Showing 210001 words to 213000 words out of 325849 words

Chapter 71 - BADAKALA

Start ads

20 Aug 2025

497

Middle Ads

_46_


"Zo zauna nan."

Saida ta k'ara yin kalar shagwab'a sosai kafin ta fara takowa a hankali tana nufoshi, k'ank'ance idonshi yayi yana mamakin k'arfin halinta, tasan fa idan ta zo me zai mata, tasan saiya mintsineta ko ya mata wata muguntar, amma duk da haka ta taho kuma a madadin ta koma ko ta nemi wajen b'uya, baisan lokacin da murmushi ya sub'uce masa ba, tabbas k'arfin hali da jarumtarta sun birge shi, ta nuna mishi zata iya hak'uri da shi duk abinda zai mata, kafin ta k'araso sai kawai ya ji babu buk'atar ya mata abinda yayi niyyar yi. Cike da tsoron nan ta zauna akan cinyarshi ta rufe fuskarta ko da ya kan iya kawo mata mari ko ja mata hanci ya matse shi, a hankali ya janye hannayenta yace "Kalleni mana, tsoro kike ji?"

Girgiza kai tayi ba tare data bud'e ba, yana kallonta shima yace "To in dai hakane kalleni."

Bud'ewa tayi ta kalli fuskarshi amma ba cikin idonshi ba, aje robar hannunshi yayi kan k'aramin teburin yana kallonta yace "Fad'a min duniyata me kike so?"

Robar hannunta ta nuna mishi tare da turo leb'enta na k'asa gaba na sama kuma ta shigar da shi ciki sosai, kallon robar yayi sannan ya kalleta yace "Amna bana son irin wannan ciye ciyen fa, da zogale ce ma tafi anfani a jiki, ki bari gobe da safe na miki alk'awarin zan samo miki zogale kinji."

Yanda tayi da fuskarta yasa shi sumbatar kumatunta dan tayi fayau da ita tayi kyau sosai, shafa kumatun yayi yace "Kiyi hak'uri kinji, ai kin yafe min ko?"

Cikin shagwab'a wai ita ga auta ta kama hannunshi dake kan fuskarta tasa babbar yatsarshi baki tana tsutsa, murmushi yayi yana d'an girgiza kai yace "Autar Tanti kenan, rigamar dai ta motsa ko? To fad'a min me zan miki da zaisa ki hak'ura."

Cike da sangarta tace "Ni kawai ka ban na ci wannan, shi nake so na ci, kuma ai ba laifina bane na beby ne."

Cikin muryar dake isar mata da sak'on kiyi hankali fa yace "Amnaaa." Da sauri tace "To kawai ka siyo min kankana."

Rugugugu! Sautin da gabanshi ya bayar kenan sanda ta ambacin sunan kankana, nisa dashi da tayi da kuma samun Amna sunyi tasiri sosai wajen mantar dashi ita, amma kuma bai kamata ace ya manta da ita ko dan abinda ya aikata mata, to amma ya zaiyi? Dole ya manta da ita tunda dai babu komai tsakaninsu, ciki ne dama yake zargin tana da kuma da akwai ciki da yanzu ya bayyana kowa yaji, dan baya tunanin Ummy zata iya yin abinda tayi yanzun, jin ta sake saka hannunshi a baki tana tsutsa yasa shi dawowa hayyacinshi, murmushin yak'e ya mata yace "To bari nayi wanka sai mu tafi tare."

D'agata yayi daga jikinshi ya nufi hanyar d'akin kwananshi, tsayawa yayi ya juyo yace "Amma ke da baki shan kankana?"

"Haka kawai nake sonta yanzu." D'akin ya nufa yana fad'in "Kinyi waya da kankanar asalin?"

Cikin d'aga murya tace "Eh, tana lafiya."

Bayan isha'i suka fita, haka kawai suka dinga yawo suna zaga gari, sun jima sosai kafin ya mata siyayyar kayan ciye ciye suka dawo gida, tana fitowa daga cikin mota ta d'an matse cikinta tace "Wash."

Kallonta yayi sanda yake fitowa yace " Ya dai?"

Duk da abune da take wayan ji amma hakan baisa ta iya fad'a masa ba sai kawai tace "Ba komai, cikina ne ya d'an juya."

Tsaye yayi har ta zagayo wurinshi ya kama hannunta yace "Ki kula fa Amna, karki ja min asara ki sani sabon aiki."

