Showing 222001 words to 225000 words out of 325849 words

Chapter 75 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

522

Middle Ads

yasa iyalinki ke matuk'ar tsoronki, Hajia idan kana son yaro ya saba da kai ya dinga jin maganarka ba tsanani ke sa haka ba, jawo shi a jiki da wasa da shi da kuma durmiya cikin al'amuranshi, shi ke sa ba mace ba har namiji ya saki jiki da kai yana fad'a maka sirrinsa, Hajia ni baki gani ba har yanzu bana iya wani sirri da mahaifiyata ba, Abba ma yanzu ne kad'ai na fara fad'a masa damuwata, ke ma hakane Hajia ya faru da ke, da ace tun farko kinsa iyayenmu a jikinki kin nuna musu so da k'auna wallahi da sanda abin nan ya faru kawu zai sanar dake ko da yasan ranki zai b'ace, kiyi hak'uri Hajia idan abinda na fad'a ya b'ata miki rai."

D'agowa tayi ta kalleshi ido cikin ido tace "Ammar me kake nufi? Wace irin soyayya ce zai nuna musu da ban nuna musu ita ba?"

Murmushi yayi yace "Hajia kina son 'ya'yanki sosai mana, saboda kin haifesu haihuwa kuma ba wasa bace, matsalar d'aya ita ce ba kya nuna musu soyayyar a zahiri."

Wani dogon tsaki taja ta gyara zamanta tace "Ban gane me kake nufi ba, kawai ka fitar min a d'aki."

Murmushin gefen labb'a ya mata ya mik'e tsaye yana kallonta yace "Zan fita Hajia, amma kiyi tunani akan abinda na fad'a miki, domin kuwa na fi kowa son ganin kan gidan nan ya had'u."

Har ya juya sai kuma ya tsaya ya juyo yace "Ban san ko zaki iya tuna ranar k'arshe da kika tab'a bin iyayenmu da addu'a ba ta alkairi, misali idan sun miki alkairi ko zasu fita aikinsu ko kuma zasuyi balaguro, Hajia ke a ganinki duk abinda suka miki abune dama da yake wajibi akansu dan haka babu buk'atar kiyi musu godiya ko addu'a, Hajia kina ganin kin haifesu kin gama musu komai a rayuwa, dan haka ya zama dole akansu suyi duk abinda kike so, amma kina mantawa da ubangijin daya hallicesu kuma ya halliceki, to Hajia ko ubangiji yana bawa bayinsa wata dama, wannan damar kuwa ita ce talala da yake mana dan mu tuba ga laifikanmu, amma ke..."

Girgiza kai kawai yayi ya fita daga d'akin, da kallo ta bishi da mamaki, to wai akan me yake magana? Soyayya? Addu'a? Jansu a jiki? Tsanani? Tab'e baki kawai tayi ta jinjina kai tace "Dan na saki jiki da kai shine har zaka fad'a min magana."

Zaune suke a falon sama suna hirar da babu nishad'i a ciki sakamakon abinda ya faru, Zeinabu ma ko fitowa ba tayi ba bare ta gansu taji kunya, Hamna na gefe d'aya k'asan carpet ta mik'e k'afafu, Shureim ma na nesa dasu saboda k'arfin pankar da suka kunna saboda guje mishi kamuwa da mura, motsawa yayi tare da fashewa da kukan daya shiga duka kunnuwan iyayen nashi biyu, autar Soueiba *Basira* ce tayi karanbanin rugansu d'aukoshi, yanda ta d'auko shi ba daidai ba yasa Hamna zabura daga zaman da take da gudu har tana take rigarta ta nufeta, tana zuwa ta rumgoshi jikinta ta karb'eshi tana kallon Basira tace "Uban wa yace ki d'aukeshi, sai kin ji masa ciwo hankalinki zai kwanta, baki ga jikinsa baiyi k'wari bane da zai juri wannan wahalar."

Tsaki tayi cike da jin haushi har zuciyarta ta juyo da niyyar zaunawa, saida ta zabura ganin Ummy ita ma ta taso a bayanta tsaye tana kallonta, wani kallo ta mata mai cike da gargad'i sannan ta karb'eshi ta koma ta zauna, gabanta fad'uwa kawai yake tana satar kallon su Soueiba da Zeituna, su dai abun ya basu mamaki na saurin zaburar da tayi kamar daga cikinta d'an ya fito, amma bayan haka basuyi tunanin komai ba, Hamna na zaunawa wayarta tayi k'ara, dubawa tayi taga Amna ce, d'auka tayi sai kawai tace "Dan Allah yer uwa ki zo."

