Showing 18001 words to 21000 words out of 325849 words

Chapter 7 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

494

Middle Ads

"Ala wadaran naka ya lalace, to badan basu da wayo ba ai ko taron dangi ne su mishi wata rana su jijjiga shi shima ya ji jikinshi, wallahi sai kiga an zaunnnn..."

Gimtse bakinta tayi dan har ga Allah ta tsorata kuma gabanta ya fad'i lokacin data d'ora idonta akan Ammar daya had'e fuska yake kallonta ido jawur kamar kullum, Ummy da suke k'ofar d'aki tsaye tasan sai yayi magana, dan haka daga can tace "Ka wuce ka tafi inda za ka."

Amma ko kallon Ummy baiyi ba kuma har yanzu bai daina kallon Zeinabu ba yace "Idan kina ganin zasu iya ki basu shawara mana tunda kun shirya rasa 'ya'yanku."

Saida Ummy ta lumshe ido, dan tasan dama sai anyi haka, shi fa in dai maganar zata zo to sai ya fad'a ko za'a yanka shi, babbar matsalar kuma shine bai damu da girman wanda zai fad'awa ba ko kuma d'acin maganar ko rashin dacewarta, zai fad'a ne in ya so kai kayi kuka dan bak'in ciki, ko kuma ka zage shi kayi tir da halinshi shi duk d'aya ne a gun shi, takawa yayi ya nufi wajen Ummy tana ganin haka ta shige d'aki ta rufe k'ofar da makulli tana wani sabon kukan, k'ofar d'akin ya tsaya yana kallon fuskar Amar da tayi jina-jina, wani irin buga k'ofa ne yayi d'aya biyu baiyi na uku ba sannan yace "Kiyi hak'uri fa ki daina kuka, kinsan zai iya ja miki ciwon kai, daga haka kuma ake kamuwa da hawan jini ko ciwon zuciya, kina so ne ace zan nuna k'warewata na zama likitan zuciya a kan ki?"

Yana fad'in haka ya juya zai bar d'akin, cak kuma ya tsaya saboda duk baya jin dad'in ganin Ummynshi na kuka saboda shi, d'an uwan shi kuma na fitar da jini a dalilinshi, juyowa yayi ya kalli Amar dake shirin bubbuga k'ofar d'akin, sake d'auke kai yayi kuma wata zuciyar na fad'a mishi ai sai ya d'auka ka damu da shi ne, a hankali ya lumshe ido ya sauke numfashi a zuciyarshi yace "Ka damu da shi mana Ammar, ku fa ko a cikin ciki tare kuka rayu, ka d'auka kai da shi kamar kuna rayuwa ne da rai d'aya."

Bud'a ido yayi ya sake kallon Amar wanda shi ma yake so ya ga sun shirya ko dan mahaifiyarsu ta ji dad'i, kamar baya son maganar haka ya motsa bakinshi yace "Muje na wanke maka ciwonka."

Da sauri ya k'araso kusanshi ya rumgumeshi dan sam bai d'auka Ammar zai fara mishi magana ba, sosai yake ta k'ara cakume shi saboda k'auna, amma me Ammar zaiyi sai kawai ya raba kanshi da shi ya had'e rai yace "Miye haka malam sai ka b'ata min kaya da jini, muje ni dallah."

Da k'arfi ya juya ya fita Amar ya bi bayan shi yana girgiza kai, lallai a duniyar nan in har shi ya kasa fahimtar d'an uwanshi to babu mahalukin da zai iya fahimtarshi bayan wanda ya halluce shi, Husseina da Soueba da dariya suka bisu har Husseina na fad'in "Kin gani ko Zeinabu, shiyasa shiga fad'an yara ke da kunya wallahi, dan Allah ki daina damuwa da rayuwarsu, mu yarda cewa haka Allah ya hallici Ammar."

Tab'e baki tayi tace "Hum! Ni bana so na ji kuna cewa wai yara, yaran nan fa ba dan dogon karatu da sukayi ba wallahi da yanzu sun aje mana jikoki bibbiyu ko sama da haka."

Dariya Zeinabu tayi tace "Gashi kema kin fad'a kince yara."

