Showing 291001 words to 294000 words out of 325849 words
saurayin naki da kika kunyata iyayenki akan shi shine ya turo miki sak'o yake kiranki da banza, wai banzar k'anwata na dafa ki na cinye."
Ita dai da bata fahimci komai ba wucewa tayi ta gaishe da Amar tana masa ya jiki, dawowa yayi yana kallonta ya ci gaba da zazzaga masifa wai duk ita taja, ko kallonshi ma ba tayi bare ta kula shi haka kowa ma yaja baki yayi shiru, saida ya kalli kowa yace "Eh mana ga d'an iska mahaukaci na magana, dole kowa ma yayi shiru, to ni na tafi sai kunje gani na a gidan yari."
Kamar zai tashi sama ya nufi k'ofar fita cikin rashin kunya Umaimah tace "...
*Insha Allah zanyi k'ok'ari nayi wata page d'in anjima amma fa idan kunyi comment, ku shirya kowa ya kawo goron d'aurin auren fitinannu na.*
*Alhamdulillah*
04/11/2020 ร 14:38 - Ummulkhairi: ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*BADAK'ALA*
๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ๐ฉโโค๏ธโ๐จ
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D'AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K'ADDARARMU_
*8* _K'ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k'ura)..._
*14* _BADAK'ALA..._
*SADAUKARWA GA*
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ _*AHALI NA*_๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
๐ซโจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_๐ค
โ *[ T.M.N.A]* โ ๐๐๏ธ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
_69_
"Yanzu dama akan ka ne aka dakar min mijina? Dan Allah yah Ammar wace irin rayuwa ce wannan kai da jan masifa shi da shan duka? Ya kamata fa ace kasan ka girma amma irin haka bai kamata ba, yanzu gashi baisan hawa ba bare sauka kawai an sauke mishi kwandon rashin mutumci, gaskiya dai akwai alhaki wallahi Allah ma ba zai barka haka ba, haba mutum sai jaraba kawai k..."
Kamar saukar aradu kowa yaji Hamna ta daka mata tsaw da cewa "Ke."
Juyawa tayi ta kalleta suka shiga kallon kallo kafin ta nuna mata shi tace "Umaimah tsaranki ne shi da kike fad'a masa haka? Saboda an daki d'an uwansa wanda na tabbata baki fi shi jin zafin a zuciyarshi ba, ki tambayi shi yah Amar d'in kiji kafin ki ci masa albasa, shin yana jin haushin d'an uwansa kan abinda ya faru yanzun?"
Cikin rashin mutumci tace "To ke kuma a wa? Dake nake bare ki sa min bakinki? Ki bari shi da nayi dashi ya tanka min mana amma bake ba."
Murmushi ta mata tace "To ai naga ba shi ne daidai ke ba, ni nan ni ce daidai da ke wallahi."
Ammar dake kallon ikon Allah saiya bushe da dariya ya nemi kujera ya zauna yace "Buga min ita a k'asa kankana, yau saina cika miki gidan nan da kankana Allah kuwa."
Kallonshi tayi ta dalla masa harara ta mayar da hankalinta kan Umaimah da tace "Kin tare masa saboda ke ce daidai dani? Ko kuma kin tare masa saboda shine uban d'anki?"
Hajia da Husseina ne suke musu magana amma bata saurare su ba saida tace "Ki d'auka a yanda kika ga zai fi miki sauk'in d'auka akan ki, amma idan zan zab'ar miki sai nace barshi dan yana uban d'ana, ai kinsan saduwa ba k'arya bace, haka ma haihuwa ba wasa bace, ai ke wannan abubuwan biyu ne yasa kike tayar mana da jijiyar wuya saboda an tab'a mijinki, ke ga mai miji maji dad'in miji."
Cikin shewa da tapa hannaye tace "Wuuuu! Alhamdulillah Ina da mijin da zan iya nunawa, kuma nagode Allah daya bani mijin da nake jin dad'in dashi, ke fa? Har yanzu gantali kike a titi har kin tsofe a gari babu mai so, sannan kaf yarana na haife su a k'ark'arshin inuwar aure, har nayi zamani na ban aje d'an dak..."
