Showing 243001 words to 246000 words out of 325849 words
gajiya, Amna da duk bata jin dad'i ne take k'ok'arin gyara zamanta amma Ameera ta hana ta damar haka, cikin saurin hawan da bata san ko na meye ba ta d'an tureta tana fad'in "Dan Allah Ameera ki matsa min na huta, haba ke kenan sai lak'uwa."
Kallonta Ammar yayi ya kamo hannunta yana fad'in "Ke taho nan kinji, rabu da uwarki ta ji da d'an k'anninku wanda ke neman koya mata masifa."
Kallon kallo dai kawai akayi amma babu wanda yace wani abu, sai Amna cikin tausa murya tace "Wane k'aninsu kuma?"
Murmushi ya mata yace "Na cikinki mana da zai iya kai tsawon wata biyu zuwa d'aya da rabi."
Shiru kawai tayi ita ma sai tunanin maganarsa data fara, suna haka Junaid ya shigo da sallama da kuma fara'a a fuskarshi, gaisawa sukayi kafin ya matsa kusan Hajia, yanda yake sunne kai yasa ta kalleshi tace "Ya dai malam?"
Cike da kunya da fargaban abinda zai faru yace "Hajia dama na zo muyi magana ne."
"Akan me?" Ta fad'a ba annashuwa a tare da ita, saida ya d'an k'ara sauta muryarsa yace "Akan Salma ne."
Ba tare data kalleshi ba tace "Wace Salma fa?"
"Salma ta tonton Sani."
Da k'arfi ta juyo kanta ta kalleshi, cikin tsananin mamaki tace "Me kuma ya had'aka da ita? Meya faru?"
Sunkuyar da kai yayi kafin yace "Hajia dama ni da ita muna soyayya ne, shine yanzu na..."
"Ka me?" Yanda tayi magana da k'arfi tare da mik'ewa yasa kowa kallonta, saida ta gyara tsayuwarta tana fuskantarshi tace "...
*Alhamdulillah*
14/10/2020 ร 00:58 - Ummulkhairi: ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*BADAK'ALA*
๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ _*AHALI NA*_๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
๐ซโจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_๐ค
โ *[ T.M.N.A]* โ ๐๐๏ธ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
_55_
"Junaid yanzu ma wani sabon rashin mutumcin ne ka zo min dashi? Ina ce kana d'aya daga cikin wanda suka fi kowa sanin bana buk'atar doguwar mu'amula tsakanin ahalina dana Inussa (yayan Alhaji), shine yanzu zaka zo min da wata banzar magana wacce k'arshe nasan zaka ce kana son auren jikarshi ne, to ban yarda ba kaji na fad'a maka, in kuma kace kaji ka gani to zan zuba maka ido a karo na biyu."
Kallonta yayi yace "Kiyi hak'uri Hajia idan ranki ya b'ace, wannan karan a shirye nake dana miki biyayya, idan har baki amince na aureta ba zan hak'ura, dan ba zan k'ara sab'ama umarninki ba."
Cike da zak'alk'alewa tace "To ban yarda ba, kaje ka nemi wata yarinyar ba dai wannan ba."
"Shikenan Hajia." Ya fad'a yana barin falon, da kallo Ammar ya bishi har ya fita, tab'e baki yayi ya d'auki Ameera dake ta narke masa ya fice shima, ko da Amna taje ta same shi har ya shiga wanka, yana fitowa duk taga yanayinshi ya canza amma ba tace komai ba, yana shiryawa cikin k'ananan kaya ya sake d'aukar makullin mota ya zo kusa da ita ya sumbaci goshinta yace "Zan fita saina dawo."
Cikin ladabi tace "A dawo lafiya." Da k'yar ya rabu da Ameer dake son saiya tafi da shi, yana fita ya d'auki hanya bai zame ko ina ba sai gidan Alhaji Inussa, ba laifi Alhaji anja shekaru ga kuma jiki da ake fama dashi, zaune yake kan kujera ko tashi baya iya wa sai an taimaka masa, hakan ne yasa Ammar jin ba dad'i sosai akan wofantar da zumuncin da akayi, dan sai yanzu da ya zo ake fad'a masa ya kusa shekara da wannan ciwon, tambayarsu yayi ya ake zaune gida dashi haka? Sai yayan Salma *Rashid* ne yake fad'a masa cewa "Ai har Niamey aka kaishi, amma sun ci ciwon ya riga daya tab'a zuciyarshi, magunguna dai aka had'omu dasu ana ta bashi, amma nan gida ma ana had'a mishi da maganin hausa."