Shigowar Junaid cikin sabon shiri yasa suka kalleshi a tare, shima dai fuskar nan a had'e take dan ranshi ya b'ace sosai, Jamil ya kalla wanda ke zaune yana latsa wayarshi yace "Kai in za ka je ka taso mu tafi."

Mik'ewa ya yi yace "Mu tafi kawai."

"Ina kuma zaku je?" Cewar Husseina, a tak'aice Jamil yace "Gidan roumji."

Zeinabu ce tace "Inda ubanninsu suka tafi zasu je, amma babu wanda zai iya fad'a mana dalilin zuwa."

A motar Junaid suka d'auki hanya ba ko waiwaiye saboda su isa da wuri, Ammar ma wani d'aki suka shiga wanda ya ware yake zuba duk wasu kaya da suka shafi na jinya, sannan har magunguna ke akwai da kayan aiki masu mahimmanci wanda babu su a ma k'asar baki d'aya, hakan yasa baya wasa wajen kula da su, zaune Amar yayi kan gado Ammar yasa k'aramin almakashi da k'ada da yan ruwan kashe ciwo yana goge masa, babu mai kallon idon wani bare magana, saida ya gama ya duba inda ke buk'atar a rufe yasa k'aramin bandeji ya rufe mishi, ba tare daya kalleshi a yace "Kana jin jiri?"

Saida ya d'an dafe kai yace "Eh, dan da k'yar ma na kawo kaina nan, na so na ce ka goye ni amma kuma..."

Kallonshi yayi yace "Amma kuma me?"

"Kana hushi da k'aninka, d'an uwanka, shak'ik'inka, sannan abokin rayuwarka." Duk yayi maganar ne cikin marairaicewa, k'ala bai ce masa ba sai ma wasu kwalaye dayake fito da su yana son d'auko wani magani, ya sha wahala kafin ya d'auko ya bud'e ya d'auki wanda yake buk'ata ya mayar da sauran, fitowa yayi daga d'akin jim kad'an ya dawo, ruwa ya bashi a roba tare da maganin yasha, d'aya maganin kuma ya sa a cikin kofi da ruwa, saida ya gama tafasa ya mik'a mishi ya shanye ya aje kofin, ba tare daya kalli fuskarshi ba yace "Ka kwanta kan gadon nan."

Ganin ya juya zai fita yasa Amar cewa "Har zuwa wane lokaci?"

Ba tare daya juyo ba yace "Har a busa k'aho."

Murmushi kawai Amar yayi shi kuma ya fice, yana fita kuma motar shi ya fad'a ya tayar, mai gadi na bud'e k'ofa ya suri motar yayi waje, hanya ya d'auka shima kamar zai tashi sama, shi ma dai kamar su Junaid hanyar gidan roumji ya nufa, sai dai duk gudunshi bai iya riskar su Junaid ba dan sun rigashi d'aukar hanya kuma suma gudu suke sosai.

*K'arfe* 06:20 na yamma Amar ya fito cikin shiri ya samu Ummy ya mata sallama yace zai tafi shima k'auye saboda kar ran Abba ya b'ace, cike da damuwa tace "Amar kayi hak'uri mana zuwa gobe sai mu tafi tare, tunda kaga ba lafiya ne da kai ba."

Dariyar gefen labb'a yayi yace "Haba Ummy lafiya ta lau fa, ki bari naje kawai kar Abba ya ga kamar bamu ji maganar sa bane, kuma kinga dukansu fa ina kyautata zaton can suka tafi, kinga gwara nima na hanzarta na tafi ko da ana sallah magriba ne saina isa."

Cikin sanyi tace "Shikenan Amar, Allah ya tsare ka ya kare gabanka da bayanka."

Murmushi yayi sosai yace "Ameen Ummy, sai mun dawo."

"A dawo lafiya." Ta fad'a tana binshi da kallo harya fita.

Yana fita su Hamna na shigowa da motonsu dan saida suka kai d'inki sannan suka dawo gida, haka ma ba jimawa Umaima ta shigo gidan tare da drebanta, sai Jamila da ta shigo gaf da magrib daga Γ©cole.