Dan bai da kuzarin da zai tashi ne amma yayi niyyar marin fuskarta, dan haka kawai ya daka mata tsawa da cewa "Umaimah."
Shiru tayi tana hararan Hamna wacce ita ma ke kallonta tana murmushi, cikin b'acin rai ya gyara zamanshi yana kallonta yace "Umaimah me yasa baki da hankali? Ta tsawarta miki ne saboda kina d'aga murya kan babba kuma d'an uwana da take da tabbacin ba zan ji dad'in abinda kika masa ba, yaushe zakiyi hankali ne wai?"
Wani harare ta sake dalla ma Hamna tana turo baki gaba tana gunguni, ba tare daya daina kallon fuskarta ba yace "Ba tace ki tambaye ni ba? Me yasa baki tambaye ni ba? To bari ni na fad'a miki kiji da babban murya, wannan dukan da d'an uwana aka wa shi wallahi ba zan sake cin abincin gidan nan ba har sai ranar da idona suka ga cikakkiyar lafiyarsa, Umaimah ina farin ciki sosai da godiya ga Allah da dukan nan ya tsaya kaina, yanzu haka na yafewa wanda yasa aka dake nin, amma da d'an uwana ya daka har abada babu yafiya tsakani na da shi, dan haka wuce d'akinki bana son ganinki a wurin nan."
A hassale ta kalleshi tace "Ni ce ma mai laifi kenan? Ba damuwa."
Ta fad'a tana wucewa d'akinta, da harara ya bita cike da takaicin hallayarta yana fad'in "Inma da damuwar fa sai me."
"Hahahahahahahahahahha, wuuuuuuuuuu, wayyo Allah na, Hajia kin gani ko?" Cewar Ammar kenan dake nufa kusan Hajia, nuna mata Hamna yayi yace "Allah Hajia yarinyar nan so na take, kiji fa yanda take fad'a dan an tab'a mata ni, wuuu! Gaskiya zamuyi kyau da aure."
D'ora kanshi yayi kan kafad'ar Hajia cikin jin kunya yace "Dan Allah Hajia ki daure ki aura mata ni, kinji?"
Me Hamna za tayi ba dariya ba, har ga Allah shirmenshi ko rashin kunyarshi suna bata haushi da takaici, amma na yau saiya bata dariya da yace wai ta daure ta aura mata shi, kallonta yayi ya kalli Hajia yace "Kin gani ko, na fad'a miki ai."
Junaid ne yace "Yanzu ya maganar d'aukar fansar to? Ka hak'ura kenan?"
Kallonshi Husseina tayi kallon ya kuma zaka tuno masa? Kallonshi yayi yace "Hak'uri fa? Ai wannan maganar ma bata taso ba yaro."
Hanyar fita yayi Hajia ta fizgo hannun Hamna cikin rad'a tace "Ki wa Allah Hamna naga kamar ke d'in aljanunshi na sonki ki dakatar dashi, karya je ya kashe d'an mutane."
Kallon Hajia tayi ta had'e fuska tace "Ni kuma Hajia? Rufa min asiri na mutu maza su binne ni, ba wani aljanu wallahi iskanci ne."
Cikin rad'a tace "Amma dai kinsan zai iya ko?"
Tunawa tayi da abinda ya faru jiya sai kawai tace "Gaskiya kuma."
Turata Hajia tayi tace "Yi sauri to ce ya hak'ura ya dawo zan aura masa ke."
Hararan Hajia tayi tace "Karku sa haukansa a kanku mana."
Da sauri ta fita daga d'akin inda Amar ya kalli Hajia yace "Da zaku ji tawa Hajia sai nace ku aurar dasu, a yanda na fahimta duka suna son junansu."
Murmushi Hajia tayi tace "Ba zasu yarda cikin sauk'i ba, amma zan musu na babba da yaro, in sun san wata ai basu san wata ba."
Husseina ma dariya tayi tace "Gaskiya kam, musamman ma Hamna dai tafi taurin kai, amma shi na ga kamar k'uli yake duk inda ya fad'i gaba ne."
Dariya Junaid yayi yace "Kai shi fa babu ruwansa, anya ma kuwa zai iya soyayya?"
