Showing 315001 words to 318000 words out of 325849 words
da wanda ya bayar da shawara aka k'irk'iri dokar, da wanda yayi rubutun dokar, da wanda yana nan aka aza dokar kai har da wanda ya aza dokar ma duk sai..."
Da sauri Ummy ta rufe mishi baki tana fad'in "Rufa mana asiri karka k'arasa fad'a, iyayenka ma zasu iya shiga ciki."
Jinjina kai yayi irin haba d'in nan, d'auke hannunta tayi ta mishi kallon fahimta tace "Ammar ka yarda ni mahaifiyarka ce?"
Jinjina kai yayi yace "Na yarda mana Ummy."
Kai tsaye ta d'ora da "Kuma ka yarda ina da girma da matsayin da zan iya sa ka ko hana ka?"
"Tabbas Ummy, kin isa har ma kin wuce."
Jinjina kai tayi alamar gamsuwa tace "In dai hakane to ina so maganar nan ta wuce, wucewa ta har abada Ammar, ka bawa al'amarin nan baya ka fuskanci rayuwarka ta gaba, 'ya'yanka da matarka ka rumgumesu ka watsar da duk wani shirme, idan har ka yarda zaka daina to ina so ka min alk'awarin da zai sani gamsuwa."
Da sauri ya rik'o hannunta yace "Wallahi Ummy na miki alk'awari har abada babu ni babu sake fad'a da wani ko tashin hankali, hasalima Ummy ko zagi ba zaki sake ji daga bakina ba, insha Allahu Ummy na miki wannan alk'awarin."
Da tsantsar farin ciki tace "Nagode sosai d'an albarka, Allah ya saka da alkairi, Allah ya maka albarka ya kareka daga sharrin masharranta."
Shima da jin dad'in addua'r ya amsa da "Ameen Ummy, ni ma nagode."
Mik'ewa tayi tana rik'e da hannunshi tace "Tashi kuje Allah ya tsare, Allah kad'e fitina a tsakaninku."
Haka suka fito suka tattara yaransu suka fita, ana yan koke koke da yan shak'e shak'e haka dai suka bar gidan da yammar nan kamar wanda aka kora.
Yanda Hamna taji ana fad'in gidan ga wanda suka je saida taje ta ga ba haka bane suna k'wauran fassarashi, ba k'arya fa Ammar yayi gini na kece raini na shiga tsara, babu ce kawai babu a cikin gidan amma hatta kayan d'aki saida ya mata sabi ya zuba, har kayan jiki kallonta kawai yake sanda take kwaso kayan jikinsu, bai hanata bane saboda tunanin tana buk'atarsu ne, amma shi babu abinda baiyi ba har yaran ma ya musu sabin kaya.
Savon gida sabuwar rayuwar ga sabon k'aramin ciki da take dashi had'e da sabbin mutane, nan suka fara rayuwarsu ta d'aukar bakin duniya da sababi, babu abinda ya rage na zamansu sai ma sababin salon shiririta da suka fito dasu.
Idan yaran na gidan kad'ai suke d'an d'aga k'afa suna rage wani abu, amma idan suka fita sai su koma yara sai abinda suka ga dama sukeyi babu mai k'wabarsu.
*Wata shida*
Yau ma ya gama shiryawa zai fita yara sun kwana wajen Ummy saboda weekend ne, tana zaune ta d'ora farantin kankana kan tulelen cikinta tana sha, ko kulata baiyi ba ya d'auki hanyar fita, baki bud'e ta kalleshi da mamakin yanda ya shareta zai fita tace "Toh! Su Ammar kuma ko magana babu shine zaka fita?"
Ba tare daya juyowa ba yace "Bani da lokacinki ne."
Ido ta zaro ta shiga kiciyar tashi tsaye rik'e da farantin tana fad'in "Wace yar iskar ce?"
Juyowa yayi ya kalleta, a hankali ya shiga takowa da wani irin kallo mai d'auke da salon mugunta, da sauri ta shiga ja baya ta fara zagaya kujerar tana fad'in "Allah karka matso nan Ammar, ka tsaya nan ka fad'a min wace shegiyar ce ta d'auki hankalinka har tasa kake jin baka da lokaci na."