*Gidan roumji*

Rana ta fad'i sosai su Junaid suka iso, tunda suka fito daga mota lieutenant da colonel ke kallonsu da mamaki, k'arasowa sukayi cikin mutane suka gaishesu da girmamawa tare da musu ta'aziya, sun shiga cikin gidan dan yiwa na cikin gida suma sai ga motar boss ta karyo kwana, da k'arfi ya ci burki ya kashe motar ya fito makulli da waya a hanu, ga kyau ga kyan tsari da hallita sai dai a wurina babu kyan hali, da k'akk'arfar tafiyar nan tashi ya k'araso yana sallama amma fa wanda yayi sa'a ne kad'ai ke ya ji sallamar dan kamar bai so yayi ba, saida yayi zaune ya tank'washe k'afafun shi kafin ya fara bawa na kusa da shi hannu, colonel kam daya tsura mishi ido a ranshi cewa yayi "Lallai yaro na, wannan da ace kai gΓ©nΓ©ral ne na soja da anshiga uku, ko mu dake iyayanka dai saida muka gaishe da mutane kafin muka zauna saboda wurin mutuwa ne, amma kai sai bayan ka zauna kake gaishe da wanda ke kusa da kai, humm."

Lieutenant kuma haushin Ammar ne d'in ya kusa kashe shi shiyasa ma ya d'auke kallonshi daga kan Ammar d'in dan kar zuciya ta kwashe shi ya mareshi, yana gama tashi ta'aziyar ya fara danna waya, da sauri Labaran ya kalleshi yace "Ammar ka shiga ciki mana ku gaisa da matan."

Kallonshi yayi lokaci d'aya kuma ya mayar da kallonshi kan wayar, yana kallon wayar tashi ya mik'e yasa takalminshi ya nufi cikin gidan a ranshi yana fad'in "Yanzu mutum na shiga zasu saka maka ido suna kallo, kowace burinta ka mata magana ta ji dad'i, mtssss, shiyasa na tsani shiga irin taron nan."

*Ikon Allah sai kallo, to Ammar me ka d'auki matan? Sai kace wasu tsofaffin...*😏

Yana kallonsu su Junaid suma suna kallonshi haka kowa ya gama ya fito, suna zuwa kuma wasu har sun nufi masallaci wasu kuma na alwala, suma alwala sukayi suka nufi masallacin, tare sukayi sallah suka fito, fitowar lieutenant da colonel yayi daidai da shigowar Amar cikin kwanar, lieutenant a ranshi yace "Wato yaran nan sun raina mutane ko? Amma laifin duk na waccen babban kwabon ne."

Tsaye yayi hakan yasa colonel ma tsayawa, su Junaid da Ammar na fitowa lieutenant yace su zo, Amar na ganinsu saboda ya hasko fitilar motarshi ya tsaya wajensu ya fito, cikin girmamawa yace "Abba ina wuninku, har kunyi sallah ko? Bara nima na yi alwala."

Zai wuce lieutenant ya dawo da shi baya ya kallesu dukansu yace "Wato da na ce ku taho gaba d'aya shine kowa yayi gaban kanshi, yanzu ribar me kuka ci da kuka nunawa mutane ku kanku ba had'e yake ba?"

Shiru sukayi dukansu suna kallon k'asa sai boss da idonshi ke kan wayarshi yana latsawa ya rumgume hannu d'aya, juyawa lieutenant yayi ya kalli Ammar d'in da ya ga ya mayar dashi wani d'an iska ma, wani haushi ne ya kashe shi sai kawai yasa tafin hannu ya bangaji k'eyar Ammar, bai ankara ba yaji bugun dan haka ya juyo ya kalli mahaifin nashi, had'e fuska yayi ba alamar wasa yace "Abba meye haka? Kai baka san cewa kai shine mutum ba? Duk wani abu mai mahimmanci a cikin k'wak'walwa yake, so kake kasa na rasa komai nawa?"

Hannu ya d'aga da nufin sake mazgeshi colonel yayi saurin rik'e hannunshi yace "Ba kamata yayi ace ka fara tambayar meya faru ba kafin duk wannan b'acin ran, ko baka kula da fuskar Amar bane, sannan ka dubi Junaid ma, baka tunanin ko wani abu ya samesu a hanyar?"

Fizge hannunshi yayi yana kallon Ammar yayi k'wafa kafin ya kallesu yace "To naji, wa zai fad'a mana meya faru?"

