Showing 15001 words to 18000 words out of 325849 words
juyaka, kai idan ma ka zama lusari har 'ya'yan daka haifa sai su juyaka yanda suke so, da k'yar ya isa shagon daya samu duk abinda take so, da kuma yasan cewa tana son yaour sosai sai kawai ya siyo ita ma, dan k'aramin aikinta ne saiya kawo tace kuma tana son ta, haka colonel ya kinkimo bak'ar ledarshi a hannu ya taho da ita, sabo da kuma sanin kan aiki yasa d'aya daga cikin yaranshi suna ganinshi yayi saurin mik'ewa zai nufi wajenshi, wasu jajayen idanu colonel ya zaro mishi hakan yasa ya k'ame wuri d'aya, cikin gidan ya haura ya shiga ya wuce d'akin, yana zuwa ya sameta zaune ita kad'ai a d'aki kamar mayya, ita ba zata iya shiga mutane ba saboda k'yank'yamin su take tana ganin ta wuce ajinsu, durk'usawa yayi akan tafukan k'afafun shi ya fara bud'e ledar yace "Hajia ruwan zan baku?"
Ba tare data kalleshi ba tace "Umm."
Bud'awa yayi ya bud'e murfin robar ya mik'a mata, karb'a tayi tasa abin goge gogen nan na hannunta ta goge bakin robar sannan tasha, gefe ya aje mata sauran yace "Ga sauran nan Hajia ko zaku buk'ata."
Wani kallo ta masa tace "Hussein yanzu dayawa ka siyo saboda kar anjima nace ina so ka sake wahala? Tafiyar ce ka ke jin wahalarta ko me?"
K'asa yayi da kanshi yace "Ba ko d'aya Hajia, na dai siyo ne ko zaku iya buk'atar su a kowane lokaci."
Cikin b'acin rai tace "To bana so Hussein, ka d'auka ka fitar min da su yanzun nan, idan buk'atar ta tashi zan sake nemanka."
D'aukar ledar yayi yace "Shikenan Hajia, Allah ya huci zuciyarki."
Har ya kusa kaiwa k'ofa tace "Ka ban lemu d'aya."
A hankali ya bud'a ledar ya fito da kwalin lemu ya sunkuya ya aje mata k'asa gefenta, yana d'agowa suka had'a ido ta mishi wani kallo tace "Cewa nayi fa ka bani, shine zaka aje k'asa."
"Yi hak'uri." Ya fad'a yana sake d'auka ya bata ga hannun, amma sai cewa tayi "Aje kawai zan d'auka." Ajewa yayi ya juya ya fita yana addu'a a ranshi Allah ya k'ara musu hak'urin zama da mahaifiyarta su, dan iyaye irin mahaifiyarsu wuyar sha'ani ne da su ba kad'an ba.
Lieutenant ne ya kira Gambo ya sanar da shi, nan fa aka bi duk 'ya'yan margayiya ana bashi yana musu ta'aziya, kafin daga bisani ya sake cewa a mik'a ta'aziyarshi ga kowa dake wuri dan ba lallai ya samu lokaci ya zo ba tunda ya riga da ya bar garin.
*Bayan tafiyarsu*
Ammar n ma shiga d'aki ya fara tunanin wanda ma zai fara kira a cikin su ukun, tunda Jibril shi baya garin watak'ila zuwa gobe yaje idan ya dawo, ba komai yake dubawa ba sai doguwar maganar da zaiyi da su, kuma ya tabbatar duk wanda ya kira saiya tambaye shi ya akayi? Ya ake ciki? Me ya faru, me zai faru? Dan haka ya yanke shawara ya kuma rubuta sak'o ya had'e duka lambobin nasu ya aika musu, kowa na inda yake wannan sak'o ya shigo na su zo gida yanzun nan zasu wuce gidan roumji Hajia Fatime ta rasu, duk basuyi mamakin ganin sak'on ba saboda ganin wanda ya turo shi, cike da jimami kowa ya antayo motarshi ya nufo gidan.
Kamar had'in baki saiya zamana babu wata tazara tsakanin zuwan nasu, kuma kowa b'angaren su yake nufa dan ya shirya babu mai tunanin aiki gobe tunda dama asabar ce, sa'a akayi Junaid zai shiga d'akin shi Amar kuma ya shigo falon, nan Amar ke tambayarshi "To wai yanzu hanya zamu d'auka kenan?"
