cewar Husseina, matsowa yayi yana kallonsu yace "Allah yasa dai ba wasiyya ce zaku bar min ba kuma, dan ba zamu bari ku tafi yanzu ba ku kad'ai kuka rage mana."

Dariya sukai sai Hassana da tace "Idan mun tashi tafiya ka rik'e mu to."

"To ba laifi." Ya fad'a yana aje Abba, zai fashe da kuka ya sake yin sama dashi yana kallonshi yace "Allah ba dan mai sunanka nan ina k'aunarshi ba da na zabgeka da mari, kaga yaro sai jarabar son jiki kamar mace."

Dariya sukayi sai Husseina da tace "Kaga magana zamuyi."

Kallonsu yayi d'aya bayan d'aya yace "Wa kuke so a kashe muku?"

"Kisa kuma?" Cewar Hassana, Husseina bata damu ba dan ita kayan gidansu ne taji fiye da haka, nan ta fad'a mishi abinda suke buk'ata da tattaunawarsu da mahaifinshi, saida ya gyara tsayuwa yace "Ku fad'i me kuke so ayi to? A watsa kowa ya tafi gidanshi? Ko kuma a musu rashin mutumci mai sanyin gaske da zaisa kowa ya tafi yana jimami? Ko kuma Ko kuma ya kike so."

Da mamaki al'amarinshi Hassana tace "Yanzu duk zaka iya yin haka? To tayaya?"

Kallonta yayi yana dariya yace "Idan so kike na tashe su ta tashin hankali, barkonon tsohuwa kawai zan sa musu kowa ya watse, ko kuma na musu turaren wuta amma fa na 'ya'yan tattasai, ko kuma na samu mata na biyasu suyi fad'a kamar masu aljanu."

Kallonta yayi yana zaro ido yace "Ke Hajia abun fa dayawa da zan iya yi."

Da sauri tave "A'a to ba haka muke so ba, kawai muna so muga gidan yayi kama dana mutuwa ne."

Kallonta yayi yace "To ku dafa wake, sannan ku samo aduwa da yalo (d'ata) da magarya ku rarraba ma kowa ku ce kayan da Alhaji yafi so ne."

Yana yayi hanyar b'angarensu Hassana tace "To ai kar mahaifinka kuma yace ayi girkin."

"Ba zai ce ba." Ya fad'a ko juyowa baiyi ba, saida yayi nisa kuma ya dawo da sauri ya tsaya gabansu yace "Wai me yasa ma baku fad'a ma kowa ba sai ni?"

Kallon juna sukayi sai kawai yayi dariya yace "Na gane ma, wato ni ne marar mutumci ko?" Sake juyawa yayi yana fad'in "Allah ya shirye ka Ammar."

Yanda ya fad'a haka akayi, amma fa babu abinda aka fasa, haka dai aka samu aka kai sati d'aya, a lokacin mutane sun rage sosai wasu ma sun koma garinsu, haka ma mahaifinsu Amna ya koma tare da tanti da ita kanta Hamna, sai Ammar daya shirya tafiya yau shi ma, lieutenant ya nemi daya zauna amma saida ya kalli Ummy yace "Zan zauna Abba idan naga kowa na so."

"Kamar ya?" Shine abinda ya tambayeshi, bai ce komai ba sai kallonta da yake, Amna ma kukan shagwab'a ta

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login