Showing 138001 words to 141000 words out of 325849 words
rakiyarta, Imranatu da Bilkisu da suka shirya tafiya da kuma Ammie suna ji suna gani sai Bilkisu ta hak'ura su biyu kad'ai, kuka Raihan keyi kamar ranta zai fita , sai duk ta jita kamar wata marar gata, haka suka d'auki hanya bayan hawaye da Sameera ta zubar ita ma.
Suna tsaye har suka ga fitarsu, Abbas juyawa yayi ya koma ciki Sameera ma juyawa tayi ta koma d'aki cike da jimamin yar ta, zata zauna kan gado sai kuma ta tsaya tana kallon bak'uwar wayar da bata san da ita ba, d'auka tayi tana k'are mata kallo tana jujjuyata, a saninta dai babu mai ita a mutanen data sani, gashi kuma ba taro akayi ba gidan bare tace wani ya manta, tunanin da tayi ne yasa taja sama sai taga ta bud'e da nufin ko zata samu wata shaida da zata nuna wayar wace, amma bud'awar ita tasa zuciyarta kusan daina aiki yayin da ta nemi numfashinta ta rasa, rawar da k'afafun ta keyi yasa ta durk'ushewa ta saki wayar, banda rawa babu abinda jikinta keyi sai hawayen da suka fara zarya a idonta, idonta sun kafe wuri d'aya kan wayar data fad'i gabanta, tana son d'auke idonta amma abun ya gagara, bud'a baki tayi tana wani irin numfashi da shashek'a duk lokaci d'aya, kai take girgizawa alamar a'a amma kuma ganin abun take yana k'aruwa, wani kukan kura tayi ta mik'e tsaye tare da wayar da gudun tsiya kamar wata yar shekara sha shida ta fita daga d'akin ko kad'an ba zaka rabata da mahaukaciya sabon kamu ba, part d'in shi ta nufa tana zuwa ta kama murfin k'ofar d'akin shi cikin sa'a ta bud'e, tana jin ta bud'e tayi wata fitinanniyar kururuwa tare da cire d'an kwalinta ta shiga d'akin, Abbas da kwantawarshi kenan jin wannan abu yasa shi tashi zaune yana kallon mai shigowa, ganinta a birkice yasan ba lafiya ba dan haka ya yunk'ura da sauri ya mik'e zai tarbeta, ai kamar mai tab'in hankali haka ta...
๐๐๐
26/06/2020 ร 19:39 - Ummulkhairi: ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*BADAK'ALA*
๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ _*AHALI NA*_๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
๐ณ๐ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```
_Bismillahir rahamanir rahim_
_23_
Da dare ana ta kai da kawowa na hidimar bikin lieutenant inda aka fara gyara kayan cefanai na girkin gobe sai jiniya da odar motoci kamar zasu fasa unguwar, jim kad'an hayaniya ta fara gauraya gidan sanda mutane ke shigowa, mutanen gidan ne suka fara kimtsawa suna umartar yara da su koma sama, saida mutanen suka fara shigowa falon kad'ai aka fahimci ashe duk dangi ne na wajen Suley da kuma wasu daga cikin dangin Soueiba da mutanen arzik'i, duk girman falon nan sai gashi cike da mutane dan mace tafi talatin wanda suka zo kawo kaya, hakan kuma ya faru ne saboda maganar da Hajia ta fad'awa Husseina shiyasa take so ta bata mamaki.
Wata kyakyawar fuskar na gani sak Husseina sai dai wannan tafi d'an tsufa, amma fa ita ma tana cikin shiga ta alfarma da kuma dattako, su Zeinabu da Sa'ada ne suka matsa kusanta suka duk'a suna gaishe ta, cike da fara'a da sakin fuska ta amsa musu kafin ta kallesu a nutse tace "Ina su Ammar ne da Junaid? Yaran nan ko kad'an basa zuwa inda mutane suke sai dai in an zo inda suke."
Murmushi Sa'ada tayi tace "Kiyi hak'uri Hajia, kinsan ayyukansu ne sai a hankali."
Murmushi tayi ita ma tace "To, haka kuka ce dai, yanzu ina Hajiar take? Kayan jikanyarta muka kawo mata."
Zeinabu ce tayi saurin mik'ewa tana fad'in "Suna ciki, bara na musu magana."
