Showing 168001 words to 171000 words out of 325849 words

Chapter 57 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

575

Middle Ads

a yanzun zata iya sakawa lieutenant ya saketa, dan haka ta mik'e tsaye tace "Zan samo mana mafita Hamna, wannan abun ba zamu bari ya fito ba, ke dai ki ci gaba da b'oyewa kar kowa ya sani, zuwa gobe zamu san abunyi, yanzu mu fita kar a d'auka wani abun muke."

Mik'ewa tayi tana kallonta tace "Ummy me zakiyi? Dan Allah ka da ki saka kanki a had'ari saboda ni, kawai ki bari kowa ma yaji, k'addara ce wacce babu wanda ya isa ya kauce mata."

Hannunta ta kama tace "Ke dai mu tafi, ai ba kowa zai fahimci haka ba, hakk'i na ne Hamna na kula da ku, amanarku aka bani."

Fita sukayi aka ci gaba da hidimar dasu, sai dai ko kad'an babu walwala a tare dasu, Hamna kuma dake tare da k'awayen ta wanda ta gayyata lokaci bayan lokaci saita shafa cikinta, a hankali take furta kalmar "Ciki." Da haka aka gama shagalin yau sai kuma na gobe idan da rai.

*Washe gari*

Tunda asuba Ummy ta samu Hamna suka keb'ea farfajiyar gidan, saida ta gyara hijabinta da tayi sallah dashi tace "Ummy lafiya kika kirani yanzu?"

Kallonta tayi sosai tace "Hamna bacci kikayi wai?"

D'an turo baki tayi gaba ba tace komai ba, murya k'asa k'asa tace "Hamna, na samo mana mafita, amma kiyi alk'awari zakiyi duk yanda na ce?"

Cike da sangarta tace "Ummy ina ji, bacci fa nake ji har yanzu."

Da tsantsar mamaki Ummy ta kalleta tace "Hamna anya kuwa kinsan abinda kike yi, gaba d'aya fa kina nuna kamar abun bai dameki ba."

Take fara'arta ta d'auke ta kalli Ummy tace "Ummy raba dare nayi ban iya rintsa ido na ba, tunani na yafi karkata kan yanda yer uwata zata d'auki al'amarin idan taji."

Cike da damuwa Ummy tace "Hamna dole ne ki tuna yer uwarki a wannan halin, amma ni nafi tunanin wani abun daban, kinsan me nafi tunani?"

Girgiza kai tayi alamar a'a, ci gaba tayi da cewa "Hamna Hajia, kinfi kowa sanin yanda ta tsani d'an da bai fito ta hanyar aure ba, domin kuwa saboda hakane ma kika ga tana nunawa kawunku Labaran k'iyayya har da ma yayanshi, kiyi tunanin hukunci ko matakin da zata d'auka, ga kuma kawunku wanda jin hakan ba zai masa dad'i ba, sannan Ammar, Hamna a tak'aice bansan wane kallo zai yiwa al'amarin ba, ina tsoron abinda zai iya faruwa."

"To Ummy yanzu meye abunyi?" Saida ta kalli k'wayar idonta sannan tace "Hamna zan karb'i cikin nan naki, ma'ana ni ya kamata kowa yasan inada ciki, bayan kin haihu saina karb'i abinda kika haifa kamar ni na haifeshi, in kuma ba haka ba Hamna sai dai a zubar da cikin nan tun kowa baisan da maganarshi ba."

Wani irin tsamm taji jikinta yayi, sai yanzu ne ta gane girman al'amarin daya tunkarota, maimakon tace wani abu saita fashe da kuka ta rumgume Ummy, ita kanta Ummy kuka ta sanya, sun fara rera kukan kenan kuma sai Ummy ta dakata ta d'ago Hamna tace "Hamna ya kike so ayi? Wallahi bana son kowa yaji labarin nan, bayan b'acin rai da zan gani har da kunya, Hamna zanji kunya sosai ta iyayenki, ki amince da d'aya daga cikin zab'in nan Hamna."

Cikin share hawaye tace "Ummy ina jin tsoro sosai wajen zubar dashi, idan wani abu ya faru sai kin fi ganin b'acin rai."

"To kenan kin amince na zama uwar jikana?" Ummy ta fad'a tana mai kafeta da ido dan jiran amsarta, kallonta ita ma tayi tace "Amma taya haka zata faru Ummy?"