Wani iska ta furzar dan ita fa bata so tana kusantar da kanta gare shi, bata so tana ganinshi akai akai wani abu take ji, tabbas kuma ba tsana bace sai dai tana jin haushinshi, kashe wayar kawai tayi ta gyara zaman kallabin doguwar rigarta ta fita.

Tana saukowa ta zo tsakiyar falon shima ya fito daga d'akin Hajia, a tare suka kalli juna da sauri ta d'auke na ta idon ta k'ara sauri dan ta fita, shima kuma cikin takon sauri yake dama shiyasa suna ka kai daf da k'ofar a tare, zata fita ba tare data bari ya wuce ba shine abinda ya bashi haushi, tsayawa yayi ya mata wani irin kallo yace "Wuce uwata."

Wani kallon sama da k'asa ta masa ta fice kam abinta, a baya ya binta yana kallo kuma ita ma can ta nufa, kawai baya jin masifa ne amma da saiya gabza mata mari ko ta koyi girmama shi, tana shiga ta sameta zaune k'asa kamar kullum, jin takonshi a bayanta yasa ta d'aure fuska tace "Me zan miki da kika kirani?"

Turo baki Amna tayi tace "Shikenan fa tunda muka dawo daga asibiti baki zo kika dubani ko ina lafiya ba."

"Akan haka kika kirani?" Gira ta d'aga mata kawai, juyawa tayi tace "Saida safe."

Da kallo kawai ta bita haka shima, zaune yayi kusan Amna yace "Yarinyar can k'uruciya na damunta."

Kallonshi tayi tace "Tana damunta ko tana damun mu?"

Saida ya rumgumota jikinshi yace "Ai ke kin kusa girma da zaran kin fara aje min yara."

*Da safe* Alhaji na zaune ya zo dubata colonel ma ya shigo dan yana son yin sammakon komawa, sallama yayi Alhaji ya amsa, saida ya kai har k'asa cikin tsananin ladabi ya gaishesu, Alhaji dai ne ya amsa banda Hajia dake kallonshi, yana d'agowa suka had'a ido yayi saurin sauke kanshi k'asa, shiru ne ya d'an ratsa d'akin kamar anyi sabuwar mutuwa, ganin dai ba zatayi magana ba yasa ya kalli Alhaji yace "Alhaji zan koma ne dama."

Cikin dattako yace "To Husseini, Allah ya tsare ya kiyaye."

"Ameen nagode." Ya fad'a yana kallon Hajia yace "Hajia zan..."

Saida ta d'ago daga jinhinar da tayi cikin katse hanzari tace "Wallahi ranka zai mugun b'aci idan ka ambaci suna na."

Marairaicewa yayi kamar yaro yace "Hajia dan Allah kiyi hak'uri ki yafe mana."

Saukowa tayi daga gadon tace "Akan me zan yafe maka? Husseini kasan me ka aikata kuwa? Ni zaka wulak'anta."

Alhaji ne ya mik'e tsaye ya kalleshi yace "Kaga tashi, tashi ka tafi inda zaka Allah ya kiyaye hanya."

D'aga kai yayi ya kallesu duka saiya kasa tashi, cikin d'aga murya Alhaji ya sake cewa "Ka tashi ka tafi nace."

Mik'ewa yayi yace "Na tafi." Yana fita Hajia ta kalleshi cike da jin haushi tace "Wai me yasa kake min hakane? Ya zanyi magana dashi kawai ka wani ce ya tafi? Ina ruwanka to da abinda zamu tattauna? Meya hana kai ka fita idan ba zaka sauraremu ba."

"Dakata Zeeya'atu." Ya fad'a yana d'aga mata hannu, d'orawa yayi da "Da alama har yanzu baki san annabi ya faku ba, to ki bud'a kunnenki da kyau ki saurareni, babu wani hukunci ko matakin da zaki d'auka kan lamarin nan, dukanmu zamu duk'ufa ne mu nemi gafarar ubangiji kan zunubanmu, dan idan da wanda yayi sanadiyar faruwan hakan to ke ce."