Zeituna da tunda suka gaishe da Amar bata sake cewa komai ba sai yanzu ne tace "Ai kuwa idan ya tashi yi zai baka mamaki, dan soyayya ma sai tafi wahalar dashi fiye da tunaninka."
Kallonta yayi yana dariya yace "Tanti Ammar kuwa zai bari soyayya ta bashi wahala, ba fa zai iya rarrashi ko lallab'a ba bare kalaman soyayya."
Amar ma dariya yayi yace "Ai daya fara ma zai ce ke dan ubanki dan kinga ina lallab'a ki."
Ihun Hamna suka ji yasa suka dakatar da dariyarsu suka fita da sauri sai Amar kad'ai ke zaune yana girgiza kai, ko da suka fito a farfajiyar suka same su yayi k'arfa k'arfa ya shiga har d'akin mai gadi ya d'auko labceciyar wuk'arsa ko kuma takobi, Hamna ce tace mai gadi ya rufe k'ofa shine fa ya d'aga takobin yace bari ya fara ta kan mai gadin, dalilin kuwarta kenan, cikin tashin hankali da son kwantar da tarzomar kowa ya shiga bashi baki, anan Hajia tace "To kai da yanzu muke maganar aurenku kuma kana so ka shiga gidan yari, kasan dai ba zan aura maka jikata bayan ka fito daga gidan nan ba ko?"
Husseina ce tace "Nima ban goyi da baya ba gaskiya, dan wata rana yar tamu zai kashe."
Cikin nutsuwa Zeituna tace "Yah Ammar, ko ba komai dan Allah kayi tunanin yaranka mana, ko so kake ka mayar dasu marayu gaba da baya? Mahaifiyarsu ma Allah ya jikanta da rahama ba zata so ba hakan ba, ko ka manta ka tab'a fad'a min bata son rigimar da kake yi."
Mik'awa mai gadi takobin yayi yace "Shikenan kun kashe wannan fitina, amma ku sani ban muku alk'awarin cewa idan na ganshi ba zan murd'e wuyan tsinanne ba."
Kallon kallo suka shigayi suna ma kansu tambayar wannan ai shine an kashe maciji ba'a sare kansa ba, can kuma sai suka ji yace "Shiit, to ai kuma banga fuskarsa ba."
Murmushi kowa ya saki na jin dad'i sai kuma ya kalli Hamna wacce tuni ta shiga rarraba ido dan tasan ba shakka zai koma kanta yace "Munafuka ke ai kin san shi, dan haka tare zamu fara yawo yanzu har sai kin nuna min shi."
Hararanshi tayi tace "Saboda banda aikin yi? Ko kuma saboda kai na ya zare?"
Da sauri Hajia tace "To kai yanzu ka yarda kayi ta yawo da matarka a gari kowa na kallo?"
Kallon Hajia yayi yana murmushi yace "Mutane ai ba zasuyi kyau ba babu ido."
"Kamar ya?" Cewar Junaid, kallonshi yayi yace "Idan na fara k'wak'ule maka ido zaka fahimta."
Dariya yayi yana matsawa daga kusan shi, ta gabanta yabi ya shafi kumatunta yana fad'in "Allah ya gafarta miki duniyata, har nayi kewarta wallahi, da yanzu tana nan tana kuka tana cewa dan Allah yah Ammar ka tausaya min, karka fita ka zauna a gida, ni ka dake ni ma indai zaka huce."
Da kallo su dai suka bishi har ya shige b'angarenshi, girgiza kai Hjia tayi tace "Allah ka shirya mana bawan nan naka, wannan idan muka k'ara samun wani kamar shi zamu mutu da ranmu." Dariya kowa yayi suka shiga ciki suna sauke ajiyar zuciya.
*Da safe* ko da ya tashi da abun ya tashi a ranshi, sai yanzu ne yake asalin jin haushin abun sosai, ya zage shi ya zage abar son shi, a hakan ma wai bayan yasa an daddaka d'an uwanshi, a gaskiya ya gama shawowa dashi ba kad'an ba, wai shi ya kira da mai k'walwar kifi kuma dak'ik'i, shiryawa yayi ya fita bai tsaya ko ina ba sai alimentation, kifi ya siyo kifin ma babba ya kamo hanya ya dawo gida.