Murmushi ta mata tace "Kin manta ni likita ce? Hamna inhar kin amince wannan ba matsala bane, zamanki gidan nan ne kawai zai bamu matsala."

"Kamar yaya?" Ta sake fad'a kanta a matuk'ar d'aure, saida suka gyara tsayuwarsu da kyau sannan tace "Zan fad'awa kawunku ina da ciki, akwai tablet d'in da zan fara sha wanda zai sauya min yanayi na, daga yanzu har zuwa lokacin da cikinki zai shiga wata hud'u zaki zauna a gidan nan, amma fa sama da wannan lokacin ba k'aramar barazana bace garemu ki ci gaba da zama anan."

Yamutsa fuska tayi alamar mamaki tace "To Ummy ina zan koma? Kinsan Hajia bata barinmu fita haka kawai, bare na koma wani wuri da zama, makarantar dana shiga ma ta koyon kwalliya da yaya na samu ta barni Ummy?"

Dafa ta Ummy tayi tace "Yanzu dai mu fara da wannan, kafin tafiyar tayi nisa zamu san abunyi a gaba."

Cikin raunin murya tace "Ummy ina jin tsoro, kar wani abu ya faru kuma a d'ora miki laifin komai."

Murmushin yak'e ta mata tace "Karki damu, koma me zai faru zan d'auka, kuma in dai har zakiyi yanda nace miki to babu abinda zai faru da yardar Allah."

A hankali ta jinjina kai tace "Shikenan Ummy, zanyi duk abinda kika fad'a min."

Murmushi ta mata sosai tace "Yawwa yarinyata, yanzu da fari ki zama jaruma, duk abinda kika ji ki dinga k'ok'arin jurewa sannan kiyi gaggawar fad'a min, ko da baki jin dad'in jikinki ka da ki bari kowa ya sani idan ba ni ba, ni kuma yanzu zan bawa *Mamuda* (dreba) kud'i ya siyo min wani magani a pharmacie, idan kika karya kumallo sai ki sha."

Jinjina kai ta sakeyi sannan Ummy ta jata suka koma ciki, kamar yanda ta fad'a bayan anyi karin kumallo ta bata magani tasha sannan suka tafi wurin wuni na biyu. Da magrib lokacin da ake shirya amare dan halarta wata walimar a lokacin kuma aka shirya aka tafi wankan angaye, kasancewar wankan farko ne dangin uwa ne sukeyi yasa Jibril yana b'angaren nashi uwa, Junaid ma haka sai kuma Ammar da Amar wanda suke gidan *Zulai* wacce yaya ce ga Sa'ada sai dai ba uwa d'aya ba haka kuma ba uba d'aya ba, dan ita duk danginta da suke ciki d'aya suna Agadez, Amar ya riga Ammar isa gidan sosai, dan har saida yayi nashi wankan ya fito sula tafi da nashi abokan Ammar bai zo ba, hakan yasa dangi suka fara fad'a da tsegumi suna fad'in Ammar ya raina mutane, wasu har sunyi shirin tafiyarsu suka ji rubdugun motoci kamar zasu fasa unguwar, a k'alla mota ma tafi guda ashirin, moto kam ko tunanin k'idayasu ma bakayi, (infa baku manta ba abokanshi ma manyan mutane ne wanda na b'oye sunan wasu kuma anan gaba zan canza sunan wasu saboda tsaro), tabbas abokai sun mishi kara tun anan, kuma dama Ammar mutum ne ruwa biyu, yana kyautata alak'arshi a waje ga kuma mutanen kirki, akasin haka kuma zakaji ba dad'i, magana dai ce zai iya fad'awa koma wanene kai kuma babu ruwanshi.

Dangin sun fito waje dan ganewa idonsu amma abokan Ammar da yake akwai shak'iyai ciki kamar shi sai suka bud'awa Ammar hanya yana shiga cikin gidan suna mishi b'arin kud'i, kud'in ma sababbi kar dasu ko karyawa babu, (harkar fa ta manya ce), haka Ammar ya dinga ratsa kud'in nan wasu har takasu yake yana shiga cikin gidan, *gaba da gabanta*, sai gashi kama daga yara har uwayen suna bin bayan kud'in nan da suka ga in aka watsa ba'a komawa ta kansu suna wasoson d'auka, nan fa gidan ya hargitse da hayaniya ana ta ihu ana tsintsar kud'i, saida ya kai k'ofar ban d'akin da zai shiga wankan da taimakon jagorancin k'anwar Zulai sannan suka daina watsa kud'in, wani daga cikin abokan ne mai sunan *Pappa* ya kalli sauran yace "To mu jira shi ya fito sai mu d'ora ko."