Dariya kawai tayi suka nufi b'angarensu, saida ya tabbatar ta nutsu harta kwanta sannan ya zo ya ga Abba suka tattauna kafin daga bisani sukayi sallama.

*Washe gari* da safe kusan duk familyn ne a falon kowa da wanda ya zo ya gaisar, Ammar ma suna kusa da Zeituna zaune shi da Amna, da k'yar Junaid ya matsa mata ta zo gaishe da mutanen ba dan ta so ba, shiyasa ma ko da ta shigo ko sallama ba tayi ba, tana kallo yana gaishe da kowa amma banda ita, ganin hakan yasa Ammar k'ura mata ido, ko shi dai ai yana gaishe da kowa da girmamawa, amma tsabar rashin kunya ita ba sallama kuma ba gaishe da mutane, ba fa zai d'auka ba, wannan iskancin ba za'a yi shi dashi ba. Junaid na juyowa inda yake dan su gaisa ya kula da kallon da yake mata, cikin dubara ya d'an ja gyalenta suka koma gefe, juyawa tayi zata fita Junaid ya bita da kallo, Ammar daya kula da kowa na wurin ya bita da kallo amma babu mai k'arfin halin da zaiyi magana yasa shi kallon Junaid yace "Matarka raina mutane ne tayi?"

Ido a tsaitsaye ya kalleshi fatanshi kawai su rabu lafiya, ita kuma juyowa tayi tana mishi wanni kallo tace "Kamar ya?"

Saida ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yace "Naga kamar kinfi k'arfin ki gaishe da mutane, me kike ji dashi to?"

Cike da rainin tace "Ina da wani abu d'aya a rayuwata, duk ta yanda aka zo min haka nake zuwa nima, an nuna min ba'a k'aunata a gidan nan, shiyasa nima ban nuna ina k'aunar kowa ba."

Idonta ya kalla yace "Amma ai kinsan girmama mutum ko? Sannan nan ba gidanki bane ko na mijinki, dolenki ki girmama duk wanda kika gani a ciki inhar kina da mutumci."

Murmushi ta masa ta rumgume hannaye a k'irji tace " Idan kuma bana da mutumcin fa?"

Mik'ewar da yayi tsaye yana d'an nad'e hannun rigarshi yasa Zeituna mik'ewa tana kallonshi tace "Dan Allah rabu da ita kaji, bata gajiya da rigima da kowa."

Kallon Zeituna yayi yace "Um um uwa barni, ina so ne na fad'a mata da yaren da zata fahimta, duk rigimar da take muku ai dan bata samu daidai da ita bane, ni ba ita zan tsawatar ma ba mijin nata zan dallawa mari a gabanta ta gani, hakan zaisa ta shiga taitayinta."

Kallon Junaid yayi rai a b'ace yace "Yo ba dan ma ya d'auki mutane 'yan iska ba har wacece wannan yarinyar da zata zauna tana mana fitsara, yaushe ta shigo gidan naka har ta fara baka kulawar da kake ganin ta isa ta taka iyayenka kuma ta zauna lafiya, to in kai ka zama fanko wallahi ni akan iyayena babu yar iskar data nemi ta raina min su kuma na kalleta, dan ubanta kuma ta jaraba ta gani idan ban fizgo hanjin yarinya ba ta baki, to miye a cikin ido banda ruwa."

"Da kyau Ammar, nagode, ka tabka rashin mutumcinka yau Hajia Zeeya'atu na bayanka, tunda shi gindinta ya mishi shamaki da zuciya."

Kowa saida ya kalli Hajia da tayi maganar nan, Amna sagale ta kalle ta wacce ta tsargu da abinda ya fad'a take jin kamar da ita yake tunda dai ita ce matarshi, Ammar kuma a ranshi yace "Tunda rashin mutumci ne kenan kin d'aure min gindi? To na fasa."

Maryama ce tace "To sai me? Ka mari mijina a gabana ka gani, wallahi da nima saina tsinke matarka da mari kuma a gabanka naga me zai faru."

Juyawa yayi ya kalli Amna dake zaune ya tintsire da dariya ya nuna Amna yace "Ke wannan? Jar bala'i! Wallahi kuwa da kinja yau kowa ya kwana da yunwa, ke ki bar bala'i yayi kwana kinji, bana fad'a da mace ni sai maza mazan ma wanda suka k'osa, idan kuma kika cikani sai dai nasa 'yar aljannata ta d'aukar min ke ta cilla a garu."

