Showing 174001 words to 177000 words out of 325849 words
babu ce kawai babu a d'akin su, hatta kayan kallo basu bari ba saida suka zuba musu, kuma kayan duk sanfiri d'aya ne kala da abinda ba'a rasa bane ya banbanta.
*Party*
Kayan da Ammar ya d'inka mata ne ta saka, leshe ne da ak'alla kud'in zasu ishi wani talakan rayuwa na tsawon watanni, kalar ruwan madara ne da bleue wanda ya k'ona sosai, haka shi shi ma tanffatsetsen yadin dake jikinshi kalarsa take, mota dai ba wata tsiya ba kam kamar suyi magana, dan wajen ajiye motoci a babban hall d'in ma kasa d'auka yayi, duk girman gurin saida aka matsu akayita had'a gumi, har ya zama ba'a jin tashin kid'an dake wurin sai jininin mutane da kuma hayaniyarsu. Da gani kasan babban biki ne na manyan mutane kuma masu tarin dangi, kowa daka gani shafar gumi yake saboda matsatsi yayi yawa, abincin kam dama ko da colonel ya samu labarin jama'ar dake wurin ya sake odar abincin a restaurent har guda biyu, da hakane aka samu abinci ya wadata a wurin, duk wanda bai samu ba to baya kusa sanda aka raba. Hasken waya kam ta ko ina ganinshi kake ana d'aukar hoto, ana cikin wannan rak'ashewa aka ce Hamna ta zo a d'auki hoto kuma a dole su sa Ammar tsakiya.
Hamna na tsayawa ta wurga masa harara tana gunguni k'asa k'asa, Ammar dake amsa waya cikin akasi idonshi suka sauka kanta tana harararsa, kashe wayar yayi ya murtuke fuska yace "Ke uban wa kike harara? Allah kankana ki kiyayeni."
Murgud'a masa baki tayi tace "Ank'i a kiyayeka, da wani abu da zakayi ne?"
Kallonta yayi da mamaki yace "Kutumar uba, ke ni kike fad'awa haka? Me..." Bai k'arasa ba ya juya ya kalli Amna dake ta doka murmushi, murmushin ya mata shima yace "Amaryar, ci gaba da murmushi irin haka kinji, bari na gama da kankana."
Bai jira amsarta ba ya sake juyowa kan Hamna ya zaro mata ido ya sassauta murya yace "A waccen ranar me kika gani? Ga dukkan alama kankana ban baki tsoro ba, dan dana tsorata ki da ko ganina kikayi sai gabanki ya fad'i, amma akwai lokaci."
K'wafa yayi ya juya gabanshi ita kuma tace "Tabbas."
Da sauri ya juyo ya kalleta, d'orawa tayi ba tare data kalleshi ba tace "Tabbas akwai lokacin da zan huce haushina a kan ka, kuma tsoro da kake magana, kai a wa zanji tsoronka? Fasik'in? To ai ko abinda ya faru ma ni baisa na kalleka a matsayin namiji ba, watak'ila baka gama k'wari bane ko kuma dai kana da k'arancin lafiya, amma dai ka sani ni banji komai."
Ruf ya rintse idonshi, yawu ya had'e masu d'acin gaske wanda suka sanya mak'walaton dake wuyanshi yin sama da k'asa, bud'a idonshi yayi wanda suka fara d'aukar launin ja, ya kasa d'auke idonshi a kanta saboda so yake ya tattartsa mata mari, amma ya rasa yanda akayi ya kasa d'aga hannun, ya tabbatar da wata ce ko Amna tuni data dafe kunci, to amma me yasa ita ya kasa. A hankali ya sake lumshe ido ya bud'e a kanta, tattaro kuzarinshi yayi yace "Da bana da lafiya da bakiyi kururuwa ba, da ban cika namiji ba da tafiyarki bata canza ba, yanzu kuma zan tabbatar da abinda kika fad'a ne idan har kika ga al'adarki a wannan watan."
Wata mummunan fad'uwa gaban Hamna yayi, kallonshi tayi tsoro ya bayyana a tare da ita, fahimtar haka da yayi yasa ya murmusa ya kalli gabanshi yace "Ba alfahari nake ba, amma inada tabbacin ke bakiyi k'osawar da har madara zata kasa zama d'an mutum a cikinki da zubawar farko ba, musamman ni da nasan na zubata a daidai a lokacin da komai ke bud'e yana maraba da kowane bak'o ya shigo."
