Showing 183001 words to 186000 words out of 325849 words
zaunar da ita yayi akan cinyar shi hakan yasa ta rintse ido sosai, wuk'ar nan ya d'ora mata a wuya yace "Kalle ni."
Tana bud'a ido taga wuk'a ce ya aza mata bata san lokacin data kwamtsa k'ara ba tasa hannayenta ta rufe fuska, lumshe ido yayi sanda siririyar muryarta ta daki kunnuwanshi, gaba d'aya jikinshi saida ya amsa, bud'e ido yayi ya aje wuk'ar ya d'auki lemu, janye hannayenta yayi yasa mata lemun a baki, amsa tayi tana sake sunne kanta, cikin taushin murya yace "Amna, kafin a d'aura aurenmu na d'auka ni dake zamu zama kamar abokan juna ne, amma gashi daga jiya zuwa yau naga sai k'ara tsorata dani kike, ba haka nake so mu zama ba Amna, ina so naga kin zama komai tawa wacce zan iya samun farin ciki a wurinki, ina so ki zama sirrin farin cikina, zan so ki zama maganin damuwata, Amna burina shine ki zama mai share hawaye na a duk sanda suka kwaranyo, Amna ki zama aminiyata kuma abokiyar shawarata, Amna *banda kowa*, sannan *banda komai*, babu wanda yake *kusanta ta*, ina so ki zama tare dani a kowane hali kuma a kowane yanayi, na sani Amna gidan nan ko kuma nace duk ahalinmu suna min kallon wani mahaukaci kuma marar kunya fitsararre marar tarbiyya, amma...amma..."
Sunkuyar da kai yayi yana furzar da wata zazzafar iska daga bakinshi, rawa muryarshi keyi kamar zaiyi kuka, zuciyarshi bugawa ta fara yi da sauri sauri, ya jima kanshi na kallon k'asa kafin ya d'ago yana kallonta sai dai basu had'a ido ba, bud'a baki yayi a hankali yace "Amna ni ba mahaukaci bane, ni ba marar tarbiyya bane, sannan ina da kunya da nutsuwa, duk abinda nake yi ina sane nake yin shi, da gangan nake yi da fatan samun kusanci a wurin iyayena, amma..."
Da sauri yasa bayan hannunshi ya goge yar k'wallar data taho mishi, da sauri ya turata gefenshi ta fad'a kan gado shi kuma ya mik'e tsaye, juya mata baya yayi yace "Har yanzu ban yi nasara, na d'auka zasu iya zama dani suji dalilin da yasa na zama haka, sun kasa fahimta har yanzu, babu mai iya gane ina jin yunwa ko na k'oshi, to tayaya ne zasu iya fahimtar abinda ke zuciyata, na zab'i na fara fito dashi ne dan kar ciwon zuciya ya kama ni a k'arshe na mutu, bansan ya zanyi da su ba."
Juyowa yayi ya kalleta wacce ita ma ta k'ura mishi ido yace "Na gaza Amna."
Ban d'aki ya shige ya barta zaune, k'urawa k'ofar ido tayi tana tunani da nanata abinda ya fad'a, ta d'an jima a haka kafin ta d'aga kafad'u tare da tab'e baki ta mik'e ta koma madafa, girkin data jima da d'orawa ta ci gaba daga inda ta tsaya, sai dai jikinta a matuk'ar sanyaye yake tana tunanin halin da mijinta ke ciki, meye damuwarsa? Meye tsakaninshi dasu Ummy? Meye ainihin abinda ke faruwa? Hak'ik'a ko ita kafin yanzu tana jin yana matsa mata ne sosai, tana ji babu kunya a al'amuransa, yana da k'arancin nutsuwa wani lokacin, kenan duk yana sane yake yi? To me yasa? Me yasa namiji kamar Ammar ke saurin zubar da hawaye? Bayan ita shaida ce akan jarumtarsa wacce ke tattare da masifa da bala'i, a sanin data mishi ko baka nemi jaraba da shi ba shi zai nemeka da ita, a sanin data mishi baya da saurin kasawa haka, mutumin ne dake tsaye tsayin daka wajen ganin ya ci galaba akan abokin karawarshi, to amma meya raunata zuciyarshi har haka? Wannan amsa ce daya kamata tasan amsarta, domin yanzu alhakin farin cikinshi na wuyanta ne, da haka ta k'arasa girkinta ta fito ta gyara wurin cin abincin, ta nufi hanyar da zata sadata da d'akinta taga ya fito daga d'aya d'akin cikin k'ananan kaya, amma abun mamaki bai yarda ya had'a ido da ita ba.
