Showing 156001 words to 159000 words out of 325849 words
dattijantaka ya amsa da "Barka Babba, anshigo?"
"Eh Alhaji." Ya amsa kanshi k'asa, jinjina kai yayi yace "To ya hidima?"
"Alhamdulillah, ya gajiyarku?" Amsawa yayi da "Angode Allah."
Cikin girmamawa ya amsa da "Allah ya k'ara girma."
Mik'ewa yayi yana fad'in "Ni zan shiga ciki Alhaji, saida safenku."
"Allah ya tashe mu lafiya, Saida safe." Nufa babban falon yayi yaji ta bayanshi ance "Alhaji barka da dare."
Tsayawa yayi ya juyo danya fahimci muryar wanene, saida ya k'araso wurin da alama shima shigowarshi kenan, hannu ya mik'awa Alhaji yana fad'in "Mai gida ga hajjaju kenan, ana shan iska."
Murmushi Alhaji yayi yace "Mijin Amna, ya kake?"
Cike da shak'iyanci yace "To gani dai, na gama komai, yanzu Hajiar nake sauraro naji lokacin data d'ibar mana da zata sa mu angonce."
Lieutenant dai tsaki yaja ya juya zai wucewarshi Ammar yace "Abba ya na ganka kai kad'ai zaka shiga wajen amarya?"
Juyowa lieutenant yayi rai a b'ace yace "Ban gane ba? Ni da ubanwa kake son gani na to?"
Saida ya kama hantsar wandonshi irin na yan gayu yace "Eh to, naga kai ka kad'ai ne babu abokin rakiya, ko kana nufin kai kad'ai zaka siyi bakin amaryar?"
A hassale lieutenant yace "Eh d'in, ni kad'ai zan shiga, kana da matsala da hakan ne?"
"Ah sosai ma." Ya fad'a yana matsowa kusanshi, hannu yasa ya karb'i ledar hannun lieutenant ya juya ya kalli Alhaji yace "Alhaji domin Allah kana ganin ya dace ace ya je wurin yarinyar nan shi kad'ai? Ka fad'a mishi ya nemi d'an rakiya mana."
Cikin dariya Alhaji yace "To banda abunka Ammaru yanzu waye zai fito daga gidanshi cikin daren nan? Kuma naga shi ba yaro ba haka ba abokan nashi, kawai ka barshi ya shige."
Ba alamar wasa yace "Alhaji ni fa dama ba nufi na kenan ba ya kira wani, masha Allah duk 'ya'yan da Allah ya hore mishi ace mun kasa rakashi saiya kira wani, gani babban d'a, kawai muje na raka ka Alhaji." Ya k'arashe maganar yana kallon lieutenant.
Haushi ne yasa lieutenant kai hannu zai fizgo ledarshi yana fad'in "Dan ubanka bani ledata, Allah ya tsareni na rasa wanda zai rakani sai kai."
Rik'e ledar yayi shima kuma Ammar ya rik'e sosai ya had'e rai kamar zaiyi fad'a, shima lieutenant fuskarshi a had'e ya kalleshi yace "Zaka sakar min ledar ko saina barar da kai a wurin nan? Ammar bana son iskanci fa, ina wasa da kai ne?"
Shima cikin hadd'ad'ar fuskarshi yace " Abba, wallahi tallahi saina raka ka ko baka so, kawai muje."
Gyara tsayuwa lieutenant yayi yana kallonshi da mamaki, hannunshi ya kama ya nufi dashi babban falon yana fad'in "Muje haba na sadaka da ita, ina fatan dai ba sai ka tsaya wani ja musu kunne ba? Tunda ai uwarmu ba hayaniya gareta ba, kawai kayi tazarce."
Dariyar da Alhaji ya tintsire da ita ne ta dawo da kallon lieutenant kanshi, ba tare daya tsagaita da dariyar ba Alhaji yace "Kawai kuje babba, koba komai shi d'in babban d'an ka ne kamar yanda ya fad'a."
Nuna Ammar yayi da yatsa yace "Alhaji da wannan mahaukacin? Haba dai."
Sai lokacin ya daina dariyar yace "Kuje kawai ba komai."
