Showing 258001 words to 261000 words out of 325849 words

Chapter 87 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

597

Middle Ads

yayi bajinta sosai. Matashi ne dake da jini a jika da ji da dala, nan fa, matarshi d'aya da yara biyu, nan aka fara shirye shiryen bikin Hamna su Amie aka fara shiga da fita, sai lokacin take tambayar Hamna me ke tsakaninsu da Ammar? Saboda taga sun had'u shi zai fita su zasu shigo ko kallonsu baiyi ba, data fad'a mata abinda ya faru sai ita kanta taji ta samu damar da zatayi aure, dan dole ta shigar da kanta wajenshi, ta mayar da wasa gaskiya ta zama mallakinshi, fad'ansu da Hamna kuma nasara ce wurinta, dan hakan na nuna Hamna ba zata shiga abinda ya shafeki ba, ma'ana ba zaisan komai a kanta ba, tunda k'awayence ne ake abisa taka dokar mutumtaka, Hamna tasan Amie sarai tasan rikakkiyar karuwar alhazan birni ce, amma duk da haka tana tare da ita, wanda hakan ma ya taka rawa sosai wajen goga mata pantin da ake mata kallon mutuniyar banza ita kanta.

An fito da anko kala har hud'u, sun shirya sun had'u da abokan ango sun fad'a musu abubuwan buk'atarsu, sun d'auki wanda hankali zai d'auka sun aje musu sauran, shirye shirye sunyi nisa sosai, amma har yanzu Hamna bata jin farin cikin da wannan aure, tana yin komai babu kuzari a ciki ko alamar so, idan suna hira da Habib wani lokacin Ammar ya kan shigo gidan, a matsayinsa na musulmi kuma wanda ya ga mutane yana sallama ya kuma bawa Habib hannu su gaisa, amma bai tab'a yarda idonshi da nata sun had'u ba sai dai ya fice, haka zata bishi da kallo har ya b'ace ma ganinta, haka ita dai take sukuku sai lokaci kuma dake k'aratowa.

*Har* bacci ya fara gaba dashi Amna ta tashe shi kan ya manta bai siyo madaran daya yara sabonta ba, kowa zai iya bacci bai sha ba amma banda *Ameera*, saida ya lumshe ido yace "Ke dai kina jin bak'in cikin kiga na kwanta baccin alhalin ke ma baki kwanta ba ko?"

Dariya tayi tace "Ta ya ba zan so ganinka kana hutawa ba? Ai farin ciki na ne."

K'ok'arin saukowa daga kan gadon yayi yana fad'in "K'arya kike, ai da sai ki tuna min tun kafin na shigo gidan."

A hankali tace "Wallahi na manta ne gaba d'aya, kuma naga tun kafin ta ida kake kawo wata."

Cikin sumalin bacci yace "Bansan ya akayi bane na manta wallahi, yanzu kuma zata hana kowa bacci a gidan nan in babu ita."

Da kallo ta bishi har ya canza kaya zuwa k'anana ya d'auki makulli yana fad'in "Allah yasa a samu a kusa."

Suna fitowa a falo ta samu Ameera kwance yanda ta barta tana ta latsa remonte tana canza tasha, kusanta ya matsa ya sunkuya yace "Gimbiya Ameera, yarinyar mamanta da babanta, yarinya yar baiwa mai sa'a, shalelen Ummy da Abba, zaki sha bonbon (alawa)?"

Kai ta girgiza mishi tare da cunno baki gaba cikin muryarta ta yara tace "A'a ni madaya na ke co."

D'agowa yayi ya kalli Amna yace "Duk yanda akayi ke kika sa mata akai ta daina yarda duk wayon da za'a mata."

Dariya tayi tace "Banda abun uban yan biyu waye zai shiga tsakaninka da yaranka?"

Ameera ya kalla yace "Muje to ki raka ni na siyo ko."

Tsil ta diro daga kujerar tana jujjuyawa inda zata ga takalminta, tana ganinsu ta d'auka tasa ta rik'e hannunshi, saida ta juyo ta ma Amna bye bye tace "Ummy sai mun dawo."

"A dawo lafiya." Ta fad'a tana zama, kallonta yayi yace "Me kike so na taho miki dashi?"