Junaid ne yace "Yanzu ba wannan ba, mu fara saurin kimtsawa dai, daga nan sai mu san abinyi, dan kasan gidan nan akwai yan gaggawa dayawa, babu wanda zai jiramu idan..."
Fitowar Ammar cikin bak'in yadi shara-shara har ana ganin farar rigarshi yasa sukayi shiru suka kalle shi, kamar dai kullum fuska a tamke ya kalli Junaid yace "Su waye yan gaggawa a gidan nan?"
Juyawa Amar yayi ya nufi d'akin shi yana fad'in "Na gode Allah da yasa tambayar nan taka ce d'an uwa, fatan alkairi."
Junaid kuma murmushi yayi yace "Ah haba dai soja, cewa nayi dayake gidan nan akwai..."
Da gudu ya shige d'akin shi ya rufo k'ofar daga ciki yake fad'in "Yan gaggawa na ce, kuma kaine farko, sai wannan kawun naka (mahaifinshi kenan) colonel yake ko me ma."
K'anan Jibril ne ya shigo da sauri wanda yake da tare da mahaifinshi Labaran a kasuwa suna kasuwanci shi ma ya shigo dan shine na uku da Ammar ya turawa sak'on duk da suna gaba dashi nesa ba kusa ba, kallonshi Ammar yayi yace "Ka fad'a ma yaran nan ina jiranku waje nan da minti biyar, idan lokacin nan ya cika baku fito ba, to zan tafiya ta ne tunda kowa da motarshi ai, amma ka fad'a musu umarnin Abba ne yace mu tafi tare."
Yana gama fad'a ya fice daga d'akin inda *Jamil* ya bi dak'unan daya nuna mishi da kallo, k'wank'wasa musu k'ofar yayi ya sanar da sak'on Ammar kafin shima ya shiga dan shiryawa.
*Minti hud'u* Amma ya fara doka wata uwar oda data firgita duk wanda ke cikin gidan, wad'anda suka san da su ake tuni suka gigice suka rasa ma abunyi, ba tare daya daina odar ba sai kuwa gasu da gudu suna rige rige, Jamil bawan Allah ko d'akin shi bai rufe ba ya taho da gudu da takalmi a hannu da k'yale alamar gogewa zaiyi ko yake cikin yi, bud'e k'ofofin motar sukayi suka zauna Junaid yace "Dan girman Allah odar ta isa haka, gamu nan fa mun shigo ko."
Amar ne ya doka wani uban tsaki saboda sai lokacin ya kula da abin goge bakin (brush) daya taho dashi a aljihu, juyawa sukayi suka kalle shi ai sai Junaid ya kwashe da dariya, cikin jin haushi Amar dan ko turare bai fesa ba yace "Kai ban son k'ananan iskanci fa."
Mayar da kallonshi yayi ga Ammar yace "Allah Ammar ba ka kyautawa, yanzu shirin ma ka barmu mu tafi a tsanake amma ba zaka iya ba, wane wace irin rayuwa ce, haba."
Juyowa yayi ya kalleshi ya had'e girar sama da k'asa yace "Kar ka fad'a min maganar banza, yan daudu ne ku ko mata da zaku ce shirinku na buk'atar b'ata lokaci?"
Cikin jin zafi Amar yace "Yan daudun ne kamar kai ba, ai kai gashi nan ka shirya a tsanake babu wanda ya takuraka, sai mu daka raina, wallahi ba dan ance Abba ne yace mu tafi tare ba da babu tsiyar da zata sanya na tafi da kai, tunda ai motarka ba fin tawa motar tayi ba."
Idon Ammar ne sukayi launin ja ya fito daga motar da k'arfi tare da zagayowa inda Amar yake a baya yana fad'in "Amar ni kake kira d'an daudu? Ni? Ni sa'anka da zaka kirani da d'an d...?"
Junaid ne yayi saurin rik'e Ammar d'in saboda bud'e murfin motar da yayi zai daki Amar da shima ke shirin fitowa, fitowa yayi a hassale shima yace "An kiraka d'an daudu, mu daka kamalta mu dasu bamu da zuciyar jin zafi ne ko me? Sai kai daka fi mu sanin ciwon kanka kenan, uban son girman tsiya, tsakani na da kai ko minti biyu babu, amma kullum kai ganinka ka girmeni da wata tazara mai tsayi."
