Showing 198001 words to 201000 words out of 325849 words

Chapter 67 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

585

Middle Ads

ya ga sai sa hannun Ammar da yake buk'ata, hakanne yasa shi kiranshi dan ya fad'a mishi ya zo, amma mummunan labari sai police ya d'auki wayar ya fad'a mishi abinda ke faruwa, tun saman hanya Amar ke maimaita jikka sha biyar d'in me da Ammar zai yarda a d'aure shi akan ta, da wannan takaicin ya isa ofishin yayi bailinshi.

Ana fitowa dashi ya ga Amar ne sai yaji ba dad'i, tsaye yayi yace "Dama wannan yaron ne ya zo fito dani? To babu inda zanje."

Rai b'ace Amar yace "Ammar kar kayi taurin kai mana, ba wasa na zo yi ba."

"To yi min fad'a ubana." Shiru Amar yayi yana kallonshi, ni yake kamar ya rufe shi da duka, amma yasan ko yayi haka shine zai sha wahala, a kausashe yace "Wuce muje."

"Babu inda zanje, an fad'a maka ni bana da kud'in fitar da kaina ne? Abba nake si ya zo wajen nan, inba haka ba kuma ina nan wallahi."

Juyawa yayi cike da takon isa da k'asaita ya shiga ciki aka rufe shi, harara Amar ya dalla mishi daga nan yace "Kai ka sani ka tabbata anan."

Da kallon zaka gane kurenka ya bishi yace "Zamu had'u ne zaka san ka harare ni yaro."

Da fari Amar shafawa yayi da al'amarin ya shiga harkokin gabanshi, saida ya tuna waye tagwaicinshi kad'ai ya sake kiran lambarshi, yanzu ma police ne suka d'auka, dan haka baiyi k'asa a gwiwa ba ya garzaya douanes ya samu lieutenant, yana fad'a mishi lieutenant ya rufe ido yana zabga masifa ta inda ya shiga bata nan yake fita ba, cewa yayi ya tafi kawai ya barshi can shiya sani amma shi babu inda zaije.

Ummy ya kira a waya da niyyar yace ta lallab'i Abba, amma sai yaga tafi ma d'aukar zafi fiye da Abban, ita ma haka ya rabu da ita ya kira wayar Ammar aka bashi shi a waya, rarrashin duniya yayi dan ya fito amma Ammar sai yaga rayuwarshi ma bata da anfani, kenan babu wanda zai zo? Kashe wayar yayi ya bayar aka aje ya koma ya kishingid'a kamar a gadon sarauta yana ci gaba da tasbihi ga ubangiji yana kuma jiran yaji wa zai zo.


Bayan magriba lieutenant ya dawo gida, a d'aki ne yake fad'a ma Zeituna cewa "Kinji wannan mahaukacin yaron abinda yayi?"

Tasan sarai da wa yake dan haka bata kula shi ba ma dan bata ji dad'i ba, saida ya kalleta yace "Dake fa nake magana kina jina."

Cikin d'an fad'a fad'a tace "To me kake so nace maka?"

"Ban gane ba? Ina fad'a miki Ammar yana ofishin yan sanda kuma d'an uwanshi yaje yayi belinshi amma ya k'i tahowa wai sai naje da kaina, shine zaki fad'i haka."

Cikin gatse tace "Oho ashe sunansa Ammar, ai na d'auka baya da suna ne."

Kallonta yayi yace "...


*Comment ya sani muku typing, ku ci gaba da haka zakuji bayani.*

*Alhamdulillah*
14/10/2020 ร  00:58 - Ummulkhairi: ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
*BADAK'ALA*
๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ _*AHALI NA*_๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```

โœช{T . N}โœช๐Ÿ“–๐Ÿ–Š๏ธ

https://www.facebook.com/101305508365889/posts/101311008365339/?substory_index=0&app=fbl


_Bismillahir rahamanir rahim_

_43_


"Ke wai ya kike neman b'ata min rai ne? Ya ina miki magana kuma kina magana kan wani abu daban."