Cikin dakiya yace "Zan zo ne nan saina fad'a miki yanda zaki fahimta."
Da sauri tace "Daga nan ma idan ka fad'a zan ji, fad'a min wacece ita?"
Da sauri ya d'ago k'afa da niyyar kamota hakan yasa ta juyawa zata zuba a guje d'aki, cikin d'aga murya yace "Hamna in kika tafi a guje da cikina ban yafe miki ba."
Da k'arfi ta juyo tana kallonshi tana ja baya da tsoron kar ya tardata, da k'arfi ya rik'o wuyan hannunta yana matsewa cikin k'eta yana fad'in "Ni na fad'a miki ina da yar iska ne a waje? Wai ke me yasa kishi ya miki yawa ne?"
Cikin zabga ihu kai kace idonta yake cirewa ta shiga fad'in "Ammar zaka karya min hannu, sake ni dan Allah sake ni, hannu na fa zai karye."
Saida ya zaunar da ita kan kujera yayi tsaye k'ik'am a kanta, ko da taga ya fara saita yatsunta tasan me zaiyi, zillewa ta fara yi tana kokawar k'watar hannunta tana fad'in "Na daina na daina, yi hak'uri ba zan sake ba, dan Allah yatsuna fa zasu karye."
Ai kuwa bai kulata ba ya shiga lank'wasa yatsunta yana tausasu suna k'ara da k'arfin tsiya ba tare da sun shirya ba ji kake k'was k'was k'wask'was, saida ya gama ya saketa ya sunkuya ya kama na k'afa, billi ta shiga yi da k'afafunta tana fad'in "Na tuba Ammar na tuna na tuba wallahi."
Saida ya gama tas ya mik'e ya gyara zaman rigarshi ya sunkuya ya sumbaci kumcinta yace "Je t'aime."
Juyawa yayi zai fita ita ma ta mik'e ta nufi d'aki, saida ta kai k'ofar d'akin shima ya kai k'ofar fitar tace "Duk yarinyar daka kalla ko ka bata hannu kuka gaisa ban yafe maka ba Ammar."
Lumshe ido yayi ya juyo kamar mai jin bacci ya kalleta, gwalo ta masa tace "Naje na fad'a ka zo mana."
Gyara tsayuwa yayi yace "Ni kuma yau in na fita sai nayi budurwa, kinsan dai ba zan zauna dake kad'ai ba haka kawai, kamar yanda nake canja abinci na haka ma ina buk'atar canja wurin hutuna, dan haka zan samo yar yarinya yar cakwai da zan iya d'auka ba tare da nayi nishi ba, ke kuma a lokacin zaki san girman da nake da shi."
Hamna da taji kamar ya soketa da mashi da sauri ta manta da wajen b'uya ne ta nufa ta fito ta nufe shi gadan gadan tana shiryin kuka tana fad'in "Ammar Ammar, zo dan Allah muyi magana, zo na baka hak'uri."
Juyawa yayi cike da jin wata isa da izza wai shima akwai wanda yake wahalarwa akan son shi ya nufi k'ofa, da sauri kamar zatayi gudu ta riskeshi yana shirin shiga gabjejiyar motarshi fara tas, rik'eshi tayi ta baya tana turo baki, juyowa yayi ya kalleta fuska a had'e yace "Ya dai malama? Sake ni sauri nake."
Ba tare data saki rigarshi ba taja ta har k'asa ta durk'usa gabanshi ba tare da jin nauyin cikinta ta marairaice tace "Ammar karka min kishiya ko ta waje ce dan Allah, ina sonka ba zan iya rabaka da kowace mace ba wallahi, dan Allah kayi hak'uri ka fad'a min duk abinda kake so da wanda baka so zan yi wallahi."
Saida yayi da gaske ya cije dariyar dake son taho mishi, kallonta yayi yana d'an basarwa yace "Kin tabbatar za kiyi komai nace miki?"
"Allah kuwa zanyi, na rantse maka."
Kamo hannunta yayi ta mik'e yana kallon fuskarta yace "Da fari ina so ki daina kirana Ammar gatsau babu sayawa, in baki manta nasha fad'a mikibana so, amma dana ga kin k'i dainawa saina zuba miki ido."