D'an d'aga ido tayi alamar zatayi tunani yace "Zaki sha ayaba?"

Kallonshi tayi saita yamutsa fuska tace "Bana jin dad'inta yanzu."

Tsayawa yayi yana mata wani shu'umin kallo yace "Tunda kika samu tawa ko?"

Bushewa tayi da dariya tare da rufe fuskarta da hannu d'aya tana fad'in "Ba haka bane."

Hararanta yayi yace "Ba haka bane kamar ya? Kin samu lafiyayya kina ta moreta tana zazzaga miki yara bigu biyu biyu dole ki ce wannan ta fita a ranki, to kiji da kyau ita wannan d'in da kika raina sanfirin aubangiji ce."

Tsayar da dariyarta tayi tace "To ai ita ma waccen d'in hakane."

Juyawa yayi yana fad'in "Tunda kince haka bari na dawo yau zan sake baki ajiyar wasu yaran, amma wannan karan uku zan ajiye."

Murmushi kawai tayi ta bisu da kallo, wannan magana kamar ya fad'a ne daidai amsawar mala'ikun rahama, a ranar ta gama al'adarta ta kimtsa kanta dan farin cikin mijinta, dama magani ne Ummy ke d'orata akai wanda shi tafi so, a ranar ma tasha zuciyarta babu tunanin komai, amma da yake akwai tsananin rabo sai gashi duk da babu tabbacin a wannan dare ya shiga amma daga lissafi za'a gane a wannan lokacin ne.

Sanda ta fara jin alamu ta d'auka ucler d'inta ce kawai ta zo mata da sabon salo, amma sai abun ya fara damunta ganin tana shan maganinta kuma a banza, saida taji bata son warin gas d'in da take aiki dashi ta fara tunanin ciki ne da ita, da sauri ta d'auki tsinken gwaji ta ma kanta, ai kuwa dai ta tabbata abinda take tunani, zaune tayi kan gado jiki a sanyaye ta dafe kai da hannaye biyu, k'walla taji sun cika mata ido tana shirin yin kuka, shigowarshi tasa ta zabura tana goge hawayen, b'oye tsinken tayi a hannunta tana kallonshi, shi ma wani tuhumammen kallo yake mata har ya tsaya gabanta yace "Lafiya?"

Kai ta girgiza masa kawai tana shirin fita daga d'akin, rik'ota yayi yana kallon fuskarta yace "Fad'a min me ya faru?"

Fuskarshi ta kalla sai kawai ta fashe da kuka ta fad'a jikinshi, cikin tashin hankali yace "Ke Amna lafiya? Me ya faru ne wai? Me aka miki? Ni ne na tab'a ki?"

Share hawayen ta fara yi hakan yasa shi tallabo fuskarta yana fad'in "Kiyi hak'uri idan nine na b'ata miki rai kinji, ban sani ba wallahi."

Girgiza kai tayi alamar a'a, had'e girar sama da k'asa yayi yace "To me ye kike ma kuka?"

A hankali ta nuna masa hannunta ta bud'eshi daga dunk'ulewar data masa, hannu yasa ya d'auki tsinken ya duba sai kawai ya kalleta yana murmushi yace "Kice min har na cika aiki?"

Cike da damuwa tace "Yah Ammar bana so? Ciki ne fa?"

Da mamaki yace "Ba kya so Amna? Cikin na wa?"

Marairaicewa tayi tace "Yah Ammar ka fahimta mana, duka fa aurenmu har yanzu bamuyi shekara hud'u ba."

Ba alamar wasa yace "Sai akayi me?"

Turo baki tayi tana d'an juyawa tana fad'in "Ni gaskiya bana so, haba kamar wata kaza."

A hankali ya juyo da ita gabanshi yana kallon idonta yace "Shin ni ne kike so ki kira zakara a fakaice ko me? Amna miye na damuwa dan kin haihu sau uku a cikin shekaru hud'u? Haihuwar ince ba Allah bane ke bayarwa ba?"

Kamar za tayi kuka ta kalleshi tace "Eh hakane yah Ammar, amma kuma ai ana so a d'an huta, ka dubi su Alhaji fa ba suyi wayo ba har yanzu.