K'iiiii Ammar yaja hannunshi har cikin falon, bai kuma yi alamar tsayawa ba har suka tunkari d'akin Zeituna, suna kaiwa bakin k'ofar babu wani tsayawa kawai ya kama murfin k'ofar zai bud'a, da sauri lieutenant ya jawoshi baya yana fad'in "Wai kai wane irin mahaukaci ne dan Allah? Haka zaka shigar mata d'aki babu k'wank'wasa k'ofa ko sallama? Kasan a wane yanayi zaka sameta?"
Wata shegiyar dariya yayi yace "Ikon Allah, Babanmu tun kafin ka shiga cikin? Ni ko a tunani na dai amarya indai budurwa ce ai yanzu za'a sameta zaune ne akan gado, akan gadon ma a tsakiyarshi."
Tsaki lieutenant yayi ya k'wank'wasa k'ofar d'akin yana hararan Ammar dake kallonshi ido cikin ido, murmushin zaka shiga hankalinka Ammar ya mishi sanda ya bud'a d'akin ya shiga, bin bayanshi yayi ba tare da yayi sallama ba kamar wanda baisan mahimmancinta ba.
Suna shiga ba b'ata lokaci ya samu kujerardake gaban madubi ya zauna, tsaf ya k'arewa d'akin kallo tare da k'urawa Zeituna ido wacce taja kallabin rigarta ta rufe fuska, ganin kallon da yake mata gashi baida niyyar fita baya so ya mishi b'aram-b'arama yasa yayi gyaran murya, a hankali cike da k'asaita ya juyo ya kalli lieutenant d'in sannan ya kalli Zeituna, ledar dake hannunshi ya aje mata gabanta yace "Amm...Zeituna ko? To ga kazarki."
Wani kallo lieutenant ya mishi amma shi ko kulashi baiyi ba sai kallon Zeituna daya sake yi a nutse ya d'an tab'e baki yace "To wai ke da wannan rigar aka kawoki ne? Meyasa baki saka leshe ko chadda ba? Ba'a miki d'inki bane?"
Wurk'il wurk'il Zeituna tayi da ido a cikin kallabinta, duk da Ammar ko ma tace mazan gidan ba mazauna gida bane, amma dai tasan Ammar baud'add'en mutum ne, lieutenant kuma kallonshi yayi rai a b'ace yace "Malam nagode da rakiyar da ka min, zaka iya tafiya ko?"
Gira ya d'aga tare da jinjina kai ya mik'e tsaye ya kalleta yace "Amaryar Abba, nasan dai kinsan mahaifiyarmu kuma kinsan wacece ita, ina fatan kafin ki shigo gidan nan kin tsarkake zuciyarki, dan akasin haka ba zai mana kyau ba mu duka, domin kuwa mahaifiyata ita ce komai nawa, zan iya yin komai akan ta duk wanda yace zai b'ata mata, fatan za'a kiyaye saimu zauna lafiya."
Kallon lieutenant yayi yace "Abba, Allah yasa auren nan daka k'ara ba zai zama silar da za ayi sanadiyar zubar hawayen Ummyna ba, dan gaskiya ba zan juri haka ba, saida safe Abba na."
Yana gama fad'a yasa kai ya bar d'akin, lieutenant kam kasa motsawa yayi kafin daga bisani ya kalleta yace "...
*Alhamdulillah*
09/09/2020 ร 17:58 - Ummulkhairi: ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*BADAK'ALA*
๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ _*AHALI NA*_๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
๐ณ๐ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```
_Bismillahir rahamanir rahim_
_29_
"Tashi muje wajen uwarsu Ammar ko."
Hawayen da take wanda baisan dasu bane ta shiga gogewa, shiru yayi yana kallonta yana mamakinta, jin shiru ita ma yasa ta fara d'aga sautin kukanta saboda ita dai abun ya fara bata tsoro, bata gama gamsuwa da cewa ita matar lieutenant bace aka samu matsala tsakanin Hamna da Amna, yanzu kuma ga kashedin da Ammar ya mata wanda yake d'a ne ga mijinta, ita kam sai yanzu ta fara hangowa kanta uk'ubar data jefa kanta ta yarda da auren Abban Ammar, kamar daga sama lieutenant yace mata "Idan kin gama kukan ki tashi mu tafi to."
Cikin rawar jiki Zeituna ta mik'e har ta k'afafun ta na hard'ewa, lura da hakan yasa lieutenant tambayar kanshi "Anya kuwa wannan mu'amular ce ta dace ka mata a matsayinta na yarinya?"