Da tsantsar gaskiyar dake tattare da ita tace "Allah daga yau ba zake sake jin baki na yace hakanen ba, *duniya ta*, nima zanyi kamar yanda yer uwata ke yi."
Ajiyar zuciya ya sauke cike da k'aunar wacce ta ambata yace "Allah ya gafarta mata."
Kamar za tayi kuka ita ma tace "Ameen."
Kallonshi tayi tace "To sai me kuma?"
Kallon fuskarta yayi yace "Ko daina min rashin kunya, bana son ina cutar dake."
A marairaice tace "Shi ma na daina."
Murmushi yayi ya shafi fuskarta yace "To shikenan babu ke babu kishiya ko ta cikin gida ce barz ta waje, yanzu kije ki huta abinki kafin na dawo na tayaki hira."
A sangarce tace "Ka kula min da kanka."
"Ke ma ki kula min da kanki." Ya fad'a yana shiga motar, ta cikin gilashi ya bita da kallo har ta shige kafin ya tayar mai gadi ya bud'e masa k'ofa ya fita. Dariya kawai yake shi kad'ai Hamna ce durk'ushe a gabanshi, yana sonta kuma ya yarda ita ma tana son shi, yana jin dad'in zamantakewarsu kuma yana alfahari da hakan, sau da dama sukanyi fad'a har ta kai basa kula juna, amma ko awa basa yi suke shirya kansu cikin sauk'i, wani lokacin ma daga inda aka samu sab'anin ake d'inkewa ya shiga wainata yana rawa da ita ko ya goye har su shirya, hakan ne yasa zaman nasu dad'i da fahimtar juna.
*Kamar* tsautsayi kam akan hanyarshi sai ga d'aya daga cikin mutanen da har yau idan ya tunasu sai yaji kamar yayi kuka, kaf tsawon rayuwarshi babu wanda suka tab'a wulak'antashi sama dasu, ba'a tab'a mishi cin zarafin da suka mishi ba, ba'a tab'a mishi abinda bai rama ba, amma su sun sha daga kalaman mahaifiyarshi, alk'awarin daya mata ya tseratar dasu daga d'aukar fansar shi.
Amma kuma yanzu ga d'aya a cikin jami'an da suka dinga hantararshi da hana shi abincinshi, yana gaba akan mota yana birka gudu sosai da hular kwanon da ba mai rufe kai ba duka, d'an lumshe ido yayi tare da bud'ewa yace "Ummy ki gafarce ni, wallahi zuciyata tsayawa za tayi idan ban d'an tokareshi ba."
Yana fad'a ya jawo belt d'inshi ya mak'ala sai kawai ya k'ara gudun motar, saida ya daidaici tayar moton kawai ya zungureshi, sai kawai ji akayi gijim ya wuntsile ya fad'i kan moton, da sauri ya taka birki haka mutane dayawa ma duk aka zagaye shi ganin soja ne fan a cikin tenue yake.
Da sauri ya fito daga motar yana rΓ©action irin abun a bazata ne ya zo, ko da ya k'araso wajenshi suka had'a ido sai yace "Yallab'ai, kai ne ashe? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, na shiga uku yau, sannu yallab'ai dan Allah kayi hak'uri, wallahi..."
Bai barshi ya k'arasa ba dan shi kanshi ko da ya ganshi a ranshi ma yace ai dole ya hak'ura, mik'ewa yayi cike da dauriya yana fad'in "Kai haba ba komai Elaji, tsautsayi idan ya wuni baya kwana ai."
Hannunshi ya damuk'o ya rik'e sosai yana fad'in "Wallahi hakane, kawai wata waya ce aka min da nake da tabbacin ba lafiya ba, kasan ai ita yar gwamnan naku nake aure, to ita ce na baro gida da tsohon ciki, shiyasa hankali na baya kwanciya idan na fito."
Murmushin dole ya mishi yace "Ah to Allah yasa alkairi, Allah ya raba lafiya, ba komai kaje kawai."
Da sauri yace "A'a ka bari na aje ka asibiti ko?"
Shima da sauri yace "A'a wallahi ka barshi, ai banji ciwo ba."
