Showing 3001 words to 6000 words out of 325849 words
d'inkin da zaka gani a jikinta na atamfa har gwara riga yar kantin, domin kuwa bata saka kaya inba ji tayi sun kama jikinta ba sosai, bata saka zane sai siket ko doguwar riga, haka Hamna bata fita wajen biki ko wani shagali ba tare da tayi k'arin gashi na kanti ba, ko tayi kitso ko ta saka shi hakanan, indai ba sallah take ba ko zata tafi islamiyya to baka ganinta da hijab duk inda take ko zataje, yanzu haka sun shiga ajin lycée shekara biyu data wuce, rawar kanta da rashin kunyarta yasa basa shiri ko kad'an da Ammar, tana da rashin kunya da fitsara da mayar da martani, shi kuma baya d'auka hakan yasa yake mata dukan mutuwa inya samu dama, dan in mahaifiyarsu ko mahaifinsu na nan basa bari su ke d'aure mata gindi, domin kuwa a hannunsu suka tashi tun suna k'anana sosai, hatta filin sada zumunta na ahalin *Gaga* da aka bud'e akafar sadarwa ta WhatsApp Ammar fita yayi saboda Hamna kawai, saboda ko hira ake muryarta ce tafi ta kowa fitowa, ga tsokanar mutane wanda ya girmeta da wanda ta girma, ga yawon turo hotuna na sallama daban na barka da rana daban na barka da dare daban, shiyasa ranshi ya b'ace ya fita saboda haushinta yake ji sosai, duk abubuwan nan da Hamna ta had'a sab'aninsu ne ke ga Amna, dan ita ko magana ma bata cika son yi ba, ba tada kwarmniya ko kad'an, dan inma Hamna ta tsokaneta sai dai tayi banza da ita, to fa da wannan ne yasa ko murmushin Ammar baka gani a gidan, ga haushin hana shi aikin da yake so, ga takaicin rashin kunyar da Hamna ke mishi in tana cikin mutane.
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️
Junaid na barin nan wajen masoyiyarshi ya nufa inda yasan zai iya ganinta, tun daga wajen masallacin ustaz Sani d'an jatau yake baza ido amma shiru harya k'arasa bakin *pacific*, wani lungu ya shiga da motar dan yasan suna zama nan ita da k'awar ta, amma rashin sa'a bai samu ganin ko d'aya daga ciki ba, kiran wayar k'awarta yayi dan Maryama bata d'aukan kiranshi tana ganin kamar yana takura mata, a lokacin sun fito daga cikin d'akinsu tana rufewa da d'an kwad'o kiran ya shigo, k'awar mai sunan *Iklima* ce ta kalleta tace "Mutuminki ne fa Mari, me zan ce mishi idan na d'auka?"
Masha Allah, tabbas Maryama mai kyau ce ta gidan gaba, ga ta doguwa sosai da d'an kumari, gashi fatarta jawur da ita duk da tana shafa mai amma kasan ita ma akwai asalin farinta, akan luma-luma kumatunta kuma wasu tsage ne suka k'awata fuskar har guda bibbiyu, a take tace "Kawai ki fad'a masa bama tare dake, kar ma ki fad'a masa na fita."
Zata d'auka kiran ya tsinke kuma sai baiyi gaggawar maidowa ba, hanyar gidansu ya nufo wanda ke bayan masallacin daya bari a farko, yana sake kira kuma Iklima ta d'auka tace "Barka da dare."
"Barka Hajia Iklima, ya kike?" Cikin sakin fuska ta amsa da "Lafiya lau, ya yau?"
Saida ya sauke ajiyar zuciya yace "Yau da dama, ina mutuniyar take? Nasan kema kinsan bata d'aukar kirana."
Kallon Maryama tayi suna kan hanyar fitowa daga gida, kewayen wata mata Maryama ta lek'a ta same su zaune a d'an filin wurin suna kallon telbijin, matar ce ta kallesu tace "Mari fita zakiyi ne?"
"Eh maman *Husna*, ina *Huda* take ne?"
Da sauri wata yarinya da ba zata wuce shekaru biyar zuwa shida ba ta mik'e tsaye ta tunkarota, tana suwa ta rik'e hannunta tace "Mamma, yau ma fita zakiyi?"