Ya nufi hanyar fita tayi saurin cewa "Yah Ammar."
Tsayawa yayi ya juyo ya kalleta amma baice komai ba, shagwab'ar da fuskarta tayi kamar ta jarirai tace "Abincinka fa."
Har ga Allah da ya so irin d'aurawer nan, amma yanayin da tayi da fuskarta saiya sashi sakin murmushi, domin kuwa abinda ya zo masa a rai ita ce Hamna, wato Hamna tafi k'warewa wajen shagwab'ar bubbuga k'afafu, ita kuma wannan gaba d'aya take canza fuskarta da yanayinta idan zatayi ta ta shagwab'ar, d'aga gira yayi yace "Kenan saida kika dafa abincin?"
Nufowa kanta yayi yana k'ok'arin cire belt d'in shi yana fad'in "Idan na rugurguza miki jiki gobe ba zaki sake bijirewa abinda na fad'a ba."
Tana ganin ta durk'ushe ta had'e hannaye biyu tasa kusa tana fad'in "Dan Allah yah Ammar kayi hak'uri ba zan k'ara ba wallahi, idan kana so ma yanzu sai nake na zubar da wanda na dafa, dan Allah karka dake ni wallahi bana son duka a jiki na."
Ganin ya kawo daf da ita amma bai cire belt d'in ba yasa ta rintse ido, yana zuwa yasa hannayenshi ya tallabota yana dariya yana kallon fuskarta, ganin bata bud'a idon ba tsabar tsorata da tayi yasa shi rumgumeta jikinshi yana fad'in "Amna yanzu fa na gama fad'a miki, shin idan ban zolayeki wa zan zolaya?"
Shiru tayi daga kukan da take rerawa ta bud'a ido ta d'ago kai ta kalleshi, yanda idonsu suka had'u ne yasa kowannensu jin wata wutar tsartsatsi ta bulbulo daga zuciyarsu, murmushi ya dalla mata ya tallabe fuskarta yace "Irin rayuwar da nake so muyi dake kenan Amna, mai cike da mutuntawa, farin ciki, annashuwa, k'aunar juna, tsokana da zolaya."
Sunkuyar da kanta tayi a cikin k'irjinshi, shi ma kuma yana jin haka saiya k'ara kwantar da ita yana shafa kanta yana sauke mata numfashi a kai, sanyanyen turarenshi mai tayar da tsikar jiki da kuma kwantar da hankali take shak'ar k'amshinsa, luf tayi kamar mai son yin bacci tare da zura hannayenta ta baya ita ma ta d'an rik'e shi amma ba sosai ba, tunanin duniya take a daidai wannan lokacin.
Ammar dai, yayansu dake matuk'ar firgita lissafinsu, wanda basa fatan a kai mishi k'ararsu idan sunyi laifi, wanda ko babu laifin ma zai iya kunyataka ya tsinka ka a cikin jama'a, yau ita ce a k'irjin shi a matsayin mata? Bata tab'a kawo haka a ranta ba, dan a wajenta abune da ba zai yiwu ba, tayi tunanin tsaf zai nuna ta yace baya sonta, ta d'auka zai kalleta ne yace Allahya tsare shi da aurenta. Kai ita kanta fa taso tace bata son shi, amma ganin shi bai furta ba yasa ta yin shiru da fammun d'inta, dan idan har ta kuskura kalmar bana sonka ta fito daga bakinta, to tsaf zai iya tisata a gaba da tab'arya yace sai yaji dalili, wannan dalilin ne ita kuma yasa bata iya fad'a ba. Tana wannan duniyar taji ya d'ago kanta ya kalleta yace "Kin iya girki ne dama?"
Kallonshi tayi a sagale, na iya girki? Me yake nufi? Kafin ta bashi amsa ya nufi wajen abincin yana fad'in "Na ga dai waccen kakar taku tafi damuwa da al'amarin tsaronku ta yanda bata barinku fita, amma kulawa daku kuma wannan bata ma san me takeyi ba."
