Showing 51001 words to 54000 words out of 325849 words

Chapter 18 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

523

Middle Ads

shiga ciki tana ta zagaye ta rasa abunyi, tana ji kamar ta rok'i wani amma tana jin tsoron k'ara neman taimako, tana haka wani matashi da gani kasan d'an makaranta ne dake shirin tafiya hutu wani garin ya mata magana, a tak'aice dai shi ya taimaka mata ya biya mata kud'in motar bayan ta fad'a mishi bata da kowa anan tana so taje gida ne, tare suka zauna kujera d'aya matashin nan duk inda aka tsaya saiya siye abu ya bata, duk da tana tsoron sakewa da shi har saida ta d'an saki jiki, kallonshi tayi tace "Dan Allah me sunanka? Sai tafiya muke har yanzu baka fad'a min ba."

Kallonta yayi yana murmushi yace "Ke ma ai baki fad'a min ba, kawai kince min kinyi b'atan kai ne shiyasa ni kuma zan taimaka miki."

Tayi tace "Sunana *Maryama*, amma wasu na kirana da Mari."

Murmushi ya mata shima yace "Ni kuma *Issa*." Da haka suka d'an dinga hira kafin Allah ya kaisu lafiya, suna sauka ya nemi lambar wayarta tace bata da, ya nemi kwatancen gidan tace bata san ya zatayi ta kwatanta mishi ita ma dan ta jima rabonta da garin, ya yarda da hakan dan ko harshenta bai gama fad'awa a hausar ba, taxi suka shigo tare har aka ajeta k'ofar gidan tanti Khadi wacce labarin abinda ya faru ya riga Mari isowa wajenta, hakan kuma ya faru ne lokacin da Mari taje gidan wata yar uwarsu, bayan tafiyarta hankalinta bai kwanta ba saita kira kakar Mari, cikin hushi ta fad'a mata wai Mari cikin shege ta musu dan tozarci, yanda abun ya daketa ne yasa ta kasa hak'ura ta kira Khadi tana tambayarta wai hakane? Ita kuma sai lokacin taji meke faruwa, ita ma dai kusan sumar tayi, amma daga baya haka ta dinga fad'a tana masifa wai Mari ta zubar musu da mutumci, su a zuri'ar su kaf babu wanda ya tab'a cikin shege sai ita, har ta wayi gari tana wannan kwakwazon, abun bai bar tunaninta ba kuma sai ga sallamar mari ta diro garin daf da magrib, tunda ta k'ura mata ido bata d'auke ba har mari ta tsargu, yan uwa in dai kaiku in baro Khadi ma bata karb'i Mari ba, cewa tayi sam ba da ita ba kawai ta koma wajen uwarta data d'aure mata gindi (duk da ta ji uwar fa suma tayi), duk magiyar duniya ba wacce bata mata ba amma ta rufe ido, har saida tace mata "Ki gode Allah da kawu *Rabi'u* baya gari abin nan ya faru, ba dan haka ba da har kasheki zai iya yi, dan shi baya lamuntar wannan iskancin." Sai lokacin Mari ta fahimci dalilin da yasa bata samu malam Rabi'u ba, kenan da yana nan da abun ya munana?haka ta fito da kunyar ganin bak'on data tsayar da niyyar ta shiga ta kawo mishi ruwa tantin ta kuma ta mishi godiya na alkairin daya mata, haka suka jera ita da shi basu san ina zasu je ba, shi dai ba zai iya tafiya da ita gidan da ya zo hutu ba, to meye abunyi, har aka gama sallah magrib suna tafiya kafin Mari shed'an ya zugata tace saurayin ya bata lambarshi zata kirashi idan taje wani wurin, rubuta mata yayi yana kallo harta b'ace ma ganinshi, doguwar tafiya tayi har ta zo wucewa ta ranpoint d'in hôpital, anan ne suka fara had'uwa da Iklima, kallon farko da Iklima ta mata sai ta ji tausayinta saboda tana tafe tana kuka da yake nuna k'unci a tare da ita, tsayar da ita tayi suka gaisa ta tambayeta ko lafiya? Da farko kasa fad'a mata komai tayi, amma sai Iklima ta mata karamci ta hanyar zuwa da ita gidan da suke zaune ita da sauran yan mata masu yawa, sauran abinci ta bata ta ci sannan tace ta saki jikinta, cikin fargaba ta kwashe komai ta fad'a mata abinda ya faru da ita, tab'e baki Iklima tayi tace ...

