Showing 294001 words to 297000 words out of 325849 words
kika hau wallahi."_
_"Babu abinda zai sauko dani."_
Dariya ta sake mata tace _"Ai kuwa d'an uwana zai sauko dake da k'arfin cin tuwo."_
Maida mata tayi da _"Ke dashi duk baku da aikin yi."_
_"Ke ma zaki samu aikin yi idan aka d'aura, dan tunanin d'an uwana ma kad'ai ya ishe ki."_
_"π‘."_ Shine abinda ta tura mata.
A safiyar aka raba goro wani kamar zaiyi wanka dashi, sam kowa ya goyi da bayan a saka k'ank'anin lokaci, hutu aka saka na babbar sallah da za ayi na yan makaranta wanda duka *sati uku* ne ya rage, ai sai Ummy ta aje maganar aiki gefe ta fara shiga da fita tana gyara yar tilon yarta data rage mata mace, duk abinda ta wa margayiya shi take mata yanzun har da k'ari na sabbin sirrika, ita kanta Hamna wani abun in tasha sai jikinta yayi sanyi, wani in tasha tsikar jikinta ce zata dinga tashi, wani kuwa sai taji jikinta har rawa yake, turaren da take sawa a ruwa wurin wanka har gadonta ya kamu da k'amshin shi ma, ta samu gyaran fata tayi luwai luwai abinta tayi masara shar da ita, kullum kuwa tana sama d'akinta bata ganin ko falon Hajia bare rana, har yanzu kuma basu had'u da jarabun nata ba dan ba d'akin yake zuwa ba, dan danan kuwa sai gashi an gama shirye shiryen sallah an gama.
_Zuma_
Idon zakara_
_Kanunfari_
_Garin rud'i_
Ka had'esu ka sha da nono ko madara.
_Minanas_
_Hakk'in daka_
_Cukui_
_Zuma_
Saika had'esu kana sha da madarar shanu d'anya
_Kankana_
_Gwanda_
_Abarba_
_Pomme (Apple)_
_Zuma_
_Madara peak_
Kayi jus na su kana sha.
_Habba cokali 2_
_Garin rid'i cokali 3_
_Garin raihan cokali 4_
_Yayan zogale yanda kake buk'ata_
Ka zuba cikin dahuwar tantabaru mace da namiji.
_Dabino_
_Nonon rak'umi_
_Hulba_
_Ayaba_
_Abarba_
_Zuma_
Ka tafasa nonon rak'umin idan ya huce saika juye shi cikin markad'add'sn dabino da ayaba da abarba ka zuba garin hulba kasha.
*Kwana uku* daya rage kowace rana da shagalin dasu Sayyada suka gwangwaza, su da abokan Ammar sunyi shagali sosai ba kama hannun yaro, Hamna kam mulkinta take buga musu son ranta, har kamu akayi cikin gidan nan amma babu wanda ya ga k'afar amarya, anyi anyi ta shirya sai ma ta fashe da kuka dole aka k'yaleta, sai nan d'aki suka mata wanka turare, Ammar kam ko a jikinshi saida yaje gaban iyaye ya kwashi shokinshi ya duk'a suka fesa masa turare kafin ya bar wurin, wannan karan ma gabjejen sa ya aiko dashi ayi girkin biki tare da jus kamar za ayi wanka dashi.
*Ranassss*
Ya baje cikin shigar fararen kaya, lieutenant colonel da Gambo da Labaran duk shigar kala d'aya ce, su Amar Jibril da sauran dangi ma matasa kamarsu duk suna cikin fararen kaya, to anko ne da aka sa kowa yayi dan dole ko bai shirya ba, anan lieutenant ya bayar da auren yarsa inda Labaran ya karb'a wa d'ansaπ (kune gayyar tsi...), daga k'arshe dai an d'aura auren *Hamna Harouna Suleymane Gaga* da *Ammar Hassan Suleymane Gaga* akan sadaki jaka hamsin mafi k'arancin dan albarkar auren.