Bin bayanshi tayi ya zauna kan kujera ita kuma ta fara zuba mishi farar shinkafar da tayi warwara gwanin kyau, sai kabeji data zagayeta da su sannan ta kuma zagayeta da karas wanda duk ta gurzasu, sai dunk'ulallen naman data jera shima kafin ta zuba sauce d'in albassar a tsakiya, tab'e baki yayi ya janyo farantin ya d'auki cokali ya kai lomar farko, kallonta yayi ya mata alama da hannu πcewa komai yayi, murmushi tayi ta ja kujera ta zauna cikin d'ard'ar tace "Ai ba ido kawai Hajia take saka mana ba, har yanda zamu kyautata rayuwarmu tasa an koya mana."
Murmushin baki da hankali ya mata ba tare daya kalleta ba, saida yayi loma bakwai har ta manta da zaiyi magana sannan taji yace "Amna."
"Um." Ta fad'a tana mayar da hankalinta kanshi, saida ya kalleta yayi kalar tausayi sosai yace "Dan Allah ki dinga girka min abinci kullum ina ci, ina yawon zama da yunwa, ki min wannan alfarmar kinji?"
"To amma yah Ammar me yasa baka san cin abinci?"
Kallonta yayi babu annuri a fuskarshi, har zai bata amsa sai kuma ya canza maganar yace "Bana da wanda zai rik'a bani a baki ne."
Sunkuyar da kai tayi a zuciyarta tace "Uban wani kakan wani ka zauna sai an baka abinci a baki? Lallai ma mutumin nan."
Kafin wata magana ta sake shiga tsakaninsu aka bud'a k'ofar d'akin aka shigo, dukansu kallon k'ofar sukayi a tare, da sakin fuska Amna tace "Autan Ummy ne?"
Bai ce komai ba kamar yanda bai saki fuskarsa daga had'ewar daya mata ba, saida ya zo inda suke yace "Zuba min nima zan ci."
Murmushi tayi tana kallonsa ta fara k'ok'arin zuba masa tana fad'in "Autan Ummy kamar ranka a b'ace? Waya tab'aka ne?"
Kujera yaja zai zauna Ammar ya sauke mishi jajayen idonshi, kallo ne da zai iya saka fitsari a wando, kallo ne dake tattare da aika sak'onni dayawa, ba kayi sallama ba, baka gaishe da mutane ba, sannan kana wani d'aurawa mutane fuska, baka ga wurin zama ba sai a nan? Sannan me ma ya kawo ka?π To bashi Amsa Kamal.
Kallon Amna yayi wacce ita ma ta kalleshi dan ta lura da kallon daya mishi, murmushi ta sake yi tace "Wai waya tab'a ka ne Kamal?"
Turo baki yayi yace "Tonton Gambo ne zai koma Niamey yanzu, shine na ce zan bishi Hajia tace a'a, wai sai dai su tafi da Hamna."
Dukansu sake bashi hankalinsu sukayi inda Ammar ya d'ora da cewa "Saboda me?"
"Nima ban sani ba." Ya fad'a yana zaunawa kan kujerar, kallonshi Amna tayi da mamaki tace "Me yasa Hajia zata tura Hamna can kuma?"
"Ba haka kawai tayi ba." Yana fad'a ya mik'e da hanzari zai bar falon, da sauri Amna ta bi bayanshi tace "Yah Ammar zan iya zuwa na ga yer uwata? Wallahi nasan ba'a son ranta zata je ba, daga ni har ita babu mai son zuwa wajen Abba saboda tanti Aissata ba k'aunarmu take ba."
Hannunta ya kamo kawai suka fita, ta k'ofar dake cikin gidan suka shiga, kai tsaye falo suka nufa ba tare daya saki hannunta ba, suna shiga Amna tayi sallama amma banda gogan, hankalinshi na kan mutanen dake cikin d'akin yana kallonsu d'aya bayan d'aya, a hankali ya saki hannunta ta gaishe da mutanen wurin, kowa ya amsa amma banda Hajia dake kallonta a hargitse, kallon mahaifinsu tayi dake zaune kan. kujera tace "Abba yanzu zaku tafi?"