Sa'ada ce tace "A'a ki barshi, ni zanje."
Mik'ewa tayi ta nufi d'akin Hajia, ba jimawa ta fito suka ci gaba da kawowa bak'i ruwa da jus jus wasu ko sanyi babu saboda basu sanar da zuwan nasu ba, minti ashirin Hajia ta d'auka kafin ta fito, fitowarta tasa kowa ya mayar da hankalinshi kan uwar yan uku, masha Allah, shine abinda wasu ke fad'a yayin da wasu ke mamakin rashin tsufan matar, wata arniyar shadda ce tasa yayin da ta watso wasu sark'a da yan kunnai da zobuna da awarwaro na zinariya, ba dan komai ba sai dan ta bayar da tsoro, dan hayaniyar da taji tasan ba zasu yarda su mata wannan gayyar ba babu wani dalili, wani d'aurin d'an kwali ne ta kashe mai sauk'in gaske wanda yasa manyan kitsonta sauka har gadon bayanta, kwalli ne kad'ai a idonta amma tayi kyau sosai sai d'aukar ido take ga jar fatar nan tayi wani shek'i, kamar d'awisu haka ta tako har ta zo kujerarta ta zauna tana shan k'amshi da k'arewa mutanen kallon hadarin kaji kallon mai bisa ruwa.
Wannan Izzar ta ta da kwarjini yasa wasu daga cikin matan ma suka manta da matsayinsu suka fara gaisheta, tabbas suna jin muryarta na amsawa amma basu ganin labb'anta na motsawa, nan dai *Hassana* (yar uwar Husseina) ta umarci a shigo da kayan, mace uku ce ta mik'e suka d'auko akwatinan masu bakwai bakwai a ciki har kala uku, da kuma d'aurin goro har guda biyu, har gaban Hajia suka diresu tana kallon akwatinan, wani matashin saurayi ne ya shigo da wani dallelen moton har falon ya aje shi inda babu mutane a ledarshi, Hassana ce ta kalli Hajia tace "To alhamdulillah, kayan Jibril ne muka kawo na Jamila, ga akwatina, ga moton da yace a kawowa amaryarsa dan ci gaba da zuwa makaranta, sai kuma..."
Ta fad'a tana saka hannu cikin jakarta ta fito da kud'i ta d'ora saman d'aya daga cikin akwatinan tace "Sai wannan, million biyu ne, sadakinta kuma sai ranar d'aurin aure."
Ko ba komai bajintar tasu ta birge Hajia, amma saita dake ta kalli Hassana wacce ita ma ba shiri suke ba tace "Ba laifi, amma yasan da cewa buzuwa zai aura ta b'angare na, ba zai birge ni ba har sai yayiduk wani abinda akeyi idan za'a auri buzuwa."
Wani murmushin gefen labb'a Hassana tayi tace "Wannan ba matsala bane, sai dai zaifi kyau ki fad'a mana yanda al'adun suke dan mu sani, duk da shima dai akwai abinda dole amaryar tayi kasancewarshi babarbare."
Wata hamshak'iyar dariya Hajia ta saki wacce ni dai tunda na fara rubutun nan banji inda tayi dariya ba, kallon Hassana tayi tace "Babarbare? Ta ina? B'angaren uwa?"
Murmushi tayi kafin ta kawar da kanta tace "Ba zan tsawwala muku ba, ina so kawai naga anyi guitar (jita) a daren d'aurin aurensu, za ayi shiga irinta buzaye ko kuwa mutum baya so, sannan ba wai Jibril ba kad'ai, har sauran angayen dole kowane ya kawo min kyautar rak'umi wanda ya amsa sunan rak'umi bayan tarewarsu da matansu, hakan kuwa shine zai sake nuna darajar yaran da kuma d'aga martabarsu."
Wani kallo Husseina dake gefe ta mata tace "Amma ai na d'auka wannan al'adar ana cikata ne idan aka samu yarinyar da mutuncinta?"
Murmushi Hajia tayi ta kalleta tace "Kina tsammanin duk yanda nake saka ido kan 'ya'ya da jikokina za'a iya samunsu da rashin kamun kai, ai wannan ba abu bane da za'a same shi a zuri'ata ba."
Murmushi Husseina tayi ta sassauta muryarta tace "Ke ina taki kyautar?"