*Yanzu ciwon kaina zai k'aru ku taimaka min da panadol da paracΓ©tamol da doliprane a kusa.*
*Alhamdulillah*
04/11/2020 Γ 14:39 - Ummulkhairi: π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨
*BADAK'ALA*
π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
π¨βπ©βπ§βπ¦ _*AHALI NA*_π¨βπ©βπ§βπ¦
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
_70_
*Biki yayi biki* ta bakin wani mawak'i, ba kid'a ba wak'a amma fa holewa ake, b'angarenshi ya sake tabka mishi gyara na rashin mutumci, haka kuma yana can ana gyara masa gidansa dan yace wannan ita ce abokiyar gwabzawa sai sun matsa daga kusan manya karsu kashe su basu shirya ba. Ita kanta Hamna k'awayenta sun mata bajinta sosai, dan har daga Niamey da Katsina wasu sun zo aurenta, taji dad'i sosai na ganinsu a kusa da ita a wannan lokaci.
Ko da magriba tayi Ummy ta tsaya tsayin daka wajen gyara amaryarta kuma surukarta, wata mahaukaciyar doguwar riga ta tsadadden tissue aka saka mata, yaji d'inki sosai mai d'aukar ido da d'aukar hankali, tun daga sama zuwa hannaye har gwiwa a matse yake, amma daga k'asa sai aka bud'e sosai yayi tsatsaye har yana jan k'asa, kwalliya ta d'auka daga wajen wata k'awarta ta ban mamaki, kwalliya ce daidai da fuskarta inda aka d'ora komai kan muhallinsa, d'aurin d'an kwali kam kamar ba hannu ne yayi aikin ba, dama duk wani abin da zata saka saida Ummy ta turare shi har da pant da bras d'inta, sannan ita ma aka sa ta zauna kan kujerar turaren bayan an turare mata jiki, abubuwan da Ummy ta k'ara bata tasha ta ci taji tana neman yin amai, tana daf da fashewa da kuka tana fad'in "Wallahi Ummy amai zanyi, ya ishe ni haka dan Allah."
Da sauri mai kwalliyar tace "Rufa min asiri Hamna karki zubo da hawaye a idon nan."
Hararanta tayi tace "Dallah kwalliyar me?"
Karb'a Ummy tayi tace "Shikenan to barshi haka, ai muna tare dake a gidan."
Ummy zata fita daga d'akin wayarta tayi k'ara, ko da ta d'auka tace "Ango ya akayi?"
Daga inda yake yace "Ummy kun shirya? Mota fa na nan tafe d'aukar kankana."
Saida ta kalli Hamna dake ta had'e rai k'awarta na cewa ta dinga murmushi dan Allah sannan tace "Me ye na sauri Ammar? Kuma nan da can d'in zata shiga mota? To ai ko hannu aka sa sai a tura motar k'ofar gidan."
"A'a Ummy sarauniya ce yau, bari mota zata kaita."
"To shikenan." Ummy ta fad'a dan abar canzen, ta d'auka mota d'aya ce yake nufi da zata d'auki amaryar, amma abun mamaki da firgita tunanin mai rai sai jininin motoci suka ji, sanda aka fito ne suka ganewa kansu sarautar Allah, kai Umy ita dai a ganinta motocin nan bana abokanshi bane kad'ai kamar harda hayarsu akayi, mota ta bawa guda arba'in baya ta kusa kaiwa hamsin, to wace tsiyar zasuyi da su, in suka shiga ina za'a kaisu, to wata motar ma yanda ta zo haka ta juya ta koma bata d'auki ko sauro ba bare mutum.
Bakin duniya, da suka kwashi matan mutane gudu na idon duniya suka dinga yi dasu, aa fa gudun ma a cikin tsari suke yin shi, dan babu motar data fita daga layin da suke, saida suka lula suka kai k'uryar ali d'an sofo sannan suka kutsi hanyar da saida ta sada su da zarya ta k'arshen k'ashe-sheshe, yawo kawai sukayi mutune tun ana jin dadi su dai har wani ya fara k'orafi saboda dare ya k'ara yi, sai lokacin kad'ai suka koma aka aje amarya aka shigar da ita gidan ta.
Iyaye duk kanta suka taru inda suke mata nasiha kan hak'uri, saida kowa ya gama na shi Hajia da Husseina su dai suka fad'a mata ta zama mai d'auke kai daga lamarin bawan Allah nan, wannan taurin kai da fad'a masa magana kai tsaye ta kiyaye, tayi kamar yer uwarta har ta koma ga Allah ba'a tab'a jin ko sautin muryarsu ba da sunan tashin hankali, ita dai sauraronsu kawai take, amma ba zata iya abinda Amna tayi ba, wacce ta fad'a mata idan wani ya b'ata mishi rai saiya huce kanta ta hanyar darzata kan gado ko kuma ya mata wanka da ruwan sanyi ko sata cin abincin da batayi niyya ba, to ita yaushe zata iya da kwatirarsa? Ai ya kasheta ko ita ta kashe shi ne kawai.