Hamna kam fashewa tayi da kuka ta taka zata bar wurin tana fad'in "Allah ya isa, Allah saiya saka min, mugu azzalumi."
Dariya yayi wacce ta fito da kyawunshi murya k'asa k'asa yace "Ba farau ke da zafi ba dama, ramau, kuma nima Allah ya isa da kika rabani da samartaka ta, muguwar kankana kawai."
Amna dai da babu abinda take ji kallonshi kawai tayi, suna had'a ido ya sakar mata murmushi yace "Ina k'aunar ki amaryata."
Kunya ce ta rufeta ta sunkuyar da kai, shi kuma kallonta yayi ya tambayi kanshi "Da gaske *kana k'aunarta*?"
D'an murgud'a baki yayi yace "Ko bana sonta ai ina k'aunar ta, kuma yanzu matata ce sannan zata zama uwar 'ya'yana insha Allah."
Tsam yayi sai alamar tashin hankali daya ziyarceshi lokaci d'aya, abinda ya fad'a mata ne ya dawo kanshi, *yanzu kuma zan tabbatar da abinda kika fad'a ne idan har kika ga al'adarki a wannan watan*! Tashin hankali, to idan fa haka ta faru? Wata zuciyar ce tace mishi "Haka ma ba zai faru ba, ai ka fad'a mata ne kawai dan ita ma taji zafi kamar yanda ta cizgaka."
D'aga kafad'a yayi alamar ko oho sannan aka ci gaba da sha'ani, sai dai har aka tashi daga taron bai sake ganin Hamna ba, wanda hakan ba k'aramin dad'i ya masa ba, dan dama ganinta cikin shigar nan data fito da komai nata yana tayar masa da hankali, sai yaga duk idon kowa a kanta yake. Nan aka koma gida aka raka kowace amarya ta sake shiga d'akinta. Duk abinda aka saka ma rana dai k'ararre ne dama, sai gashi anyi an gama kowa ya kama gabanshi an bar amare da angaye da halinsu.
*12:00* da sallama Jibril ya shigo d'akin da ledoji a hannunshi, Jamila dake zaune tsakiyar gadon kasa amsawa tayi dan gabanta ne taji ya tsananta fad'uwa, har saida ya zauna kusanta bata motsa ba, ganin bata da niyyar magana yasa ya aje ledojin hannunshi ya yaye mayafin nata yana kallon fuskarta, ajiyar zuciya ya sauke ya d'anyi k'asa da kanshi sannan yace "Jamila."
Saida ta had'e yawu yafi sau biyar kafin ta amsa k'asan mak'oshi da "Na'am."
Murmushi yayi jin firgici a cikin muryarta yace "Muje muyi alwala ko."
Jinjina kai kawai tayi alamar to sannan ta sauko a hankali ta fad'a ban d'aki, yana zaune yana jiranta har ta fito, saida ya k'urawa fuskarta ido ganin ta wanke kwalliyar dake fuskar, mik'ewa yayi shima ya shiga, ba jimawa ya fito ya samu ta shinfid'a sallaya, gaba ya tsaya ita kuma daga gefenshi a baya suka kabbara sallah.
A wajensu Junaid ma hakance ta kasance, bayan sun idar da sallah zai janyo ledojin shi yaga ta mik'e, da mamaki yace "Zauna mana, zo ki cika cikinki Hajia ta."
Kallonshi tayi tace "Ina zuwa, zan canza kaya ne."
A gabanshi, yana kallo ta zage rigarta ya rage sai bras a jikinta a k'arshe ma bras d'in cireta tayi ta saka ta bacci sannan ta janye siket d'in ta, yana kallo ta cire pant d'in ta ta saka na rigar baccin, juyowa tayi ta zo ta zauna kusa da shi cikin jijjiga jiki irin na yan duniya, nan suka fara cin kazar yana bata a baki ita ma tana bashi, tun basu ida ba wasan ya sauya ya kuma girmama suka haura kan gadon mulki.