Saida ya gyara tsayuwa yace "Amna ince dai ni na miki cikin?"

D'aga kai tayi alamar eh, d'orawa yayi da "Kuma ni zaki haifa ma yaran ko?"

Nan ma kai ta d'aga sannan yace "To indai nine uban ina son kayana, ko duk wata ne ki bultso min su zan karb'a, duk wanda kika ga ya miki kallon rashin mutumci kallon daya nuna ana mamakin haihuwarki, to ki kalli k'wayar idon mace ki fad'a mata duk macen da mijinta ke sonta ita ke rirritsa."

*To fa kunji wanda basa son haihuwa*

Cire kayan jikinsa ya fara yi zai shiga wanka yana fad'in "Ke ba ma dan baki da hankali ba sakarya ce ke, to miye na ki na damuwa ke da bake kika ma kanki cikin ba, ba saida na tab'a ki ba sannan kika yi cikin, wacce miji bai damu da ita ba zai tab'ata ne, yanzu fa da a shekara hud'un nan bamu samu haihuwa bane saiya zama tashin hankali har ana nuna mu da baki, a'a ka na daddage nayi cikin shima sai an min uya shege da buru-uba, to naje nayi d'in kiyi abinda za kiyi idan kin isa."

Ban d'akin ya shiga tana ganin haka ta fito daga d'akin bata zame ko ina ba sai b'angaren Hajia, dan in ta zauna ya fito ma d'orawa zaiyi har jarabar ta motsa ya tattausheta a banza, dan yanzu ya fad'a mata ba duka ba zagi amma taji a jikinta, ita kuma a yanda Allah ya halliceta har tafi son dukan ma kan irin wawurar daya mata wani lokaci wacce ta kwana tana amai ga zazzab'i, duk da dai tasan yafi ta ma damuwa da kanta indai aka ce tana da ciki ko tana shayarwa, tanan b'angaren kam sai san barka.

Ai kam dai kamar yanda tayi tunani ne, dan ko da ya fito da masifar ya fito yana fad'in "Ke ni ban ma yarda dake ba, wallahi sai kin fad'a min ni ne ba kya so ko yaran ne kike bak'in cikin haifa min, in kuma raino da shayarwa ne baki iyawa fad'a min na ji."

Shirun da yaji yasa ya d'auka ko tana falo, haka ya fito da towel d'in niyyar shi in tayi wasa ta sha matsa, amma sai bai same ta ba, murmushi yayi ya jinjina kai yace "Wato ta bar min gidan ma gaba d'aya ko, ga dodo wanda baisan ciwon kansa ba, ga mahaukaci idan nayi na gaji na bari kenan."

Komawa yayi ciki yayi k'wafa yace "Zaki dawo ai zan ritsaki ne."

*Sati uku* ya rage bikin Hamna, yau kuma ta tashi da shagalin bikin k'awarta da ita ma zatayi aure, ta shirya ma bikin sosai saboda a cewarta shine fitarta na k'arshe kafin ta fara gyaran jiki, d'aya daga cikin abokan Ammar ne na gaban goshinshi zaiyi mata ta biyu, dan haka babu abinda bai shirya halarta ba shima dan saka mishi da alkairin daya mishi. Rana ta farko anyi k'umshi, ta ganshi ya ganta sanda suka je d'aukar abinci, amma kai ka rantse wasu abokan hamayya ne dan babu wanda ya nuna yasan wani ma, a daren ranar akayi kamu inda aka rak'ashe sosai, ya kalleta yafi sau cikin carbi, tana wahalar da zuciyarshi sosai, tana gigita lissafinshi, tana sage mishi duk gwiwoyinshi, yana kishinta fiye da hangen mai tunani, yana jin zafin ganin tana bayyanar da abinda ya kamata ace ta mayar dashi sirrinsa shi kad'ai, sai dai babu ta yanda zai fahimtar da ita haka, baisan ta wace hanya zai bi ya nuna mata yafi kowa son ganin ta killace kanta, amma ya zaiyi da abinda yafi k'arfin wuta inji kishiyar k'onanniya, ya zuba mata ido tayi abinda take so, ko ba komai ma ai ta kusa zama ta wani, mallakin wanin shi ce ita.