"Ai matsalar iyayenmu kenan, zaki shekara dubu kina kare mutumcinki, amma rana d'aya idan tsautsayi ya fad'a miki ki kayi ciki to sun manta, nima abinda ya faru dani kenan, sai dai ni da amincewata na yarda da saurayin saboda ina son shi, shigar rabo yasa na samu ciki, amma haka suka fara min horon yunwa ga tsanani ko kulani basa yi a gidan, ça tsangwama da hanta ta yayyu na, shiyasa ni kuma da naga yunwa na neman halakani na bar musu gidan, yanzu nan nake rayuwata duk da mahaifiyata na so na koma gidan yanzu, kuma cikin dana fito da shi ina haihuwarshi na kaiwa ubanshi, ni kuma na ci gaba da neman kud'i na."

Da mamaki Mari ta kalleta tace "Kenan ke ba korarki sukayi ba? Amma me yasa ba zaki koma ba tunda suna so ki koma? Sannan meye sana'ar da kike anan d'in?"

Duk wata tambaya da Mari ta mata saida ta bata amsar ta, amma sai Mari ta k'yamaci abun ta nuna ba zata iya ba, dan haka Iklima tace "To idan kina ganin yanzu a duniyar nan ana taimako dan Allah ki fita ki jaraba nema ki gani, mace dai ba zata iya miki taimakon da a yanzu kike buk'ata ba sai namiji, to ki jaraba neman taimakon mazan ki gani idan basu miki kallon sama da k'asa ba."

Mik'ewa tayi zata fita tace "Ki samu ruwa kiyi wanka, idan kin gama ki rufe min k'ofar d'akin dan ba ni kad'ai ke zaune ciki ba, idan har baki samu taimakon ba zaki iya dawowa ki same ni tunda kinga inda nake."

Da kallo ta bita harta fita, tana fita ita ma ta d'auki jakar kayanta ta fito ta kama hanya, ina zata je? Wa zata nema taimako? Abinda ya sameta dalilin neman taimakon ne fa, tana cikin tafiyar ta tsaya bakin titi kamar wacce zata tsallaka amma tunaninta ba nan yake ba, tana haka kuwa wani matashin saurayi da alama irin yaran nan ne masu jiran shago ya mata magana, maganar ma bata alkairi ba saita banza, wai a nawa zata siyar zai biya? Jin haka saita tsorata ta dawo baya gidan Iklima, a gurguje dai nan suka had'e suka fara wannan rayuwa ta k'ask'anci, kamar yanda Mari tace ita k'aramar karuwa ce, domin kuwa duk kud'in da zata samu basa wuce na yan buk'atu abin ci abin sha yar sutura marar tsada, ciki kuma na girma tana rainonshi tare da tunanin irin tarbiyar da zata bawa wannan cikin idan ya fito, saida cikinta ya tsufa ta daina fita sai Iklima kad'ai, a wannan lokacin sai take jin Iklima kamar yer uwa da suka fito ciki d'aya, tana haihuwa ma Iklima ce tsaye kan komai kamar ita akawa haihuwar, har akayi suna sai dai *Nurul Huda* bata samun gatan da aka yanka mata rago ba har yau maganar da ake tana shekara shida da haihuwa, bayan haihuwarta tayi arba'in suka ci gaba daga inda suka tsaya, bata sake waiwayar gida ba bare tasan meke faruwa, sai dai tana had'uwa da yayan Khadi a cikin gari har ma su gaisa, lokacin da suka samu kud'i ne sai suka kama gidan hanya wanda duk matan aure ne a gidan, mace d'aya suke abin arzik'i da ita maman Husna, ita ma bata nuna musu tsana ko kyara shiyasa, ana haka Junaid ya ganta wajen bikin wani abokinshi sunje d'aukar abinci gidansu k'awar amaryar wacce ita ta asassa taron suna tsakiyar fili suna rawa, ita ba abokiyar ango bace bare kuma amarya, kawai mawak'in ne mutuminsu shine ya gayyace su kuma suka je, dama kuma in zasuje irin wannan shiri ake na musamman, dan ko rigar nono basa sakawa bare wando saboda ana so komai yasan an motsa shi, haka kawai yarinyar ta mishi yaji ta birge shi, ya kasa gajiya da kallonta, daga ranar ne fa yake bibiyar rayuwarta kuma har yanzu bai daina ba duk da yasan wacece ita, tak'aitaccen labarin Maryama kenan.