Amar ma har har sukayi sallah suka ci abinci idonsu bai had'u ba, har zuciyarshi baya son Umaimah so na soyayya, amma babu yanda zaiyi duk da yana da halin da zai iya ce ma Hajia bai sonta kuma ta amince, amma yayi hakanne saboda yan uwanshi. Yanzun haka kayan bacci ne ya sanya a d'akin shi ya dawo d'akin, tsaye ya sameta ita ma tayi shirin baccinta, k'ala bai ce mata ba ya haye gado ya kwanta, tana ganin haka ta kashe wutar d'akin ta d'auko bargo a ledarshi ta cire ta shinfid'a k'asa, ta d'auko matashin kai zata koma ya tashi zaune yana kallonta, cike da halin ko in kula yace "Kinga dawo nan ki kwanta, meye na kwanciya a k'asan kuma bayan ga gado?"
Sam bata ji dad'in yanda ya mata magana ba, haka ta taso ta d'an zauna amma bata kwanta ba, shi ma daya kwanta baccin kasa d'aukar shi yayi yana kallonta, ganin haka ba zata gyara su ba yasa shi zura mata hannunshi alamar ta taho yace "Zo k'anwata."
Kallonshi tayi ta kalli hannun, saida ta sunkuyar da kai sannan ta mik'a mishi hannun, jawota yayi ta matso kusa dashi ya rumgumota a jikinshi, d'aya hannun yasa yana shafa kumatunta a hankali, a haka haka kuma sai bacci yayi gaba da ita, a hankali ya gyara mata kwanciyarta ya ja mata lallausan bargon dake kan gadon sannan shima ya kwanta.
A b'angaren *babban yaya* kuma nashi salon daban yake dana kowa, domin kuwa yana shigo ya hangeta tsakiyar gado ta nad'e k'afafu, tsaye yayi ya aje ledojinshi k'asa yace "...
๐
*Alhamdulillah*
_Idan naga ruwan comment zakuji wani insha Allah._
09/09/2020 ร 17:58 - Ummulkhairi: ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*BADAK'ALA*
๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ _*AHALI NA*_๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
๐ณ๐ช *TAURARIN NIGER*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```
_Bismillahir rahamanir rahim_
_35_
"Amarya haka ake tarban miji?"
Wani fad'uwar gaba taji, amma sai tayi shiru bata d'ago ba, takowa yayi saida ya tsaya kanta ya janye mayafin fuskarta, tallabo hab'arta yayi ya saka idonta cikin nashi, murmushi ya mata yace "Ai na d'auka kuka ne kike? Dana tambayeki kuka me kike?"
Sunkuyar da kanta tayi tana k'ok'arin mayar da mayafin sai kuma yace "Kinga ta so ki gani."
Hannayenta ya kamo ta sauko daga kan gadon suna fuskantar juna, tsaye k'ik'am ya mata yace "Taimaka min na cire wannan kayan, kinsan fa ban saba saka irin wannan kayan ba, kawai dai dan yana bikina ne ina so na fito a angona."
Kasa kallonshi tayi sai kallon k'asa da take tana shafa wuyanta da tafin hannunta, ita fa wannan tijarar tashi ce tasa take shakkar aurenshi, ya zai ce ta taimaka mishi ya cire kaya? Ba ma zai barta ta mori amarcin ba wannan, kafeta yayi da ido yace "Ke dake fa nake."
Da sauri ta kalleshi cikin tsoro ta zura hannu saman kanshi ta d'auke mishi hular, ajeta tayi kan gado ta kalleshi kamar zata fashe da kuka tana aika mishi da kallon dan Allah ka k'yale ni haka, hannu ya d'aga kamar zai mareta yana fad'in "Dallah ni kar ki min kuka, mage kawai."
Ja baya tayi har ta fad'a kan gadon zaune tana binshi da kallo, cire babbar rigar yayi ya cilla mata ya rufe mata fuska, janye rigar tayi ta hangeshi ya shiga ban d'aki, k'amshin rigar daya daketa ne yasa ta k'ara mannata a hanci tana shak'a tana lumshe ido, tunaninta yanda zata iya wannan bahagon yayan nata take, wani k'asaitaccen murmushi ta saki saboda ganin sam bai b'ata nuna mata k'iyayya ba, tana cikin sakin murmushin nan ya fito ba tare data sani ba dan bai rufe k'ofar duka ba lokacin daya shiga, yana sauke ido a kanta yace "Jikanyar Hajia har na fara kasheki ne? To ai baki ga komai ba, sai ma anjima ko?"