Kallonshi yayi yace "Ina takardun jinyar tashi?"
Juyawa yayi ya kalli amaryar Alhajin yace "Hajia ina takardun suke?"
Tashi tayi cike da manyantaka ta shiga d'aki, d'aukowa tayi ta kawo masa ta bashi, dubawa ya dinga yi kamar ba zaiyi magana ba yana nazartarsu kafin ya kalli Sani dake tsaye yace "Tonton ciwon nan na k'afarsa yana k'amari ne saboda maganin hausar da ake bashi, ciwonshi ya kai matakin da zai buk'aci zama kusa da likita, dan haka ku d'auke shi mu kaishi asibiti."
Cikin jin nauyi Sani yace "Amma Ammar ai ba ayi haka ba, daka bari su yaya *Lawali* su zo sai muji ta bakinsu."
Mik'ewa yayi tsaye yace "Dan ciwon ba'a jikinku yake ba ne zaku fad'i haka, to idan kun gama shawarar saiku same shi a asibiti na, ni zan d'auki nauyin komai da za'a mishi, amma ba zai sake kwana a gidan nan ba da ciwo."
Rashid ya kalla yace "Kama shi mu tafi."
Kama shi sukayi ya mik'e inda ya fara dogara sanda har suka fita, baya suka zaunar dashi sai Rashid dake gaba tare da Ammar, ko da suka je asibiti cikin gaggawa yake komai ya ware mishi d'aki na musamman, cikin k'warewa da salo ya fara bashi kulawar da yake buk'ata a lokacin, har magunguna saida ya canza mishi ya siyo a aljihunshi, lokacin daya kammala komai ya d'auki hanyar komawa gida dare yayi sosai, dan haka ko da yaje ya samu Amna ma har tayi bacci, bai takurata ba sai kwantawa da yayi tunani fal zuciyarshi.
Washe gari ko da ya fito daga falon Hajia Amar ya gani tsaye ya kafe wuri d'aya da ido, bin wajen yayi da kallo sai yaga Farisa ce da k'annanta zasu tafi makaranta, tab'e baki yayi ya matso kusanshi ya dafa shi yace "Matsalar zuciya ce?"
A d'an tsorace ya kalleshi sai kuma yayi murmushi yace "Kamar ya?"
Saida ya kalli k'ofar gidan yace "Da alama akwai wani abu da kake ji, ko ba haka ba?"
Matse bakinshi yayi cikin sanyin jiki yace "Kuskure ne, amma bai kamata na bari haka ta faru ba tun farko."
Gyara tsayuwa Ammar yayi yace "Kuskure kamar ya? Soyayyar taka ce kuskure ko kuma wacce kake so ce bai kamata ka so ta ba?"
Shima gyara tsayuwa yayi yace "Wacce nake so mana, kai fa kasan komai."
Girgiza kai yayi yace "A'a ban sani ba, fad'a min miye matsalar?"
Cikin nutsuwa Amar yace "Ammar kasan fa Hajia ba son doguwar mu'amula take tsakaninmu da Hajiarsu Jibril ba, sannan ina auren Umaimah wanda dukansu yan uwa ne, kaga abune da ba zai yiwu ba ai."
Wani kallo ya masa kamar na wanda baisan ciwon kansa ba kafin yace "Yanzu Amar wannan har dalili ne da zai iya sawa ka hak'ura da wacce kake so? Hajia ba tana nusar damu dasu bane saboda Allah, tana so muyi nesa dasu ne saboda izzarta da wani buri na zuciyarta, hakan haka saika haramtawa kanka abinda Allah ya hallata maka."
K'ara matsawa yayi kusanshi ya sake dafa shi yace "D'an uwa, daga ni har kai mun sani ba wai kowa ya auri wacce zuciyarsa ke so bane, umarninta ne muka bi mukayi biyayya, kada ka tauye kanka ta b'angaren abinda kake so in har ba sab'on Allah bane, idan kace zakayi haka kuma wallahi zaka wahalar da kanka ne sannan ka wujijjiga zuciyarka, idan bar Hajia tace bata yarda ba ka tambayeta dalili? Sannan ta fad'a maka hujjar k'in amincewarta."