Shiru sukayi sai wuk'i-wuk'i da ido da sukeyi, Labaran ne ya kalli Jamil yace "Kai ba tambayarku ake ba kuka mana shiru?"

Jamil kam kallon Ammar yayi wanda ya ga ya kalleshi, idonshi kad'ai suka fassara mishi manufar kallonshi, dan haka ya ja baki yayi gum saboda tsoro, sai dai ya manta gaba da gabanta, colonel ne cikin tsawa yace " Wai ya ana muku magana kuka mana shiru? Shin ku yan mata ne bare ku d'auka son ku muke."

Wani kallo Ammar ya mishi yace "Idan ma yan mata ne mu sai mu tsaya muna sauraron tsofaffi irinku."

Labaran kam bushewa yayi da dariya inda lieutenant ya zabura zai bugeshi Labaran d'in ya rik'e shi, cikin dariyarshi yace "To ai gaskiya ya fad'a, tsofaffin ne mu mana."

Kamar daga sama suka ji saukar mari ji kake "Tauuuuuu."

Da sauri Junaid ya dafe kunci saboda wani mahaukacin mari da colonel ya watsa mishi yana fad'in "Iskanci kai, ana muku magana zaku d'auke mu wasu shashashu."

Lieutenant ne yace "Meye haka saboda Allah? Yanzu shine kenan yayi laifi a wurin nan? Me ya sa ba zaka mari wannan ba dake kusa da kai yana mana shak'iyanci sai wannan? Saboda a ganinka wannan ne ka haifa su kuma wad'annan duk 'ya'yan yan uwanka ne, mtsss."

Lieutenant Jamil ya kalla ya zaro ido yace "Yanzu zaku fad'a mana meya faru da har yasa ku ka k'i bin umarnin dana baku na a taho tare?"

Cikin rawar murya Jamil yace " Dama da zamu..."

Karaf Amar ya karb'a da cewa "Ni ne fa na samu had'ari akan moton wani abokina, shine da na zo gida sai aka ce su Junaid su taho saboda Ammar shi ya duba min ciwon, bayan Ummy ta zo gida kuma sai shima suka ce ya taho, ni kuma ganin duk sun taho yasa na kasa hak'ura na taho."

Colonel ne ya kalli Junaid yace "To kai kuma uban wa ya ci uwaka a bakin na ka?"

Bawan Allah Junaid sai lokacin ya d'auke hannu daga kuncinshi yace "To ni kuma waye zai dake ni a baki ina d'an soja guda."

Jinjina kai yayi yace "Da kyau to tunda kana tuna hakan."

Mayar da kallonshi yayi kan boss da ke harkar gabanshi kamar baisan sunayi ba ya kamo hannunshi yace "Soja d'an soja muje ko."

Wucewa sukayi inda suma suka bi bayansu lieutenant na jin haushin colonel saboda sam baya ganin laifin Ammar, zaka iya cewa ma yafi nuna mishi k'auna fiye da Junaid da kuma Umaima da Jamila.

Bayan sunyi sallah isha'i aka fito da abinci aka ci, lokacin ne suka fara haramar komawa gida dan sun fahimci kwana anan ba zai musu ba, har cikin gida suka samu Hajia suka fad'a mata, sam Amar bai yarda ya had'u da ita ba dan saita tambayeshi meya same shi, ita kuma k'aramin aikinta ne ta musu bala'i a gidan rasuwa, da k'yar ta yarda zata kwana dan cewa tayi zafi kasheta zaiyi kafin safiya, saida Alhaji yasa baki yace shima zai kwana anan dan bai dace ta bar wurin ba daga yanzu har zuwa kwana uku, haka dai ta hak'ura amma tace ba tayi alk'awarin zama har sadakar uku ba, nan suka juyo dukansu sai Hajia da Alhaji acan, ba tare da wata matsala ba Allah ya kawosu gida lafiya, kowa wajen na shi iyali ya nufa ya samu yayi wanka, k'arfe *10:00* na dare lieutenant Hassan da colonel Hussein da Labaran suka hallara kan babban teburin cin abinci, in dai har suna gari dama sukan had'u ko dan su tattauna matsalar data shafesu, Soueba ce yau take zuba musu duk abinda zasu ci, tana cikin zuba musu ruwa da lemu ta kalli mijinta Labaran tace "...


