Showing 261001 words to 264000 words out of 325849 words

Chapter 88 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

553

Middle Ads

da jin haushi, saida ya gama kallon kowa ya d'ago daga jinginar da yayi yana kallon kowa.

Cikin taushin murya da girmamawa yace "Barkanku da safiya iyayena kakanni na da yayuna da k'annaina na kaina."

Wasu tab'e baki sukayi suna tunanin abinda ya tarasu ya fad'a musu kenan ko me? D'orawa yayi da "A yanda nasan danginmu da gulma da jin dad'in yad'a labari nasan izuwa yanzu kowa yasan abinda ya faru jiya na fasa auren yarinyar nan, to akan shi ne dama zamuyi magana."

Kallon kallo suka wa junansu tare da k'ananan maganganu na abinda ya fad'a wai gulma, ba tare da damuwa ya d'ora da "Naji da kunnuwa na na gani da idona a cikin gidan nan masu cewa wai an fasa aurenta saboda hanyar data d'aukarwa kanta marar b'illewa, da jimawa a cikin gari naji da kunnuwana masu zaginta da aibatata, kuma maganar ta samu matashiya ne daga cikin gidan nan, da ku ahalinta ake zaginta a cikin gari saboda shigarta, mu'amularta da k'awayenta, amma abun tambayar anan su waye silar lalacewarta? Su waye sanadiyar rugujewar aurenta?"

Tsit kowa yayi sai zuba masa ido da akayi, Hamna kuma dake zaune kan kujera tare da Amna da Umaimah ne ta kalleshi tace "Malam, duk yawan mutanen wurin nan sai akai na ne kawai zakayi maudi'inka."

Ko kallonta baiyi ba kamar baisan da hallitarta ba ya ci gaba da cewa "Kune silar komai wallahi."

Alhaji *Mani* ne yace "Ya zaka ce mune sila kuma? Yarinyar da take ganin ta waye tana da ilimi da kud'i."

Cikin jin haushi Hamna ta mik'e ta kalleshi tace "Na zauna ne saboda yan uwana dana gani amma ba dan jin shirmenka ba."

Juyawa tayi zata fita ya kalli kowa na wuri yana murmushi yace "Kun gani, babu wanda yayi yunk'urin yi mata magana kan abinda tayi yanzun, kai tsaye ta nuna ni mashirmanci ne kuma zaman nan baida anfani, bata duba kasancewata babba a gareta ba, hakan bai isa a gareku da zai zama dalilin da zaku tsawatar mata ba."

Mik'ewa yayi tsaye yace "To ku saurara, dalilin had'uwar nan ba wai saboda ita bane, wani babban kuskuren mu ne na ke so na tunatar daku shi dan ku gyara, idan kuma baku gyara ba ni dai Allah ya gani kuma ya sani na tunatar daku, tunda a cikin nan akwai wad'anda zan iya musu fad'a, akwai wanda na isa na d'auki bulala na zane su, haka kuma akwai wad'anda ko kallon da bai dace ba zan iya musu ba."

Cikin misaltawa da hannu yace "Naji zafi sosai har zuciyata sanda nake tsintar k'ananan maganganu a cikin gari cewa Hamna wai tana abinda take so, daga cikin gidan nan ban tab'a gani ko jin ance anga wanda ya tsawatar mata ba, ban tab'a ganin wanda yace mata ta canza shiga ko kayan jikinta ba, a cikin gidan nan ma babu wanda ya damu da ita bare kuma daga waje, kuma abinda na lura ya jawo hakan ba zai wuce wariyar launin fatar da ake nunawa ba, wai yau lalacewar ahalin nan ya kai matsayin da kowa nashi kawai ya sani, babu wanda zai iya kallon d'an dan uwanshi ya mishi magana ko fad'a kan abinda yayi bai dace ba, kowa yafi son ya tsaya daga nesa yana nuna d'an uwanshi da baki, wannan wace irin rayuwa ce?"