Da murmushi ta shafa fuskarta tace "Fita zanyi Huda, amma yau ba zan jima ba zan dawo kinji."
Marairaicewa tayi ta k'ara matse hannunta tace "Mamma kullum haka kike cewa ba zaki jima ba, me ya sa ba zakiyi zamanki a gida ba?"
Ba annuri a fuskarta tace "Saboda saina fita muke samu mu ci abinci." Hannu tasa a jakarta ta fito da dala ashirin (ba zasu gaza naira ashirin ba), bata tayi tace "Gashi kije Aminu ki siyo madara kisha, idan kinji bacci kije lungunmu ki kwanta nayi shinfid'a."
Juyawa tayi zata fita taji ta rik'e hannunta, tana juyowa yarinyar tace "Mamma meyasa ke saida dare kike nemo mana abinci? Ki dinga zuwa da rana mana tunda baki komai a wannan lokacin."
A hankali ta zage hannunta daga na yarinyar ta sake juyawa, kamar saukar ruwan sama ta tsinci muryar Huda na cewa "Mamma kenan da gaske ke 'yar iska ce?"
Tsayawa tayi amma bata iya juyowa ba saboda hawayen da take, Iklima na ganin haka ta fice ta barta, da sauri ta taka ta barta nan ta fita, amma saboda wayo da kuma k'uruciya sai yarinyar ta fito da gudu har k'ofar gida tana kuka cikin d'aga murya tace "Ashe dama ban da uba, ni shegiya ce, to ni dai bana son neman abincin naki hakanan, daga yau ba zan sake cin abincinki ba idan kin kawo, kije kawai karma ki..."
Marin da Maryama ta d'auke ta dashi yasa yarinyar fad'uwa k'asa, wani daga cikin masu zama a k'ofar gidan ne ya kama Huda ya d'auke ta yana rarrashi.
Iklima dake amsa wayar Junaid shi kuma a daidai lokacin ya k'araso k'ofar gidan, cikin rashin sani tace "Mari ai tun rana rabona da ita dana barota gida, izuwa yanzu kuma nasan ta yada zango a wani wurin."
Daga inda yake ya hango fitowarta sai Maryama dake bayanta, daga cikin wayar yayi murmushi yace "...
*Allah ka mana kyakyawan k'arshe.*👏
18/05/2020 à 13:46 - Ummulkhairi: 👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*BADAK'ALA*
👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
👨👩👧👦 _*AHALI NA*_👨👩👧👦
_Bismillahir rahamanir rahim_
_2_
Daga cikin wayar yayi murmushi yace "Karki damu ma naga hasken idaniyar tawa."
Da sauri ta d'auke wayar daga kunne ta juya hagu bata ganshi, tana juyawa dama ta hangoshi yana fitowa daga motar, a hankali ta fara takawa wajen shi sai Maryama dake biye da ita a baya wacce bata san meke faruwa ba, saida taga Iklima ta tsaya wajenshi kad'ai ta fahimci mayenta ne ya sake dawowa, tsaki tayi ta tafi a harzuk'e zata wucesu kamar bata gansu ba ma, da sauri ya tare gabanta da gudu gudu, kallon juna sukayi kafin tace "Malam matsa min a hanya ko."
Kai ya girgiza duk yayi kalar tausayi yace "Ba zan iya ba Maryama."
Tab'e baki tayi tace "To saika zauna kayi gadin wurin ko, ai shi zaka iya na sani dan kamar kaine ka yankewa wahala cibiya lokacin da ta zo duniya."
Murmushi yayi dan kalaman da suka fi wannan ma ya jisu a bakinta, zata rab'a ta wuceshi ya sake tare gabanta yace "Dan Allah Maryama ki saurare ni, wai me ya sa har yanzu idonki sun kasa gane miki masoyinki na gaskiya ne? Maryama me ya sa ba zaki yarda da soyayyar da nake miki ba?"