*Ci gaban labari*

Ya jinjina sosai da jin labarin, shirun da yayi yana tunani barkatai yasa Iklima mik'ewa tace "Na tafi ni saida safe."
Bai iya kallonta ba har ta wuce, da k'yar shima ya tashi ya shiga motarshi sai dai babu kuzari a tare da shi, gida ya nufa cike da k'warin gwiwar jin wani hukunci daya yanke yana daf da isa gidan.

➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️

Tun yamma Hamna ke son amsar wayarta a hannun Ammar amma ta rasa yanda zatayi, har saida akayi sallah isha'i sannan ta shirya cikin shiga irin ta Amna sak ta nufi b'angaren na samari, tana isa bakin k'ofar ta tsaya tana k'wank'wasawa tare da yin sallama, Ammar da ke zaune falo shi kad'ai yana latsa wayarshi sai wayar Hamna aje gefenshi, a hankali ya d'ago kai ya sauke kan k'ofar, take kuma ya mayar da kallonshi kan wayarshi duk da dai muryar da Hamna keyi tayi sak data Amna, saida ya d'auki kusan minti biyar bai sake d'agowa ba kafin yace "Shigo." A hakan ma ba tare daya kalli k'ofar ba.

Cikin nutsuwa kamar yanda tasan yer uwarta nayi ta shigo tana sake wata sallamar, bai amsa ba bai kuma kalleta ba har ta tsaya tsakiyar falon, a sanin data mishi yasa bata tsaya b'ata lokaci ba ta fara bayani kamar haka "Yaya Ammar, dama zan kira Mamanmu ne a wayar Hamna saboda tawa babu kati a ciki, sai tace wayar tana hannunka kuma kaga idan akayi sallah isha'i ba'a barinmu fita ko yara bare..."

Wannan bayani da take jin shi yake kamar saukan ruwan sama da k'ank'ara a tsakiyar kanshi, k'aguwa tasa ya d'auko wayar dan dama ta ishe shi saboda wayan kiran da ake ya mik'o mata, hannu ta zuro ta karb'a tace "Nagode."

Sai lokacin kad'ai idonshi suka kalli na ta idon, gabanshi ne yaji ya fad'i da sauri ya d'auke idonshi daga kanta, juyawa tayi zata fita a lokacin kuma Jibril ya shigo falon da kular abinci a hannunshi, saida ta kusa kaiwa k'ofa ta juyo ta kece da dariya tace "Allah sarki boss, a hakane kake cewa kana son zama soja bayan baka iya gane waye wannan waye wannan, to kai fa ina ganin ko namiji ya zo maka a shigar mace saika yarda."

Tunda ta fara magana yake hasosho irin muguntar da zai mata, hakan yasa shi kallon Jibril da suka fi kusa cikin kaushin murya yace "Wallahi kai zai ci wa uwa idan har baka rik'e min ita ba."

Tsuru Jibril yayi ya juya ya kalli Hamna data tattare zanin atamfarta, to shi taya ma zai fara rik'e ta ne? Juyowa yayi ya kalli Ammar daya had'e fuskar nan kamar hadarin gabas, sai kawai ya juya da sauri ya nufi k'ofa, Hamna na ganin haka ta rufa a guje da tunanin ita zai kama, shi kuma yasan sai Ammar ya cuce shi, tunda kuma ba zai iya kamota ba gwara ya bar masa gidan, da kallo duka ya bisu kafin yayi k'wafa yace " *Kankana* kenan, zaki shigo hannu na ne, zaki gane shayi ruwa ne."Jibril kam k'ofar gidan ya zauna a teburin mai gadi yana cin abincin suna 'yar hira.