A sannu sannu aka watse aka barta ita kadai, zaune kan gado tana k'arewa d'akin kallo, saida ta gama tas sannan ta mayar da fuskarta cikin babban mayafinta tana kallon hannayenta masu ban lalle, Ammar? Ammar? Mahaukaci ne fa suka had'ata dashi.
*Uwar Lalla kinji fa?*
*Yana* saman hanya tare da Amar na tuk'i sai su Junaid a baya lieutenant ya kira shi, d'auka yayi lieutenant yace "Kana ina Ammar?"
"Abba ina kan hanya."
Cikin d'an jin kunya yace "Ka siye kaza ne?"
Murmushi yayi yace "Abba duk angon dake son jin dad'i dolenshi ai ya siyo kaza."
Su Amar kallonshi sukayi sai Abba da yace "To ka siyo guda biyu ina son d'aya nima."
Tafin hannu yasa ya rufe fuska wai kunya yana fad'in "Lah Abba na wallahi ka bani kunya, kai ma kaza kake so? Kenan dai uwata zata mana k'ane."
Had'e fuska yayi yace "Kai bana son iskanci, ita kad'ai ce mai k'wan haihuwa? To da uwarka nake ni."
Ido ya zaro cike da shak'iyanci yace "Kai Abba na Ummy fa, kayi hak'uri dan Allah kaje wajen uwa Zeitu."
"Ammar." Ya fad'a cikin muryar karsashi, a hankali yace "Na'am Abba."
"To ka siyo ka kawo min, kuma dan ubanka da kai zamu je siyan bakin uwarta ka tunda kai ka zigeta har yanzu bata kula ni."
Tintsirewa yayi da dariya yace "Abba na karka damu, ni d'in nan nine na rabaku kuma ni zan had'a ku, bari na siyo maka kaji manya guda uku, d'aya ta yau d'aya ta gobe d'aya ta jibi."
Girgiza kai lieutenant yayi kawai ya kashe wayar, shi kam gyara zama yayi kamar mai shirin bacci yana fad'in "Abba ba dan karka karya min uwa ba ma ai da saina saka maka magani a kazar nan."
Dariya suka saka inda Junaid yace "D'an iska dai baiji dad'i ba wallahi."
"Inji uban wa?" Ya fad'a idonshi a rufe, Jibril ne yace "Inji shi mana."
Wata k'arar ya fitar a bakinshi irin a banza kenan, Amar yace ma "Muje a siyowa Abba kaji, shi ma yau dad'i yake so yaji."
Kallonshi Amar yayi yace "Yanzu kai banda abunka ina Hassan ina wannan abu na yara? Ai sai ku masu tafasashen jini."
Bud'a ido yayi ya kalleshi sama da k'asa yace "Ko yanzu ka had'ashi da yarinya Allah zaka yi mamakin sakamakon da zai haifar."
Su dai dariya suke har suka isa wajen maduguπ, tik'a tik'an kaji ya siya kafin suka wuce gida, da shigarsu suka samu lieutenant a waje, wuyan rigarshi ya shak'a yace "Sai mun je ka bata hak'uri, tunda ka hure mata kunne yanzu gaisuwarma sai dai kaji ta wani ce, ina kwana."
Dariya yayi yace "Abba sake ni to ai ba guduwa zanyi ba."
Sakinshi yayi suka shiga ciki gidan ya d'an fara yin shiru alamar kowa ya tafi bawa makwancinshi hakk'inshi, kai tsaye d'akin Ummy suka shige a tare.
Ja sukayi suka tsaya ganin Ummy ta gama saka doguwar rigar bacci har k'asa tana d'aure gashinta da k'aramin mad'auri, kallonshi Ammar yayi yana dariya yace "Abba da alama ita ma hak'uri zaka bata, to gashi ni na tafi kafin na makance."
Juyawa yayi yana ajiye leda d'aya lieutenant ya jawoshi, juyowa tayi ta kallesu tace "Ya zaku shigo haka babu sallama?"