Cikin madafa ya shiga dashi su Zeituna na ta k'ok'arin had'a abin kari, da kanshi ya d'auki babban faranti ya juye shi ciki ya d'auki wuk'a, suna kallon ikon Allah su dai ya cire kanshi tare da bud'e cikinshi, kwatta kwatta ya dinga k'arewa kan kifin kallo, basu ankara ba suka ji ya jefa wuk'ar ta bigi tagar dake kallon bayan gidan yana fad'in "Kaji haushi Ammar, ya had'aka da kifi kuma babu abinda kayi."
Juyawa yayi zai fita ya ga duk suna kallonshi, nuna musu kifin yayi yace "Ku je ku duba kuga k'walwar tashi sai kuji dad'i tunda ya kamanta ni dashi." A hassale ya fita rai b'ace ya bar gidan gaba d'aya.
*Tunda safe* lieutenant yaje dan su tafi, k'in fitowa tayi da farko amma tanti Ardayi tace ba za ayi wannan da ita ba, hannunta ta kamo ta damk'awa lieutenant sannan tace "To Allah ya kiyaye gaba, Allah ya kaiku lafiya sannan aci gaba da hak'uri."
Saida ya duk'a har k'asa yace "Nagode Hajia, Allah ya k'ara girma da d'aukaka."
Ko da suka fito waje ta fincike hannunta ta tafi da sauri ta shiga ta zauna inda dreba ya bud'e mata, rumgume hannaye tayi sai had'e rai take har suka d'auki hanya, babu wanda yace ma wani uffan har sukayi doguwar tafiya, lokaci lokaci ya kan kalleta sai yayi murmushi ya juya shima, wai hushi take bayan ita ce mai laifi, saida sukayi doguwar tafiya suka tsaya kan hanya wata k'aramar shago ya kalleta yace "In akwai abinda kike so ki fad'a min?"
Shiru tayi kamar ba taji ba saida ya sake maimaitawa tace "Bana buk'atar komai."
Kallonta yayi sannan ya kalli dreba yace "Mu tafi kawai."
Suna hanya Hadiza ta kirata sosai suka gaisa kamar yanda suka saba kafin daga bisani suyi sallama, ko da yaji yasan da wa take magana dan haka ba tare daya kalleta ba yace "Mutuniyar kirki ce, dukansu sun yafe laifin da aka musu."
Ita ma ba tare data kalleshi ba tace "Uwa ce ita, dole ta fahimci abinda yanda ya kamata."
Murmushi yayi ya lumshe idonshi, shima fa yanzu baya jin haushinta kan abinda tayi, irin dai kawai shi namiji ne ba zai sauko da wuri ba, to kuma sai ita ma Ummyn ta hau sama, dan tun daga maganar nan bata k'ara cewa komai ba har suka isa garinsu.
Hajia da kanta ta kira Hadiza ta sanar da ita maganar nan fa babu fashi, kawai su ma yaransu addu'a ta alkairi, haka ma Gambo ta kirashi ta fad'a mishi ya kuma ce wuk'a da nama na hannunta duk yanda tayi su addu'a da kuma yanda take so ne nasu, da kuma su Ummy suka dawo da dare take sanar dasu, duka dai kowa farin ciki ya nuna, amma da Ummy ta samu Hamna da maganar saita nuna ita fa bata so, duk k'ok'arin Ummy na son fahimtar da ita ta dage kan ita bata son auren Ammar, ba wai ba zata iya aurenshi bane kasancewarshi tsohon mijin yer uwarta yasa ba zata iya zama dashi ba ita, k'arshe dai haka Ummy ta rabu da ita dan karta takura ta har ta amince ba da son ranta ba.
*Da sauri*
*Abu* kamar da wasa sai magana ta girmama inda Hajia tace mishi za'a saka musu rana, amma fa duk abinda yasan ya ma Amna sanda zai aureta ita ma saiya mata shi, bai musa ba yace ya ji ya gani shi ai yaga abinda ya gani kuma yaji abinda yaji a na farkon ma, dan haka ribarshi ce bata wani ba.