Nuna kanta tayi tace "Ni? Ni fa kace! To me nayi ni d'in? Ce musu nayi su aikata? Ko kuma ina wurin sanda suka aikata bare ya zama laifina ne dana barsu suka aikata."

Saida ya tsaya daf da ita yace "Ke kin manta abinda ake fad'a ne cewa duk abinda kayi shi za ayi maka?Ai indai zakayi d'in to fa ka kwana da shirin sai an maka."

Rarraba ido ta fara yi alamar rashin gaskiya, sai kuma ta nad'e tabarmar kunyarta da hauka tace "Ban gane ba? Kana nufin nima nayi ne ko?"

Dariyar kin raina min hankali ma ya mata yace "Ni bance ba, amma dai ki sake kula ki kuma nemi yafiyar ubangijinki, idan ba haka ba wallahi yanzu irin abunuwan nan suka fara faruwa, kuma ki sani su ne zasuyi ajalinki, dan haka zaifi kyau ki koma ga Allah ta yanda in mutuwar ma ta zo ki cika da imani cikin kyakyawan yanayi."

K'wank'wasa k'ofar suka ji anyi wanda yasa su kallon k'ofar, Alhaji ne yace "Shigo."

Ammar ne tare da Amar da Amna da kuma Jibril, da sallama suka shigo dukansu, gaishesu sukayi sosai kafin su kalli Hajia su ce "Ya jiki?"

Saida ta wani d'aure fuska tace "Da sauk'i."

Ammar ne yace "Hajia kin karya kuwa?"

Girgiza kai tayi alamar a'a, juyawa yayi yana fad'in "Ya kamata ki daina jinkirin nan fa."

Amna ce tayi saurin cewa "Yah Ammar bari na karb'o."

Tsayawa yayi ita kuma ta fita, Alhaji ne yace "Ina Junaid yake?"

Amar ne yace "Anya Junaid ya kwana gidan nan kuwa? Dan ni dai jiya sai dare sosai na shigo amma banga motar shi ba, yanzu ma kuma babu motarshi a wajen ajiyewa."

Kai Alhaji ya girgiza, Amar ne ya fara mik'ewa yace "Zan wuce ni lokaci na tafiya, Hajia Allah k'ara sauk'i."

Saida ya mik'e tace "Shalele ka zauna tare dani mana, kai kad'ai nake son gani a kusa dani, wasu banda b'ata min rai babu abinda suke yi."

Ta k'arashe maganar tana kallon Alhaji da kuma Ammar, murmushi dukansu sukayi sai Amar da yace "Kiyi hak'uri Hajia, wallahi akwai aiki sosai a ofishi, amma na miki alk'awarin zan dawo da wuri sai na zo mu zauna."

Murmushi ta masa tace "To karka manta fa, saika dawo."

Ficewa yayi Amna kuma ta shigo, Jibril ma tashi yayi ya fita haka ma Alhaji, yau ma kamar jiya da kanshi ya zuba abincin ya zauna kusa da ita ya fara d'ebowa a cokalin ya nufi bakinta, kawar da kai tayi tace "Bani zan ci da kai na."

Girgiza kai yayi yace "Idan da kanki ne ba zaki ci dayawa."

Sake tura mata cokalin yayi ta bud'a baki ta karb'a, yana cikin bata Ummy da lieutenant suka shigo tare, su ma gaishe ta sukayi da tambayar jikinta ta amsa ba yabo ba fallasa, kallonta Ammar yayi ya d'an sunkuya yace "Baki tambaye su Shureim ba."

Kallonshi tayi amma yanda yake kallonta yasa taji ta kasa masa gardama, kallon lieutenant yayi dake rik'e dashi kamar zata bud'a baki sai kuma ta ga ai ba girmanta bane sai kawai ta sake kawar da kanta, Ummy da lieutenant mamaki suke sosai har da Amna ganin wai Hajia ce ke karb'an abinci daga hannunshi, da wannan mamakin Ummy tace "Hajia Allah k'ara sauk'i, zan tafi gurin aiki amma ba zan jima ba saboda na dawo kusa dake."

Ko kallonta ba tayi ba harta fita, lieutenant ma sallama ya mata suka fita, Amna ce ta kalleshi tace "Yah Ammar zan duba Hamna na dawo."