Iyayen na zaune a falo suna hira k'asa kasa saboda Hajia na d'aki kar a dameta, wayar Zeinabu ce tayi k'ara tana neman agaji, d'auka tayi ta duba mai kiran hakan yasa gabanta tsinkewa ya fad'i, datse kiran tayi kafin ta mik'e tace tana zuwa ta shiga d'akin ta, maida kiran tayi da sauri kuwa aka d'auka ana fad'in "Eh lallai Zeinabu kin cika 'yar halak, yanzu har ni zan dinga kiranki amma kina kashewa? To yayi kyau, ni dama ba wani abu yasa na kiraki ba na kira ne inji ya ake ciki? Wata kusan biyu kenan ba sak'onki bana mijinki, shine nake so naji ina aka kwana?"

Har yanzu gabanta bai bar fad'uwa ba a haka ta amsa mata murya k'asa k'asa da " *Inna* Dan Allah kiyi hak'uri, wallahi bana shareki bane, abubuwa ne suka min yawa, colonel kuma nasan ba wai bai nemeki bane aiki ne dai yasha kanshi, amma kiyi hak'uri insha Allahu gobe zan aika miki da kud'in wata d'aya kafin colonel ya dawo."

Da k'arfi tsohuwar tace "Duba Zeinabu, kinfi kowa sanin bana son ana min wasa da maganar kud'i, ki tabbatar gobe kin aiko min kud'in da zanyi cefanai dasu dan kayan abinci na sun k'are, sannan ba zan iya tsayawa jiran mijinki ba, ki kirashi a waya ki fad'a masa ya aiko min da sak'on kamar yanda mukayi yarjejeniya da ku, idan kuma ba haka ba wallahi wallahi *asiri zai tonu*, ehe!"

Da sauri tace "A'a Inna ba sai anyi haka ba, insha Allahu zan tura miki nawa sak'on gobe nan, yanzu ma dan dare yayi ne, colonel kuma zan kirashi yanzu na tuna mishi dan nasan sha'afa yayi."

Cike da gadara tsohuwar tace "To, kashe waya."

Cikin sanyin jiki Zeinabu ta datse kiran ta sake kiran lambar colonel, yana ganin lambar ta yayi murmushin da ba kowa zai iya gane murmushi yayi ba ya d'auka, cikin wani irin amon murya da ba zaka fahimci yanayin da mai ita ke ciki ba yace "Ai na d'auka ba zaki kirani ba, ashe dai ina da rana ta."

"Ni ba abinda yasa na kiraka kenan ba, na kira ne na fad'a maka Inna ta kirani yanzu, bansan dalilin daya hanaka cika alk'awarin daka d'auka ba a wannan watan da har ta kira ni take k'ok'arin tayar min da hankali."

Daga b'angaren shi ya amsa da "Kin kira ne kenan dan ki min fad'a ko me? Saboda ke ce uwata zaki tsareni kina fad'a min maganar nan."

Ita ma a hassale tace "Amma ai kasan kai ka d'auki alk'awari ko? Dan haka dole ka cika."

"Idan na k'i fa? Dukana zakiyi? Wai ko dan kinga bana kusanki ne zaki nemi ki min iskanci?"

Murmushi tayi kamar a gabanshi tace "Ba ma zaka yarda ba wallahi, tunda ka fara dole ka kai k'arshe tunda laifinka ne koma menene."

Wai, colonel Hussein da yake ji kamar ya ganta gabanshi ne ya harzuk'o yace "Laifi na? Laifi na ma kike cewa? A waccen ranar ni nace kiyi abinda zai tayar min da hankali? Ko kuma tursasaki nayi? Ba da amincewarki komai ya faru ba?"

K'asa tayi da ta ta muryar tace "Duk da ba tursasani kayi ba ai ba kana nemana na amince maka ba, sannan bani na ce ka kirani inda kake ba, da kuma na zo kaga zan tayar maka da hankali me ya sa ba kayi gaggawar korata daga wajenka ba?"

D'orawa tayi da "Duk kai ka ja mana wallahi, ba dan kasa tsoron Hajia a ranka ba da yanzu muna rayuwa cikin salama, amma tsoron wanda baida wutar da zai samu ya saka mu sai aikata laifi muke akan wani laifin."