Husseina ya kalla da Hassana da Hajia yace "Kune manyan da suka rage mana a ahalin nan, kuna da dama da iko a hannunku yanda zaku iya tank'wasa duk wani k'aramin tsagera, saboda kuwa ku kuka haifi iyayenmu, amma me kukeyi dan gyara iyalin nan?"

Matse bakinshi yayi yace "Kowa nashi yaja ya killaceshi a jikinshi yake bashi kulawa, d'aya ba zata iya iya tattaunawa akan matsalar data shafi d'aya ba, ko da na tashi a gidan nan cikin sauk'i na fahimci wacece kakata wacce ta haifi mahaifina, wanda ba haka ya kamata abun ya zama ba, yanda gidan nan ke da girma da mutane ya ci ace yaro zai sha matuk'ar wahala kafin ya gane mahaifiyarshi ma bare kuma kaka."

Kallon Husseina yayi yace "Bansan asalin meye tsakaninki da Hajia ba, amma yanda ke ma kike nuna baki damu da al'amuran 'ya'yanta ba abun babu dad'i, sanin kanki ne Alhaji baya nuna banbanci tsakanin wanda suke nashi da wanda suke na yan uwanshi, amma a gaban idonshi duk wani al'amari daya kamata kiyi magana saiki zuba ido kina kallo, saboda a ganinki ai ahalin Hajia ne ke kuma ba kya son shiga sabgarta, amma ya ci ace kina yi ko dan d'an uwanki."

Sauran mutanen ya kalla yace "Yau da kuka ga yarinyar nan akan titi cikin shigar da bata dace ba, kowa na da iko da hujjar da zai iya mata d'an banza duka, kuma babu abinda zai faru duk inda za aje, ku dubeku kuma da kuke gida d'aya, kuna sane da duk rashin mutumcin da take amma kuna kallo, ba komai ya kawo hakan ba sai dukanku kowa yana ji cewa ba ciki d'aya suka fito da ita ba."

Yayi maganar ne yana nuna su Amar da hannu, d'orawa yayi da "Dukanku nan babu wanda baya zarewa k'anninsa ido wanda suka fito ciki d'aya, amma wanda suke yan uwan juna kuma duk abinda yayi sai ka kalleshi da ido ko ka nuna baiyi laifi ba."

Juyawa yayi ga lieutenant da Ummy yace "Tanti Hadiza data baku amanar yaran nan ta baku ne da tunanin zaku tarbiyancesu kamar yanda ita ma zatayi, bakuyi laifi ba da kuka nuna musu soyayya har baku ganin laifinsu, amma kun kasa gane abinda ke daidai dasu da wanda ba daidai bane, kunfi kowa sanin tanti mace tsayayya da jajircewa kan abu, mace ce ita da bata yarda da raini ko shashanci ba, domin kuwa a rashin son wannan abubuwan ne ma yasa yau bata gidan nan, saboda ta k'i yarda a mulketa da ranta da lafiyarta, me kuke tsammanin zata ji idan taji an fasa auren 'yarta? Musamman ma taji dalilin fasa auren."

Hajia ya kalla yana murmushi yace "Hajia, Hajia, Hajia, nasan nan da zan bawa kowa dama ya fad'i dalilinsa na yin shiru, to kowa zai ce ne ke ce baki bayar da damar shiga hurumin iyalinki ba, suna da gaskiya ta wani b'angaren, amma ni dai a gani na ba hujja bace da zata sa kowa ya k'yale kuma yana ganin ba daidai ba, Hajia bansan me ye a kanki ba, amma ni dai kina birgeni, saboda jajircewarki da tsananinki kan iyalinki ya taka muhimmiyar rawa wajen hana faruwar wasu abubuwan, daga sanda kikayi shiru kuma sai komai ya fara lalacewa, matsalar d'aya ita ce ba kya jan iyalinki a jiki ta yanda zasu saba dake, idan akwai sabo tsakaninki dasu zasu iya fad'a miki komai daya shafesu babu tsoro, amma tsoron nufo ki ma Hajia yana gigita wasu, wasu duk maganar da zasuyi sai sun anbaci sunanki da cewa kar a ja musu matsala, misali Ummy na."