Nunfasawa yayi ya ci gaba da cewa "Kar kayi wasa da damarka yaro, inhar kana sonta to kawai ka fad'a a gida asan abunyi."
Murmushi Amar yayi yace "Daga yanda kake magana d'an uwa kamar kai ma ka fad'a soyayyar nan ko?"
Murmushi yayi shima yace "Sosai ma, amma ni dalili na da yasa na hak'ura da soyayyata yafi naka k'arfi gaskiya."
Da mamaki yace "Kamar ya? Me yasa ka hak'ura da soyayyarka? Bansan da sarewa ba haka ma tsoro, na d'auka idan ka samu wacce kake so zaka tsaya ne wajen ganin ka same ta ko da hakan zai iya janyo yak'i."
Cikin fad'ad'a murmushi yace "Amar wasu abubuwa basa buk'atar jarumta ko rashin tsoro, kai halal d'in bata haramta maka halal d'inka ba, karin maganar hausa ne da ake cewa wai *ana barin halak ko dan kunya*, ni tawa halal d'in ta haramta mani wata halal d'in ne."
Wani kallo ya bishi dashi na son gano abinda yake nufi, shi kanshi saida ya ji bugun zuciyarshi ya k'aru da sauri sauri, cike da mamaki da tsoron abinda zai fad'a yace "Ammar, kar dai kace min kankana kake so?"
Rintse ido yayi tare da buga tagumin rashin jin dad'i, ya jima haka kafin ya bud'e ido ya kalleshi, wata iska ya furzar mai zafi tare da d'aga kafad'u yace "Amna duniyata ce, uwar 'ya'yana ce, kwanciyar hankali na ce da farin ciki na, k'aramin abu idan ya gilma ta gaban rayuwata marar dad'i gurinta nake zuwa na samu nutsuwa, ba zan iya mata butulci ba har na bari tasan abinda ke zuciyata ba, Hamna kuma ita ce burin zuciya ta, abincin ruhina sannan mafarkina, su biyun sun sani tsakiya bansan ya zanyi ba, *sune k'addarata*, na d'auka da hannu biyu har naga yanda ubangiji zaiyi dani."
Yana gama fad'a ya bar wurin, da kallo ya bishi sai yaji kamar ya zubar masa da hawaye, shima cikin k'warin gwiwa ya shiga wajen Hajia dan fad'a mata abinda ke ranshi babu b'ata lokaci, bayan sun gaisa yake sanar da ita shi fa yana son k'ara aure, cike da mamaki tace "Shalele aure kuma? Yaushe akayi auren naku da har zaka k'ara wani? Umaimar bata kwantar maka da hankali ne?"
Cikin turo baki yace "Hajia kawai ina so na k'ara auren ne, dan Allah kada ki hanani."
Girgiza kai tayi tace "Ba zan hana ka ba, amma fad'a min wace yarinya ka samu?"
"Farisa." Ya fad'a ko kallonta baiyi ba, k'ank'ance ido tayi tace "Wai me yasa ba kwa ganewa ne yaran nan? Shalele ya zaka min haka? Wace Farisa kuma yarinyar da ko jinin al'ada yanzu ne ta fara shi."
Kallonta yayi yace "Eh ita Hajia, a hakan ta min wallahi ina so."
"Kayi hak'uri shalele ka nemi wata, ba zan yarda a sanadiyarku ba na rasa ji da kaina da d'aukakata ba."
Kallonta yayi da matuk'ar mamaki, amma daya tuna abinda Ammar ya fad'a masa sai yace "Hajia d'aukakarki? Yanzu akan hakane zaki hana mu abinda zuciyarmu ke so?"
Shiru ta masa sai kawai yace "To Hajia me yasa ba kya son aure na da ita?"
"Saboda kakarta tsohuwar karuwa ce, ita kuma wannan rayuwa tana bin ahalina kamar yanda yan biyu ke bin mahaifa, a dalilin auren Farisa kana iya haihuwar yaran da zasu addabeka."
Cikin jinjina kai yace "Hakane, na gani kam, to amma Hajia taya su tanti Zeinabu suka samu Junaid ta wannan hanyar bayan kuma hakan ba d'ab'iar zuri'arki bace? Ko dai zama da Hajiar..."