Kai ya jinjina mata ta fita, saida ya gama bata ya bata maganin tasha ya mayar da komai ya aje sannan ya kalleta, cikin dakakkiyar murya yace "Hajia gaskiya Alhaji ya fad'a miki, akwai buk'atar mu tuba ga Allah."

Ya fad'i hakane saboda sanda ya riga kowa isowa bakin k'ofa yaji kalamanshi na k'arshe cewa *"Dan haka zaifi kyau ki koma ga Allah ta yanda in mutuwar ma ta zo ki cika da imani cikin kyakyawan k'arshe."*

Ido ta zaro tana kallonshi, duk tsoro ya bayyana tare da ita tace "Me? Ammar lab'e kake mana dama?"

Murmushi ya mata yana girgiza kai yace "Banda wannan lokacin Hajia, watak'ila Allah yasa na jini saboda akwai abinda zan iya yi akai."

"Me kaji d'in?" Ta fad'a idonta a waje, saida ya had'e dariyarshi ya kalli idonta sosai yace *"K'uruciyarki, rayuwarki ta baya Hajia, wacce babbu wanda yasan da ita sai Alhaji sai kuma ni da naji yana fad'a a cikin addu'o'inshi."*

Cikin rawar hannu ta d'oki hannunta na dama ta rufe baki da taji numfashinta na neman gagararta, a hankali a hankali ta fara lumshe idonta da taji kanta na juyawa tare da sara mata, mik'ewa yayi ya kwantar da ita kan matashi, yatsu biyu yasa ya dafa kanta inda yaga tana dafewa da hannu, bud'a jakarshi yayi ya fara dube dube, da k'arfi ya d'aga daga sunkuyawar da yayi yace "Shiit."

Da gudun bala'i ya juya ya fita, kamar wanda kura ta biyo haka yake gudu har wanda suka ganshi suka tsaya kallonshi, b'angarensu na samartaka ya shiga cikin sauri yake bud'a kowane d'aki ya shiga, d'akin magungunanshi ya shiga cikin sauri sosai ya d'auko kwalin wata allura da abin k'arin numfashi (oxygène) haka ya rumgumoshi a jikinshi ya sake fitowa da gudu.

Yana shigowa ya sameta yanda ya barta sai jan numfashi take, cikin gaggawa ya samu wuri ya aje bunburutun oxygène d'in ya jona ya saka mata, wasu allurai ya had'a yasa a ciki take wani iska ya dinga taimakawa Hajia wajen numfashi inda daga k'asa kuma wasu ruwa ke ta tafasa, k'ura mata ido yayi yana kallo sannu sannu numfashinta ya fara saisaituwa, ajiyar zuciya ya sauke tare da jawo kujerar gaban madubinta ya zauna yana kallonta, Zeituna ce ta shigo da sallama ya amsa, kallonta yayi yace "Uwa antashi lafiya?"

Tana kallon Hajia tace "Antashi lafiya? Ya kuma naga an sa ma Hajia wannan?"

Kallonta yayi shima sai kawai ya bushe da dariya yace "Kin ganta nan fa sai alamun margaya take nunawa."

Duk da tana lumshe ido bacci na son d'aukarta saida ta kalleshi, hannun dake kusa dashi ta d'aga mishi tana son kama nashi hannun, da sauri ya had'a hannunshi da na ta, da alama magana take so tayi sai kuma ta fara lumshe ido, a haka kuma bacci ya d'auke ta ya saki sannunta, haka kawai yaji ba zai iya yin nisa da ita ba a halin da take ciki, dan haka ya kira asibiti ya fad'a musu yana da wani marar lafiyar da yake dubawa, duk wanda zai gani yau a basu rendez vous da yamma.

Sosai Labaran ya mishi fad'a da nuna baiji dad'in abinda ya faru ba, Soueiba dai abinda ta fad'a mishi shine, tunda hakan ya faru da farko dai ayi hak'uri tunda ba jiya ko yau bane haka ta faru ba, sannan su rik'e yarinyar su kula da ita tunda dai dama duk yan uwa ne, a banza ma zasu iya rik'eta bare kuma jikanyarsu ce, na biyu kuma Jamila dake ikrarin ya rabu da ita suyi k'ok'ari su ga auren bai mutu saboda wannan matsalar, da haka ta kwantar masa da hankali suka fuskanci gaba.