Ba alamar farin ciki ita ma tace "Na fad'a maka gaskiyar abinda ke raina shine, bana jin dad'in halin ko in kula da kake nuna mishi, shi ma fa haihuwarshi akayi, yana da rai da zuciya, yana jin zafi haka kuma yasan meye farin ciki, dubi ka gani d'azu kafin fitarka a gabana ka kira d'an uwan haihuwarshi kake tambayar lambar account d'in shi, me yasa shi baka kira shi ba? Kana jin kunya ne saboda shine babba ko kuma saboda baka k'aunarshi ne? Ni ban tab'a ganin iyaye irinku ba wallahi, gaskiya Abban Ammar ba zan yarda na haifi abinda ke cikin nan nawa ba shima kana nuna mishi wannan k'iyayyar, sam ba zan lamunta ba wallahi, gwara ka fad'a min tun yanzu in baka son 'ya'yanka ne saina zubar da cik..."

"Ke." Wannan tsawar daya mata ce tasa tayi shiru tana kallonshi, baya k'aunarshi? Baya k'aunar 'ya'yanshi? K'iyayya? To wai duk meye na fad'in haka? Me na aikata da yasa ta tunzura haka har take fad'in maganganun nan? Kallonta yayi sai dai ya kasa cewa komai yana son sanin abinda take nufi, ganin bai ce komai ba sai kallonta yake yasa ta matso kusanshi ta rik'o hannunshi tana mai tausasa muryarta tace "Abban Ammar, kayi hak'uri da d'aga muryar da nayi a gabanka, amma ka sani wallahi abunne baya min dad'i ko kad'an, bansan ko har yanzu baku fahimta bane, ni marainiya ce babu uwa babu uba, nayi wayo a tare dasu amma ban girma dasu, sai dai duk da haka nasan soyayyarsu da yanda suka jani a jikinsu, hakan yasa har yanzu ina kewarsu kewar kulawarsu gare ni, duk sanda na tuna saina zubar da k'walla, haka duk sanda na ga maraya irina saina tausaya masa, karo na farko da naga wanda iyayensa ke raye kuma nake jin tausayinsa, shine Ammar, yana rayuwa tare daku a gida d'aya, amma hakan baisa kun iya fahimtarshi ba, a d'an zaman da nayi tare da ku da bai haura wata d'aya ba na lura da abubuwa da dama."

Saida ta share hawayen da suka taho mata sannan ta ci gaba da cewa "Ban tab'a ganin Ummy ta amsa sallamarsa ba, ban tab'a ganin ta amsa gaisuwa ko maganar da zai mata cikin dad'in rai ba, hasalima yana shigowa inda take zaka ga ta canza fuska daga murmushi zuwa had'e rai, haka zai juya ya fita ba tare data bishi da kallo ba, bata damu ya ci abinci ko bai ci ba, ya ya kwana ya kuma ya tashi? Amma Amar, haba-haba take dashi da nuna masa kulawa, bayan ta amsa gaisuwarshi zata zata tambaye shi abinci fa? Idan yana buk'ata da kanta take bashi ya ci, to me yasa shi d'ayan bata mishi haka, ka duba kaga lokacin bikinsu, Amar na ta kai da kawowa tsakanin waje da d'akinta suna ta shawara, amma shi Ammar shi kad'ai yake harkokinshi babu mai kula shi a gidan nan, kowa d'ansa ya sani kowa ya kama wanda yake k'auna ya rumgume, to me yasa? Shi ba d'an gidan nan bane? Ko kuma wani abu ya muku wanda kuke hushi dashi har haka?"

Kuka ne ya ci k'arfinta ta sunkuyar da kanta, saida ta saita nutsuwarta kafin ta d'ago tana kallonshi tace "Wallahi idan nice ake nuna wa wannan bambamcin na tabbata zan iya cutar da kaina, dan zanga kamar babu mai so na ne kawai gwara ma na mutu, Abban Ammar dan Allah ko sau d'aya ne ka zauna da yaronka ka fahimci matsalarshi kasan me yake ciki, ina tabbatar maka cikin sauk'i zaka fuskance shi, misali ni mana, wa zaiyi zaton zan samu wata girmamawa daga wajenshi? Amma sai gashi na ci darajar samun sunan uwa daga bakinshi, dan Allah kayi tunani akan abinda na fad'a maka, idan har kayi tunanin abinda ya dace nasan Ammar zai kwana gidan ubanshi yau, idan kuma kayi tunanin daka saba yi kullum to zai kwana a magark'ama, amma ka sani kar kuyi kuka da kowa duk ranar da kuka kaishi mak'ura har yayi abinda sunanku zai bazu a cikin gari."