Da k'arfi tace "Saboda duk maza halinku d'aya ne, kana son samun soyayyata ne saboda kawai kana son jikina, kuma na fad'a maka ni yanzu a ruwa nake, karuwa ce ni, ba buk'atar saika yaudareni kafin ka samu jikina, 2000f cfa (jaka biyu) kad'ai ka bani zan iya kwana tare da kai, saboda ni k'aramar karuwa ce da aka cewa *je ki kya gani*, abinci kawai nake nema da zan ciyar da kaina da kuma 'yata, tunda muma halitta ce ba zamu iya rayuwa babu abinci ba, amma kai ka tsaya sai wahalar da kanka kane kana b'ata min lokacin da rera min wani banzan wak'anka wai kana so na, mtssss."
Tunda ta fara magana ya saki baki yana kallon nata k'aramin bakin, har k'asan zuciyarshi tana birgeshi, yana son kallon kyakyawar fuskarta mai d'auke da tsagu har hud'u, wanda kowane kunci ya samu bibbiyu, amma ta kasa fahimtarshi har yanzu, wani murmushi yayi mai kama da ciwo yace "Yanzu akan jaka biyu kad'ai Maryama kike wofantar da kanki ga mazan da basu san ciwon kansu ba? Maryama akan kud'in da ba zasu iya siya miki ko zanin atamfa ba kike kwanciya da duk d'a namijin daya miki magana? Maryama taya zaki illatar da kanki da gangan alhalin kinsan ba kya da kud'in warakar matsalarki ba?"
Hannayenshi yasa aljihu ya lalaba ya fito da duka kud'in dake cikin ak'alla sun ba jaka d'ari biyu baya ya janyo hannunta ya damk'a mata kud'in a hannu kamar zaiyi kuka yace "Karb'i wannan kiyi duk buk'atunki iya na yau kawai, ni kuma na miki alk'awari kowace safiya zan kawo miki adadin wannan kud'in dan biyan buk'atar ki kawai data 'yarki, amma ki min alk'awarin babu ke babu sake kula wani namijin, ki bani tabbacin zaki kula min da kanki za kuma tsare min mutumcinki, dan Allah Maryama."
A hankali ta raba hannunta da nashi ta sakar masa kud'in a hannunsa tana kallon cikin idonshi tace " Bana buk'atar taimako daga wajen kowa, zanyi aiki da jikina wajen samo mana halak d'in da zamu ci, amma bana son kud'in ka, kad'an d'in da nake samu sunfi min masu yawan da zasu fito a hannun kowane d'a namiji."
"D'a namiji! D'a namiji! Maryama kullum maganarki kenan d'a namiji, wai wace irin ta'sa namiji yayi miki haka da har kika mana kud'in goro haka? Ki fad'a min ni kuma zan tsaya tsayin daka wajen ganin na goge waccen bak'in fantin da waccen mutumin yayi mana, sannan ki bar tunanin halak kike ci ke da yarki, kud'i ne da kika samu ta hanyar sab'awa ubangiji."
Kallon idonshi tayi wanda suka cicciko da hawaye tayi wani murmushi tace "Ba zaka tab'a iya goge wannan bak'in fantin ba, kamar yanda ba zaka iya dawo min da mahaifina dana rasa ba a dalilin wautar d'a namiji irinka, haka kuma ba zaka tab'a sawa mahaifiyata ta kalli idona ba bare harta min magana irin ta uwa da d'iya, dan haka dan Allah Junaid ka rabu dani nayi rayuwata, ka barni na k'arasa k'azamar rayuwa ta a haka ba tare daka tuna min da baya ba, ina farin ciki da hakan."
Murmushi ya mata yace "Magana kawai kikayi akan baya, amma gashi har na iya hango triste (damuwa) d'in da kike ciki, Maryama tu es en colère (kina cikin hushi), kamar fansa ce kike son d'auka ko kuma dai hushi ne ke sakaki abinda kikeyi."
Cikin k'ok'arin b'oye damuwarta tace "Laise moi en paix (ka bani lafiya)."
Wucewa tayi yabi bayanta da kallo, Iklima ce ta zo wucewa ta gabanshi ya bata kud'in nan yace "Dan Allah Iklima ki rik'e wannan kud'in kuyi wani anfanin dashi, sannan ki sanar da Maryama irin son da nake mata, wallahi ko misk'ala zarra bana da niyyar cutar da ita, aurenta nake so nayi, yau d'in nan har nayi magana da magabata na, kuma na samu amincewar kowa, ita kad'ai ta rage min na samu ta ta amincewar, na rok'e ki Iklima ki taimaka min na shawo kanta."