Bai fita ko ina ba sai wayarsa da yake dannawa yana gudanar da harkokin daga nan zaune, agogon hannunshi ya kalla sannan ya kalli Hajia, tabbatarwa da yayi daga yanzu zuwa kowane lokaci zata farka yasa shi fita daga d'akin ya fito, a falo ya gansu zaune suna ta hira abinsu cikin raha, fuska a had'e ya kalleta yace "Ke had'a ma Hajia abinda zata ci, amma kada kisa arΓ΄me (d'and'ano) tare da abinsha naturel."

Kamar bata ji ba dan haka ya sake kallonta yace "Dake nake fa."

Saida ta harari gefenta ta mik'e tana fad'in "Sai kace banda suna wani wai ke, menene ma'anar ke?"

Kallonta yayi ya cije leb'en k'asa, zai matso kusanta ta rufa da sauri ta shige madafar, dariya Amna tayi ta girgiza kai tace "Naga ranar da zaku girma."

Kallonta yayi yace "Amna nine ban girma ba? Ni kike had'awa da waccen yarinyar? Ni Amna?"

Kanta yayi kamar zai mazgeta hakan yasa ta rufe fuska da hannaye cikin muryar kuka tace "Kayi hak'uri to ba kai ba, ni ita nake nufi."

Dariya yayi ya sunkuya ya sumbaceta ya juya ya koma d'akin Hajia, minti arba'in ta d'auka kafin ta shigo d'akin da sallama, d'agowa yayi yana kallonta har ta shigo ta aje farantin hannunta, juyawa tayi zata fita yace "...


*Alhamdulillah*
14/10/2020 Γ  00:58 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_50_


"Uban waye zai zuba miki?"

Juyowa tayi ta murgud'a baki tace "Kai musaki ne?"

Tattare rigarta tayi ta tafi a guje, takon da baifi uku ba ya rik'o wuyan rigarta da k'arfi yayi baya da ita, k'ara tayi wacce tasa Hajia k'arasa bud'e idonta ta kallesu, hannu ya d'aga da niyyar kasheta da mari, amma me sai yaji ba zai iya tab'a lafiyar jikinta har haka ba, tsaki ya ma kansa kafin yasa k'arfinsa ya damk'i gashinta yana fad'in "Sa'anki ne ni?"

K'ara tayi tare da rintse ido tana k'ok'arin cire hannunshi a kanta, hannu ya d'aga kamar zai mareta, da sauri ta rik'e k'afarshi cikin kuka tace "Yi hak'uri to zanyi, zan zuba, zan zuba wallahi, dan Allah yi hak'uri."

Da k'arfi yace "Tashi to."

Tashi tayi ta dawo inda ta aje kwanukan ta fara zubawa, saida ta gama ta mik'a mishi tace "Gashi."

D'aga idonshi yayi ya mata wani kallo yace "Aje a kaina."

Saida ta turo mishi baki kafin ta aje gefen gadon, juyawa tayi saida ta bud'a k'ofar tayi shirin rufeta sannan ta zuro kai tace "Allah ya saka min cutar daka min."

Tana fad'a ta ari na kare, cikin nutsuwa ya bita da kallon rashin fahimta, cutar daya mata? Wace cutar kenan? Abinda ya faru baya ko kuma yanzu? Tab'e baki yayi ya mik'e ya kama Hajia ta tashi, saukowa tayi daga kan gadon yana rik'e da hannayenta, ta mik'e tsaye Zeituna ta shigo da sallama, da sauri ta k'araso tana kwance goyon Fatima ta aje kan gadon tace "Yah Ammar bari na kaita."

Sakinta yayi suka shiga ban d'aki shi kuma ya d'auki Fatima yana mata wasa, baki kawai ta wanko ta fitota koma ta zauna, ita ta zuba abinci ya bata da kanta ta ci tasha lemu, maganin ya bata ta bata sannan yace ta d'an zauna, amsar Fatima tayi suka fita dan aikin gabanta, kallonta yayi shima yace "Hajia nima zan tafi asibiti yanzu, dan Allah kada kiyi wasa da magunan nan."

Ya fad'a yana nuna mata su, juyawa yayi zai fita tace "Ammar zo."

Juyowa yayi ya tsaya ta nuna masa

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login