Cak ya tsaya da maganarsa saboda hannun data d'aga da niyyar marinsa sai kuma ta tsaya, kallonshi tayi ido jawur kamar zatayi kuka ta nuna masa k'ofa tace "Fita, fitar min a d'aki."
Mik'ewa yayi ya kalleta yace "Kiyi hak'uri Hajia, Umaimah ba irin matar da nake so bace, ba zan iya hak'urin zama da ita ba gaskiya har bak'in cikinta ya kashe ni, ki taimaka ki yarda da aure na da Farisa."
Fita yayi ya rufe mata d'akin, zaune tayi kan gado ta fara wa kanta karatun tanutsu, wata rana fa komai zai iya fitowa in tayi wasa, to miye mafita daya wuce ta amince da buk'atarsu, take ta sawa zuciyarta ruwan sanyi ta d'auki niyyar gyarawa ko dan kar a mata dariya ma.
*Da dare* ma kowa na harkar gabanshi ya wuce d'akin Ummy data kira shi a waya tace ya zo, da sallama ya shiga ya zauna yace "Ummy gani kince na zo."
A hankalce ta kalleshi tace "Ammar, da izinin ka aje Baba Inussa a asibiti?"
Kallonta yayi yace "Ummy kafin nayi taimako saina nemi izinin wani? Kawai naga yana buk'atar kulawar asibiti ne shiyasa na d'aukeshi."
"Amma kasan hakan me zai iya janyowa kuwa? Me yasa baka tsoron abin fad'a ne?"
Nisawa yayi yace "Ummy ba haka bane, kamar yanda zamu iya bayar da komai namu ga Alhaji matsayinsa na kakanmu haka shima Alhajin, wani k'aramin abune daya faru tsakaninsu shekaru da dama, mu bamu san komai ba bai kamata mu tayasu hura wutar ba."
Cikin d'aga murya tace "Ammar, ina so ka sallameshi daga asibitin nan ka kaishi wata ko kuma ka mayar dashi gida ka ci gaba da bashi kulawar, amma zamanshi a asibiti zai janyo maka matsala da ma ni kaina, ni kuma wallahi ba zan yarda ka k'ara ja min banzayen matsaloli ba ina zamana lafiya."
Kallonta yayi fuskarsa a had'e yace "Kiyi hak'uri Ummy, a gaskiya ba zan iya d'aukeshi daga nan ba, bugun k'irji nayi na nuna na isa dashi shiyasa na kawo shi nan, saboda tsoron Hajia kawai ba zan lalata aikin alkairin da nayi niyya ba, Ummy ke ma ya kamata ace kin rage tsoron nan da kike mata, tsoron Hajia yana saki kina aikata kuskure a kowane numfashi na rayuwarki."
Tsuru ta masa da ido, gaskiya ne abinda ya fad'a fa, amma da yake abun ya gyauraya da jininta saita rufe ido tace "Naji ina tsoronta, kawai ina so ka d'aukeshi daga asibitin nan."
Kallon mamaki ya mata yace "Hajia Alhaji ne fa d'an uwan Alhaji na Abbanmu, ya zaki ce a masa haka?"
Cike da k'aguwa tace "To naji, idan ba zaka fitar dashi ba ka fad'awa Hajia tasan da zamanshi, kaga idan ta amince shikenan saiya zauna."
Tashi yayi tsaye ya juya mata baya yana fad'in "Hajia dai, Hajia dai, wai abun alkairi ma saika nemi umarnin Hajia, to wai ita ta busa mana rayuwar nan ne ko me?"
Mik'ewa Ummy tayi ita ma tace "Na sani dama ba zaka yi ba, ban isa na saka kayi ba saboda baka d'auke ni bakin komai ba, kaje kayi duk abinda kaga dama, amma ka sani shirme ko haukanka ba zai k'ara sani a damuwa ba, yanzu b'ace min a gani."
Kallonta yayi yace "Ummy me yasa kullum sai ki kore ni daga wajenki? Kina yawan fad'a min b'ace min da gani, me yasa?"
Cikin b'acin rai ta juya mishi baya tace "Saboda ban son ganin na ka."