Junaid dake ta rik'on Ammar yana bashi hak'uri cikin b'acin rai ya sa gwiwar hannunshi ya buge shi a baki yana fad'in "Dallah sakeni malam, kana ji yaro yana fad'a min magana son ranshi."
Junaid daya ji hanb'ara a baki baisan sanda ma ya sake shin ba, tuni jini ya gabce mishi harda hanci ma, sai kuwa Ammar ya cakumi wuyan Amar da hannu biyu ya shak'e shi sosai yana fad'in "Ni kake wa iskanci, ko sakan d'aya na baka ince dai ni na fara shan iskan duniyar? Shine zaka tsaya kana raina min wayo dan kawai kunga ina k'yale ku."
😔 'Yan biyu a madadin had'in kai sai gashi Ammar da Amar suna dakuwa kamar yara k'anana, amma Amar yafi galabaita saboda har yanzu Ammar bai sake shi ba daga shak'ewar daya mi shi, duk da haka kuma sai kai yake buga mishi a nashi kan, a d'aya b'angaren kuma yasa gwiwar k'afar shi sai tokara mishi yake a ciki, shi kuma duk dukan da yake ma Ammar d'in ma ba ji yake ba, ai kuwa gani Ammar zaiyi kisan kai yasa Junaid dake jinyar kanshi da Jamil suka fara k'ok'arin b'anb'are shi, dan tuni fuskar Amar ta fara had'a jini daga baki da hanci, amma saboda bak'ar zuciya ta Ammar sai ya dinga kai musu haura suma, ana cikin haka Ummy da ta ga mutuwar Hajia Fatime a kafar sada zumunta na alahlin Gaga ta taho gida suka ji muryar ta tace "Junaid, Jamil, ku barshi ya kashe shi."
Tana fad'a ta wuce b'angaren su ko kallonsu batayi ba, su Junaid kuma basu bar raba su ba saida Junaid ya tattara k'arfin shi ya fizgo Ammar daga jikin Amar yana fad'in "Dallah malam sake shi ko."
Amar na jin ya samu numfashi ya durk'ushe a wurin yana mayar da numfashin wahala, Jamil ne ya taimaka mishi ya mik'e suka nufi b'angaren iyayen sai Junaid daya bi bayansu bayan ya k'arewa Ammar kallo wanda ya buga murfin mota da k'arfi ya juya ya koma b'angaren su, suna shiga ciki suka ci karo da Zeinabu da faranti a hannu, tana ganin Amar a yamutse tace "Jamil lafiya? Meya same shi haka? Allah yasa dai ba hatsari yayi ba."
Kafin ya bata amsa Junaid ya shigo bakinshi har ya fara kumbura kuma har yanzu yana fitar da jini kad'an kad'an, da sauri ta saki farantin ta k'arasa ga Junaid tana fad'in "Kai wai lafiya? Meya sameku ne haka?"
Cike da k'aguwa Junaid ya d'an janye hannunta data tab'a shi yace "Umma ba komai, ba had'ari mukayi ba."
A lokacin Jamil harya zaunar da Amar kan kujera ya nufi d'akin Ummy dan ta fito ta duba shi, Zeinabu ce ta kalli Junaid tace "In ba had'ari kukayi ba to me kukayi? Dubeku fa."
Shima zama yayi a kujera ranshi a b'ace yana murza bakinshi, Soueba ba ta fito yayi daidai da fitowar Jamil dan Ummy tace babu inda zataje can su suka sani, Soueba ce ta kalli Jamil tace "Kai wai lafiya; meya faru ne haka? Meya samu Amar d'in."
Cike da damuwa yace " Mama ba komai, dan Allah kije ki samu Ummy ki fad'a mata Amar na zubar da jini ta zo ta duba shi, ni na mata magana amma ta k'i fitowa."
Amar na jin haka ya mik'e ya nufi d'akin Ummy duk da jirin dake son kwasar sa, cikin fad'a da hushi Zeinabu tace "Wai duk uban da aka tambaya sai yace ba komai bayan ga komai d'in, to koma menene ya faru ba sai ku fad'a ba, idan har kunsan ba zaku fad'a ba meye na shigo mana d'in? Wato inda iyayenku ne maza suka k'ura muku ido da tuni kun sakar musu zance, amma dake mune marainanku da muke wasa da ku kowane na hancin uwa sai dai yace ba komai, to kuje da ku da ba komai d'in duk kun ci uwarku."