Rintse ido tayi saboda jin k'arar ya bugi wani abu da yake nuna mata da ita ce a kusa da ita ya kaiwa wannan haura, datse hak'oran shi yayi ya rasa bakin magana, ina ma zai ji an kawo masa hari ta baya ko ya samu damar huce wannan haushin, jin baiyi magana yasa tace "Ni duk ba wannan ba, kayi azamar turawa Inna kud'in ta kamar yanda kukayi da ita, dan ni dai ba zan so asiri na dana yarona ya tonu ba a wannan lokacin, gaskiyar magana kenan."

"Kutumar bala'i." Inji colonel a cikin zuciyarshi dan har yanzu ya kasa sakin hak'oran shi, "Wannan ma ai raini ne, Zeinabu umarni ne take bani ko me? Ni? Ni? Ina!" Buga wayar yayi a bango ta baje tare da kai wa bangon naushi, Zeinabu dai ta fad'i abinda ke ranta ta kashe waya ta dawo falo.

Jibril ne a d'akin kakarshi bayan ya gama cin abinci suna hira, kallonta yayi da fara'a a fuskarshi yace "Yar tsohuwa, insha Allahu idan aure na da Amna ya tashi da kaina zan tuk'aki ki kaini wajen dangi Baba, dan wallahi ina so na gansu sosai."

Tunda yayi maganar nan ta had'e fuska tayi shiru, jin shirun yasa yace "Hajia, wai a wane gari dangin mahaifin Baba suke? Na gaji da tambayar Umma akan wannan."

Ba alamar wasa ta kalleshi tace "Kenan ni ce yanzu zaka dama? Malam tashi ka fitar min daga d'aki."

Da mamaki ya kalleta yace "Hajia, kema damuwar ce kamar yanda Umma ke damuwa a duk sanda na mata magana makamanciyar wannan?"

Cikin d'aga murya tace "Ban sani ba Jibril, kuma in har baka son gayyato fushina to kayi gaggawar janye wannan k'udirin naka na son ganin dangin mahaifin mahaifinka."

Mik'ewa yayi da tsantsar mamaki yace "Saboda me? Meyasa Hajia baku so ana..."

"Na ce ka fita." Ta fad'a da k'arfin gaske, juyawa yayi jiki a sanyaye ya fita yana tunanin meke faruwa, fitowa yayi k'ofar gidan da tunanin shiga motarshi daya bari anan, Junaid ya had'u da shi zai shigo hakan yasa ya tsaya ya fito suka gaisa, Jibril ne yace "Na ga yau sai wani farin ciki kake mutumina, ko dai Maryama ta amince ne?"

Wani murmushin ya sake yi yace "Bata amince ba, amma dai na gano hanyar da zanbi nasa ta amince."

"Wace hanya kenan?" Ya tambaya da zumud'i, da murmushin gefen labb'a yace " *Zan je garinsu, sannan na shirya tsakaninta da mahaifiyarta da sauran danginta."*

Da fara'a Jibril yace "Eh to kuma fa ka zo da dubara, kana shirya tsakaninsu zaka ga ta amince kosu su amince da kai."

Kallonshi yayi yace "Amma dai zaku rakani ko?"

Zaro ido yayi yace " Ni da wa?"

Hararanshi yayi yace "Kai da zaratan 'yan uwa na mana."

"Har da Ammar?" Cewar Jibril, ba wasa yace "Har da shi mana, ai watak'ila ma ya mana anfani fiye da kai, dan in mukayi sa'a muka had'u da wani tsagera a cikin dangin mai taurin kai shi zai mana maganinshi."

Juyawa Jibril yayi zai nufi motarshi yana fad'in "Shikenan to sai kuje babu ni."

Da sauri ya rik'o shi yana dariya yace "Kai haba daga wasa, kai fa zaka nuna mana hanyar ma tunda ai kasan hanyar *Gouré*."

Cak ya tsaya ya juyo yana kallon Junaid, Goure, wannan yarinyar? Tana nan har yanzu? A ina take? Ina zanje na sameta? Rik'e hannun Junaid yayi yace "Da gaske kake? Yaushe zamu tafi?"

"Eh to, ni ko gobe ma zan iya tafiya, amma ka bari mu fara jin ta bakin su Ammar da Amar."

Hannunshi ya kama zuwa cikin gidan yana fad'in

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login