Anyi bridel a rana ta biyu inda yan mata ne zalla da amarya, sai kuma rana ta uku da angaye ne suka shirya tasu didimar, ya jima da shiryawa ya fita saboda kai da kawonshi yawa gare shi, lokacin da suka zo yana k'ofar gidan da ake gwangwajewar tare da wasu abokinsu suna shigar da ruwan roba ciki, yana juyowa motarsu ta danno wajen, ta glishin motarta ya fara hangosu suna fitowa daga ciki, su hud'u babu mai k'asa da shekara ashirin da biyar a cikin, sun rik'a sun tumbatsa sai haniniya sukeπŸ™ˆ, in ba wanda yasan su ba kai kace ba girman garin musulmi bane, dogaye riguna ne duka jikinsu iri d'aya, kalar pink ce sai yar kwalliyar da aka musu a tsakiyar k'ugun rigar, sun kama su sosai a jiki sun fito da duka hallitinsu, dogayen takalmi ne k'afar kowace sai k'ananan poshet a hannayensu, biyu daga ciki haka suka zuba atach d'in babu kitso babu d'an kwali, Amie kuma kitso ne na atach mai kamar na roba, sai Hamna dake da korde a kanta kitson yayi kyau sosai, kallabin Amie a hannunta yake ta rik'e, Hamna kuma ta d'an d'aura shi ne tsakiyar kan wanda kamar jira yake a tab'a shi ma ya b'are, dukansu sun sha uwar kwalliya mai d'aukar hankali. Har sun fara d'aukar hotuna ko da ta ganshi sai kawai ta shige ita ma, Amie ce ta zo kusanshi tace "Namijin duniya barka."

Juyowa yayi ya kalleta yace "Barkanki."

Yana fad'a ya wuce ciki shi ma ya barta, bin bayansu tayi suka shiga ciki, anata shagali ba kama hannun yaro, kowa na farin ciki da dariya amma banda shi, kujera ya samu ya zauna ya buga tagumi yana kallonta, rawa suke tare da k'awayen inda angayen ke musu lik'i suna jin dad'in kallonsu, jikinta ya bata yana kallonta shiyasa ma bata yarda sun had'a ido ba, shi kuma yana mamakin yanda take son zama, ke da za ayi aurenki amma gida suka bari ta fito, wannan wace irin rayuwa ce akayi a gidan nan? Tab'e baki yayi alamar ba ruwanshi matsalarsu ce.


Mutum mugun icce (ina yawan fad'in haka), duk abin alkairi sai wani ya kawo cikas, daren yau dai ko da Hamna ta dawo gida ta riski tashin hankalin da bata tab'a tsammaninshi ba, jin kunya tozarci k'ask'anci duka taji a wannan rana, sati uku ya rage aurenta amma yau an turo manya daga gidansu Habib wai an fasa, abun takaici shine wai mahaifinshi yace "...


*Alhamdulillah*
14/10/2020 Γ  00:58 - Ummulkhairi: πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
*BADAK'ALA*
πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._

*SADAUKARWA GA*

πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ _*AHALI NA*_πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦

πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_60_


Wai babanshi yace "Sai dai in bayan ranshi zai aureta, amma da ranshi dai har abada kam."

Habib fa abun bai masa dad'i ba, amma danginshi da matarshi su abun ya musu dad'i, a ranar haka aka kwana ana jajanta wannan magana kowa na fad'in albarkacin bakinshi, kowa yana son gano bakin zaren dan yaji dad'in fad'a, Amna kwana tayi tana kukan fasa auren yar uwarta, amma ita Hamna ko a jikinta dan sai taji wani sanyi ma.

*Da safe* bayan ya dawo daga d'aurin aure ya shigo falon dan gaishe da Ummy, Soueiba Zeinabu da Hassana ya samu suna hirar abinda ya faru, abun mamakin kuma kowace hasashenta take fad'i wanda ya janyo fasuwar auren nan, shigowa kawai yayi bai kulasu ba, saida ya gaisheta ya fito ya gaishe su ya fita, zai nufi b'angarenshi ya kira wayar Amar, yana d'auka yace mishi "Har yanzu kana cikin grp d'in ahalin gaga?"