Tana ji sama sama aka saka ranar kawo kayan, haka duk take kallonsu da wutsiyar ido da gari ya waye taga suna shirin tarban bak'i, dan wannan karan tunda abun ya sauya daga dangin lieutenant zuwa na Ummy ga kuma abokan arzik'i da dangin Hadiza duk sun hallara, kamar yau ake d'aurin auren saboda yanda ake ta kayaniya ta ko ina.
Da yamma aka shiga shigo da akwatina, tunda taji bud'a gabanta ya shiga fad'uwa tana tambayar kanta wai dama da gaske suke? Ammar? Ita? Lallai za'a mutu, tana sama ita dai tana jin gidan kamar zai tsage, a sama sama take jiyo maganganun mutane inda suke fad'in "Lallai wani hanin ga Allah baiwa ne, wani jinkirin kuma alkairi ne."
Saida aka ci aka sud'e an kawo ashirin ta arzik'i an koma da arba'in ta arzik'i, dan Hajia ta bud'e bakin jakarta ta zazzagawa kud'i rashin mutumci, a cewarta *auren sabon shalelenta ne* sannan ba k'arya k'ok'arinshi ya birgeta duk da dai tasan kud'i sun sake zaunawa yanzu, amma shima ya rintse ido sosai wajen kashe yayan banki.
Cikin k'ank'anin lokaci Hamna ta fara ganin statu d'in yan uwa har sun manna hotonta dana Ammar da kayan da kud'i da goro, statu d'in Sayyada (gaisuwa gare ki, sannunki da k'ok'ari da juriyar bayar da labarin yan uwan nan naki, wallahi kina k'ok'ari dasu๐ amma dan Allah karki fad'a ma cousine d'inki Hamna), d'aya hoton akwatina ne har goma ras an jerasu wasu na bin wasu, sai hoto na gaba inda aka bud'e dukansu kowa taf take da kaya har suna amai, sai na gaba d'aurin goro har guda hud'u da kud'i zube kan carpet yan jaka goma goma na million biyu, sai wata malet daban mai d'auke da tanfatsetsiyar sark'ar zinariya k'irar Agadez babu algus a cikin tare da awarwaro, wacce ita kad'ai ma kud'inta sun ishi mai rai rayuwa.
Ba tace bata ji dad'i ba gaskiya, dan saida ta murmusa ma amma bata san na miye tayi ba, amma daga nan ta shiga tunanin yanda zasu yi rayuwa da mutumin nan, a gaskiya ba zata iya rayuwarshi ba ta sani, bata sani ba waye zai wahalar da wani cikin ita ko shi, gashi bata da ta cewa yanzu tunda sun riga da sun gama magana ba zata kunyata su ba, idan kuma iska ne jikinta dake hanata aure, to ta sani shi zai dakatar da auren inhar lokacin aurenta baiyi ba.
Washe gari tana duba sak'onni WhatsApp d'inta ta samu sak'on Amie wacce rabonta da ita har ta manta, sak'o ne na neman tijara gajera kamar haka _"Burinki ya cika tunda gashi zaki auri mijin da yer uwarki ta bari bayan ta mutu."_
Ji tayi ba zata hak'ura ba ta maida mata da _"Na d'auka kin jima da fahimtar bana mu'amula da munafiki, amma bansan wace uwar kike nema tare dani ba."_
_"Ba ko d'aya, sai dai har yanzu ina tausaya ma yar uwarki, sannan da kike cewa baki zama da munafiki, ni ya kamata na fad'i haka, ko ke baki lura dana bar kulaki ba tunda nasan wacece ke ba."_
_"To kenan meya kaiki yi min magana kenan?"_
_"Dan na tayaki murna."_
Cewar Hamna _"Na ko gode."_
_"Mtsssss, anji haushin duniya, ki rasa wacce zaki ci amanar sai yar uwarki."_
Fita harkarta kawai tayi dan a ganinta ba zata b'ata lokaci kanta ba, sak'on Sayyada ta shiga wacce ke tambayarta ankon da zata fiddo musu, dariya kawai ta mata ita ma ta share ta, dan haka ta turo mata da "Karki d'aukeni yar iska mana Hamna, zan zo gidan da kaina naje na fito da anko."
Maida mata tayi da _"Hakan shi yafi, amma duk abinda zakuyi tsakaninku ne ni bana ciki."_
Dariya ta mata ita ma tace _"Zaki sauko ne daga inda