K'uri ya mata da ido yana kallonta ta juya masa baya, rintse ido yayi yana sauke numfashi yana son zuciyarsa ta kwanta, bud'a ido yayi har sunyi ja sosai jijiyar kanshi duk ta fito, dunk'ule hannunshi yayi ya daki bangon wurin, juya baya yayi shima a lokacin ta juyo da sauri, yana juyowa suka had'a ido yace "Ba kya son gani na? Ni d'an halak ne Ummy kuma mai biyayya, tunda har kika fad'a da bakinki ba kya son ganina zan miki nesa da kaina ta hanyar samar miki da farin ciki, amma duk da haka duk ranar da kika buk'aci na zo gareki zan zo da saurina, saboda ke mahaifiyata ce kuma ina son ki, *ina sonki sosai* Ummy."
Fita yayi daga d'akin sai kawai Ummy ta durk'ushe ta fashe da kukan da bata san ma na miye ba. Shima yana fita bai kula kowa ba ya nufi b'angarensu, Amna na zaune cikin k'ananan kaya riga da wando sai yara dake wasarsu, cikin dakakkiyar murya yace "Ki shirya kayan yaran nan da safe zamu tafi Niamey."
Zaro ido tayi ta bishi da kallon mamaki shi kuma kai tsaye d'akin shi ya shiga, kamar hauka haka ya shiga had'a kayanshi yana turawa a akwati, jin Amna ta shigo shi kuma baya so ya zubar da hawaye gabanta ko ya sauke hushinshi akanta yasa shi saurin shigewa ban d'aki, da kallo ta bishi cikin sanyin jiki ta kalli kayan da yake ta bankawa a akwati, a hankali ta shiga gyara zaman kayan tana saitasu, tsawon lokaci kafin ya fito yana ganinta ya sunkuyar da kai yace "Bana no ki aje min kaya, kije ki had'a naki dana yaran nan, idan kuma ba zaki tafi ba ke kika sani zan d'auki yarana."
Da sauri tace "Amma yah..." Da k'arfi kamar zai tsaga d'akin yace "Amna bana son tambayar banza, kiyi abinda na fad'a miki kawai."
Shagwab'e fuska tayi ta sake takowa zata matso ya sake daka mata tsawa "Amna ki fita ki bani wuri, bansan ganin kowa a kusa dani, bana so na sauke b'acin rai na akan ki."
Da sauri ta sake takowa gabanshi tana fad'in "Na yarda ka huc..."
Wani bazawarin mari ne ya d'auke fuskarta dashi da yasa ta fad'awa kan gado da k'arfi ta kifa gaba d'aya, rintse ido yayi dan har cikin ranshi yaji marin, cikin hushi da fad'a yace "Na fad'a miki kiyi nesa dani, wai ke ba kya fahimta ne? Ki dinga yin nesa dani kamar yanda kowa keyi mana, yanzu gashi kinsa na mareki a banza."
Juya baya yayi da k'arfi yana dafe kanshi, cikin rawar jiki na bala'in marin data sha tana karkarwa ta mik'e, cike da k'arfin hali ta rik'o hannunshi ta juyo dashi gabanta, suna had'a ido ta fashe da kuka tana shafa kanshi ta ko ina tana fad'in "Dan Allah yah Ammar ka daina, tsorata ni kake idan kayi irin hushin, bana so ka daina kaji, na yarda ka huce a kaina amma karka cutar da kanka ko wani, dan Allah kaji."
Tsakiyar idonta yake kallo sai yaji hawaye na fitowa a idonshi, cakumarta yayi da k'arfi ya matse yace "Me yasa Amna? Me yasa Amna?"
Kuka kawai take har da ajiyar zuciya, jawota yayi jikinshi sosai ya rumgumeta, tun yana yi a hankali har ya fara saka k'arfi yana matseta sosai kamar zai mayar da ita ciki, duk da tana jin zafi amma haka ta daure, sun jima haka kafin ya d'ago ba alamar annuri ya saketa ya juya zai bar d'akin, da sauri ta rik'o hannunshi tace "Ina kuma zaka je?"
A hassale yace "Yaro ne ni Amna da sai kin tambaye ni inda zanje?"
Girgiza masa kai tayi tace "A'a, amma ba zan barka ka fita a halin nan ba yah Ammar, idan ka fita ranka a b'ace zaka