Sakin hannunshi tayi ta shiga ban d'aki, gaba d'aya lieutenant rasa jijiyoyinshi yayi kamar an tsinkasu, yana so ya gyara ko da tsayuwarsa amma ya gagara, sai dunk'ule hannunshi da yayi sosai kamar zai naushi wani, yafi minti ashirin a wurin nan kafin ya samu da k'yar ya d'aga k'afarshi ya juya ya fita, lambu yaje ya samu kujera ya zauna, durmiya yayi tunanin abinda ta fad'a mishi, babu komai a ciki face zallar tsagwaron gaskiya, to amma inda matsalar take shi bai tab'a tunanin hakan rashin kyautawa ne ba, bai tab'a tunanin hakan zai iya zama wani abu ba duba dashi ba yaron goye ne ba da sai an kula dashi, da wannan tunanin ya kasa katab'us sai tubka da warwara yake. Ko da ta fito bata ganshi ta fito da niyyar zuwa wajen Amna, acan ta hangeshi zaune cikin lambu yayi shiru, girgiza kai kawai tayi ta wuce inda zata je, saidai a tunaninta ba zai je ya dawo da shi ba, dan haka ta tafi da sake wani shirin da zaisa dole yaje.

K'wank'wasa k'ofar tayi hakan yasa Amna tahowa da sauri, tana bud'a k'ofar ta ga Zeituna take ta bayyanar da damuwarta tare da fuszar da iska, kaucewa tayi a hanya ta shiga ciki sannan ta mayar da k'ofar ta rufe, juyowa Zeituna tayi ta kalleta tace "Amna lafiya kike?"

Cike da damuwa tace "Aunty Zeituna ina lafiya, yah Ammar tun safe ya fita har yanzu bai dawo ba, ya fad'a min zai jima amma ban d'auka zai jima haka ba, wallahi gabana sai fad'uwa yake ina jin tsoron abinda ya same shi."

Kallonta tayi da tausayawa tace "Kenan baki san mijinki na ofishin 'yan sanda ba?"

Zaro ido tayi tsoro da tashin hankali ya ziyarce ta tace "Ofishin yan sanda? Meya faru dashi? Wane laifi yayi?"

Dafata tayi tace "Kwantar da hankali Amna, ba wani babban laifi bane."

"Amma kuma yake hannun yan sanda? Me yake faruwa aunty Zeituna?"

Nan ta kwashe komai ta fad'a mata, cikin kuka wanda yafi kama dana shagwab'a tace "Yanzu aunty Zeituna Abba ba zai je ba kenan? A can zasu barshi ya kwana? Allah ba zai yiwu ba."

Murmushi ta mata tace "Nima na zo fad'a miki abinda in ki kayi ne mijinki zai kwana tare dake yau."

Da sauri ta rik'e hannunta tace "Fad'a min aunty Zeituna, me zanyi?"

Cikin murmushi tace "Kawo kunnenki kiji." Wani abu ta fad'a mata wanda nima an fad'a min abinda ta fad'a mata amma ni zan fad'a muku a rubuce, kallonta tayi tace "Kin tabbatar zaiyi aiki?"

Cike da son tabbatar mata tace "Amna dole zai fito miki da mijinki ko baya so, kawai ke dai ki jajirce ki zama mai naci kan hallayar mijinki."

Duk da tana jin ciwo a k'afafunta na bak'ar wahalar da tasha amma saboda k'arfin hali da gudu ta nufi d'aki tana fad'in "Nagode aunty Zeituna."

Jim kad'an ta fito da mayafi ta yafa a kafad'a ta shiga madafa, kwandon saka kwanukan abinci ta dauko ta fito, kan teburin cin abinci ta nufa ta jera kwanonin abincin tare da robar ruwa da lemu da kuma lemu orange da ayaba, saida ta zo gaban Zeituna dake ta binta da kallo tace "Aunty haka yayi?"