Haka kuwa akayi, k'anwar Zulai da su Husseina ne bakin k'ofar ban d'akin suna cewa "Ammar wallahi kayi wankan kirki karka zubar da ruwan nan ka fito."

Ammar dake shirin cire dogon wandonshi jin haka yasa ya tsaya yana murmushin mugunta yace "Ya banyi tunanin haka ba? Shawara mai kyau."

Tsaf ya mayar da kayanshi jikinshi, bai tsaya komai ba ya d'auki bokitin ruwan wanda shi kanshi sabo ne Zulai ta siya, sannan kayan had'in da aka had'a cikin ruwan masu yawan gaske da kyau, uwa uba turaruka da aka zuba ciki masu tsada da k'amshi, ba b'ata lokaci ya juye ruwan a k'asa suka tafi a banza sannan ya aje bokitin ya fito, sana jin bud'e k'ofar shi wasu mata biyu suka rangad'a uwar bud'a kai kace buzaye ne su na asali, suma abokan suna ganin haka suka sake matsowa, uku daga cikin abokan wanda kana ganin kayan jikinsu zaka san naira ta kwanta tare Pappa ne suka sake zaro kud'i a aljihu suka fara tarara mishi kamar ruwa, gud'ar da matan ne keyi kamar zugasu ne suke wajen zuba kud'in, ganin har zasu fita basu daina ba abun harya k'azamce yasa su Husseina suka taresu tace "Dan Allah yara ku daina zuba kud'in nan haka ya isa, angode muku Allah ya saka da alkairi."

Wani mai cikar kamala da haiba ne a ciki yace "Hajia karki damu, Ammar namu ne, lokacin na mu bikin yayi fiye da abinda mukeyi yanzun, wannan ba komai bane."

K'anwar Zulai ce tace "Duk da haka dai ai sai ku ragawa ranar bikin, tunda yanzu ne aka fara."

Pappa ne yace "A'a tanti, mu a wurin mu shagalin bikin Ammar tun jiya aka fara shi, ranar biki ma a shirye muke zamuyi fiye da haka, kawai ku bamu hanya."

Ai kuwa wucewa sukayi ba tare da sun daina ba, Ammar na shiga mota ya saki murmushi, dan ko ba komai yaji dad'in abinda Pappa ya fad'a, daga nan gida suka wuce, su tarar anata hidima kamar yau ne bikin, kafatanin ahalin Gaga babu wanda baya da ankon gallelen leshin da akayi, sai amare da aka ma shiga irin ta barebari (asalin mahaifiyarsu Suley), sunyi kyau sosai musamman ma Amna kayan sun karb'e ta haka ma kalar shud'i da sararin samaniya, hatta gyaren kan da aka musu irin na barebari ne wanda ya fito sosai ake ganinshi, nan abokan Ammar suka kutsa dashi d'akin shi suka sashi ya canza kaya zuwa chadda kalar ruwan samaniya sannan suka fito, filin taron suka kaishi inda suka d'auke su hotuna shi da amaryarshi, yau ma dai kamar jiya lafiya aka gama caskalewar aka kwanta kuma sai gobe idan gari ya waye a d'ora.

Gida yayi shiru baka jin motsin kowa da komai, Ummy ce tasa lieutenant gaba sai rufe fuska take alamar ita kunya take ji, shi kam banda kallonta babu abinda yake yi har yace "Uwar yan biyu wai meye haka? ko dai kin tuna da k'uruciya ne?"

Sake rufe fuska tayi da pilown dake hannunta tana murmushi, shima fad'ad'a murmushin yayi yace "Dan Allah ki fad'a min meke faruwa, ko kuma nayi hushi."

D'agowa tayi da sauri ta kalleshi tace "Zan fad'a to."

Zuro mata kunne yayi yace "To ina jinki."