Cikin taushin murya Amar yace "Dan Allah d'an uwa ka rabu da ita."

Kallon Maryama yayi ita ma yace "Gaskiya baki kyauta ba, banyi tsammanin haka daga gareki ba."

Zaune Ammar yayi yana kallon Amar yana fad'in "To dama me kake tsammani? Baka ga kakan nan nata ba mai masifar fad'a kamar Hajiar gidanmu."

Amar da suke kallon juna ne ya mishi alama da ido cewa Hajiar fa na kallonka, duk da ya fahimci me yake nufi sai kawai ya gyara zamanshi ya ci uwar fuska kamar bashi ba, Husseina kad'ai ta iya fito da dariyarta amma sauran duk sun gimtse ta su, Hajia da kamar ta fashe ce tace "Shiyasa ba ma tab'a zama lafiya ni da kai, ba dai nice mai masifar fad'a ba? Zaka gani, akwai ranar da zaka nemi kaji ma fad'an nawa amma na maka nisa."

Kallonta yayi fuska a had'e yace "Haba Hajiata, raha ce fa kawai, ke kinsan dani dake bata b'acewa, fad'an ki ai ni jinshi nake kamar kukan tsintsaye matuk'ar dad'i a kunne."

Maryama dai basu ma san lokacin data fita ba tare da Junaid, yau ma fad'a sukayi sosai saboda yaji zafin abinda Ammar ya mishi, kuma yasan gaskiya ya fad'a mishi shiyasa ma bai biye mishi ba, amma fa daya mare shi da sai dai cikinsu d'aya ya kashe wani, yanzun ma k'ara fad'a mishi tayi dan sam zaman gidan nan nashi ya fice mata a rai, bata damu ta bar gidan ba tunda kowa na gidan baida mutumci a cewarta.

*Misalin 09:00* na safe Tanti Hadiza ta zo gidan, babban falon ta fara shiga cike da fargaban kalaman da zata ji daga Hajia, a lokacin tana d'akin Alhaji dan haka ta samu tarba mai kyau daga su Zeinabu da Soueiba da kuma Zeituna da bata tab'a ganinta ba ido da ido sai yau, a falon suke suna ta hira ta yaushe rabo inda suka cika mata gabanta da abun sha da ci, fitowar Hajia yasa duk wannan farin cikin ya b'ace kowa ta kama jikinta, duk da ta gane wacece amma bata wani kulata ba ta kalli Zeituna tace "Zaman me kuke anan? Ina ce aiki kuke a madafa."

"Eh Hajia." Ta fad'a tana mik'ewa ta nufi madafar, su Zeinabu ma mik'ewa sukayi inda Hadiza ke mamaki da maganar zuci cewa "Har yanzu bata canza ashe, yaushe matar nan zata daina bautar da matan 'ya'yanta? Allah ya kyauta."

Daga tsaye take k'are mata kallo sama da k'asa, murmushin gefen labb'a ta mata ta kawar da kai daga kallonta tana danna wayar hannunta tace "Wani ko a cikin kaskon mai ka saka shi haka zaka ciro shi a tsiyace, ank'i d'ana ba, amma sanyin ac da abincin gidanshi kad'ai ya isa ya gyara maka jiki."

Nufa tayi kan kujerarta ta zauna k'afa d'aya kan d'aya tace "Ina manta wani abu fa, wasu haka suke zuwa duniya a wahalce kuma su koma babu nasara."

Ita ma murmushin tayi wanda bai fito da hak'oranta ba ta mik'e tana kallonta tace "Ina kwana Hajia."

K'ala ba tace mata ba dan haka ta juya zata fita sai kuma ta kalleta tace "Ba wai zama a cikin daula bane ke nuna kayi nasarar zuwanka duniya, ni a gurina nasarar da soyayyata ma tayi ma nasara ce, wasu basa da sa'ar zama da wanda suke so, ni kuma yanzu haka ina cikin farin cikin da na tabbatar sauran matan gidan nan basa cikinshi, idan kuma k'arya na fad'a ki tambayi kowace kiji zata fad'a miki indai har gaskiya zasu fad'i."