Ganin sai sauri take ta fita daga d'akin yasa ya rik'o hannunta ta baya, cak ta tsaya ta juyo da sauri ta kalleshi, suna had'a ido saita sake b'arkewa da kuka ta rufe fuska da hannu d'ayan, a lokacin tausayinta ne yaji ya daki zuciyarshi, tunawa da yayi har yanzu baiji muryarta ta fito fili ba, a hankali ya jawo hannunta ya kwantar da ita kan k'irjinshi, wani lafiyayyan masauki ya mata a cikin jikinshi tare da zagayeta da hannayenshi ya fara daddab'a ta alamar tayi shiru, Zeituna kam take kukanta ya tsaya kamar anyi ruwa an d'auke, shiru tayi yayin da bak'on al'amarin ya nemi zautar da tunaninta, a d'aya b'angare kuma numfashinta ne taji yana kokawar barin gangar jikinta, wannan mafarki mai cike da tarin al'ajabi da rud'u ya addabeta, har yanzu ta kasa tashi daga wannan baccin da ba zata kira shi da mummunan bacci ba, haka kuma ta kasa yin farin ciki ko da a iya mafarkin ne, wani zazzab'i ne taji yana neman rufeta har jikinta ya fara b'ari saboda rashin sabon yanayin data tsinci kanta a ciki. Shi kanshi lieutenant wani bak'on al'amari ne ya ziyarce shi, amma saiya dake ya ci gaba da shafa har yayi k'arfin halin fizgo nutsuwarshi ya d'an sunkuyo yana lek'o fuskarta cikin dakusashiyar murya yace "Kukan ya isa haka, karki damu da halin Ammar, muma kanmu haka muke fama da shi, ya kamata ace kinsan shi bai kamata ya baki wahala ba, kinji ko? Ka da ki sake zubar masa da hawaye, idan ya fahimci haka zaki shiga tara a hannunshi, ba zai duba matsayinki na matar mahaifinshi ba, dan ko uwarshi ce zai iya yi mata haka, karki damu kinji."
Har ga Allah Zeituna ba kukan abinda Ammar ya fad'a mata take yi ba, amma jin abinda lieutenant ya fad'a saita tambayi kanta "Meyasa yake tunanin Ammar ne ya sani kuka? Me Ammar yayi da har yayi tunanin maganganunshi ne suka b'ata min rai? Soyayyar mahaifiyarshi ce ya nuna min a fili, hakan kuma ya birge ni sosai, tabbas shi d'in mai k'aunar mahaifiyarsa ne, tunda har kai mahaifinshi ya maka kashedi akanta."
A hankali lieutenant ya raba jikinsu tare da nufa k'ofa, hakan kuma shi ya dawo da hankalinta kanshi, a hankali ta bi bayanshi gabanta na fad'uwa na fargaban abinda zata tarar, yana shiga d'akin da sallama ya samu Ummy ta fito daga wanka da doguwar rigar bacci mai laushin gaske ta zallar audiga, kanta babu d'an kwali sai dogon gashinta daya sha kitso yake kwance har gadon bayanta, tana ganinsu tayi saurin juyawa bayanta ta d'auki wata hula ta d'ora akan tana mai fad'ad'a murmushinta tana fad'in "Sannunku da zuwa."
Murmushi ya mata yace "Sannu da hutawa uwar 'yan biyu."
Kallon Zeituna tayi wacce kanta ke k'asa tana wasa da hannayenta tace "Amarya sannu ko."
K'ala ba tace ba haka kuma bata kalleta ba sai ita ta sauko daga kan gadon ta kama hannunta ta juyo ta kalli lieutenant da harya zauna bakin gadon tace "'Yallab'ai ba dai har yanzu baka bar k'anwata ta huta ba?"
Murmushi yayi yace "To me tayi da take buk'atar hutun?"
Kallon Zeituna tayi tace "Duk da haka dai tana buk'atar ta huta yallab'ai."
Da hannu ya mata alama yana fad'in "Zo zauna to magana zamuyi."
Matsawa tayi kusanshi amma bata zauna ba tayi murmushi cike da dattako tace "Yallab'ai nasan meya kawoka, dan haka ba sai ka wahalar da kanka ba, Zeituna k'anwata ce kuma abokiyar zama na, insha Allahu zamu zauna lafiya ta yanda zakayi alfahari damu, mun riga da mun fahimci junanmu, tunda ba yau muka san juna da ita ba, nasan wacece Zeituna, duk da ana cewa d'an adam ya kan sauya, amma ina da yak'ini akan Zeituna cewar ba zata canza ba, yarinyar kirki ce ita d'in, tana girmamani da ganin darajata, zanyi k'ok'ari naga na rik'e wannan girman sannan nima na bata matsayinta, insha Allahu na maka alk'awarin ba zaka tab'a samun mu da wata matsala ba, kawai kuje ku kwanta."