"Yanzu zamu koma auta ta, amma tare da Hamna zan tafi." Duk yayi maganar ne jiki a sanyaye, da d'an mamaki tace "Amma Abba me yasa zaka tafi da ita yanzu? Kai fa kake cewa kafi son zamanmu anan."
"Yanzu kuma ya sauya, zai tafi da ita tunda anyi hutu, kuma ba aure ne da ita ba tunda ta k'i aure."
A tare suka kalleta ita da Ammar, kallon ladabi da tsoro ta mata, yayin da shi kuma ya bita da kallon to sai akayi yaya kuma? Hajia kifa kiyaye ni, meye na wani d'auketa daga nan d'in? Jin bbu wanda yace wani abu yasa Amna ta tunkari d'akinsu na sama da sauri dan ta samu Hamna, tana shiga ta sameta zaune bakin gado da alama kuka take, k'arasawa tayi ta zauna kusanta ta dafata tace "Rabin jikina, kuka kike? Na sani dama ba zaki so tafiya ba, amma me yasa Hajia tace a tafi dake?"
D'an d'ago kanta tayi ta kalleta tace "Nima bansan dalilinta ba rabin jiki, kawai dan bata son gani na a gidan nan."
Da sauri tace "A'a rabin jiki, karki fad'i haka mana, kinfi kowa sanin yanda Hajia bata san muyi nesa da ita, ina ga dai ko dan baki amince da auren yah Junaid bane."
Tab'e baki tayi alamar ko oho, jin ba tace komai ba yasa Amna mik'ewa tsaye ta kamata tana fad'in"Taso, tashi muje ki bata hak'uri dan Allah, ba zan yarda ta rabani dake ba a lokacin da nafi buk'atarki a kusa da ni."
Mik'ewa tayi cike da kasala tace "Amna ba zata hak'ura ba, kefa kin sani."
Janta tayi da k'arfi suka nufi hanyar fita, a lokacin ne wani tunani ya zo ma Hamna, a take sai taji tana buk'atar yin nisa da gidan ma ko dan yer uwarta, dan har yanzu bata iya kallon k'wayar idonta idan ta tuna tasan mijinta kafin ita, duk da tursasata akayi amma abun kunya ne a wurinta. Sai dai kuma Ummy na buk'atar zamanta anan ko dan abinda ke cikinta, *ciki?* Shine abinda ta sake maimaitawa, hawaye taji sun taho mata a wannan lokacin, bata ankara ba sai ji tayi sua sauka kan matattakala suna sauka k'asa, yanayinta ne ya sake canzawa gaba d'aya, sanyin jijiyoyinta suka rub'anya ta yanda suke daf da tsinkewa, tun daga nesa take kallon mutanen dake k'asa, hawayen ne ke ci gaba da zubo mata saboda tasan a halin yanzu yer uwarta ba zata ji dad'in abinda zata mata ba, dan kuwa k'aryata ta ne zatayi a gaban mutane, tasan za taji zafi sosai sai dai zata fahimci dalilinta, sai dai kuma bata san yaushe ne ba?.
Tunda suka taho ya k'ura mata ido, kallon k'wak'waf ne yake mata na son gano yanayin da take ciki, sai dai garin kallon nan na jaraba ne ya fara hango wani abun, canji ne sosai wanda shi dai bai santa da shi ba, amma ganin baida hujjar da zai tabbatarwa kanshi yasa shi faa fafutukar neman hujjar, bai daina binta da wannan kallon mai firgita wanda ake ma ba suka k'araso, Amna na rik'e da hannunta suka tunkari wurin Hajia da niyyar mata magana, amma sai Ammar yasha gabansu kamar sojon da zai bincikesu, idon Hamna ya kalla sosai tare da mata wani tuhumammen kallo ya nuna idonta da yatsa kamar zai tsoneta yace "Sai kace wata mai ciki sai k'yak'yabta ido kike, ko tafiyarce ba kya so?"