Hassana ce ta kalleta sannan ta kalli Hajia tace "Ba damuwa, zamuyi duk abinda kika ce, ai Jamila da Jibril yan uwan juna ne, ko kyauta zai iya siya mata jajayen rak'uma bare kuma ya karb'i budurcinta."
Suna kammalawa sukayi sallama inda Hajia ta bud'a jakar hannunta k'arama ta bawa Sa'ada kud'i har jaka d'ari biyu tace ta basu tukuici kamar yanda akeyi, su kansu k'in amsar tukuicin sukayi suka ce ai yayi yawa, da k'yar Sa'ada ta matsa musu suka karb'a suka bar gidan kowa da abun fad'a a baki.
Suna tafiya Ummy ta zarce b'angaren samarin ta shiga da sallama, Amar Jibril da Junaid da kuma Ammar ta samu zaune a falon, gaishe ta sukayi dukansu banda Ammar da hankalinshi ke kan tv, zaune tayi tana kallon Jibril tace "Bak'i har sun tafi, munga kaya masha Allah, Allah ya sanya alkairi?"
Da murmushi ya amsa da "Ameen aunty."
Kallon Amar tayi tace "Saura ku, na ku sai yaushe?"
Amar ne yace "Ummy gobe mu ma zamu kawo."
Dukansu ta kalla tace "Sai kun shirya da kyau, dan Hajia tace za'a gudanar da wasu daga cikin al'adunsu na buzaye, musamman ma ku."
Ta fada da nuna su Ammar ta ci gaba da cewa "Tunda kunga ni kaina buzuwa ce, dan haka dole zata fi karkata abun ta b'angaren ku."
Amar ne yace "Ba damuwa bane Ummy, matsalar ni dai wannan k'aton rawanin ne bana tunanin zan iya d'aurawa."
Dariya tayi tace "Da kaina zan d'aura maka, tunda saika d'aura shine zaka fito a buzun."
Mik'ewa tayi tace "Saida safenku, ku kwanta da wuri kunsan gobe ne fa auren ubanku."
Sai lokacin Ammar ya kalleta ta wutsiyar ido ya kuma d'auke kan shi, fita tayi inda Ammar ya mik'e zai shiga d'aki, Amar ne yace "Ka tabbatar ka tashi da wuri fa, dan Abba yace ni da kai ne zamu take masa baya muna karb'ar bak'i."
Juyowa yayi ya kalleshi k'ala baice ba ya shige ciki ya barsu, Jibril ne ya gyara zama yace "Yau fa mutanen sun motsa."
Murmushi Amar yayi yace "Allah dai ya kyauta."
"Ameen." Cewar Junaid.
A nesa da k'ofar gidan ya paka mota ya tsaya inda kawu Mamu ya shiga dan kiran Zeituna, ba laifi gidan ya kaure da cacaniya alamar dai biki za ayi gobe, tuni dama ansa Zeituna ta shirya cikin wani kalar d'inki na atamfa wanda ba dan ta sanya hijab ba sai a mata dariya, dan kaf dangin babu mai wayewa ta zamani haka ita ma, dan ba k'awaye gareta ba bare tasan abu mai kyau ko marar kyau, lalle da kitso ma tayi sa'a a unguwar aka samu wanda suka iya suka mata, wata doguwar jagira aka ja mata tare da shafa mata jan jan-baki, fitowa tayi tana hard'e k'afafu saboda tsoron abinda zata tarar, tana isa ta inda yake ta tsaya kanta k'asa, tunda ta taho lieutenant ke hangenta yana raya abubuwa da dama, tana tsayawa ya sauke gilashin murya a d'an kausashe yace "Sai ki shigo ko, kinga ni ba yaro bane bare na fito na tsaya kowa na kallo na."
Gabanta ne ya tsananta fad'uwa ta zagaya ta kama k'ofar ta shiga, da k'yar ta janyo k'ofar ta rufe ta sake mayar da kanta k'asa tana wasa da yatsunta daga cikin hijabi, kamar yace ke ta zuba a guje take ji, wai yau gata a mota da Abban Ammar ana shirin d'aura musu aure gobe, jin shirun ne yasa ta tsargu ba tare data d'ago ba tace "Ina wuni."
Ajiyar zuciya ya sauke dan dama yana jiran tayi magana ne, kallonta yayi yace "Lafiya lau, ya hidima?"