Cikin b'acin rai Junaid yace "Dan Allah Umma meye haka? Mun fad'a miki ba komai ba shikenan maganar ta wuce ba, zaunawa zamuyi mu fad'a muku Amar da Ammar ne suka samu sab'ani har ta kaisu ga doke doke."
Mik'ewa yayi zai bar d'akin dan yana jin haushin surutun uwarshi da tseguminta, abun magana da ba na magana ba ita duk d'aya ne a gurinta, da gudu gudu ta tare gabanshi tana kallon bakinshi tace "Ammar fa ka ce? Halan kai kuma tsakaninsu ka shiga shiyasa ya maka wannan dukan?"
Rab'ata kawai yayi ya bar d'akin hakan ya k'ara hassalata ta fara d'aga murya tana fad'in "Ni na sani mana wani abu ai sai wannan mugun, wai shi Ammar meya d'auki kanshi a cikin gidan nan ne? Haka kawai ka addabar mana yara basu da damar da zasu wataya a gidan ubansu, kai ne kullum zuciya da cin zalin yan uwan ka, duba kiga yanda ya fasawa d'an uwanshi fuska, shi kuma wannan daga rabo ya fasa mishi baki, meye anfanin haka dan Allah? To wallahi na daina yarda daga yau, yanda yake jin haihuwarshi akayi a gidan nan haka suma yaranmu haihuwarsu mukayi, kuma nak'uda bata fi nakudaba bare yace uwarshi ta fi mu shan wahala, dan haka wallahi daga yanzu ni zan dinga tarewa kai na fad'an tunda dai shi mugu ne na gidan gaba."
Wannan b'ab'atun ne yasa Hajia Husseina fitowa daga d'akin ta, Soueba ce tace "Dan Allah Zeinabu kiyi hak'uri, da Ammar da Junaid ai duk d'aya ne a gurinki kamar 'ya'ya suke a wajenki, dan sun samu sab'ani bai kamata ace muna jin zafi haka ba, yan uwane su kuma mabiyi da mabiyi, dole dama ana samun haka saboda zaman tare, amma bai kamata ki dinga fad'in haka a kan shi ba."
Hajia Husseina ce tace "Lafiya ku kuma meke faruwa ne?"
Zeinabu ce tace "Hajia, Ammar ne ke fad'a da Amar, Junaid daga zai raba kawai ya samu shima ya bubbuge shi saboda fin k'arfi, shine yanzu nake magana Soueba take nuna min ba hakanan ba, to dan Allah yanzu su Ammar yara ne da za ace har yanzu suna fad'a? Sanda sukayi fad'an k'uruciyar wa ya tab'a cewa wani abu, ko da suna yara ma kullum shine ke saka mana yara kuka, kuma yanzu ace sun girma ma ba zasu huta daga kaidin shi ba saboda shi ya zama wani shaid'an."
Murmushi Husseina tayi tace "Ai gaskiya Soueba ta fad'a, ba kina kwaroronton sun samu sab'ani yanzu ba? To zuwa gobe ko jibi a falon nan zaki tarar da su kuma suna wasa tare kamar lokacin da suke yaran, kuma kema kin sani ko wasa suke sunfi tsokanar Ammar d'in, amma shi ko magana bai cika son yi ba, kenan meye abun wannan fad'an?"
Amar da yana shiga d'akin ya samu Ummy zaune kan kujerar coiffeuse (dressing miror) zunbur ta mik'e tana kallonshi ta nuna mishi k'ofar fita tana fad'in "Fitar min a d'aki Amar, fita."
Cikin muryarshi ta shan wahala ga dishi-dishin da yake gani yace "Ummy kiyi hak'uri na fad'a miki ab..."
Cikin tsawa tace "Ka fad'a min me Amar? Me zaka fad'a min? Shin Amar tun yaushe nake fad'a maka ka dinga hak'uri da halin d'an uwanka? Sau nawa ina fad'a maka kai da shi akwai banbanci na hallaya ka dinga kiyaye b'acin ranshi? Amar na fad'a maka kai ne d'an uwanshi wanda ko bayan ba ranmu zaka iya tsaya mishi duk da shine babba, me ya sa ba zaka dinga hak'uri ba da duk maganar da zata fito daga bakinshi? Tunda kafi kowa sanin halinshi magana indai har ta zo bakinshi ko ni uwarshi fad'a min yake bare kuma wani, amma ku tsaya kamar yara yan shekara biyar wai kuna fad'a, fad'a Amar da girmanku da komai? Amar so kuke duk gidan nan na zama mujiya ko kuma kamar wacce ta haifi annoba?"