Ya fad'a nunata da hannu ya d'ora da cewa "Ita ce surukarki ta farko a gidan nan kuma matar babban d'an ki, a k'alla yanzu tana da shekara talatin da shida a gidan nan, amma wannan shekarun basu sa ta samu kusanci dake ba, har yau har yanzu bata iya kallon cikin idonki ta fad'a miki abinda ya dace da ita ko ya'yanta, uwa ta kan sadaukar da komai nata akan yaranta, amma banda Ummynmu, a jimawarta gidan nan ta kai matsayin da zata iya zartar da hukunci kuma ya yanku, amma har yanzu zuciyarta rawa take idan tana tare dake, jikinta b'ari yake idan tana magana dake, hakan ne yasa ta b'oye miki al'amari mai girman gaske wanda ya kamata ace kin sanshi, da kin nuna ita 'yarki ce data fad'a miki ko da ba zaki ji dad'i ba."

Dukansu ya kalla yace "Rayuwar nan bata da anfani idan ba zaka anfani d'an uwanka ba, ya kamata mu san yanzu mun rasa dattawan da suka rage mana, dukanmu yanzu anan mu ne muka rage ma junanmu, mu rik'e zumuncinmu kar muyi wasa dashi, mu kula junanmu kamar yanda zamu kula wanda muka fito ciki d'aya dasu, idan haka ta kasance wallahi ba *Ammar* marar kunya da rashin tarbiya d'aya za'a samu ba, za'a samu wasu Ammar d'in ma, sannan marasa jin magana ire iren yarinyar can..."

Ya fad'a yana nuna Hamna dake tsaye inda take yace "Indan har Ammar baiyi magana ba Amar zaiyi, idan Junaid baiyi ba Jibril zai tsawatar, idan Jamil baiyi ba akwai Abdul Rashid, in basu min magana ba akwai *Nura* akwai akwai akwai...etc, dole yara zasu gyara su kimtsu, dan in baka had'u da wane akan hanyarka ba zaka had'u da waninshi."


A shek'e ya kalli kowa yace "Yanzu ma nasan akwai wanda zasu ce na tarasu ina musu rashin kunya da fitsara, to ku gafarce ni duk wanda na b'ata masa rai, kuma nayi mamakin zuwanku haka da gaggawa, watak'ila kun d'auka wata dukiyar ce aka sake ganowa da Alhaji ya bari, shine kowa ya zo d'aukar nashi kason, ba'a d'auka ni na kira taron ba."

K'arashe maganar yayi da dariya, magana ta gaskiya akwai wad'anda a lokacin suka ji yaron ya birgesu, dayawa daga ciki abu ne da yake ci musu tuwo a k'warya, amma sai gashi yayi magana ya tab'o kowa. Gogan kam Amna ya kalla ya mik'a mata hannu, Amna da taji soyayyar mijinta ta sake huda zuciyarta cikin murmushi ta mik'o masa hannu ya kamota, saida ya kalli kowa yace "To ku rufe da salatin annabi, Allah yasa mu dace."

Amna ya kalla yace "Duniyata muje ki sauke ni, a sama nake wallahi."

Ta gabanta suka wuce inda kowa ya bisu da kallo, numfashi kawai kake ji na fita a wurin, sun jima zaune haka kafin Hajia ta sunkuyar da kanta tace "Kuyi hak'uri, yayi maganganu da dama a wurin nan, amma duka nice mai laifi saboda ni ce ban bayar da fuskar da za'a shiga shirgin iyalina ba, ba nayi haka bane dan bana so a rab'eni ko zuri'ata ba, kawai dai ina so ne naga tawa zuri'ar ta banbanta data kowa, ina so naga babu mutanen kirki irinsu, amma ban tab'a tunanin hakan zai zama matsala da zai iya kawo rabuwar kai ba, ku gafarceni dan Allah ku yafe min."

Alhaji Mani ne yace "Kamar yanda yaron nan ya fad'a ne Hajia ba laifinki bane ke kad'ai, mgana ta gaskiya mu ma muna da laifi, tunda ko baki so zamu iya magana amma muka yi shiru, amma yanzu dai tunda k'aramin yaro ya d'ora mu a hanya sai a yafi juna a kuma gyara gaba."