Wandon dake jikin Ummy ne kawai ya mata shamaki da saurin b'allowar fitsari, sai dai ta tabbatar kayan cikinta zamansu ya sauya, dan juyawar da sukayi mota ce kawai za tayi wannan harurun da kai yayin da ta jirkice ta fantsama katantawwa da kai. Hamna kuma numfashinta ne taji ta nema ta rasa, hakan ne ya haddasa mata rufe ido sai k'wayar idonta dake juyawa, Amna kuma kallonshi tayi ba tare da tunanin komai ba tana murmushi, dan ita yanzu ta fara fahimtar mijin nata, sannan da yace yana sane yake komai yasa tayi damarar shanye duk wata katob'ara tashi, kowa madale wajen abinda yayi tunani kenan ba Hajia kad'ai ba, wato rashin kunyar ce ko? Kamar a mafarki sai gani sukayi yasa hannu ya tallaba kanta yana k'ok'arin bud'e mata ido, dan shi dai a matsayinshi na likita duk da ba abinda ya karanta ba kenan, amma da kallo da kuma ji zai iya gane larurar wani majinyacin, yana cikin kiciniyar nan Ummy dake kallonsa kamar mahaukaci ganin yana neman b'alle mata lik'i yasa ta tahowa da k'arfin tsiya, k'arfin da yafi k'arfin kuzarinta da d'ab'iarta, tana zuwa gabanshi ta d'aga hannu iya k'arfinta ta wanke fuskarshi da mari.
K'arfin marin yasa shi duk'ar da kai gefe d'aya dafe da kunci, ya jima haka yana sauraron masifar da Ummy ke mishi, cikin hargagi da zautuwar tunani take fad'in "Baka da hankali ne? Wannan wace irin fitsara ce? A gidan uban wa ka koyo wannan tarbiyar? Anya Ammar kai d'ana ne kuwa? Ka sani fa a hanyar aure na same ka ba da zina ba."
Hannun Hamna ta kama da niyyar barin wurin taji Hajia tace "...
*Saboda farin cikin isar da yarinyata lafiya d'akin mijinta.*π
09/09/2020 Γ 17:58 - Ummulkhairi: π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨
*BADAK'ALA*
π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_ (sai Allah)
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura...)_
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
π¨βπ©βπ§βπ¦ *AHALI NA*π¨βπ©βπ§βπ¦
Β©π
*π³πͺTAURARIN NIGER..*
```(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)```
βͺ{T . N}βͺπποΈ
https://www.facebook.com/Taurarin-Niger-100155928500614/
_Bismillahir rahamanir rahim_
_39_
Hajia ce tace "Malama meye na tunzura haka? So kike ki rufe bakinmu mu kasa fad'ar rashin kunyar d'an ki? To dawo da ita tafiya zasuyi."
Juyowa sukayi suka tsaya sai rarraba ido suke alamar rashin gaskiya, a lokacin ne Hajia ta kalli Hamna da kyau, kallabi ne jikinta wanda bai rufe mata jiki ba, tabbas Hajia tasan ita da Amna ba ma'abota bras bane, dan gabansu a cike yake kuma pampam dashi, su Umaimah ne sarakan sawa kullum, amma ganin yau sun mata wata irin cikowa kamar mai ciki yasa ita kanta sai taji ba dan Ammar ba mutuminta bane data yarda da abinda ya fad'a, Ummy dake cike da razani da tsoro tuni ta ga kallon da Hajia ke mata, da sauri tace "Hajia kinsan shi da shirmen banza, bai san me yake fad'a ba wani lokacin, komai ya zo bakinshi saiya fad'a."
Amna ce ta kalli Ummy ranta a matuk'ar b'ace na marin data wa mijinta, d'an k'aramin iska ta furzar irin na rashin jin dad'in nan kafin ta matsa kusa da Ammar da har yanzu ya k'asa d'agowa, a hankali ta kama hannunshi tana kallonshi, ganin bai kulata ba yasa ta kalli Hajia tace "Hajia dan Allah kiyi hak'uri ki barta anan, wallahi bata san tafiya ita ma."
Wani kallo ta mata tace "Ita ta fad'a miki bata so? Ko kin ari bakinta ne kin ci mata albassa?"
Kallon Hamna tayi tace "Na sani bata so, kuma gata nan ku tambayeta."
Mahaifinsu ne yace "To ko bata so ba dole ta hak'ura ta so ba tunda Hajia tace a tafi da ita."
Hajia ce ta kalli Hamna tace "Ke kika fad'a mata ba kya son tafiyar?"
Kallon Hajia tayi ta kalli Amna da ita ma ta kafeta da ido, kallon kiyi hak'uri ta mata sannan ta kalli Ummy dake