Komawa tayi ta zauna cike da damuwa kamar zata fashe da kuka, cikin sanyin jiki da rashin jin dad'i ya durk'usa kusanta ya rik'e k'afar ta yace "Dan Allah Ummy kiyi hak'uri ki yafe mana, wallahi har cikin raina bana jin dad'i na ga kina damuwa akan halin Ammar, Ummy in kina damuwa da halinshi hakan zai iya janyo mishi fushin ubangiji, kiyi hak'uri dan Allah ki daina Ummy, nayi kuskure dana kula shi, amma na miki alk'awari hakan ba zata sake faruwa insha Allahu."
Hawaye ne suka taho mata ta d'ora kanshi a saman cinyarta ta kasa cewa komai, ita yanzu babban tashin hankalinta idan Hajia ta zo ta ga Amar da wannan ciwon a fuska, tashin hankalin zai fara ne idan aka ce Ammar ne ya dake shi, _kowane d'an adam da wanda Allah yake jarabtarshi da son shi, Hajia ita ta ta jarabta Amar ce, duk cikin 'ya'ya da jikoki babu wanda Hajia ke nunawa k'auna kamar Amar, babu wanda take nuna damuwarta a kanshi kamar Amar, takai ta kawo Amar na iya mata magana kan wani hukunci data yanke kuma ta janye shi, tun yana yaro yake samun kulawarta da soyayyarta, hatta yayesu da za ayi ita ta amshi Amar hannunta, kuma sun fara samun rashin jituwa ne da Ammar saboda kullum shi ke nasara akan Amar in dai ana fad'a, da kaji Amar na kuka to Ammar ne ba makawa, ita kuma saita dinga wa Ammar fad'a tana nuna mishi tsana a fili, hakan yasa shima baya wani k'aunar ta bare al'amuranta,_ to wannan ne yanzu damuwarta dan tasan sai rai ya b'ace fiye da yau, tana cikin wannan tunanin suka ji muryar Zeinabu na wannan fad'a, cikin sanyin murya tace wa Amar "Ka ji ko, na tabbata suna magana ne akan abinda ya faru."
Mik'ewa Amar yayi yace "Ummy ni fa bana jin dad'i na ji ana fad'an maganganun marasa dad'i akan d'an uwa na, zanje na fad'a musu kar wanda ya damu da abinda ya faru yanzu, tsakaninmu ne wannan kuma zuwa anjima zamu shirya."
Rik'e hannunshi tayi tace "Bara na duba maka ciwonka tukuna."
Zage hannunshi yayi yace "A'a Ummy zan dawo yanzu, kinsan tanti (Zeinabu)da ji-nini."
Mik'ewa tayi ita ma ta bi bayanshi, suna tsaye lokacin Husseina ke tambayar lafiya? Duk abinda ta fad'a akan kunnensu, Amar zai tafi wajenta Ummy ta rik'e shi, tana cikin wannan fad'an kuma sai ga Ammar ya shigo falon da takonshi na k'arfi kamar zai tashi k'asa.
Tunda ya koma b'angaren su tunanin Ummy ya dameshi yasan yanzu tana can tana kuka, shiyasa ya tashi yayi wanka ya canza kayan jikinshi zuwa wata shadda ruwan k'asa ya fito, tunda ya doso falon ya ji wannan hayaniyar ya sake tamke fuska kar ma aga damarshi, Zeinabu na fad'in "Ai dan ya ga wuri ne shiyasa yake mana iskancin son ranshi, suma ba dan suna wasu sakarkaru ragwaye ba har yaushe mutum kamarku wanda duk cikinsu babu wanda ya bawa wata biyu da haihuwa amma ku tsaya yana lallasaku son ranshi."
Husseina dai murmushi ne nata tace "Zeinabu ai abun a jini yake, tun daga yanayin tafiyarsu zaki duba, zaki fahimci ko a tafiya shi da k'arfi yake tashi sab'anin su."
Tsaki tayi tace