Da mamaki ta kalleshi tace "Kana nufin ka sanar a gidanku zaka aure ta?"
Cike da tabbatarwa yace "Na sanar mana."
"Kuma sun amince ka ce?"
"Sosai ma, wallahi da gaske nake Iklima."
Ajiyar zuciya ta sauke tace "Kuma ka fad'a musu irin matar da kake son aure?"
"Na fad'a musu Iklima, amma ban fad'a musu tana da 'ya ba, abu mai mahimmanci su san wacece zan aura."
Zata wuce yace "Kud'in fa?"
Juyowa tayi tace "Ka barshi kawai mun gode, idan na karb'a zamu samu matsala da Mari ne."
Wucewa tayi shi kam yabi bayansu da addu'ar shiriya, cikin sanyin jiki kamar kullum ya shiga motarshi ya kamo hanyar gida dan babu abinda zai tsinta a wajen.
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️
Su Hamna yan mata sune a falon sama tare da yara ta kunna wak'a a wayarta sai rawa take yaran na biyarta a baya, Amna na zaune tana kallonsu tana dariya, sai Umminsu Ammar da ita ma take kallonsu tana dariyar tare da mahaifiyar Junaid, a gefe ma k'anwar Junaid ce *Jamila* duk da ba ita ke bi mishi ba, amma ita ce daidai su ma'ana warin haihuwa, dan yayarta *Umaima* bata cika son hayaniya ba itama, tana da tsatsauran ra'ayi, ita d'in ce wacce suka zama k'awaye da ita suna ta kallonsu, wannan hayaniyar ce tasa Ammar daya dawo falon ya zauna yana danna wayarshi yayi tsaki yafi dubu, in dai yace yaje yanzu dan yayi musu magana Ummi za tace ai zai takura ma yaranta ne, kuma yana da tabbacin in yaje sai ranshi ya sake b'aci saboda *kankana* *(sunan daya sakawa Hamna kenan saboda soyayyarta da kankana*😂), su kam basu san tsiyar da yake ba sai rawarsu suke kwasa, wannan dum-dum d'in da wajen ke amsawa yasa yake jin kamar benen zai fad'o mishi a kai, wani wawan tsaki ya sake ja yace "Wannan yarinyar wallahi saina karya mata k'afa ta yanda gobe ba zata iya rawar ba ma, ayi yarinya kamar dujal ne ya haifeta, mtssss."
Wasu lambobi ya danna saiga lambar Amna ta bayyana a wayar tashi, kira ya aika mata da shi ta d'auka cikr da nutsuwa da fad'uwar gaba dan ita har ga Allah tana tsoronshi, duk da akwai banbanci tsakanin Hamna da Amna mai yawa, domin kuwa Hamna na da tsoron k'ananun dabbobi irun su k'adangare, kyankyaso, tsaka dacdai sauransu, Amna kuma bata tsoron wannan halittu kamar yanda take tsoron Ammar, Hamna kuma bata da zuciya da sanin ciwon kai, dan duk maganar da zaka fad'a mata komai zafinta saira karkad'e tace ko a kwalar rigarta, shiyasa duk maganganun da Ammar ke fad'a mata bata jin zafi, sai dai kuma akwai yab'a magana ita ma, dan tsoron da Amna ke masa ita bata mishi, idan taga ta shiga hannunshi kad'ai take tsorata da razana, sab'anin Amna kuma da magana ke mata mugun zafi, tana da zuciya da hushi, a tak'aice ma dai ita masifaffiyar amma fa ga wanda ya tab'a ta, idan kuma ka ganta zaka d'auka ko hannu ka saka mata a baki ba zata ciza ba, amma idan tana fad'a ko tayi zuciya to babu kyau, cikin sanyin murya ta amsa da "Na'am yaya Ammar."
Sai kace a gabanshi take saboda yanda ya wani sake had'e rai murya k'asan mak'oshi yace "Ki fad'awa yarinyar nan ta kashe mana kid'an nan, idan kuma na samesu a nan ran uban kowa saiya b'ace."