Cike da jin dad'i da kuma k'aunarta ya sakar mata murmushi yace "Allah ya miki albarka uwarsu Ammar, nagode miki sosai, hak'ik'a samun mace irinki a zamanin nan sai an tona, Allah ya bar min ke."
Murmushi tayi kanta k'asa tace "Nagode."
Kallon Zeituna yayi dake tsaye kanta k'asa har yanzu yace " Ke me zaki iya cewa to? Kin dai ji abinda yer uwarki ta fad'a."
Rau rau ta fara yi da ido ko d'agowa ba tayi ba bare tayi magana, murmushi Ummy tayi tace "Yallab'ai kai bai ma kasan ai ba zatayi magana, kunya take ji har yanzu, amma ka bata d'an lokaci k'ank'ane."
Mik'ewa yayi yana fad'in "Shikenan to, saida safe ko."
Zeituna na jin haka ta juya da sauri dan barin d'akin, shi kuma ko a jikinshi saida ya jawo kan Ummy ya manna mata sumba a goshi tare da shafar gefen fuskarta kafin ya sake ce mata "Saida safe masoyiyata, ki kular min da kanki."
Murmushi kawai ta masa har ya fita, yana fita ta fad'a kan gado ruf da ciki tayi shiru, tabbas ta so tayi kuka, amma kuma cikin ikon Allah saita fi k'arfin zuciyarta har bacci ya d'auke ta. A wajen lieutenant kam shima yasha gwagwarmaya da zuciyarshi, dan so da dama zuciyarshi ce ke tunasar dashi wannan auren fa na mahaifina ne, duk rashin kulawar da zan nuna mata kamar na wofantar da maganar mahaifina ne, da hakane fa har suka kwanta bacci yayi dubarar mayar da ita matarshi ta sunna.
*07:05* duk da yau asabar ce amma kowa na gidan ya gama shiryawa, yara sunyi shirin islamiyya manya kuma zasu fita, Hajia na zaune a inda ta saba zama, Zeinabu da Soueiba da Ummy na ci gaba da gyaran gidan tare da Iya, sai su Nana dake ta k'ok'arin kammala abin karin kumallo, colonel ma cikin shirin tafiya ya fito ya gaishe da Hajia, kamar kullum ta amsa babu wani sakin fuska bare sa albarkarta, bai jira komai ba ya d'auki hanya tare da masu tsaron lafiyarsa dake biye da shi. Tun a falonsu suka had'e kowa ya fito daga d'akin shi, hannu Amar ya bashi yana fad'in "Malam Ammar ka tashi lafiya?"
Hannu ya mik'a mishi a cikin mak'oshi ya amsa da "Um." Murmushi kawai yayi yace "Tun jiya ina ta nemanka ban ganka ba, ina ka shiga ne haka?"
Ba tare daya kalleshi ba yace "Yaushe ka fara aikin jarida?"
Wani murmushin ya sake yi yace "Daga tambayar k'waya d'aya? To Allah ya baka hak'uri."
Fuska a had'e yace mishi "Idan ya bani kabi dare ka k'wace mana."
Girgiza kai kawai Amar yayi yace "Kasan banji dad'in rashin ganinka ko d'aya daga cikin sabgar Abba ba, Ammar meyasa kake haka? Ba kyau fa."
A daidai farfajiyar gidan yayi tsaye ya juyo ya kalleshi yace " Dan Allah Amar samu madaki ka bibbige ni, shine kad'ai zaisa nasan baka ji dad'i ba, yau ni naga jaraba, dole ne saina je d'aurin auren? Yanzu da banje ba meya faru? An fasa ne? Ina ce amaryar a gidan nan ta kwana kuma tare dashi."
Juyawa yayi a fusace ya tunkari falon Hajia yana fad'in "Kawai mutum ka addabeni ka addabi rayuwata, kuma ni na fad'a maka banje ba? Ina ce ni na rakashi ma d'akin amaryar, haka kawai ka dameni da surutu."
Amar na jin abinda ya fad'a ya matso da sauri yace "Me kace? Ka raka shi fa naji ka ce?"