Saida ta sake rufe ido tace "Dama ai...dama, nayi b'atan wata ne, kuma n...na auna da kaina na tabbatar, cewa su Ammar zzza..su samu k'ane."

"Me?" Lieutenant ya fad'a da k'arfi tana kallonta...


*Alhamdulillah*

*Yawan sharhi, yawan rubutu.*
09/09/2020 ร  17:58 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```


๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
*A SANADIN K'AUNA*
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜

_Barka my BK, ina tayaki murnar kammala wannan novel naki, Allah ubangiji ya baki ladan fad'akarwa, Allah ya saka miki da alkairinsa, kurakuren da kikayi a ciki ya yafe miki, sai mun jiki a next novel idan Allah ya amince._


_Bismillahir rahamanir rahim_

_33_


Baki har kunne lieutenant yace "Uwar yan biyu da gaske kike fad'a min maganar nan kuwa?"

Kallonshi tayi tace "Da gaske mana, muna irin wannan wasar ne?" Girgiza kai yayi yace "A'a."

Kallon gefe yayi yace "Kai amma wannan abu sa mamaki da kuma d'aure kai."

Kallonta yayi yace "Wato ke idan na fahimceki irin haihuwar rak'uma kikeyi, kai Allah nagode maka abisa wannan kyautar."

*Washe gari* da sassafe lieutenant ya fito cike da farin ciki da zumud'i, duk da yana jin nauyin fitowa kai tsaye ya fad'awa Hajia Sa'ada na da ciki, amma yayi niyyar fad'a mata ko da a birkice ne yanda zata gane ko da kuwa hakan na nufin yayi wani abu a aikace ne da zaisa ta fahimta, dan rashin fad'a mata da wuri zaisa yasa fad'a da tsegumi ranar da cikin ya bayyana. Yana isowa falonta saiya samu Zeituna kwance akan kujera da alamar galabaita a tare da ita, da sauri ya k'arasa ganin babu Hajia a wurin, yana zuwa ya zauna ya kamta ta tashi zaune yana kallonta yace "Zeituna lafiya? Me yake damunki ne? Me kike yi anan kwance?"

Saida ta k'ara yamutsa fuska tace "Bana jin dad'i ne, ko baccin kirki banyi ba saboda amai."

Cike da nuna kulawa hankali a tashe yace "Subhananallah! Amma kuma shine baki fad'a min ba kika ja baki kikayi shiru, to tashi mu tafi asibiti a duba ki."

Kallonshi tayi tace "Duk likitocin da muke da su a gidan nan sai mun tafi asibiti?"

D'an dafe kai yayi tare da tashi tsaye yace "Wallahi na sha'afa, bari na wa Sa'ada magana saita duba ki."

D'akin Ummy ya nufa da rawar k'afa, zai shiga Hajia ta fito daga nata d'akin, ido hud'u da sukayi ya sashi tsayawa ya sunkuya yace "Ina kwana Hajia."

Saida ta harareshi sama da k'asa tace "Meye kuma na wannan rawar k'afar zaka shiga d'akin ta? Ina ce ga amaryar can ka baro a falo, Hassan anya kuwa baka zama lusarin namiji ba."

Cike da ladabi yace "Yi hak'uri Hajia, dama yarinyar can ce bata da lafiya, shine zan kira Sa'ada ta dubata."

Kallon Zeituna tayi ta kuma kalleshi tace "To sai me? Nace sai akayi yaya? Akan bata da lafiya ne kake wannan saurin kamar zaka tashi sama?"

Dogon tsaki taja kafin tace "Meke damunta? Nasan dai ba zai wuce tace ciki ne da ita ba ko? To kayi farin ciki zaka sake zama uba a wannan shekarun naka."

Lieutenant da yake jin kamar yayi kuka jin abinda ta fad'a yasa ranshi sanyi, idan Zeituna ma ciki ne da ita shi kam Alhamdulillah, mata biyu a lokaci d'aya zasu sake haifa min yara, watak'ila ma a cikinsu wata ta haifi yan biyu, tunanin hakane yasa shi sakin murmushi, yana ganin Hajia ta nufi falon ya biyo bayanta, tana zuwa ta zauna tana k'arewa Zeituna kallo, fuska a had'e tace "Kinyi farin ciki ko? Hankalinki saiya kwanta tunda gashi kin nuna min kun gyauraya ke da Hassan har zaki haihu dashi kema."