Mik'ewa yayi ya mishi sallama ya juyo zai koma mota, murmushi yayi murya k'asa k'asa yace "Da ubanka ne zai kaika asibitin, daka yarda ka shigo mota ta da nufin na kaika asibiti da sai dai a wuce da kai morgue daga nan, kad'an ma ka gani wallahi Ummy ta cece ku."
Bayan ya dawo daga inda yaje gida ya wuce, yara na ganinshi suka ce ai sai dai ya koma dasu, da k'yar ya lallab'asu suka rabu, saida ya keb'e da Ummy yace "Ummy dan Allah ki yafe min duk laifin da kika san na miki, kina sane ko rashin sani."
Da murmushi a fuskarta tace "Ba komai Ammar, na.
yafe maka duniya da lahira."
"Nagode Ummy." Ya fad'a yana musu sallama ya bar gidan, saida yaje ya samu Hamna ya shiga fad'a mata abinda ya faru dalla dalla sala sala, ita dai tayi dariya kamar cikinta zai fashe, daga bisani kuma ta raka shi addu'a.
*Rayuwa kenan*, abun kamar jiya ne aka fara sai gashi yanzu da aurensu *shekara uku* kenan, yanzun ma namiji ta haifa wanda ya ci sunan *Hassan* suke mishi alkunya da *Elhaj*, Ammar ya tayar da billi shi fa yan uku yake so ya haifa, Hamna kuma dake k'ok'arin cika alk'awarinta duk in yana tijara yanzu sai dai tayi gum da baki tana saurarenshi, in yayi ya gaji sai ya koma ya fara juye mata yana kiran ta raina shi ta d'aukeshi mahaukaci ne, duk da haka bata kula shi sai dai ta bar mishi wajen har sai ya gaji dan kanshi.
*Yau* hankalin Jibril in yayi dubu ya tashi, yarinyar da yake saka mata ido, yarinyar da duk inda zata je tare da dreba take, amma aka wayi gari da sunan taje Γ©cole kawai ya had'e da ita a wani babban store tare da k'awayenta da kayan makarantarsu alamar daga can suka wuce, hakan na nufin tana fita daga makarantar kenan? Ya so mata dukan mutuwa sannan yaji daga ina suke kuma ina zasu je, amma Jamila ta shiga tsakani tace ba za ayi haka da ita ba, tunda tace abu suka je siya kuma su koma kawai ya hak'ura, amma tsoron kar wani ya mishi kutse a rayuwar yarinyarshi da kuma kiyaye maimaituwar tarihi sai kawai ya yanke wani tsatsauran hukunci a kanta.
*Sadiq* zaman d'a yake ga Husseina, ya yarda da yaron yana d'aya daga cikin masu kula mishi da mangazarshi da ake aje kaya, ganin tunda yan uwa ne kawai yasa shi cewa in yana sonta ya bashi aurenta, yaro ya ga banza ta ina zai bijire? Sai kawai yace yana so shima ya amince, kamar wasa sai manya suka shiga maganar akayi komai a gaggauce, inda yace zata kammala karatunta a gidan mijinta.
*Alhamdulillah*
04/11/2020 Γ 14:40 - Ummulkhairi: π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨
*BADAK'ALA*
π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨π©ββ€οΈβπ¨
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
π¨βπ©βπ§βπ¦ _*AHALI NA*_π¨βπ©βπ§βπ¦
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
_78_
*Zo* ka ga uban amarya uban d'aurin aure Ammar, shi Jibril ya bawa d'aurin auren wanda hakan ya masa dad'i, Mari tayi jarabar a kai mata Huda ayi biki ranar bikin sai a dawo da ita, amma Jibril sam ya gama fita harkar Mari yace ai kawai ta zo in tana so amma babu inda Huda zata je, har Amar saida ta ma magana a waya wai ya lallab'ashi, amma shima hak'uri ya bata yace Jibril bai amince ba.
*Yau* d'aurin auren Huda, Ammar ya kashe d'aurin hula ya k'ayatu cikin babban riga ta wani gallelen boyel bleue bics, ya gama had'uwa da tsaruwa fiye da ma angon.
Hamna ma ta gama shiryawa cikin shaddarta gezna colour bleue omo zasu tafi tare, tsaye suke dukansu gaban madubi yana ci gaba da gyara zaman hularsa, ita ma kallabi ta gama d'auri ta d'auki turare zata fesa ya fige yace "Turaren me kike buk'ata?"