Su Hassana da jikinsu yayi sanyi ne yace "Allah ya yafe mana baki d'aya."

"Ameen." Aka amsa dashi duk d'akin sai kuma aka kwashi hira, Zeituna ce ta mik'e tare da su Shafa'atu tace suje to a d'ora girki, tunda an riga da an had'u kafin kowa ya tafi, madafa suka nufa sai mazan da suka fita waje, a wannan taro na wannan rana wanda Ammar ne silarshi har suka d'ora zubin kara wanda musababbinshi had'uwa ce ake son a dinga yi duk wata, ba'a fitar da yan mata ko yaran mata ko tsofaffi ba, duk mai so ne wanda ya ga zai iya duk wata, babu wanda ya yarda aka barshi a baya duk da za'a dinga zuba kud'i, amma a lokacin abun ya shiga zuciyar kowa ba kud'in ne abun dubawa ba sai girman zumuncin da za ayi.

*A dole* ta gyara ba dan tana so ba, πŸ˜‚(rubdugu) rubdugun da akayi akanta kad'ai yasa ta d'an saya shigarta, hatta su Amie ta daina yarda yanzu su zo gidan nan sai dai su had'u a salon d'inta, amma a haka wata rana Amie na zuwa amma bayan ta sako hijab.

*Bayan wata biyu* Hajia ta tisa k'eyar Hamna da Amna Umaimah dasu Jamila suka tafi hadj, wanda tafiyar Amna ta bawa mutane mamaki sanda aka ji ta tafi da ciki, lafiya sukayi aikinsu suka gama suka dawo lafiya, har yanzu ba wani hijab take fita dashi ba, sai ma uwayen rigunan data kwaso tafiyarsu masu kyau, kusan yanzu su tafi sakawa indai ba gida ka sameta ba ka ganta da riga da siket ko da zani. Yau ma tsaf ta shirya ta tafi wani babban mall dan siyayyar abin buk'atarta, ta shiga tana cikin duba abinda take so kawai suka had'e da Habib.

Kallon da yake mata yana tunanin ya mata magana ko kuma ya k'yaleta, shi fa ko yanzu aka yardar masa zai aure ta, amma ganin irin kallon da take masa yasa shi kallonta kawai shima, wucewa taje yi ta gabanshi sai kuma hanyar ta d'an matse, karkatawa tayi zata wuce ta kalleshi tace "Malam zan wuce."

Mamaki ta bashi ganin yanda ta nuna kamar basu tab'a sanin juna ba, kauce mata yayi a hanya zata wuce yace "Hamna abun ba ko gaisuwa?"

Kallonshi tayi ta wurga masa harara taja tsaki ta wuce, da kallo ya bita duk sai yaji babu dad'i, tana gama abinda ya kawota ta juya ta tafi, a hanyarta ta komawa ta had'u da Alhaji *Sabi'u*, babban shahararren d'an kasuwa, babban mutum ne mai iyali da tunbiπŸ˜‚, sanda suka tsaya bakin madakatar danja a lokacin ya sakar mata na mujiya, ba mutumin kirki bane ko kad'an, indai zaiga mace to fa babu lafiya hankalinsa tashi yake, binta yayi a baya har ta isa gida, gira d'aya ya d'aga sama ya cije leb'e sanda yaga gidan data shiga, lallai ko giyar wake yasha bai isa ya tunkari gidan nan da sunan zai wa yar gidan lalata ba, yana da sani sosai akan mutanen gidan, kama daga gwamnansu Gambo, lieutenant na douanes da kuma colonel na soja, kai ba ma zai yiwu ya fara ba wallahi indai yana son kansa da mutumci, amma kuma ya gani yana so saiya kenan?.

*Bari Fan's badak'ala su fad'a maka yanda zakayi? Ni ma idan kuka min comment saina baku wata page muji me zaiyi*.