Cikin ladabi ta sake kallonta tace "Kiyi hak'uri abisa abinda ya faru, ganin Amna na zo wacce kullum ke min k'orafin ban zo naga gidanta ba, kuma tace gidan jikin wannan yake shiyasa na lek'o mu gaisa kar nima na watsar daku kamar yanda kukayi, ko ba komai ina da 'ya'ya a gidan nan."

Fita kawai tayi ta barta, tana ganin gidan tasan shine dan haka kawai ta shiga, sallama ta dinga rafkawa har Jamila da Amna suka lek'o su da su kafi kusa, dukansu rumgumeta sukayi da farin ciki, Amna har kuka tayi na ganin mahaifiyarta, haka suka shiga ciki ta zuba mata kayan tab'awa inda suka bud'e shafin hira, a k'alla awanta uku kafin ta tashi suka shiga wajen Umaimah da Maryama suka gaisa, data fito zata tafi a lokacin Amna ke cewa "Mama ki jira yah Ammar yanzu zaki ganshi tunda na fad'a mishi kin zo, ba zaiji dad'i ba idan ya samu kin tafiyarki."

Dariya ta mata tace "To ni dashi kusan kullum ba muna had'uwa ba, kowace juma'a fa sai yaje madarunfa."

Zaro ido tayi tace "Mama kowace juma'a? Amma shine bai tab'a fad'a min ba."

Dariya tayi zatayi magana sai gashi ya shigo da makullin mota a hannu, da farin ciki da ladabi suka gaisa kafin yace "Tanti har kin fito ne? Amma ai baki jima ba."

Da murmushi tace "Haba dai ina laifi ai na jima anan, zan wuce can gida ne wajensu Inna zuwa bayan sallah la'asar kuma saina koma."

"Amma kun gaisa da mutanen ciki kuwa?" Saida tayi dariya ta kalleshi tace "Mun gaisa, harda kakarka ma."

Dariya yayi shima yace "Ashe kunsha hira." Dariya tayi kafin ta kalli Amna tace "Ki koma ciki ni zan tafi, sai kuma na sake dawowa ganinki ko auta."

Cikin shagwab'a ta kwantar da kanta a kafad'arta tace "Mama yaushe zaki dawo?"

Kallon Ammar tayi da tunanin abinda zata fad'a mata sai kawai yace "Sai kin haihu mana zata dawo."

Kunya ce tasa Amna k'ara sunkuyar da kanta tana murmushi, Tanti kuma a ranta tace "D'ana kenan, anyi halin ba ."

Ammar ne yace "Muje tanti saina ajeku." Kallonshi tayi tace "A'a haba daka barshi ma, watak'ila akwai abinda kake wannan shirmammar ta taso ka."

"Ku zo muje kawai, ai babu abinda yafi mana ku." Ya fad'a yana nufa hanyar fita, rik'eta Amna tayi sosai wai babu inda zata je, abu da gaske sai kuwa tasa kuka ita sai dai ta tafi da ita, ita ma rumgumeta tayi tana fad'in "Saurare ni auta, kina ji na da kyau?"

Kai ta d'aga alamar eh, cikin fitar da kowace kalma take fad'a mata "Kiyi hak'uri ki koma d'akinki ki zauna, na miki alk'awarin zan sake dawowa ba da jimawa ba, wannan kukan yasa dama tun farko ban zo ba, amma idan kikayi shiru yanzu to zan sake dawowa kuma na taho miki da abinda kika fi so, zuwa lokacin nasan Hamna ta dawo kinga ita ma na ganta."

Turo baki tayi tana d'aga kafad'a da fad'in "Um um, um im, ban yarda ba ni gaskiya, kuma Hamna ma wa yasan ranar dawowarta."

"Au ba zaki hak'ura ba kenan?" Cikin turo baki tace "Na k'iya."

"Shikenan to nasan maganinki." Ta fad'a tana kallon inda Ammar ke tsaye, cikin d'aure fuska tace "Yarona zo ka min maganinta tunda bata jin rarrashi."

Takowa ya fara yi da k'arfi yana fad'in "Ai kuwa tanti bari kiga yanda zanyi da 'yar banza." Takalmanshi ya ciro yana shirin wurga mata da gudu ta koma d'aki tana rusa kuka, dariya suka saka mata inda tanti tace "Ai maganinki kenan, da kin kwantar da hankalinki da munyi sallama cikin farin ciki."