Kamar wata marar gaskiya haka ta lallab'a ta aje mishi rigar bata yarda sun had'a ido ba, matsowa yayi ya kama hannunta ta mik'e tsaye ya turata gaba yace "Je kiyi alwala ki zo muyi sallah, tunda ke ma kina da tsarki yau kwana zamuyi muna ibada."
Juyowa tayi ta kalleshi baki bud'e, ta fara tsoratada al'amarin nashi kam, wani dolon murmushi ya mata yace "Yi sauri mana, ko so kike saina fara nuna miki komai a fili."
K'ara k'ank'ance k'aramin bakinta tayi ta juya kamar wacce k'wai ya fashe ma cikin ciki, kamar a mafarki sai ji tayi an mareta a mazaunai, juyowa tayi da k'arfi ta kalleshi, kashe mata ido yayi yana d'an cije leb'en k'asa, da sauri ta sake juyawa ta shige ban d'aki, had'e fuska yayi kamar ba shine ke dariyar nan ba ya juyo ya d'auki sallaya yana shinfid'awa yana fad'in "Kaji min yarinya, ku mata kun d'auka ku kad'ai kuka iya kwarkwasa ko, to ni ma da nayi niyya dana zama karawi."
Duk da ta gama alwalar amma saita kasa fitowa tana tunanin abinda zata tarar, ganin shiru yasa shi sanyo kai cikin ban d'akin, had'a ido sukayi tana tsaye gaban madubi ta jinjina a bango, ba tare daya shiga ba ya zura hannunshi ya kamota suka fito, suna zuwa ta samu hijabi ta saka suka kabbara sallah, suna kammalawa daga nan ya juyo ya fuskanceta, hannunshi ya zura ya d'an janye hijabinta daga kanta ya dafa kan nata ya karanta mata addu'a "Allahumma ini as'alukha khairuha wa khairu ba jabaltaha alaihi, wa a'uzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi."
D'auke hannun yayi ya k'ara gyara zama ya k'ura mata ido yace "Amna, yau gani ni dake a d'aki d'aya a matsayin mata da miji, wannan wani al'amari ne daga ubangiji, domin kuwa a rayuwata ban tab'a tunanin zaki zama matata ba, sai dai ina farin ciki da kasancewarki matata d'in, dan zan iya cewa ko Ummy data raineku bata kaini saninku ba, yarinyar kirki ce ke, dan haka ina fatan Allah ya bamu zaman lafiya."
Cikin sanyanyar murya tace "Ameen."
K'arawa yayi da cewa "Amna, nasan kuna zuwa islamiyya, zan iya sanin zurfin karatunki?"
Ba tare da sun had'a ido ba ta fara mishi bayanin matakin karatunta, kallonta yayi yace "Amma me yasa baki fara karanta arba'una hadisi ba har ki fahimce shi sannan ki fara bulugul maram? Duk littafin hadisin da zaki karanta idan baki karantashi ba ba zaki fahimci abubuwa dayawa ba, domin kuwa wasu malaman sunce gaba d'aya kafatanin musuluncin yana dunk'ule ne a cikin hadisai k'waya talatin, kuma wad'annan hadisan guda talatin suna cikin littafin arba'una hadisi, yayin da wani malamin shi kuma yace ai gaba d'aya addinin ma yana cikin hadisi guda d'aya ne tak, kuma wannan hadisin shima yana cikin littafin, kinga kenan indai har kina so ki fahimta zaifi miki ki fara dashi, idan kikayi nasarar kammalashi saiki fara da muwadd'a, kin gane?"
A hankali ta jinjina kai alamar eh, mik'ewa yayi tsaye yace "Ki d'auko ledar ce ki juye abin ciki a faranti."