*Alhamdulillah*
14/10/2020 Γ  00:58 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_61_


Maganar aure ya shigo da ita dan ya samu abinda yake so, mutum ne dake iya b'atar da ko nawa ne dan ya samu biyan buk'atarsa, ita bata sanshi ba dan ko ganinshi bata tab'a yi ba, wani shu'umin mutum ne daya san kan tsiya kowace iri, kai tsaye gidan ya fara zuwa ya gabatar da kanshi ga manyanta, saboda kowa yayi karatun tanastu yasa Hajia da kuma lieutenant cewa sun gamsu da kamalarshi, daga yanda suka mata magana ya nuna umarni ne suke bata data aure shi, abinda ta fad'a musu kawai shine "Allah ya zab'a mana mafi alkairi.

A ranar da ya zo dan su fahimci junansu data ganshi saida ta tsorata, zuciyarta ta tashi sosai saboda ba wai muni ne fa shi ba, gashi da tsayi da babban tunbi, sannan bak'i wulik dashi sai idon kwartayeπŸ™ˆ, da k'yar ta iya gaisawa dashi kafin tace zata koma bata jin dad'i, Ammar ne ya shigo farfajiyar b'angaren Hajia zai shiga falon yana d'auke da Ameera a kafad'arshi, saida gabanshi ya fad'i daya ga wanda take tare dashi, me ya had'ata da Sabi'u kuma har gidansu? Yana k'arasawa bai kalleta ba ya bashi hannu yana fad'in "Alhajin Allah kaine a gidan mu?"

Wuk'il wuk'il yayi da ido dan duk jikinshi ya mace ya sare da al'amarin yarinyar, yaji a jikinshi wannan ita ce yarinya ta farko data birgeshi kuma bai samu biyan buk'ata ba, dan shi sai yanzu ne ya tuna ashe wannan pand'ararren ma a gidan nan yake, to shi ina zai iya da jarabar bawan Allahn nan, yo shi ko baya da iyali ai zai k'wauracewa kwatirarsa bare kuma yana da wanda baya san sa su a matsala.

Da k'yar ya bashi hannu yana fad'in "Alhaji Ammar kana lafiya."

Ta gefen ido ya kalleshi yace "To lafiyar nan dai da dama, jiya ai nayi croisement da kai a babban titi."

Kallonshi yayi da mamaki dan shi dai yasan jiya duk a yawace yawacen shi bai isa can wajen ba, cikin k'yabta ido na marar gaskiya yace "Wane lokaci?"

Cikin murmushin mugunta yace "Nasan dama baka ganni ba, amma ni na ganka tare da wata cikar, da farko ma na d'auka madame ce wallahi, sai daga baya na ankare ashe ba ita bace, ai na so tsayar da kai dan ni kaina kayan sun birge ni fa, kai Alhajin nan ka iya zab'ar harka."

Ko da ya gama fad'a kuma ya shige yana mishi dariyar mugunta, kawai ya fad'i hakane fa dan ya ankarar da ita in ma bata san waye ba, in kuma ta sani to tasan da irin mutumin da take mu'amula, kallonshi tayi sai taga kawai yana ta zufa, da k'yar ya kalleta yana washe mata baki, yamutsa fuska tayi tace "Saida safe."

Da kallo kawai ya bita, tana shigewa ya mik'e ya kalli k'ofar ya nunata da hannu yace "Wannan Ammar wannan Ammar Allah ya tsine maka albarka, shegen yaro mai kama da kafiran farko."

Juyawa ya fita ba tare da tunanin sake dawowa ba, ita ma ko da ta shiga bata iya cewa komai ba kawai ta zubawa sarautar Allah ido, su Jibril kuma dake fita su suka samo cikakken bayanan shi, dan haka ana jin waye shi aka ce wannan magana ba ita ba kamarta, tayi farin ciki saboda ta tsira daga wannan tullu, *bayan wata d'aya* kuma Allah ya sake had'ata da d'an abokin lieutenant, shima dan danan magana ta kankama har an saka ranar kawo kaya, sai dai shi kuma matsalar ance matarsa ce fitinanniya namber one, dan a cikin gida ma ita ke mulki, lieutenant ne yace baya

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login