Shiru tayi kamar ba taji ba, kallonta yayi kamar ya shareta sai kuma yace "Tun yaushe kike so na? Kuma kina ganin hukuncin da Alhaji ya yanke bai tauyeki ba? Har zuciyarki zaki iya zama da ni?"
Zeituna dake jin tambayoyinshi kamar saukar guduma a kanta tasan ba zata iya amsawa ba, sai kawai ta fashe da kuka tasa hannu ta toshe baki, sororo yayi yana kallonta da mamakin kukan na meye? Wani abu ya fad'a daya b'ata mata rai? Ko kuma sangarta ce tana so ya fara rawar k'afa yana rarrashinta? Ai ko abinda ba zai yiwu ba kenan, fuska ba annuri yace "Meye na kuka kuma? Na fad'i wani abu ne? Ko kuma dai takuraki akayi?"
Girgiza kai tayi hakan yasa yace "Shin akwai wani abu da kike buk'ata ne?"
Nan ma girgiza kai tayi hakan yasa ya kawar da kansa yace "To ni zan tafi, saida safe ko?"
Ji tayi wani kukan ya taho mata wanda yasa tayi saurin bud'e k'ofar ta fito, rufewa tayi ta taka da hanzari ta tunkarin gidan, saida ya ga shigarta kad'ai ya ja d'an k'aramin tsaki ya tayar da motar ya bar unguwar.
*11: 49* na dare Ammar ya mik'e zaune tsakiyar gadonshi, tsaki yayi tare da kama hantsar wandonshi yace "Shikenan mutum idan baida aure baya da nutsuwa har abada."
Sakin wandon yayi ya sauko daga kan gadon, ban d'aki ya shiga ba wani jimawa ya fito, rigar wandon baccinshi ya d'auka fara ya saka ya fito, duk wani kwanon abinci daya gani a falon nasu saida ya duba amma babu abinci, fridge ya duba nan ma sai lemu kawai da ruwa, wani tsakin ya kuma ja tare da nufa k'ofar fita, acan bayan gida yake jin hayaniyar matan suna aiki, kai tsaye falon Hajia ya shiga wanda ke bud'e har yanzu saboda matan basu shiga ba bare a rufe, madafa ya wuce da niyyar shiga sai yaji k'ofar a rufe, baiyi mamaki ba dan dama idan dare yayi ana rufe k'ofofin ko ina, dawowa yayi da niyyar fita kawai dan ba zai iya jura jin bak'ar magana daga bakin kowa ba, ta kusurwar d'akin Alhaji yabi zai wuce sai yaji motsi, d'an murmushi yayi ya matso ya kama k'ofar zai bud'e sai yaji muryar Alhaji na magana da alama addu'a yake yana fad'in " *Allah kaine Allah, Allah kai kace mu rok'eka zaka amsa mana, gashi ina rok'onka kaina k'asa, Allah ka kare min zuri'ata da ahalina, Allah ka karesu daga aikata alfasha, Allah ka kare min 'ya'ya da jikokina daga sharrin zina, Allah ka kub'utar dasu da ikonka, Allah kai shaidane ban tab'a aikata zina ba, ban tab'a k'etara iyakar wani ba ta hanyar cin zarafin iyalinshi, amma ya zama dole na rok'awa iyalina kariya saboda sharrin zamani, sannan iyali suna kimtsuwa ne idan ka zab'ar musu uwa ta gari, nayi kuskure tun farko dana amince da auren Zeeya'atu, duk da a waccen lokacin ina da k'arancin ilimin addini ban kuma farga ba saida muka hayayyafa, Allah ina rok'onka ka kare min zuri'ata kada zunubin zina da mahaifiya ko kakarsu ta aikata a lokacin k'uruciyarta ya shafesu, Allah ka nesanta su da laifin zubar da cikin da mahaifiya kuma kakarsu tayi kar ma ya shafesu daidai da k'wayar zarra, Allah ka sani baiwar nan taka har yanzu bata neman shiriya daga waccen laifin, kullum tsanar mazinata take k'arawa a zuciyarta saboda tasan muninta, Allah ka shiryeta dan tsarkin mulkinka, Allah ka farkar da ita ta gane kurenta na baya ta buba gareshi, astagfirullah, astagfirullah, astagfirullah ya Allah.*"
Jin wannan addua'r yasa Ammar sakin k'ofar yayi jim, Hajia? Hajia dai, wannan shine dalilinta na tsaurara sa idonta akan zuri'ar ta kenan? Wannan shine dalilin da yasa take k'in yayan da aka haifa bata hanyar aure ba? Ashe ita ma tayi rayuwarta a baya ta holewa? Kukan da cikinshi yayi ne na yunwa ya farkar da shi daga tunaninshi, dafe cikin yayi ya juya ya kalli d'akin Ummy, murtuke fuska yayi kafin ya tukari d'akin da niyyar tambayarta makullin madafa, dan ba zai tambayeta abinci ba yasan zata fad'i bak'a ne, yana isa ya zura hannu zai bud'a sai yaga k'ofar ba rufe take ruf ba, turawa yayi ya ga ta bud'e sai kawai ya shiga cikin takon isa da k'asaita.