Sake tsayawa yayi ya juyo a hassale yace "Eh haka nace, ni na raka shi, da matsala?"
Girgiza kai yayi dan ya fahimci yau ya tashi da yan sababin, shine ya fara shiga falon ba sallama kamar kullum inda Amar ke biye dashi da sallama, kujerar dake gefen Hajia ya zauna ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana fad'in "Ina jin dad'in zaman kujerar, bansan meyasa ba bana gajiya da zamanta."
Kallon Hajia yayi wacce ita ma ta kafe shi da ido tana kallonshi, murmushin nan dai daya saba mata na iskanci ya mata yace "Au na manta fa, ashe ni d'in jinin Hajia ne, jika na farko ga hajajju mutan makka, dole ne kujerar nan ta dinga burgeni, ashe gado nayi, dan naga kema ke da kujerar nan kamar kujerar mulki ce, duk wanda zai bud'e idonshi a gidan nan to zai wayi gari ne ya ganki a samanta, haka kuma duk wanda zai kwana to zai rufe idonshi ne bayan ya miki gani na k'arshe a kanta."
Had'e rai tayi tace "Kai ka kiyaye ni, meya kawoka nan d'akin?"
Dariya ya mata yace "Karki damu Hajiata, insha Allahu ko a lahira saikin zauna kan kujerar nan a matsayin shugabar tsofaffi ta gidan aljanna."
Hannu ta kai cikin zafin nama zata mareshi, da azama cikin isa da k'asaita ya cabko hannunta ya rik'e sosai, kallon baki da hankali ya mata yasa d'aya hannu yana shafar hannunta yana kallon k'wayar idonta, tana kallonshi ya kai hannun a bakinshi ya sumbaci bayan hannun nata kafin ya kalli hannun yace "Ni kam Hajia in tambayeki mana?"
Jin tayi shiru tana kallon sarautar Allah yasa yace "Nasan dai zamanin kina budurwa hannayenki abun sha'awa ne? To amma ya akayi yanzu naga sun zama haka? Duk sunyi tamoji sun jeme sai aukin jijiyoyi kamar..."
Fizge hannunta da tayi yasa yayi shiru ya kalleta, hararenshi tayi tace "Allah ya wadaranka Ammar, wallahi ba dan kayi kama da shalele ba da sai nace kai ba jini na bane, amma ba laifinka ban nawa ne."
Gyara zama yayi irin ya sa mata bak'in ciki yana fad'in "Da gaske? To amma me yasa kika ce haka? Kina nufin duk ahalin nan naki ni kad'ai ne d'an baiwar da yayi nasarar ya gadoki ta ko wani fanni?"
Sakin baki tayi da alamar mamaki a fuskarta, za tayi magana ya sake cewa "Kuma da kika ce muna kama da shalele, shin shine yayi kama dani ko nine nayi kama dashi? Ko kuma dai ke ce mukayi kama dake?"
Nuna shi tayi da yatsa tace "Dan ubanka in kana k'aunar uwarka ka tashi ka bar d'akin, wallahi ban son ganinka."
Tsaf ya mik'e ya kalleta yace "Idan kika ce ba kya son gani na a cikin gidan nan ma zan iya daina zuwa, amma fa saboda soyayyar uwata, dan ba zai yiwu na bar gidan nan ba bayan kuma nine babban magajin gidan."
Wani kallo ta mishi a shek'e tace "Wai kai a ganinka kaine babban magajin gidan nan?"
Dariyar rainin hankali ya mata yace "Ba'a ganina bane, a ganin kowa ma hakane, shiyasa fa hausawa suka ce *ko ba'a sonka a haifeka da fari*, gashi dai ni d'in ba sona kuke ba amma kuma ni na fara bultsowa duniyar, kai wallahi ni d'in mai sa'a ne."
Hannu ya bawa Hajia da nufin su kashe yana fad'in "Ban biyar Hajia ta, Allah ina mugun sonki."
A daidai lokacin da Ummy ta fito daga madafa kenan, yayi daidai da fitowar lieutenant da Zeituna a bayanshi Hajia tace " *Ni kuma na tsaneka Ammar, kaji da kyau, wallahi bana sonka har zuciya ta, bana son mu'amula da kai saboda kamar mahaukaci kake, Ammar ba dan ina asibitin ba a lokacin da uwarka ta haifeka da sai nace kai ba jini