Yana fad'a ya kashe kiran tare da ci gaba da abinda yake, Amna kuma kallon wayar tayi kafin ta kalli Hamna tace "To shakira ya isa haka ko tunda *boss* yace a kashe wak'ar nan, da alama kuna damunsa ne."
Kallonta Hamna tayi masha Allah kam kyakyawa ne ajin farko, suna da diri da k'ira gwanin ban sha'awa, amma duk da haka Hamna tafi haske sosai da tsayi kad'an, tab'e baki tayi tace "Shine ya kiraki kenan?"
Da ido kawai ta mata alamar eh, ci gaba tayi da rawarta tace "Ki kira ki fad'a masa bai isa ya katse mana jin dad'in mu ba, dan haka yanzu muka fara."
*Hajia Zeinabu* (mahaifiyar Junaid) ce tace "Um um fa Hamna, hanyar lafiya abita da shekara, tunda yace ku kashe to ku kashe, ko kuma ki jasu kuje d'akin ku sai kuyi acan."
Wata kyakyawar mata mai k'aramin jiki ce fara kuma doguwa ce tace "Saboda yace baya so shikenan sai a daina? Me zai hana ya fita waje tunda namiji ne shi, amma yana cikin gida kamar wata garar kunya."
Zeinabu ce tace "Da dai kin basu shawara su koma ciki zaifi ai."
Hamna ce ta kalli yaran tace "Kai mu ci gaba da nishad'inmu, kunsan boss ba fara'a yake ba bare maganar nishad'i, shi ya sa yake kishi da duk wanda yake yinsu."
Tana maganar ne tana amma sai taga yaran kowa yayi zaune tare da mak'alewa wuri d'aya, tab'e baki tayi tace "Sai kace mala'ika nr shi daga ya turo sak'o ta waya amma duk kun tsorata."
Kallonta ne ya kai kan Amna data kafeta da ido, cikin dubara Amna ta d'ora hannunta a bakinta da yatsa d'aya take mata nuni da k'ofar shigowa falon, da k'yar ta fahimci abinda take nuna mata ta juya dan ganin ko meye, ai ko ido cikin ido suka kalli juna ita da Ammar wanda yake tsaye k'ik'am ya cije gefen labb'enshi na k'asa, ai da gudu Hamna ta koma bayan Ummi tana mata rad'a wai "Dan Allah Ummi ki bashi hak'uri mu samu ya bar gidan nan."
Ummi da tunda ta ganshi ta had'e rai kamar dai shi kalloshi take sosai, ganin yanda take kallonshi yasan sai ranshi ya b'ace in yayi magana, dan k'aramin aiki ne a gurin Ummi ta zageshi a gabansu har ma tayi yunk'urin marin shi, dan haka yayi k'wafa ya juya ya bar d'akin, yaran na gabin haka suka daka tsalle da shewa wai ya tafi bai dake su ba.
Yana barin nan kai tsaye asibitinsu ya wuce mai sunan *Clinik Aminci*, (na canza mata suna saboda kar na saka na ainahin sunan familyn ya fito fili), yana zuwa ya fito daga mota ya tunkari shiga ciki, a babban falon da mutane ke zama ya samu duk gurin zaman an cikeshi, kuma yana da tabbacin wanda yake da rendez-vous (appointment) da su ne, wata irin sallama ce yayi wanda na farko kawai yaji shi sai wanda suka ga bakinshi ya motsa, dan ranshi b'acewa yake idan ya zo asibitin ma, a ganinshi da yanzu watak'ila yana filin daga suna bada wuta, amma an zaunar dashi yana tambayar lafiyar mutane (mutum baya sanin abinda yake, haka kuma baka sanin mahimmancin abinda ke hannunka saika rasa shi), malamar asibitin dake zaune akan babban teburi wacce ita ke kula da wanda zasu shiga da kuma fara duba lafiyarsu, kallonshi kawai tayi dan ko ta gaishe shi ma ba amsawa zaiyi ba, tsaye yayi gabanta ya sauke jajayen idonshi akanta yace "Zan shiga, su bi layi da kyau, a kuma dinga shiga da hanzari saboda gudun b'ata min lokaci."
"Ok docteur." Ta fad'a tana bin bayanshi