"Sosai ma, ai kawai ki basu mamaki." Ta fad'a tana kanne mata ido, tare suka fita inda Zeituna ta koma b'angarensu ita kuma ta fita, saida ta kai bakin titi kad'ai ta samu adaidaita sahu ta shiga, ba jimawa sosai mai adaidaitar ya sadata da inda zataje dan babu nisa sosai, bayan ta shiga ta fad'i wanda ta zo gani da cewa abinci ta kawo masa, abunka ga idan mutum wani babbu ne ko mai alak'a da babba, izinin ganinshi aka mata ta zauna inda aka nuna mata gabanta na ta fad'uwa dan bata tab'a zuwa ba sai yau dalilin mijinta. Da wani tako ne ya fito wanda yafi kama da fitowar sarki daga cikin gida zuwa kan karagar mulkinshi, kallonshi take a hankali soyayyarshi tana narkewa a zuciyarta, k'arfin halinshi da sababinshi yasa ta sakin murmushi, sab'anin shi da yana ganinta ranshi ya b'ace ya k'ara sauri a tafiyarshi ya k'araso wajenta, yana zuwa ba tare daya zauna ba ya zaro mata ido yace "Ke kuma meya kawo ki nan?"

Saida ta daure sosai kafin ta samu k'warin gwiwar cewa "Wajenka na zo mana."

Fizgo hannunta yayi ya mik'ar da ita tsaye yana fad'in "Amna baki da hankali ne? D'an iska kika mayar dani ko me? A wannan lokacin kika fito daga gida kika zo nan kuma da wannan shigar?"

Kallon kanta tayi, riga da siket d'in na leshe wanda suka amshi jikinta sune matsalar? Ko kuma d'aurin data b'ata lokaci ta kashe wajen d'aura shi? Kwalliyar fuskarta ko kuma mayafin data yafa? Kallonshi tayi tana turo baki gaba duk tayi kalar wallahi kuka zan ma ka tab'ani, a hassale yace "Billahil azim kifar dake zanyi wurin nan kika min kuka, ke ni d'an iska ne?"

Girgiza kai tayi da sauri tana fad'in "A'a." Rik'e k'ugu yayi yace "To uban wa yace ki fito haka? Kuma waya kawo ki nan?"

Saida ta k'ara yin kalar tausayi sannan tace "Aunty Zeituna ce."

"To waya kawo ki?" Ya sake jifarta da tambayar, saida ta d'anyi baya kad'an tana kallonshi sannan tace "Adaidaita...Ahhhhh." Ta fad'a da k'arfi saboda d'aga hannu da yayi kamar zai kifeta da mari, a hankali ta bud'e idonta jin bai sauke mata yatsunshi ba a kumci, kallonshi tayi sai taga ya k'ura mata ido yana kallo, da kankana ce da yanzu ta zuba a guje, amma ita
saita tsaya ko kasheta zaiyi, abun ne ya bashi dariya sai kawai ya figo hannunta ta fad'a jikinshi ya rumgumeta yana dariya yace "Mahaukaciya, ke baki iya guduwa ba idan za'a dake ki."

Cikin shagwab'a tace "To yah Ammar taya zan iya tsere maka? Mai guduwarma (Hamna) naga in kayi niyya kana ritsata duk inda take."

Lumshe ido yayi yana sakin murmushi kafin ya d'agota yace "Yanzu to ki koma gida, amma k'asa zaki tafi in ba kya son ki jazawa masu adaidaita bala'i, kinji ko." Ya fad'a ba alamar wasa a tare dashi.

Shagwab'e fuska tayi tace "To ai ni ban zo dan na koma ba, nan zan kwana tare da kai."

K'ura mata ido yayi yana kallo, ya jima yana tausar kansa kafin yayi nasarar kwantar da hankalinshi yace "Amna kuka kike so kiyi ne?"

Da sauri ta rik'e hannayenshi tana fad'in "Bana so, amma kuma ina nan tare da kai yah Ammar."

"Me yasa?" Ya fad'a yana son k'watar hannayenshi, saida ta langab'e kai tace "Aunty Zeituna tace idan na zo nan dole Abba ma zai zo yayi belinka da kanshi."

Kallonta yayi sosai yayi murmushi yace "Uwa ta shiga al'amarin?"

Kai ta jinjina masa alamar eh, sai kawai ya zauna kan bencin ya sashi tsakiya yace "Zuba min abinci na ci kinji yarinya, tunda uwata ta shiga lamarin nasan ma dole zai zo."