Mik'ewa tayi ita ma ta d'auko ledar shi kuma taga ya fita, ita ma fitowa tayi inda ta tabbatar nan ne madafa ta shiga, d'auko faranti tayi da cup biyu ta dawo, har ta juye ta zuba komai shiru bai dawo ba, bakin gado ta zauna tana jiran ya shigo taji yanda zasu k'are dashi, ai kuwa yana shigowa ta kalleshi lokaci d'aya ta sauke idonta k'asa, farin dogon wando ne jikinshi na zallar kad'a da farar singlet, saida ya aje wayarshi a hannu ya k'araso yana fad'in "Wai ke me kike nufi? Kunya ce kike ji? Ina ce dai tare muka rayu gidan nan, kin sanni tun lokacin ina yawo da gajeran wando, haka nima na sanki tun ina saka miki wando da kaina, to kuma miye na wannan nok'ewar, dallah tashi ki canza kaya ki zo ki ci abinci cikinki yayi nauyi, idan ba so kike ki b'ata min rai ba yanzu na karya miki k'afafu."
Tashi tayi da sauri ta nufi wajen kaya ta kuma nufa ban d'aki, ganin duk ta diririce yasa ya kama hannunta har ban d'aki, gashi dai sun shigo kuma babu alamar zai fita, cire mata hijabin jikinta yayi da d'an kwali ya jefosu kan gado dan bai rufe k'ofar ba, juyata yayi ya kama zip d'in rigarta ya cire, sake juyota yayi ya kama rigar zai zageta ta k'asa, da sauri ta d'an rik'e rigar tana kallonshi a tsorace, kallonta yayi gira a had'e yace "Meye? Amna kina so na ci uwaki ne a daren nan?"
A hankali ta girgiza masa kai idonta har sun cika da k'walla, ko a jikinshi sai ma kama rigar da yayi ya zuge mata ita ta k'asa, sunkuyawa yayi ya fitar da rigar daga k'afafun ta ya d'ago, Amna da tuni tasa hannayenta ta rufe jikinta ta rintse ido, kamar daga sama taji yace "Wow, 'yar k'anwata ce ta zama haka? Lallai kun girma, gobe dole naje na yiwa kakarku godiya, domin kuwa ta min zab'in daya dace dani, kamar tasan irin yanda nake son matata ta kasance."
Sunkuyar da kanta ta sake yi shi kuma bai kula ma da tsiyar da take ba, rumgume hannayen shi yayi a k'irji yana k'are mata kallo, duk da ta rufe abubuwa dayawa amma bai hana shi gane wasu abubuwan ba shima, fad'in k'ugunta da cikinta yasa mazaunanta suka zama masu d'aukar hankali, fuskarta ya koma kallo d'an k'aramin bakinta da kurmin idonta, wata tausassan dariya yayi a daidai lokacin Amna ta gaji da yin shiru ta bud'a ido a hankali, suna had'a ido ta sake rufe ido ta juya baya, hakanne ya bashi damar kallon kayan da suke d'aukar hankalinshi, jefo rigar yayi bata ko sauka akan gadon ba, rumgume ta yayi ta baya yasa hannun dama yana shafa mazaunanta, har ga Allah inhar zai fad'i gaskiya a lokacin daya ruk'unk'umeta saida yaji yanda jikinta ke rawa, amma kuma tsikar jikinta duk ta tashi, dan kar ya saba mata da tsoronshi yasa ya taushe abinda yake ji a lokacin, sakinta yayi yace "Maza kiyi wankan ki fito ina jiranki."
Bata iya cewa komai ba saida taji ya rufo mata k'ofar, ajiyar zuciya ta sauke idonta na zubo da hawayen da suka mak'ale, da k'yar ta iya wanka ta fito, nan ma ta sameshi kwance akan gadon kamar jiranta yake, saukowa yayi ya bud'a wajen kayanta ya shiga bincika, wata riga ya samu iya gwiwa tsayinta fara k'al tare da wandonta a jikin rigar, d'aukowa yayi ya juyo gareta tana zaune tana shafa mai ya rufe robar man yace "Kina shafawa ne saboda jikinyi kiyi tsantsi na kasa kama ki da kyau, muguwa."
Ita dai k'ala ba tace ba sai turare daya d'auka yana ta fesa mata har saman kai da bayanta saida ya feshe, mik'ar da