Juyawa tayi tana fad'in "Ko da yake ai kamar uba kamar d'ansa, ba mamaki kam."
K'arasa shiga sukayi inda lieutenant ke fad'in "To miye a ciki dan bamuyi sallama ba, kai da kaya ai duk mallakar wuya ne."
Kallonshi tayi fuska a had'e tace "Amma ai shi yaron mamallakina ne, ba shine ya mallake ni ba."
Kallon juna sukayi da Ammar yace "Wannan shalelen Hajia ko bayan raina fa shi zai rik'eki."
Ba alamar wasa tace "Shiyasa dama ka k'i bani takardata saboda kaga ka kusa mutuwa, kana so dole sai nayi maka wankan takaba."
Gaba d'aya suka juya suka kalleshi yana dariya, zaune Ummy tayi bakin gadon tana kallonshi, saida ya gaji da kanshi yace "Ummy Abba na kike wa fatan mutuwa? To ai bai tsufa ba."
Da hannu ta nuna masa tace "Ka duba da kyau ka gani, kwana nawa ne ya rage masa yayi ritaya (retraite)?"
Murmushi yayi yace "Amma Ummy ai a wajen aiki ne zaiyi ritaya, a gida kuwa yana nan da k'ark'onshi."
Lieutenant ta kalla tana d'an jujjuya baki tace "Zaku iya fita idan kun gama abinda ya kawo ku."
Kallon juna suka sake yi sai yayi laushi sosai yace "Abba ni zan tafi fatan nasara, mata uku ne dama ke matuk'ar jigata ni a duniyar nan, ga d'ayar nan."
Ya nuna Ummy sannan yace "D'ayar kuma yau ta shiga hannu na, d'ayan kuma kullum ina mata addu'a Allah ya kai rahama k'abarinta."
Saida har ya fita lieutenant ya bi bayanshi yace "Kai ni fa uwar nan taka tsoro ma take bani, ua zanyi da ita ne?"
"Kawo kunnenka kaji Abba." Mik'o masa yayi ya masa rad'a, saida ya gama ya kalleshi baki sake yace "Ammar kaji tsoron Allah, yanzu haka kake so na wa uwarka abinda ko da k'uruciya banyi ba."
Da ido da gira ya masa alamar kawai yayi kafin yace "Abba saida safe, karna tsaya gyara tsofaffin hannu ni kuma na samu matsala."
Da kallo ya bishi har ya fita, komawa yayi ciki ya sameta har ta kwanta, cire babbar rigarshi yayi ya shiga wanka, ya jima a ciki kafin ya fito ya saka doguwar riga ya zauna kusanta, hannu yasa ya tayar da ita zaune yana kallon fuskarta, cike da rarrashi yace "Sa'adatu na, fushin me kike yi dani haka har yanzu?"
Kawar da kai tayi gefe ta k'ara tsuke baki, murmushi yayi yace "Haba uwar ya'yana, matar da babu mai irinta a duniyar nan, kiyi hak'uri mana ki daina hushin nan Allah ba kya kyau da hushi, kifa tuna bamu tab'a samun sab'ani ba da ke."
Kallonshi tayi tace "Kasan da haka amma shine kan k'aramin abu zaka sauya min, naje neman sulhu kuma wai har kace min k'ofa a bud'e take na tafi baka rik'e ni, hummm."
Matsawa tayi daga kusanshi shi kam dariya ma yake mata yanda d'an bakin nan ke masifa, sake rage murya yayi ya kama hannunta yana murzawa yace "Naji na d'auki laifina to a yafe min."
Shiru tayi dan haka yace "Kinsan wani abu kuwa?"
D'an kallonshi tayi lokaci d'aya ta d'auke idonta, cikin murmushi da son sauko da ita yace "Wallahi *uwar Amna* ina sonki sosai, ban tab'a sanin cewa ba kece ni ba sai da abun nan ya faru, dana zauna saina tambayi kaina, ashe dama ke ce kika sa na zama haka? Kin mayar dani babban mutum, kinsa na zama mai fad'a a ji a k'asar nan, kinsa na zama Baba har da kaka ma, ni kam a rayuwa me zan miki daya wuce na rumgumeki a k'irjina har mutuwa ta same mu a haka."