Murmushi tayi ta fito da kwanukan ta soma zuba mishi abincin, har ta d'auki cokali zata fara bashi saiya girgiza mata kai, aje cokalin tayi ta wanke hannunta ta fara bashi da hannunta, yana ci yake ce mata wai tayi hak'uri na rashin zamanshi gida a tare da ita, uffan ba tace ba sai yanka mishi loma da take tana aika masa.

Tana komawa b'angaresu ta samu lieutenant a inda ta barshi, shiga tayi ta tsaya gabanshi tana kallonshi, ta jima tsaye amma bai motsa ba alamun baisan da zuwanta ba, ajiyar zuciya ya sauke tare da d'an juyo da kanshi hakane yasa ya ganta, cikin basarwa ya d'an had'e fuska yace "Ya dai?"

Murmushi ta masa tace "Ba komai."

Bai ce komai ba sai juyar da kansa da yayi, ita ma ba yanayin wasa a tare da ita tace "Yallab'ai akwai matsala fa."

Kallonta yayi yace "Matsalar me kuma?"

Saida ta gyara tsayuwa ta mayar da hannayenta bayanta sannan tace "Yanzu daga b'angaren Amna nake, na sameta tana ta kuka saboda rashin sanin halin da mijinta ke ciki, dana fad'a mata tayi hak'uri dan ba zaka je ka fito dashi saita d'auki mayafinta ta fita, da k'yar ma ta fad'a min tace zata je wajen mijinta ne tunda babu mai k'aunarshi."

Kamar an tsikare shi haka ya tashi tsaye yana mata wani mugun kallo cikin d'aga murya yace "Babu mai k'aunarshi? Wai wace irin magana ce kikeyi haka? Taya kike tunanin zamu haifi d'an a cikinmu amma mu ce ba ma k'aunarshi, akan me zaki fad'a mata haka kuma har ki bari ta fita a wannan lokacin, ke a ina kika tab'a ganin haka?"

Ba tare data nuna tsoron yanayinshi ba tace "Akan ku mana, kanku na fara gani."

Jinjina kai yayi yace "Ok, to ni kuma yau zan nuna miki k'arya kike, ina son d'ana kuma ina k'aunarshi fiye da komai dana mallaka a duniya."

Fuuu ya rab'ata zai wuce cike da shak'iyanci sai cewa tayi "Taya zan tabbatar ina daga nan bansan me ya faru a can ba?"

Tsayawa yayi ya juyoya kalleta da mamaki, raina shi ne tayi kome? Shi kananta ne da zata mayar dashi abokin wasanta? Saida ya jinkina mata kai yace "K'arfin shaukin da zan nuna masa zai riskeki har gidan nan."

Juyawa yayi ya fita ta bishi da murmushi Allah ya bada sa'a, tun a hanya yake k'ulla kalar k'aunar da zai nuna masa, to wai a kan me zata fad'a masa baya k'aunar d'an shi, ko bata san shine sanyin idaniyarshi na farko bane? Bata san duk suna mishi abinda suke mishi ne ba dan suna son ya gyaru ya zama na k'warai? Ta manta da duk fafutukar da yake saboda 'ya'yanshi yake yinta sannan Ammar shine magajinshi na farko? Me yasa bata tambaye shi me yaji ba a sanda aka fad'a mishi an rufe mishi? Amma ba komai zai nuna mata ba haka bane abinda take cewa ta ganin, da wannan tunanin ya isa ya baka tsandareriyar motar data sanar da jami'an babban mutum ya shigo, sanin sosai suka masa ba sanin shanu ba, dan haka suka sara masa cikin girmamawa ya shiga ciki, ikon Allah sai kallo, ganinshi hankali kwance matarshi na ciyar dashi cikin nishad'i, abinda ya aikata ya cancanta ya bibbige shi amma ba hali, k'wafa kawai yayi ya shiga inda zai samu belinshi. Cikin mutuntawa aka fad'a mishi ai Amar ya biya tarar kawai zasu iya tafiya, amma gobe da safe saiya dawo a musu sulhu saboda gaba, duk da haka saida ta d'ebo kud'in da baisan ko nawa bane ya zube kan teburin kafin suka fito, sai lokacin

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login