*Mu had'u a shafi na gaba insha Allah.*βœ‹

*Allah ka mana kyakyawan k'arshe*πŸ‘
27/05/2020 Γ  14:46 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K'URA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*


πŸ’ž _*MASOYA NA*_πŸ’•



*πŸ˜‚ Nasan za ku sha mamaki sosai ganin na dawo da ci gaban sanin masoyi, to ku kwantar da hankulanku kusha kallo kawai, duba da akwai wasu abubuwa daya kamatain ace an warwaresu tun a na farko, amma Allah bai nufa ba sai yanzu idan ya ara mana rai da lafiya, insha Allahu abun zai k'ayatar da ku fiye ma da na farko, kuma wannan shi zai zama na k'arshe da yardar Allah.*

_Bismillahir rahamanir rahim_

_1_


_Idan masu karatu basu manta ba mun tsaya a waccen labarin *Sameera* na da ciki na wata biyar, sannan Abbas na shirin had'a *Raihan* aure da *Abdul* d'an wajen Abbas mai biwa *Husnah* da zaran ta kammala secondary d'in ta, to zamu d'auki labarin daga bayan haihuwar Sameera muyi gaba insha Allah._

*Abbas* ne zaune tare da Abba (mahaifin Sameera Mus'ab) da kuma Umma (mahaifiyar Abbas Falmata) a gefensu, cikin hushi Abba yace "Ina! Wannan ma maganar banza ce, wallahi ba zan tab'a bari ku had'a *Raihan* da tsatson wannan mutumin ba, *Abba*? Ina! Ba dai d'an Abba ba wallahi, mutumin daya cutar da kai ya cuce mu gaba d'aya."

Cikin taushin murya da nutsuwa Umma tace "A gaskiya nima abin bai kwanta min a rai ba, kuma naga ma du-du-du yaron shekararshi nawa? Bai ko gama mallakar hankalin kanshi ba, sannan ita kanta Raihan d'in nawa take da har zaku fara maganar aurar da ita? Shekara goma fa, ba kwa tunanin ku zo ku tsayar da magana akan ga wanda za'a bata, a k'arshe zuciyarta ta kamu da son wani kuma ba shi ba, tunda zata ci gaba da zuwa makarantarta ai."

Abba ne yace "Wannan ma abun dubawa ne, irin wannan had'in tun da k'uruciya yana da matsala gaskiya, bansan me kuka gani ba da har kuke tunani had'a su."

Cike da kulawa *Sameera* ta kalleta tace "Hakane Umma, amma ai ba yanzu za'a musu auren ba, sai nan da shekara hud'u, kunga a lokacin ya samu cikakkiyar shekara ashirin da uku, ita kuma ta koba komai dai ta zama balagaggiya, sannan ba zamu had'a su bane haka kawai, zamu fara tambayar ra'ayin du akan lamarin."

"Yanzu in banda abinki *takwarata* ina Raihan ina wani sanin so? Ko ta amsa miki da eh wallahi idan ta mallaki hankalin kanta zata iya canza magana, 'yar shekara goma fa ake miki magana ba 'yar sha shida ba ko sama da haka."

Cikin tafasar zuci Abba yace "Kunga, ni ba k'arancin shekarun yaron bane damuwa ta, tunda ko yanzu aka mishu aure za'a samu kyakyawan sakamako daga gareshi ta hanyar zuri'a, kuma idan da shak'uwa da fahimta duk wannan ba matsala bace a tsakaninsu, kawai dai yaron ne bai min ba saboda kasancewarshi d'an mak'iyina."

A hankali *Abbas* ya d'ago ya kallesu cikin nutsuwa da girmamawa yace "Abba, Umma, sam banyi tunanin wannan maganar zata iya rasa muhalli a zuk'atanku, Abba, ko fa ubangijin daya hallicemu baya kamamu da laifin da waninmu ya aikata, ina ganin kamar rashin adalci ne da kuma dacewa ace zamu hukunta *Abdul Malik* akan laifin da mahaifinshi ne ya aikata, duba da lokacin da abun ya faru ko kanshi bai sani ba, namiji ne shi ba

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login