Wuuuu (lieutenant kana wuta fa), Ummy fa tuni tajita ta saman bakwai akan gajimare tana shillawa, wallahi ya fasa mata kai sosai dan haka ta yafe ta hak'ura, kai idan ma da abinda yake buk'ata ya fad'a mata a shirye take, murmushin da bata shirya masa bane ya zo mata, yana ganin haka ya saki murmushin shima yana godewa wanda ya musu farrak'u tun farko.π
*B'angaren amare*
Da sallama ya bud'a k'ofar d'akin ya shiga, tsaya yayi yana kallonta da shu'umin murmushin da shi kad'ai yasan ma'anarsa, takowa ya farayi yana mata wak'a yana fad'in "*"Amarya ta ango wanene mijinta? Ammar ne mijinta, yau ga Hamna ga Ammar sai fa yanda ta yiwu." *Amarya ta ango wanene mijinta? Ammar ne mijinta, yau ga Hamna ga Ammar sai fa yanda ta yiwu."*
Ita ba tayi dariya ba tayi kuka ba, takaici duk ya isheta ta kuma san gaskiyarsa fa sai yanda ta yiwun, ko motsawa ba tayi ba bare ta amsa mishi ko sallamar, aje ledojin hannunshi yayi ya shiga rage kayan jikinshi, kallonta yayi ko ina a rufe baya ganin komai, dan rigar ma ta bazu kan gadon kamar zata rufe shi dan dai yana da girma sosai, murmushi ya sake yi yace "Kankana ki rufawa kanki asiri ki cire mayafin nan kisha iska."
Shiru kamar bata san yana yi ba, jinjina kai yayi yace "Komai bak'in cikinki dai Hamna yau kin zama tawa, nasan dai haushi kike ji na aureki ko? Ya kamata ki gane nine mijinki a duniya haka ma a lahira, kuma in baki manta ba dama na fad'a miki zanyi iko akan ki."
Ko da ya gama ya shiga ban d'aki, wanka ya tsala ya d'auro alwala kafin ya fito, doguwar riga ya saka yana kallonta yace "Tashi kiyi alwala malamar k'arya, munafuka ta ganta a hannu duk ta nutsu sai salati take."
Dan ta samu lafiyarsa cikin muryar data karyar da gabanshi tace "Bana sallah."
Murmushi ya saki tare da mata kallon zaki gane kurenki ne yarinya, tappi ya shinfid'a ya kabarta sallahrshi, raka'a biyu yayi ya sallame ya sake kabbara wata yayi biyu ya sallame, saida ya kwarara addu'a ya kalleta ba tare data gyara ko da zamanta ba yace "Na aika miki taki kema."
Tashi yayi ya fita sai gashi ya shigo da faranti, duk abinda ke cikin ledojin nan ya juye ya girke gabanta, bata ankara ba taji ya fincike mayafinta ya aje kan gadon yace "Gyara min zaman nan naki."
A hankali ta d'aga kanta, wata irin fad'uwa gabanshi yayi sai yaga kamar ba ita ba, kyawun ya wuce misali har ido take d'auka, k'amshi kam kamar zai saka shi bacci, gyara zamanshi yayi ya b'allo k'afar kaza ya nufi bakinta da ita, girgiza kai tayi tana hararanshi, murmushi ya mata yace "Kiyi abinda kika ga dama zan rama, yanzu fara cika min cikinki."
A hassala tace "Na ce bana ci Ammar."
Wani kallo ya mata, a ranshi yace "Ammar, zaki daina zuwa anjima."
Aje naman yayi yana kallon idonta yace "Kankana ko ki ci ki taimakawa kanki, ko kuma na d'ura miki da tsiya har sai kinyi aman wahala, ko kuma na baki ba sai kin b'ata hannunki ba, wane kika zab'a?"
Idonta taji sun ciko da k'walla, hak'uri ta fara bawa kanta dan su rabu lafiya amma ba tace komai ba, sake d'aukar naman yayi ya kai bakinta, juya kai tayi tasa hannunta ta d'an tsakuro tasa bakinta, kallonta ya shiga yi yana ta cewa ta ci ta k'oshi, data tsaya saiya tsorata da cewa zai auka mata shi da kanshi, tun tana ci da yanga harta fara turawa da tsiya tana gangaro da hawayen bak'in ciki, saida taji ba zata iya ba ta kalle shi tace "Allah ya ishe ni haka."
Sauka yayi daga