Kallonshi tayi tace "Cikin mutane fa zan shiga."
Shareta kawai yayi ya aje kwalbar ya d'auki na shi turaren zai fesa, da sauri ita ma ta fige tana ja baya da gudu tana fad'in "Tunda ban saka ba wallahi kai ma ba zaka saka ba, duk mu tafi haka."
Juyawa yayi ya kalleta yace "Hamna kawo min turaren nan."
Hanyar fita tayi tana fad'in "Ba zan bayar ba Allah."
Ko da ta fita d'akinshi ta nufa da niyyar shiga ta rufe ta d'auke turarukan dake nan, dan tasan su zai nema duk da dai yafi aikida wanda ke d'akinta, amma kafin ta rufe ya biyota yana tattare babbar rigar yana fad'in "Ke in rashin mutumcin kike ji saina kwab'e wallahi mu daku yanzu nan."
Baya tayi tana fad'in "Me yayi zafi da zamu daku ni da kai? Turare dai ne ba zaka saka ba kai ma in dai ban saka ba."
Ko da taga ya tafi a guje zai kamota saita tsorata kawai ta buga kwalbar k'asa ta kuwa fashe saboda akan tiles ne babu carpet wurin, bud'e baki yayi da ido yana kallon kwalbar.
Saida ya b'ata rai ya kalleta yace "Hamna ni kika fasawa turare? Ni Hamna, ai ko zaki ga rashin mutumci a gidan nan."
K'uri ta masa da ido tana so tace ba dagangan tayi ba amma ta kasa, cire babbar rigar yayi ya aje kan gado ya tunkareta, ihu kawai ta saki dan ba zata iya guduwa ba kan hanyar fitar yake tsaye, saida ya tak'ark'are yasa k'arfi ya kimkimeta gaba d'aya, bai tsaya komai ba ya shiga wani irin juyin bala'i da ita yana hajijiya, tun tana ganin d'akin tana gane komai, har saida jiri ya d'ebeta ta dinga ganin d'akin na juyawa gaba d'aya.
A hankali taji kamar kanta zai cire duk tunani da lissafinta sun fara barin kwanyar kanta, rik'eshi tayi gam ta rintse ido tana jiran ranar da zai sauke ta, saida ya gamsu cewa ta kuru yanzu kad'ai ya direta k'asa, ganin wani luuuuu da tayi kamar zata kifa yasa shi b'anb'are hannayenta data rik'eshi gam, ai tuni d'aurin d'an kwalin ya rigata kaiwa k'asa duk suka watse a wurin, dafe k'asa tayi sosai saboda har yanzu juyawa ake da ita.
Rigarshi ya saka ya kalleta yace "Idan ki kayi wasa Hamna d'aurin auren nan da za ayi har da nawa za'a d'aura, kuma ke nake jira karki b'ata min lokaci."
Saida ya kai k'ofa zai fita ya juyo yace "Amma Hamna Allah ya saka min wannan wulak'ancin da kika min, yanzu waccen turaren kike sona saka mai warin yan wuta?"
Hamna da a lokacin kad'ai ta fara jin dama dama kallonshi tayi tace "Kenan kasan k'amshin yan wutan?"
Saida ya wani had'e fuska yace "Ina d'an ji kad'an kad'an."
Mik'ewa tayi tana ganin yana juya mata a hankali tace "A jikinka kake ji ko?"
πππ
Da sauri ya dawo d'akin yana fad'in "Fito kai tsaye kice d'an wuta ne ni mana."
Hannayenta ta d'aga tana tare shi dan ba zata iya gudun ba tana fad'in "Ni fa tambayarka ne nayi a jikinka kake ji ko a jikin wani."
Juyawa yayi zai fita yana fad'in "Kinyi sa'a yau nake aurar da 'ya wallahi, da sai na miki cikin yan uku."
K'eyarshi ta ma gwalo tana fad'in "To inba d'an wutar ba wannan jirin daka d'iba dani kamar wacce ta hau jirgin sama."
Tafiya suke a hanya tana d'aura d'an kwali, cike da nishad'i yake