Suna nufa k'ofa Ammar yace "Tanti karki damu, insha Allahu zan kawo miki ita tayi sati d'aya, dan yanzu ta fara kumburo min baki kenan har illa masha allahu indai ba ganinki ta sake yi ba."

Dariya tayi tace "Auta ce ku barta tayi rigimarta, amma zaka iya barinta tayi sati d'aya ko?"

Kallonta yayi sai yaga ita ma kallonshi take kallo mai nuna na fa sanka ba zaka iya ba, sunkuyar da kai kawai yayi yana murmushin jin dad'in yanda ta san shi sosai tare da fatan ina ma mahaifiyarshi ce ta mishi wannan fahimtar, fita sukayi inda ya kaita gidansu dan ta gaisa da yan uwanta.

Kamar yanda ya fad'a kam ya cika alk'awari, ba tare daya fad'a mata ba kawai yace ta shirya, sai kawai ganin tayi sun d'auki hanyar garin, tunda ta ga haka ta fara murna tana jin dad'i sosai, da suka je saida ya wuni kafin ya juyo ya barota, murna a gurin Amna ba magana yau zata kwana tare da ummanta, ba ita kad'ai ba ita kanta tanti tayi farin ciki sosai, da dare da sukayi waya da Hamna ta fad'a mata gata nan ita kanta sai taji kamar tayi hira, anan take tambayarta me yasa yanzu ta b'oye lambarta in aka kirata sai dai ya nuna numéro unkwnon sannan me yasa bata Whastup? Haka kawai shine abinda ta fad'a mata, a wajensu Hamna ma da Ummy komai yana tafiyar musu daidai, sai dai basa cikin kwanciyar hankali, kullum Hamna tana fad'a ma Ummy idan fa asiri ya tonu tana jin tsoron abinda zai faru, ita ma kuma ta sani akwai gagarumar matsala, amma a ganinta lokaci ya k'ure musu.

Tanti Hadiza ta ga abinda yafi k'arfinta, bata san yaushe kuma a wane lokaci Amna ta zama marar kunya ba, dan tunda ta zo idan yau bai zo ba gobe zai zo, a gabanta saita rumgume shi ko ta sumbace shi, idan suka shiga d'akinta duk da babu abinda ke shiga tsakaninsu, amma irin yanda yake jin dariyarsu da maganganu k'asa k'asa abin nasa kanta girma, idan kuma dare yayi suna waya wani abun idan ta fad'a saita kalleta da mamaki, shiyasa yanzu daya shigo gidan ita kuma saita shiga mak'ota ko kuma ta shige d'akin mijinta ita ma, a haka ta kammala sati d'ayan nan suka koma gida.

Lieutenant ya fara mata k'orafi kan rashin dawowarta kan lokacin data fad'a mishi, amma sai take fad'a mishi basu gama bane ya k'ara hak'uri, har saida Hajia ta fara fad'a wanda Ummy tace kamar wak'a take jin fad'an nata, tunda dai har ta riga data tafi to anyi mai wuyar, a haka har lokaci ya k'ara kwararawa.

*Bayan Wata Biyar*

*France*: tunda ta shiga watan ta dama aka basu lokacin da za'a kawota kafin ta fara nak'uda, dan haka k'arfe *11: 54* suka shiga da ita d'akin haihuwa, Ummy bata san tana kuka ba saida wata banasariya ta dafa ta tace mata ta dinga mata addu'a zata haihu lafiya, tunaninta a lokacin shine idan fa aka samu matsala ya zatayi? Alwala ta d'auro ta shiga fad'awa Allah kukanta, bata matsa daga kan sallayar ba misalin *12:38* aka sanar da ita haihuwar Hamna lafiya, yaron bai dameta ba sai mahaifiyar da take tambayar ya take? Lafiya lau ita ma aka fad'a mata, saida tayi sujadar godiya ga ubangiji kafin ta shiga ganinta, murmushin daya sub'uce mata ne yasa Hamna dake kwance kallonta tace "Ummy lafiya?"

Dake tsaye inda take kusan gadon jaririn ta sake dariya taja hancin yaron tace "Ya rantse saiya zo duniya, gashi dai ya zo yanzu kuma *BADAK'ALAR* zata fara musamman mahaukacin ubansa yasan dashi."

Jim ta d'anyi saboda

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login