Mahaukacin turarenshi ne ( *Respond*)ya ganar da ita shine, da sauri ta d'ago ta sauke ido a kanshi saida gabanta ya fad'i, mamaki take meya shigo dashi a wannan lokacin d'akin Ummy? Dare fa yayi, shi kanshi mamaki yake ganinta a tsakiyar gadon Ummy zaune da littafinta na makaranta da kuma farantin kankana a gabanta, cikin kallon tuhuma ya tsaya gaban gadon fuska a had'e yace "Me kike anan d'akin?"
D'auke idonta tayi daga kanshi ta harareshi ta wutsiyar ido a zuciyarta tace "Kai baka ga abinda nake bane?"
A zahiri kuma cewa tayi "Karatu nake."
Cike da kallon raini yace "Yawon biki ya hanaki d'aukar darasinki ko? Da alama kuma jarabawa zakuyi gobe, to Allah yasa ki fad'i watak'ila ki shiga hankalinki."
Baki bud'e ta kalleshi da mamaki irin wace irin magana ce wannan? Fahimtar kallon yasa shi cewa "Eh naje na fad'a, ko zaki ci min uwa ne?"
Wani murmushin baka da hankali ta masa tace "Ah haba dai ranka shi dad'e, ni na isa, Allah dai ya k'ara girma."
"Zaki iya mana, ba kece sarauniyar ce min Allah ya isa ba."
Yanda yayi maganar yasa ta zabura ta durka daga kan gadon da nufin shigewa ban d'aki, da sauri yasha gabanta ya tsaya k'ik'am, sai lokacin ya k'are mata kallo ya fahimci ashe wando ne iya gwiwa a jikinta da rigarshi saidai basu kamata ba, sai wata hula data saka bak'a mai duwatsu masu k'yali a gabanta, kasancewar yafi ta tsayi sosai yasa yayi k'asa da kanshi yana kallon k'irjin ta wanda da gani kasan rigarce kawai babu bras, kawar da kanshi yayi ya d'an cije leb'e, ba tare daya kalleta ba yace "Koma ki zauna, ai idan na tashi hukuntaki duk inda zaki shiga zan biki."
Turo baki tayi gaba ta kalleshi kamar zatayi kuka, yana kallonta yayi saurin d'auke kanshi ya furta "Ya Allah." Lumshe ido yayi ya d'aga kai sama, wannan yanayin da tayi ba k'aramin tashin hankalinshi tayi ba, "Meyasa take birgeshi wani lokacin?"
Kafin ya samu amsa ya sake kallonta rai a b'ace saboda halin da take k'ok'arin jefashi yace "Ki koma ki zauna na ce."
Kamar sakara haka ta saki baki da tunanin to meyasa kai ba zaka tafiyarka ba? Juyawar da tayi ita tafi sa shi yin nadama, gaskiya Allah ya musu hallita ta wannan fanni kam sai godiyar Allah, juyawa yayi ya zagaya inda ya fara tsayawa ita ma ta koma ta zauna, kankanar da take sha ya d'auki yanka d'aya yasa a baki ya guntsira, wani matashin murmushi yayi yace "Kankana."
Kallonshi tayi sai kuma ta mayar da kallonta ga littafinta, sauran daya rage hannunshi ya mik'o mata da fad'in "Sha."
Wani yamutsa fuska tayi alamar k'yama k'arara, sake zuro mata yayi kamar zai saka mata a baki hakan yasa tayi saurin kawar da kanta, cikin tsawa