K'asa tayi da kanta tana wanda da yatsun hannunta, tana so ta tashi ta koma d'akin ta sai dai tana jin tsoro, lieutenant da farin ciki ya gama baibayeshi ne ya kalli Hajia yace " Hajia ai ita kanta Sa'ada bata da lafiya."

Wani kallo ta watso mishi mai kama dana k'yama tana cewa "Ban gane bata da lafiya? Meya sameta ita kuma?"

Shiru yayi haka ita ma kallonshi take tana jiran amsa, fahimta da tayi yasa ta canza yanayin kallon da take masa tace "Me kake nufi? Hassan wai ita ma Sa'ada ciki ne da ita kake so kace?"

Sunkuyar da kai yayi baice komai ba wanda yayi daidai da fitowar Ummy daga madafa, k'ura mata ido tayi tana kallo harta k'araso kusansu, babu wani abinda ya sauya a jikinta, dama ita d'in jawur yake kuma ba k'iba ce da ita ba, idan da akwai abinda za tace ta mata bai wuce tace ta d'an rame ba, saida Ummy ta gaishe da Hajia da lieutenant tare da bashi kofin shayin dake hannunta, ta juya zata koma ga aikinsu kenan Hajia tace "Sa'ada, wai ciki kika ce mishi kina da?"

Wata irin kunya ce ta rufe Ummy tare da fad'uwar gaba, shiru tayi ba tace komai ba sai zazzare ido take, Hajia na ganin haka cikin hushi tace "Amma dai ke akwai jahila, yanzu Sa'ada da girmanki ne zaki wani d'auki ciki? Shekararki nawa rabonki da ki haihu? Har an fidda rai da sake samun haihuwa daga gareki sai kawai yanzu ki wani ce kina da ciki, anya kuwa dan Allah ne kika yarda kika samu cikin nan, kenan dama can kina haihuwar kawai iskanci ne yasa sai lokacin da kika yi niyya kike yinta, ko kuma dai dan kinga kishiyarki na da ciki ne kema kika d'auka?"

Tsaki Hajia tayi tare da mik'ewa ta bar falon zuwa farfajiyar gidan, Ummy da kanta ke k'asa saida taga fitarta ta d'ago a hankali ta sauke ido akan Zeituna, ido hud'u sukayi dukansu hawaye ne suke, da sauri Ummy ta juya ta shiga d'akin ta tana kuka, ita ma Zeituna fashewa tayi da kuka wanda yasa lieutenant rasa yanda zaiyi, kallonta kawai yake bai iya cewa tayi shiru ba, dan shi kanshi abinda Hajia ta mishi ji yake kamar yayi kukan, dan har yanzu baiga dalilin da zaisa mahaifiyarshi ta dinga tozartashi irin haka haba ba har a gaban matanshi.

Ammar ne ya shigo falon cikin shiri da alamar fita zaiyi rik'e da leda a hannunshi, ba tare da lieutenant ya san da zuwanshi ba ya tsaya bayanshi yana kallon Zeituna dake zubar da hawaye, cike da nuna damuwarshi a kanta yace "Uwa lafiya? Meya faru kike kuka?"

A d'an tsorace lieutenant ya juyo dan baiyi tsammanin mutum a bayanshi ba, ganin Ammar yasa yayi tsaki cikin jin haushi yace "Kai wane irin sakarai ne? Sai yaushe ne zaka fara sallama idan ka shigo wuri? Dubi yanda ka tsorata ni dan Allah."

Ko kallon inda yake baiyi ba yace "Dama a tsoracen kake shiyasa, meya samu uwata nake so na sani har take kuka?"

Mik'ewa yayi tsaye yace "Idan an fad'a maka me zakayi? Zak..." Bai k'arasa ba Zeituna ta d'ago kai ta kalleshi tace "Dan Allah Abban Ammar."

Kallonta yayi ita kuma ta dinga lumshe mishi manyan idonta masu yalwar gashi, juyawa yayi ya fice a fusace daga falon, matsowa yayi kusanta yace "Uwa me aka miki kike kuka?"

Girgiza kai tayi tace "Ba komai, bana jin dad'i ne."

Murmushin ba gaskiya

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login