"Eh." Amar ya fad'a a tak'aice, d'orawa yayi da "Ka fad'a musu akwai taro gobe a gidan margayi Alhaji Suley, idan mutum ba zai samu damar zuwa ba ya turo wanda zai iya wakiltarshi."

Da sauri Amar yace "Taro kuma? Na me?"

"Kayi abinda nace." Yana gama fad'a ya kashe wayar, kamar yanda ya fad'a haka Amar yayi, ya kira taron da babbar murya inda kowa ya amsa da zai zo, kowa tunaninshi da hasashenshi bai tab'a hasaso mishi abinda Ammar d'in ke shirin yi ba.

*K'wansu da k'wark'watarsu* haka suka taru amma banda yara, d'akin ya kaure da hira kowa na jiran yaji abinda zai masa dad'i, yasan kowa zai zo shiyasa ma yake kwance yana shan baccinshi hankali kwance, cikin abokan wasansu ne wata ta kalli Amna tace "Wai ke ina wannan d'an rainin hankalin ne? Ko kuma gadinshi zamuyi ne?"

Cikin murmushi Amna tace "To miye a ciki ma idan kunyi gadin na shi? Ai ya isa har ya batse."

Cikin uwaye ne wata tace "Ki dai taimaka ki nemo mana shi tunda ance yana ciki bai fita ba, muna da abunyi nan da kike ganinmu."

Mik'ewa tayi tace "To bari naga idan zan iya." Fita tayi tana tunanin kalar mutanen da zata samu sun hau kanshi yau idan ta tashe shi, sun dai kwanta lafiya lau, amma yanzu zata iya tashinshi ya burma mata ashar yace waya aiketa? Wani iska ta furzar data tuna ai gata zai mata idan ita kad'ai ma ya kunyatar d'in, ko da ta shiga har d'akin na shi ta wuce, yanda ta barshi haka ta same shi, a hankali ta k'arasa ta kwanta bayanshi tana shafa bayanshi, ta jima haka kafin tasa harshenta cikin kunnenta tana karkad'ashi, a hankali ya fara motsa kanshi tare da mimmik'e k'afafunshi, juyowa yayi idonshi rufe ya k'ara matseta jikinshi, ganin abinda take mishi yana ratsa shi sosai yasa ta cire harshenta ta kalli fuskarshi tana murmushi tace "Barka da safiya."

Kallonta yayi ya k'ara matsota kusa dashi ya fara sinsinar wuyanta yana shafa bayanta har ya zura hannunshi cikin rigarta, a hankali taji ya fara b'alle bras yana son kaiwa wani wurin, rik'e hannunshi tayi ta kalleshi tace "Duniyata bak'inka fa sun iso tun tuni kai kad'ai suke jira."

Lumshe ido yayi ya jawo kanta ya rad'a mata a kunne cewa "Je envie de toi chΓ©rie."

Kallonshi tayi tana dariya tace "Daga tashinka daga bacci?"

Turo baki yayi yace "Ce toi qui ma attaquΓ©."

Murmushi tayi tace "Ok, yanzu ka tashi ka shirya sai mu tafi."

Ajiyar zuciya ya sauke ya tashi zaune, sauka yayi daga kan gadon ya d'auki doguwar rigarshi fara tas ta saka, turare ya fesa kafin yaja hannunta suka fita, cikin takon isa da mulki da izza dake nuna wannan yaron na Hajia ne ya shigoπŸ˜‚, murmushi yayi ganin cikin k'ank'anin lokaci wai suka taru haka, bai gaishe da kowa ba ya tsallaka ya zauna kujerar da Hajia ke zama kasancewar bata fito ba saboda hayaniyar mutanen, kamar tasan da zuwanshi kam sai gata ta fito, kanshi tayi gadan gadan dan son zama kan kujerarta, gyara zama yayi ya shige cikin kujerar sosai ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana shafar gemunshi da hannu, ko da Hajia taga haka kawai tayi shataletale ta zauna kusa da su Hassana da Husseina, dan tasan in tace ya tashi zai fad'i wani abu ne da zaisa a mata dariya, kowa kallonshi yake cikin rashin mutumci

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login